المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : عشرة حُجُب بين العبد وربه


هيئة الإشراف
_16 _January _2014هـ الموافق 16-01-2014م, 12:33 AM
عشرة حُجُب بين العبد وربه


قال رحمه الله في "مدارج السالكين": (المكاشفةُ الصحيحةُ علومٌ يُحْدِثُها الرَّبُّ سبحانه وتعالى في قلبِ العبدِ، ويطْلِعُهُ بها على أمورٍ تخفى على غيرِه، وقد يُواليها وقد يُمْسِكُها عنه بالغفلةِ عنها، ويواريها عنه بالغين الذي يغشَى قلبَه وهو أرقُّ الحجبِ أو بالغيمِ وهو أغلظُ منه أو بالرَّانِ وهو أشدّها فالأوَّل يقع للأنبياء عليهم السلام كما قال النبي صلى الله عليه وسلم: (( إنَّه لَيُغان على قلبي وإني لأستغفر الله أكثر من سبعين مرة))
والثاني يكون للمؤمنين، والثالث لمن غلبت عليه الشقوة؛ قال الله تعالى: {كلا بل ران على قلوبهم ما كانوا يكسبون}
قال ابن عباس وغيره: (هو الذنب بعد الذنب يغطي القلب حتى يصير كالران عليه).
والحُجُبُ عَشَرَة:
- حِجَابُ التعطيل ونفيِ حقائقِ الأسماء والصفات وهو أغلظُها؛ فلا يتهيَّأ لصاحبِ هذا الحجابِ أن يعرفَ اللهَ ولا يصل إليه ألبتة إلا كما يتهيَّأ للحجر أن يصعدَ إلى فوق.
الثاني: حجاب الشرك ، وهو أن يتعبَّد قلبه لغير الله.
الثالث: حجاب البدعة القولية ؛ كحجاب أهل الأهواء والمقالات الفاسدة على اختلافها.
الرابع : حجاب البدعة العملية ؛ كحجاب أهل السلوك المبتدعين في طريقهم وسلوكهم.
الخامس : حجاب أهل الكبائر الباطنة؛ كحجاب أهل الكبر والعجب والرياء والحسد والفخر والخيلاء ونحوها.
السادس: حجاب أهل الكبائر الظاهرة، وحجابهم أرقّ من حجاب إخوانهم من أهل الكبائر الباطنة مع كثرة عباداتهم وزهاداتهم واجتهاداتهم؛ فكبائر هؤلاء أقرب إلى التوبة من كبائر أولئك؛ فإنَّها قد صارت مقامات لهم لا يتحاشون من إظهارها وإخراجها في قوالب عبادة ومعرفة؛ فأهلُ الكبائر الظاهرة أدنى إلى السلامة منهم، وقلوبهم خير من قلوبهم.
السابع: حجاب أهل الصغائر.
الثامن: حجاب أهل الفضلات والتوسع في المباحات.
التاسع: حجاب أهل الغفلة عن استحضارِ ما خُلقوا له وأريد منهم وما لله عليهم من دوام ذكره وشكره وعبوديته.
العاشر: حجاب المجتهدين السالكين المشمرين في السير عن المقصود.
فهذه عشر حجب بين القلب وبين الله سبحانه وتعالى تحول بينه وبين هذا الشأن، وهذه الحجب تنشأ من أربعة عناصر:
- عنصر النفس.
- وعنصر الشيطان.
- وعنصر الدنيا.
- وعنصر الهوى.
فلا يمكن كشف هذه الحجب مع بقاء أصولها وعناصرها في القلب ألبتة، وهذه الأربعة العناصر تفسد القول والعمل والقصد والطريق بحسب غلبتها وقلَّتها؛ فتقطع طريق القول والعمل والقصد أن يصل إلى القلب، وما وصل منه إلى القلب قطعت عليه الطريق أن يصل إلى الربّ؛ فبين القول والعمل وبين القلب مسافة يسافر فيها العبد إلى قلبه ليرى عجائب ما هنالك، وفي هذه المسافة قطَّاع الطريق المذكورون؛ فإن حاربهم وخلصَ العملُ إلى قلبه دار فيه وطلب النفوذ من هناك إلى الله؛ فإنه لا يستقرُّ دون الوصول إليه، {وأن إلى ربك المنتهى} فإذا وصل إلى الله سبحانه أثابه عليه مزيدا في إيمانه ويقينه ومعرفته وعقله، وجمَّل به ظاهرَه وباطنَه؛ فهداه به لأحسن الأخلاق والأعمال، وصرف عنه به سيء الأخلاق والأعمال، وأقام الله سبحانه من ذلك العمل للقلب جنداً يحارب به قطّاع الطريق للوصول إليه :
- فيحارب الدنيا بالزهد فيها وإخراجها من قلبه، ولا يضرُّه أن تكونَ في يده وبيته، ولا يمنعُ ذلك من قوَّة يقينه بالآخرة.
- ويحارب الشيطانَ بترك الاستجابةِ لداعي الهوى؛ فإنَّ الشيطانَ مع الهوى لا يفارقه.
- ويحارب الهوى بتحكيم الأمر المطلق، والوقوف معه بحيث لا يبقى له هوى فيما يفعله ويتركه.
- ويحارب النفس بقوَّةِ الإخلاص.
هذا كله إذا وجد العملُ منفذا من القلبِ إلى الربِّ سبحانه وتعالى، وإن دار فيه ولم يجد منفذا وَثَبَتْ عليه النفسُ فأخذته وصيرته جندا لها؛ فصالت به وعلَت وطغَت؛ فتراه أزهدَ ما يكون وأعبدَ ما يكون وأشدَّه اجتهاداً، وهو أبعد ما يكون عن الله!!
وأصحاب الكبائر أقربُ قلوباً إلى الله منه، وأدنى منه إلى الإخلاص والخلاص!!
- فانظر إلى السَّجَّاد العَبَّاد الزَّاهد الذي بين عينيه أثر السجودِ؛ كيف أورثه طغيانُ عملِه أن أنكرَ على النبيُّ صلى الله عليه وسلم؟!
وأورث أصحابَه احتقارَ المسلمين حتى سلُّوا عليهم سيوفَهم واستباحُوا دماءَهم.
- وانظر إلى الشرِّيب السكِّير الذي كان كثيراً ما يؤتى به إلى النبي صلى الله عليه وسلم فيحدُّه على الشراب؛ كيف قامت به قوَّة إيمانه ويقينه ومحبته لله ورسوله وتواضعه وانكساره لله حتى نهى رسول الله عن لعنته؟!!
فظهر بهذا أن طغيانَ المعاصي أسلم عاقبةً من طغيان الطاعات.
وقد روى الإمامُ أحمدُ في كتابِ الزهدِ أنَّ الله سبحانه أوحى إلى موسى: [يا موسى أنذر الصدِّيقين فإني لا أضعُ عدلي على أحد إلا عذَّبتُه من غير أن أظلمَه، وبشِّر الخطَّائين فإنَّه لا يتعاظَمُنِي ذنبٌ أن أغفره] ).

طاهر جبريل دكو
_18 _January _2015هـ الموافق 18-01-2015م, 12:24 PM
عشرة حُجُب بين العبد وربه

ABUBUWA GOMA DA SU KE SHAMAKANCE TSAKANIN BAWA DA UBANGIJINSA.

A cikin madarijussalikin Ibnul Kayyim – Allah Ya yi masa rahama - ya ce:

Mukashafa ingantacciya ita ce wasu ilmummuka da Ubangiji mai tsarki da daukaka Ya ke samar wa a cikin zuciyar bawa sai Ya tsinkayar da shi ga wasu al'amura da su ka buya ga waninsa, Ya kan tabbatar masa da shi na lokaci mai tsawo ko kuma Ya kame shi daga barnin sa idan ya gafala ya bar kulawa da shi Ya lullube shi da murfi da ake kira (Alghainu) wanda shi ne mafi sauki daga cikin murafen da ke rufe zuciya, ko kuma da rufin da ake cewa (alghaimu) shi ya dara wancan a kauri, ko kuma da rufin da ake cewa (Raanu) wanda shi ne mafi tsanani cikin su.

Na farkon ya kan faru hatta ga annabawa (amincin Allah ya tabbata a gare su) Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce:"

(( إنَّه لَيُغان على قلبي وإني لأستغفر الله أكثر من سبعين مرة))

Ma'ana: " Lallai akan sanya wani rufi a zuciyata kuma lallai ni na kan yi istigfari sama da sau saba'in"

Na biyu kuma ya kan faru da muminai, na ukun kuma ya kan faru da wanda rashin rabo ya yi galaba akan sa Allah (Madaukakin sarki) Ya ce:

{كلا بل ران على قلوبهم ما كانوا يكسبون}

Ma'ana: " A'aha! Ba haka ba, abin da su ka kasance suna aikatawa ya yi tsatsa a kan zukatansu" Suratul Mudaffifin aya ta 14.

Abdullahi dan Abbas da waninsa su ka ce: shi ne zunubi bayan zunubi wanda ya ke rufe zuciya har ya kasance tamkar tsatsa a kansa.

Rufin da ke samun zuciya guda goma ne:

Na daya rufin da ke samun zuciya sakamakon karyata hakikanin sunayen Allah da sifofinSa, kuma shi ne mafi kaurin rufi ga zuciya, saboda haka ma'abucin irin wannan rufin ba zai taba samun ikon sanin Allah ba, kuma ba zai samu isa gare Shi ba kwatakwata kamar yadda bai yiwuwa dutse ya haura sama da kan sa.

Na biyu: Rufin da ke samun zuciya a sakamakon shirka, watau zuciyarsa ta yi bauta ga wanin Allah.

Na uku: Rufin da ke samun zuciya sakamako aikata bidi'a ta furuci, kamar bidi'ar masu bin son zuciya da maganganu na banza mabambanta (watau wadanda ake jingina su ga addini alhali ba su da dalili daga Allah ko ManzonSa).

Na hudu: Rufin da ke samun zuciya sakamakon aikata bidi'a ta aikin gabbai, kamar bidi'ar ma su kirkirar wasu dabi'u (da sunan addini) a cikin darikokinsu da.

Na biyar: Rufin da ke samun zukatan ma su aikata kaba'ira boyayyu, watau manya- mayan zunubbai da su ke da lalaka da halayya, kamar rufin da ke samun zukatan ma su girman kai da kasaita da riya da hassada da alfahari da takama da makamantansu.

Na shida: Rufin da ke samun zukatan ma su aikata kaba'ira na zahiri, rufin wadannan ya fi sauki sama da rufin 'yan uwansu ma su aikata kaba'ira boyayyu, tare da yawan ibadarsu da gudun duniyarsu da kokarinsu, saboda zunubban wadannan ya fi kusa ga tuba sama da na wadancan, domin ya riga ya zame musu jiki har ba su jin kunyar bayyana shi a matsayin bauta da ilimi, saboda haka ma'abuta zunubbai na zahiri sun fi su kusa da aminci, kuma zukatansu sun fi na su alheri.

Na bakwai: Rufin da ke samun zukatan ma su aikata kananan zunubbai.

Na takwasa: Rufin da ke samun zukatan ma su zurfafawa a cikin halal sama da bukata.

Na tara: Rufin da ke samun zukatan ma su rafkana daga tuna abin da aka halicce su domin sa kuma abin da aka nema daga gare su da abin da Allah ke da shi akansu na hakkin dawwama a kan ambatonSa da bauta gare Shi.

Na goma: Rufin da ke samun zukatan ma su kokari wadanda su ka kama hanya suka nade kafar wando don tafiya su ka nesanta daga manufa.

Wadannan su ne hijabai goma da su ke shamakancewa tsakanin zuciyar bawa da Allah mai tsarki da daukaka, su kange tsakaninsa da wannan sha'anin, kuma wadannan hijaban suna samuwa ne daga asali guda hudu: Rai, da shedan, da Duniya da son zuciya.

Ba zai taba yiwuwa a samu yayewar wadannan hijaban ba matukar asalinsu ya na nan a cikin zuciya, kuma wadannan asullan guda hudu suna bata magana da aiki da manufa da hanya gwargwadon yadda suka yi galaba akan zuciya ko kankantarta; sai su katse hanyar magana da aiki da manufa su hana su isa ga zuciya, wanda ya samu isa ga zuciyar ma sai su hana shi isa zuwa ga Allah, saboda haka a tsakanin magana da aiki da zuciya akwai tazara mai nisan gaske wanda bawa zai shafe shi zuwa zuciyarsa domin ya ga abubuwan ban mamaki a wurin.

A wannan tazarar akwai 'yan fashi ambatattu, idan ya yake su kuma aikin ya isa ga zuciyarsa sai ya game shi, daga nan kuma sai ya nemi isa zuwa ga Allah domin ba zai taba samun matabbata ba har sai ya isa gare shi Allah Ya ce:

{وأن إلى ربك المنتهى}

Ma'ana: " Kuma lallai wurin tukewa zuwa ga Ubangijinka ya ke"

Idan ya samu isa zuwa ga Allah sai Ya saka masa da Karin imaninsa da yakininsa da saninsa da hankalinsa. Kuma ya kyautata shi da shi cikinsa da wajensa sannan Ya shiryar da shi zuwa ga mafi kyawu dabi'u da ayyuka, Ya raba shi da munanan dabi'u da ayyuka, kuma Allah Ya tanadar wa wannan zuciyar runduna da za ta rika kare ta daga 'yan fashin kan hanya, ma su hana cimma buri.

Sai ya yaki Duniya ta hanyar gudun ta da fidda ita daga zuciyarsa, ba bu laifi don ta kasance a hannunsa da gidansa, wannan ba zai hana karfin yakininsa ba game da lahira.

Sai ya yaki shedan ta hanyar barin bin son zuciya, domin lallai shedan ya na tare da son zuciya ba ya rabuwa da shi.

Sai ya yaki son zuciya ta hanyar hukunta umarnin Allah, duk inda ya ke suna tare ta yadda ba abin da zai saura tare da shi na son zuciya cikin abin da ya ke aikatawa ko abin da ya ke bari.

Sai ya yaki ransa da karfin ikhlasi.

Wannan dukka sai idan aiki ya samu dammar wucewa daga zuciyar bawa zuwa ga Allah mai tsarki da daukaka, amma idan ya gewaya a cikinsa bai samu wucewa ba sai rai ya rike shi ya mayar da shi sojansa, saboda haka sai ya yi shisshigi ya wuce iyaka ya yi girman kai, sai ka gan shi da yawan tsantseni da yawan ibada ga tsananin kokari, amma a lokacin ya fi nisa da Allah. Ma su aikata kaba'ira ma sun fi su kusancin zuciya ga Allah, kuma sun fi su kusanci ga ikhlasi da kubuta.

Ka dubi wannan mai yawan sujjada mai yawan bauta mai yawan gudun duniya wanda tsakanin idanunsa ma ana ganin alamar sujjada, yadda iliminsa mai sa shisshigi da wuce iyaka ya kai shi ga yin inkari ga Annabi (sallallahu alaihi wasallam)? Kuma ya kai 'yan uwansa ga raina musulmi har su ka zare takubba akansu su ka kuma halitta jinanensu.

Sannan ka yi dubi zuwa ga mashayin giyan nan mai yawan maye wanda ake yawan kawo shi wurin Annabi (sallallahu alaihi wasallam) ya yi masa haddin shan giya, yadda karfin imaninsa da yakininsa da kaunarsa ga Allah da ManzonSa da kankan da kansa da sakankancewarsa ga Allah – ya sa har sai da Manzon Allah ya hana la'antarsa.

Da wannan sai ya bayyana – mana - cewa shsshigi da wuce iyaka na sabo ya fi sauki daga shsshigi da wuce iyaka na da'a.

Imamu Ahmad ya ruwaito a cikin kitabu zzuhd cewa Allah (mai tsarki da daukaka) Ya yi wahayi zuwa ga Annabi Musa (sallallahu alaihi wa sallam) cewa:

[يا موسى أنذر الصدِّيقين فإني لا أضعُ عدلي على أحد إلا عذَّبتُه من غير أن أظلمَه، وبشِّر الخطَّائين فإنَّه لا يتعاظَمُنِي ذنبٌ أن أغفره]

Ma'ana: "Ya Musa! Ka yi gargadi ga siddikai, domin lallai Ni ba Na sanya adalciNa akan wani face na azabtar da shi ba tare da Na zalunce shi ba, kuma ka yi albishir ga ma su kuskure, domin lallai girman zunubi ba ya hana Ni gafarta shi.