المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس الثالث عشر: ترجمة تفسير سورة البروج من كتاب: التفسير الميسر


طاهر جبريل دكو
_28 _December _2013هـ الموافق 28-12-2013م, 10:32 AM
وَالسَّمَاءِ ذَاتِ الْبُرُوجِ (1)
Ina rantsuwa da sama ma'abuciyar masaukayya na taurari.
وَالْيَوْمِ الْمَوْعُودِ (2)
Da yininda akayi alkawarin (zuwansa)
وَشَاهِدٍ وَمَشْهُودٍ (3)
Da mai sheda da wanda ake yin sheda akansa.
قُتِلَ أَصْحَابُ الْأُخْدُودِ (4)
An la'anci mutanen rami.
النَّارِ ذَاتِ الْوَقُودِ (5)
Wuta ce ma'abuciyar huruwa.
إِذْ هُمْ عَلَيْهَا قُعُودٌ (6)
Yayinda suke gefenta suna zazzaune.
وَهُمْ عَلَى مَا يَفْعَلُونَ بِالْمُؤْمِنِينَ شُهُودٌ (7)
Alhali su bisa ga abinda suke aikatawa ga muminai, halartattune
وَمَا نَقَمُوا مِنْهُمْ إِلَّا أَنْ يُؤْمِنُوا بِاللَّهِ الْعَزِيزِ الْحَمِيدِ (8)
Kuma basu tuhumcesu ba face don sunyi imani da Allah mabuwayi abin godiya.
الَّذِي لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَاللَّهُ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌ (9)
Wanda Shi keda mulkin sammai da kasa, kuma Allah akan dukkan komai halartacce ne.

Sharhi: Allah (madaukai) Yayi rantsuwa da sama ma'abuciyar masukayya wadanda rana da wata suke bi takai, da ranar kiyama da Allah Yayi wa halitta alkawarin zai tarasu a cikinsa, da mai sheda da zaiyi sheda da wanda za'ayi sheda akansa. Allah (tsarkakakken sarki) Yana rantsuwa da duk abinda Ya so daga halittunSa, amma abin halitta kam baya halatta gareshi yayi rantsuwa da wanin Allah, domin rantsuwa da wanin Allah shirkace. An la'anci wadanda suka tona rami cikin kasa rami mai girma domin azabtar da muminai kuma suka hura wuta mai tsananin ruruwa, yayinda suka zauna a bakin ramin suna masu lazimtan sa, alhali su gameda abinda suke aikatawa na horo da azabtarwa suna halarce. Kuma basu rike su da wannan ukubar mai tsanani ba face don sunyi imani da Allah mabuwayi wanda ba'a galaba akanSa, abin godiya cikin maganganunSa da ayyukanSa da sifofinSa, wanda shi keda mulkin sammai da kasa, kuma Shi – tsarki ya tabbata agareShi- akn komai halartaccene babu abinda ke buya gareShi.
إِنَّ الَّذِينَ فَتَنُوا الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ ثُمَّ لَمْ يَتُوبُوا فَلَهُمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمْ عَذَابُ الْحَرِيقِ (10)
Lallaine wadanda suka fitini muminai maza da muminai mata sannan basu tuba ba, suna da azabar jahannama, kuma suna da azabar gobara.

Sharhi: lallai wadanda suka kona muminai maza da muminai mata da wuta domin su kawar dasu daga addinin Allah sa'annan kuma basu tubaba, to a lahira suna da azabar jahannama, kuma sunada azaba mai tsanani mai kuna.

إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَهُمْ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ ذَلِكَ الْفَوْزُ الْكَبِيرُ (11)
Lallaine wadanda sukayi imani kuma suka aikata ayyukan kwarai sunada gidajen Aljanna, koramu na gudana a karkashinsu, wancan shine rabo mai girma.


Sharhi: lallai wadanda suka gaskata Allah da manzonSa kuma suka aikata ayyuka kyawawa suna da (gidajen) aljanna, wadanda koramu ke gudana a karkashin benayenta da bishiyoyinta, wancan rabone mai girma.
إِنَّ بَطْشَ رَبِّكَ لَشَدِيدٌ (12)
Lallaine damkar Ubangijinka mai tsananice kwarai.
إِنَّهُ هُوَ يُبْدِئُ وَيُعِيدُ (13)
Lallai ne Shi, Shine mai faran halitta kuma Ya mayar da ita (bayan mutuwa)
وَهُوَ الْغَفُورُ الْوَدُودُ (14)
Kuma Shine mai yawan gafara wanda muminai ke so sama da komai kumaYake sonsu.
ذُو الْعَرْشِ الْمَجِيدُ (15)
Ma'abucin al'arshi mai girma.
فَعَّالٌ لِمَا يُرِيدُ (16)
Mai aiwatar da abinda Yake nufi.

Sharhi: lallai daukan fansar Ubangijinka da azabarSa ga makiyanSa tabbas abune mai girma matsananci. Lallai Shi, Shine Yake farar halitta sa'annan Ya dawo da ita, kuma Shi mai gafarane ga wanda ya tuba mai tsananin so da kauna ga waliyyansa (wato muminai), ma'abucin al'arshi mai girma wanda Ya kai makura wurin falala da karimci, mai aikkata abinda yaga dama, duk abinda Ya nufata baya gagaranSa.
هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ الْجُنُودِ (17)
Shin labarin rundunoni yazo maka?
فِرْعَوْنَ وَثَمُودَ (18)
Fir'auna da Samudawa.
بَلِ الَّذِينَ كَفَرُوا فِي تَكْذِيبٍ (19)
A'aha! Wadanda suka kafirta suna cikin karyatawa.
وَاللَّهُ مِنْ وَرَائِهِمْ مُحِيطٌ (20)
Alhali Allah daga bayansu mai kewaye (ne garesu).
بَلْ هُوَ قُرْآنٌ مَجِيدٌ (21)
A'aha! Shi Alkur'anine mai girma.
فِي لَوْحٍ مَحْفُوظٍ (22)
A cikin allo tsararre.

Sharhi: shin labarin rundunonin kafirai ya iso gareka – ya kai wannan manzon- Masu karyata annabawansu? Fir'auna da Samudawa da abinda ya saukam musu na azaba da horo? Mutane basu yi la'akari da hakan ba, a'aha, wadanda suka kafirta suna cikin cigaba da karyatawa kamar yadda dabi'ar wadanda suka gabacesu ta kasance, alhali Allah Ya gewaye su da iliminSa da kuduraSa, babu abinda ke buya gareShi daga su har ayyukansu. Kuma Alkur'ani ba yadda masu karyatawa mushirikai suke riyawa bane na cewa wai shi wakene kuma sihirine, sai suka karyata game dashi, bahaka bane, shi (Alkur'ani) abin karantawane mai girma mai daraja, a cikin (lauhul mahfuz) allo tsararre, canji ko jirkice baya shigansa.