تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : عشرة أسباب تعين على الصبر على البلاء


هيئة الإشراف
_16 _January _2014هـ الموافق 16-01-2014م, 12:29 AM
عشرة أسباب تعين على الصبر على البلاء


قال رحمه الله في "طريق الهجرتين": (والصبر على البلاء ينشأ من أسباب عديدة:
أحدها: شهودُ جزائِها وثوابها.
الثاني: شهودُ تكفيرها للسيئات ومَحْوِهَا لها.
الثالث: شهودُ القَدَرِ السابق الجاري بها وأنها مقدَّرةٌ في أمِّ الكتاب قبل أن يُخْلَقَ؛ فلا بدَّ منها؛ فجزَعُه لا يزيده إلا بلاء.
الرابع: شهودُه حقَّ الله عليه في تلك البلوى، وواجبَه فيها الصبر بلا خلاف بين الأمة، أو الصبر والرضا على أحد القولين؛ فهو مأمور بأداء حقِّ الله وعبوديته عليه في تلك البلوى؛ فلا بد له منه وإلا تضاعفت عليه.
الخامس: شهود ترتّبها عليه بذنبه؛ كما قالَ الله تعالى: {وما أصابكم من مصيبة فبما كسبت أيديكم} فهذا عامٌّ في كل مصيبة دقيقةٍ وجليلة؛ فيشْغَلُه شهودَ هذا السببِ بالاستغفارِ الذي هو أعظمُ الأسباب في دفع تلك المصيبة؛ قال عليُّ بن أبي طالب: (ما نزل بلاء إلا بذنب، ولا رُفع بلاء إلا بتوبة).
السادس: أن يعلمَ أن الله قد ارتضاها له واختارها وقسَمَها، وأنَّ العبودية تقتضي رضاه بما رَضِيَ له به سيده ومولاه؛ فإن لم يوفِ قدْرَ المقَامِ حقَّه فهو لضَعْفِهِ؛ فلينزلْ إلى مقامِ الصبر عليها؛ فإن نزلَ عنه نزلَ إلى مقامِ الظلم وتعدِّي الحقّ.
السابع: أن يعلمَ أن هذه المصيبة هي داءِ نافع ساقَه إليه الطبيبُ العليم بمصلحته الرحيم به؛ فليصبرْ على تجرُّعِه ولا يتقيَّأه بتسخُّطِه وشكْوَاه فيذهبُ نفْعُه باطلا.
الثامن: أن يعلم أن في عُقْبَى هذا الدواء من الشفاء والعافية والصحة وزوال الألم ما لم تحصل بدونه؛ فإذا طالعتْ نفسُه كراهةَ هذا الدواءِ ومرارَتَه؛ فلينظرْ إلى عاقبته وحُسْنِ تأثيره، قال تعالى: {وعسى أن تكرهوا شيئا وهو خير لكم وعسى أن تحبوا شيئا وهو شر لكم والله يعلم وأنتم لا تعلمون} وقال الله تعالى: {فعسى أن تكرهوا شيئا ويجعل الله فيه خيرا كثيرا}، وفي مثل هذا القائل:
لعل عتبك محمود عواقبه ... وربما صحت الأجسام بالعلل

التاسع: أن يعلمَ أن المصيبةَ ما جاءَتْ لتهلِكَه وتقتُلَه، وإنما جاءت لِتَمْتَحِنَ صبْرَه وتبْتَلِيَه؛ فيتبيّن حينئذ هل يصلح لاستخدامه؟ وجعْلِه من أوليائه وحزبه أم لا؟
فإن ثبت اصطفاه واجتباه، وخلع عليه خِلَعَ الإكرام وألبسه ملابسَ الفضل، وجعل أولياءه وحزبه خدماً له وعوناً له، وإن انقلب على وجهه ونكص على عقبيه طُرِدَ وصُفع قفاه وأُقِصي، وتضاعفت عليه المصيبة وهو لا يشعر في الحال بتضاعفها وزيادتها، ولكن سيعلمُ بعد ذلك بأنَّ المصيبةَ في حقِّه صارت مصائب، كما يعلمُ الصابرُ أنَّ المصيبةَ في حقِّهِ صارَتْ نِعَماً عديدة، وما بين هاتين المنزلتين المتباينتين إلا صبرُ ساعة، وتشجيعُ القلب في تلك الساعة، والمصيبة لا بدَّ أن تقلع عن هذا وهذا، ولكن تقلع عن هذا بأنواع الكرامات والخيرات، وعن الآخرِ بالحرمان والخذلان؛ لأن ذلك تقدير العزيز العليم، وفضل الله يؤتيه من يشاء، والله ذو الفضل العظيم.
العاشر: أن يعلم أن الله يربّي عبدَه على السراء والضراء والنعمة والبلاء؛ فيستخرج منه عبوديَّته في جميع الأحوال؛ فإن العبدَ على الحقيقة من قام بعبودية الله على اختلاف الأحوال، وأما عبدُ السرَّاء والعافيةِ الذي يعبد الله على حرفٍ؛ فإن أصابه خير اطمأنَّ به، وإن أصابته فتنة انقلب على وجهه؛ فليس من عبيده الذين اختارهم لعبوديته؛ فلا ريب أنَّ الإيمان الذي يثبتُ على محلِّ الابتلاء والعافية هو الإيمان النافع وقت الحاجة، وأما إيمان العافية فلا يكاد يصحب العبد ويبلغه منازل المؤمنين، وإنما يصحبه إيمان يثبت على البلاء والعافية؛ فالابتلاء كِير العبد ومَحَكُّ إيمانه؛ فإما أن يخرج تِبْرا أحمر، وإما أن يخرج زغلاً محضاً، وإما أن يخرج فيه مادّتان ذهبية ونحاسية فلا يزال به البلاء حتى يخرج المادة النحاسية من ذهبه، ويبقى ذهبا خالصا؛ فلو علم العبد أن نعمة الله عليه في البلاء ليست بدون نعمة الله عليه في العافية لشغل قلبه بشكره ولسانه: "اللهم أعني على ذكرك وشكر وحسن عبادتك"، وكيف لا يشكر من قيَّض له ما يستخرج خبَثَه ونُحَاسَه، وصيَّرَه تِبْرا خالصاً يصلح لمجاورته والنظر إليه في داره؟!!

فهذه الأسباب ونحوها تثمرُ الصبرَ على البلاء؛ فإن قويت أثمرت الرضا والشكر؛ فنسأل الله أن يسترنا بعافيته، ولا يفضحنا بابتلائه، بمنّه وكرمه).

طاهر جبريل دكو
_15 _November _2014هـ الموافق 15-11-2014م, 08:17 AM
ABUBUWAN DA KE TAIMAKAWA YIN HAKURI A KAN JARRABAWA

Hakuri a a kan jarrabawa ya na faruwa ne daga sabubba mabambanta:
Na dayan su shi ne; sanin sakamakonsa da ladansa.
Na biyu; sanin kankarewar sa ga laifuffuka da shafewarsa gare su.
Na uku; sanin cewa kaddara ta riga ta gabata game da shi, kuma lallai shi kaddararre ne a cikin Lauhul mahfuz tun kafin a halicce shi, saboda haka babu ma kawa sai ya faru, don haka mitarsa da raki ba za ta kara masa komai ba face bala'i.
Na hudu: Sanin hakkin Allah a kan sa cikin wannan jarrabawar, da sanin cewa wajibinsa shi ne yin hakuri, ba tare da sabani ba a tsakanin al'umma (watau a kan wajibcin yin hakuri da jarrabawa).
Da hakuri da yarda bisa daya daga cikin maganganu biyu (na malamai watau shi hakuri babu sabani kan cewa wajibi ne, amma yarda da jarrabawar wannan kuma wani mataki ne da ke gaba da yin hakuri amma shi an samu sabanin malamai game da wajibcin sa har zuwa maganganu biyu) saboda haka shi wanda aka umurta ne da bada hakkin Allah da hakkin bauta da ke kansa a cikin wannan jarrabawar, babu makawa gare shi in ba haka ba kuma sai musibar ta ninninku masa.
Na biyar: sanin cewa (an jarrabe shi ne) sakamakon zunubbansa, kamar yadda Allah- madaukaki – Ya ce:
وَمَا أَصَابَكُمْ مِنْ مُصِيبَةٍ فَبِمَا كَسَبَتْ أَيْدِيكُمْ وَيَعْفُو عَنْ كَثِيرٍ سورة الشورى (30)
Ma'ana: Kuma duk abin da ya same ku na musiba, to daga abin da hannayenku suka aikata ne. (SuratuAsshura 30).
Kuma wannan ya game dukkan zunubbai babbansu da kananansu. Saboda haka sai sanin wannan sababin ya sa ya shagaltu da istigifari wanda shi ne mafi girman sababi na tunkude musiba, Aliyu dan Abi Dalibi (Allah Ya kara masa yarda) ya ce; azaba ba ta taba sauka ba face sakamakon zunubi, kuma ba a dauke wani bala'i face sakamakon tuba.
Na shida: Ya san cewa Allah Ya riga Ya yarda da ita gare shi, kuma Ya zabe shi, kuma Ya kasafta, kuma (ya san cewa) lallai bauta ta na hukunta yardarsa da abin da shugabansa kuma majibincin al'amarinsa Ya yarda da shi gare shi, idan bai iya cika wannan matakin ba to sakamakon rauninsa ne, saboda haka sai ya sauka zuwa ga matakin hakuri da ita (wato kaddarar) idan ya sauka daga gare shi (watau matakin hakuri) to ya sauka zuwa ga matakin zalunci kenan da ketare gaskiya (watau ya yarda da kaddara, in ya gaza wannan matakin to ya yi hakuri da kaddarar, idan ya gaza matakin hakuri kuwa to sai matakin zalunci da ketare gaskiya).
Na bakwai: Ya san cewa lallai wannan musibar magani ne mai amfani, kuma likita ne ma sani game da maslahar sa mai tausayinsa Ya aiko ta zuwa gare shi, saboda haka sai ya yi hakuri a kan kwankwadarsa, kuma ka da ya amayo shi ta hanyar fushi da yawan mitarsa, sai amfaninsa (watau maganin) ya gushe a banza.

Na takwas: Ya san cewa lallai abin da ke tare da wannan maganin na waraka da lafiya da gushewar radadi ba ya samuwa sai da shi, to idan ransa tatsinkayi (abin) ki da ke cikin wannan maganin da dacinsa, sai kuma ya yi dubi zuwa ga karshensa da kyan tasirinsa. Allah – Madaukaki – Ya ce:
فَعَسَى أَنْ تَكْرَهُوا شَيْئًا وَيَجْعَلَ اللَّهُ فِيهِ خَيْرًا كَثِيرًا سورة النساء (19)
Ma'ana: Akwai yiwuwan ku kyamaci wani abu alhali Allah Ya sanya wani alheri mai yawa a cikinsa. (Suratu Annisa'i 19)
Game da irin wannan ne mai fadi yake fadi:

لعلّ عتبك محمود عواقبه ... وربما صحت الأجسام بالعلل.
Ma'ana: Watakila aibunka ya zama mai godadden karshe = yana yuwuwa kuma jiki ya kyautatu da cututtuka.
Na tara: Kuma ya san cewa musiba ba ta zo ne domin ta halaka shi ta kashe shi ba, a a kawai ta zo ne domin ta jarrabe shi kuma ta gwada hakurinsa. Da haka sai ya bayyana cewa shin ya dace ya zama cikin waliyyan Allah kuma rundunarSa wadanda za a yi amfani da su (wurin daga addini)?

To idan ya jure (ya yi hakuri) sai Ya zabe shi Ya daukaka matsayinsa daga matakin karimci zuwa mataki na fifiko kuma Ya sanya waliyyansa da rundunarSa su zama ma su hidima gare shi kuma ma su taimakonsa, idan kuma ya nuna gazawarsa ga yin hakurin da juriya, sai Ya kore shi ya nisantar da shi kuma musibar ta nunnunku a kansa alhalin shi ba ya gane karuwar (musibar) da nunnunkuwar ta, amma daga baya zai fahimci cewa musiba daya ta zama musibu da yawa a gare shi, kamar yadda mai hakuri zai gane cewa musiba ta zame ni'imomi ma su yawa a gare shi. Babu abin da ke tsakanin wadannan matakan guda biyu wadanda suke nesa da juna face hakurin dan kankanin lokaci, da karfafan zuciya a wannan lokaci, saboda haka musiba babu makawa za ta fizga daga wannan haka ma daga wannan, amma takan fizgo nau'uka ne na karamomi da alherai ga wannan (wato mai hakuri) ga dayan kuma (watau mara hakuri) ta haramta masa alheri ta kai shi ga tabewa (wato rashi nasara) saboda wannan kaddara ce ta Mabuwayi Ma sani, falalar Allah kuma Yana bada ita ne ga wanda Ya so, kuma Allah Ma'abucin falala ne mai girma.
Na goma: Ya sani cewa lallai Allah Ya na renon bawanSa ne a kan abubuwa ma su faranta rai da ma su bakantawa, da ni'ima da jarrabawa, saboda haka sai Ya bayyana gaskiyar zamansa bawa (gare shi) cikin wadannan halayen dukka. Saboda bawan Allah na gaskiya shi ne wanda ya tsayu a kan bautar Allah cikin yanayi mabambanta, amma bawan (da bautarsa) ta takaita a (lokacin) farin ciki (kawai) wanda ya ke bautar Allah a bangare daya kawai, idan alheri ya same shi sai ya (samu) nutsuwa game da shi (wato ya yi farin ciki da shi), idan kuma fitina ta sauka a kansa sai ya juya baya a kan fuskarsa, to wannan baya daga cikin zababbun bayansa (watau zababbun bayin Allah), babu shakka lallai imanin da ke tabbata a lokacin jarrabawa da lafiya shi ne imani mai amfani lokacin bukata, amma imanin lafiya (wato na wanda bai shiga wata jarrabawa ba) bai cika kasancewa tare da bawa ba har ya isar da shi zuwa ga matakai na muminai, irin imanin da ke kasancewa tare da shi kawai shi ne imanin da ke iya tabbata a halin jarrabawa da halin lafiya.
Saboda haka, ita jarrabawa ita ce (kamar) zuga zugin bawa a mahallin imaninsa, ko dai ya fidda (xanyen) zinari jazur, ko kuma ya fitar da shi gaba daya tashi daya ya na danye sharaf, ko kuma abubuwa biyu su fito daga cikinsa; zinari da karfe, ba zai gushe ba cikin jarrabawa har sai ya ware karfe daga zinarinsa, sai ya saura zinari tsantsa.
Da bawa ya san cewa ni'imar Allah ga gare shi a halin lafiya ba ta taba rabuwa da jarrabawarSa ga bawa, zai zaburar da zuciyarsa (a kan yin hakuri) da harshensa a kan godiya (ya na mai cewa) Ya Allah! Ka taimake ni a kan ambatonKa da gode maKa da kyautata bauta gare Ka, ya ya ba zai gode wa wanda ya huwace masa abin da zai fitar masa da daudarsa da karfen cikinsa ya mai da shi zallan zinari, yadda zai dace da makwabtaka da Shi da kuma dubi zuwa gare Shi a cikin gidanSa (wato AljannanSa)? (a takaice ma'anar wannan na goman shi ne, abin da Allah ya jarrabi bawa da shi na musiba alheri ne ga bawa saboda tamkar zugazugi ya keg a zinarin da ke cakude da bakin karfe, wutan da zugazugi ke ba shi duk da cewa zafi ne amma ya na tace mummuna ne daga gare shi ya bar tataccen zinari ba tare da wani dauda ba a cikin sa. To haka nan jarrabawa ta keg a bawa, ta na tace munanan dabi'u kuma ta na kade zunubbai da dai shauransu Allah Shi ne ma fi sani)
To wadannan sabubban da makamantansu suna haifar da hakuri a kan bala'i, idan suka karfafa kuma sai su haifar da yarda da godiya. Muna roqon Allah – da baiwarSa da karimcinSa - Ya suturta mu da afuwarSa, ka da Ya tona asirinmu da jarrabawarSa.