المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : عشرة أسباب تجلب محبة الله تعالى


هيئة الإشراف
_16 _January _2014هـ الموافق 16-01-2014م, 12:26 AM
عشرة أسباب تجلب محبة الله تعالى


قال رحمه الله في مدارج السالكين: (فصل في الأسباب الجالبة للمحبَّة والموجِبة لها وهي عشرة:
أحدُها: قراءةُ القرآن بالتدبر والتفهّم لمعانيه وما أُريدَ به، كتدبّر الكتابِ الذي يحفظه العبدُ ويشرحه؛ ليتفهَّم مُرادَ صاحبه منه.
الثاني: التقرب إلى الله بالنوافل بعد الفرائض فإنها توصله إلى درجة المحبوبيَّة بعد المحبة.
الثالث: دوام ذكره على كل حال باللسان والقلب والعمل والحال فنصيبه من المحبة على قدر نصيبه من هذا الذكر.
الرابع: إيثارُ محابّه على محابّك عند غلَبَات الهوى، والتسَنُّمُ إلى محابّه وإن صَعُبَ المرتقى.
الخامس: مطالعة القلب لأسمائه وصفاته، ومشاهدتها ومعرفتها، وتقلّبه في رياض هذه المعرفة ومباديها؛ فمن عرف الله بأسمائه وصفاته وأفعاله أحبَّه لا محالة، ولهذا كانت المعطّلة والفرعونية والجهمية قطاّع الطريق على القلوب بينها وبين الوصول إلى المحبوب.
السادس: مشاهدة برِّه وإحسانه وآلائه ونعمه الباطنة والظاهرة فإنها داعية إلى محبته.
السابع: وهو من أعجبها، انكسار القلب بكليته بين يدي الله تعالى، وليس في التعبير عن هذا المعنى غير الأسماء والعبارات.
الثامن: الخلوة به وقت النزول الإلهي لمناجاته وتلاوة كلامه، والوقوف بالقلب والتأدُّب بأدب العبودية بين يديه، ثم ختم ذلك بالاستغفار والتوبة.
التاسع: مجالسةُ المحبين الصادقين، والتقاطُ أطايب ثمرات كلامهم كما ينتقى أطايب الثمر، ولا تتكلَّم إلا إذا ترجَّحتْ مصلحةُ الكلام، وعلمتَ أنَّ فيه مزيدا لحالك ومنفعةً لغيرك.
العاشر: مباعدةُ كلِّ سببٍ يحولُ بينَ القلب وبينَ اللهِ عزَّ وجلَّ.

فمِنْ هذه الأسباب العشرة وصلَ المحبُّونَ إلى منازل المحبَّة ودخلوا على الحبيبِ، وَمَلاكُ ذلك كلِّه أمران:
- استعدادُ الرُّوحِ لهذا الشأن.
- وانفتاحُ عينِ البصيرةِ.
وبالله التوفيق).ا.هـ.

طاهر جبريل دكو
_21 _November _2014هـ الموافق 21-11-2014م, 07:44 AM
SABUBBA GOMA DA SU KE SA ALLAH YA KAUNACI BAWA
(Ibnul Kayyim) - Allah Ya yi masa rahama - a cikin madarijussalikina ya ce: Fasali game da sabubba masu jawo kaunar (Allah) kuma masu wajabta ta, su goma ne.
Na Dayan su: Karatun Alkur'ani tare da daukar izina da fahimtar ma'anoninsa damanufofinsa, kamar lura da tintintini cikin wani littafin da bawa ke haddacewa kuma ya ke masa fashin baki domin kokarin fahimtar manufofin mawallafin sa game da shi.
Na Biyu: Neman kusanci zuwa ga Allah ta hanyar aikata nafilfilu bayan farillai, domin yin (nafilfilu) zai kai shi ga matsayin dan gataci bayan ya kasance abin so.
Na Uku: Dawwama a kan ambatonSa cikin ko wane hali, da harce da zuciya da aiki da hali, saboda kason sa cikin kaunar da zai samu na Allah ya rataya ne ga kasonsa a cikin wannan zikirin (watau ambaton Allah)
Na Hudu: Fifita abin da Allah Ya ke so bisa ga abin da kai ka ke so a yayin da son zuciya ke yin rinjayi. Da daukakuwa zuwa ga abin da Ya ke so ko da kuwa hawa kai ya tsananta.
Na Biyar: Tsinkayar zuciya ga sunayenSa da sifofinSa da sanin su tare da halarto ma'anoninsu, da jujjuyawarsa a cikin dausayin wannan ilimin da abubuwan da suka ginu akai. Domin duk wanda ya san Allah da sunyenSa da sifofinSa da ayyukanSa, to babu makawa sai ya kaunace Shi, saboda haka ne ma ya sa masu karyatawa da bata sunayen Allah da sifofinSa da masu akidar fir'aunanci da masu bin akidar jahamiyyanci su ka zama masu katse hanyar da ta ke sadar da zuciya zuwa ga abin kauna.
Na Shida: Halartowa da tunawa da kyautatawarSa da ni'imominSa na fili da na boye, domin lallai hakan ya na zama sababi na kaunarSa.
Na Bakwai; kuma ya na daga cikin mafi burgewar cikin sa: Shi ne karayar zuciya kacokam dinta a gaban Allah.
Na Takwas: Kebancewa da zuciyar domin ganawa da Shi da tilawar maganarSa da ladabtuwa da ladabi na bauta a gabanSa yayin da Ya ke sauka saman Duniya, sa'annan da kammala hakan da neman gafara da tuba zuwa ga Allah.
Na Tara: Zama tare da masu kaunar Allah kauna ta gaskiya, da tsittsintar dadada daga maganganunsu kamar yadda ake tsittsintar 'ya'yan itaciya. Kuma ka da ka yi magana har sai in maslahar yin maganar ta rinjaya kuma a cikin ta akwai abin da zai kare ka kuma ya amfani waninka.
Na Goma: Nisantar dukkan sababin da ke zama shamaki tsakanin zuciya da Allah Mai girma da buwaya.

Da wadanna sabubban goma ne masoya Allah suka kai ga matakai na kaunar Allah, kuma su ka samu shiga a wurin abin kaunarsu, jigon wadannan abubuwa dukka kuwa abubuwa ne guda biyu;
Tattala zuciya domin wannan aikin, da bude idanuwa na basira.
Allah Shi ne mai datarwa.