المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس الرابع عشر: ترجمة تفسير سورة الطارق من كتاب: التفسير الميسر


طاهر جبريل دكو
_29 _December _2013هـ الموافق 29-12-2013م, 12:49 AM
وَالسَّمَاءِ وَالطَّارِقِ (1)
Ina rantsuwa da sama da kuma Darik.
وَمَا أَدْرَاكَ مَا الطَّارِقُ (2)
To mai ya sanar da kai abinda ake cewa Darik ?
النَّجْمُ الثَّاقِبُ (3)
Shine tauraronnan mai tsananin haske.
إِنْ كُلُّ نَفْسٍ لَمَّا عَلَيْهَا حَافِظٌ (4)
Babu wani rai face akansa akwai wani tsaro.


Sharhi: Allah (tsarkakakke) Yayi rantsuwa da sama da tauraron dake fitowa da daddare. Kuma me ya sanar da kai girman wannan tauraron? Shine tauraronnan mai haske mai kyalkyali. Babu wata rai face an wakilta mala'ika akanta wanda zai rika kiyaye ayyukanta, domin ayi mata hisabi akai ranan kiyama.
فَلْيَنْظُرِ الْإِنْسَانُ مِمَّ خُلِقَ (5)
To mutum yayi dubi mana, daga me aka halittashi?
خُلِقَ مِنْ مَاءٍ دَافِقٍ (6)
An halicceshine daga ruwa mai tunkudan juna.
يَخْرُجُ مِنْ بَيْنِ الصُّلْبِ وَالتَّرَائِبِ (7)
Yana fita daga tsakanin tsatso da karankarman kirji.
إِنَّهُ عَلَى رَجْعِهِ لَقَادِرٌ (8)
Lallai ne Shi (Allah), ga mayar dashi (mutum) tabbas mai iyawane.

Sharhi: to mutumin dake karyata tashin alkiyama ya duba mana, daga me aka halicceshine? Sabda ya san cewa lallaine maido da halittan mutum bai fi halittansa ba a karon farko, an halicceshine daga maniyyi wanda aka zuba shi a cikin mahaifa a cikin gaggawa, yana fitowa daga tsakanin tsatson na miji da kirjin mace, lallai wanda Ya halicci mutum daga wannan ruwan tabbas Yanada kudura akan dawo da shi zuwaga rayuwa bayan mutuwa.
يَوْمَ تُبْلَى السَّرَائِرُ (9)
Ranar da ake jarraba asirai.
فَمَا لَهُ مِنْ قُوَّةٍ وَلَا نَاصِرٍ (10)
Saboda haka bashida wani karfi, kuma bashida mai taimako (da zai iya kareshi daga azabar Allah).

Sharhi: ranan da za'a jarraba sirrori gameda abinda ta boye, kuma a rarrabe tsakanin mai kyau da mummunansa, saboda haka mutum bashida wani karfin da zai iya kare kansa, kuma bashida wani matemaki da zai iya tunkude azabar Allah daga barinsa.
وَالسَّمَاءِ ذَاتِ الرَّجْعِ (11)
Ina rantsuwa da sama ma'abuciyar ruwa mai komawa yana yankewa.
وَالْأَرْضِ ذَاتِ الصَّدْعِ (12)
Da kasa ma'abuciyar tsagewa.
إِنَّهُ لَقَوْلٌ فَصْلٌ (13)
Lallaine shi (Alkur'ani) hakika maganace dalla dalla.
وَمَا هُوَ بِالْهَزْلِ (14)
Kuma shi ba wasa bane.

Sharhi: (Allah Yace) Ina rantsuwa da sama ma'abuciyar ruwa mai maimaituwa, da kasa ma'abuciyar tsatstsagewa saboda abinda ke ratsata na tsirrai, lallai alkur'ani maganace mai rarrabewa tsakanin gaskiya da karya, kuma shi ba wasa bane. Baya halatta ga abin halitta yayi rantsuwa da wanin Allah inko yayi to hakika yayi shirka.
إِنَّهُمْ يَكِيدُونَ كَيْدًا (15)
Lallai ne su suna kulla kaidi kaidin gaske.
وَأَكِيدُ كَيْدًا (16)
Kuma Ni ina yin kaidi (garesu).
فَمَهِّلِ الْكَافِرِينَ أَمْهِلْهُمْ رُوَيْدًا (17)
Saboda haka kayiwa kafirai jinkiri, ka dakata musu sannu sannu.
Sharhi: lallai masu karyata manzon Allah (s. a.w) da Alkur'ani, suna kaidi kuma suna makirci saboda su tunkude gaskiya da kaidinnasu kuma su karfafa karya, kuma Nima Ina kaidi domin bayyana gaskiya koda kafirai sun ki. Saboda haka kada ka yi musu gaggawa-ya kai wannan manzon- gameda neman saukar ukuba akansu. A'a ka jinkirta musu ka saurara musu kadan kadan kuma kada ka gaggauta musu, da sannu zaka ga abinda zai faru dasu na azaba da horo da ukuba da halaka.