طاهر جبريل دكو
_28 _December _2013هـ الموافق 28-12-2013م, 02:12 AM
كَلَّا إِنَّ كِتَابَ الْأَبْرَارِ لَفِي عِلِّيِّينَ (18)
A'aha! Hakika littafin masu da'a yana cikin illiyyina.
وَمَا أَدْرَاكَ مَا عِلِّيُّونَ (19)
Kuma menene ya sanar da kai abinda ake cewa illiyyuna?
كِتَابٌ مَرْقُومٌ (20)
Wani littafine rubutacce.
يَشْهَدُهُ الْمُقَرَّبُونَ (21)
Mukarrabai (wato mala'iku mafiya kusanci ga Allah) suke halartansa.
Sharhi: tabbas littafin masu biyayya – wadanda sune masu takawa- yana cikin martabobi madaukaka a cikin aljanna, me ya sanar da kai – ya kai wannan Annabi- wadannan martabobin madaukaka? Littafin masu biyayya dai an riga an rubutashi an gama da shi, ba'a kari a cikinsa kuma ba'a ragi, mala'iku mukarrabai na kowane sama suna ganinsa.
إِنَّ الْأَبْرَارَ لَفِي نَعِيمٍ (22)
Lallai ne masu da'a ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.
عَلَى الْأَرَائِكِ يَنْظُرُونَ (23)
Akan karagu sonata kallo.
تَعْرِفُ فِي وُجُوهِهِمْ نَضْرَةَ النَّعِيمِ (24)
Kana sanin a cikin fuskokinsu akwai kwarjinin ni'ima.
يُسْقَوْنَ مِنْ رَحِيقٍ مَخْتُومٍ (25)
Ana shayar dasu daga wata giya rufaffiya.
خِتَامُهُ مِسْكٌ وَفِي ذَلِكَ فَلْيَتَنَافَسِ الْمُتَنَافِسُونَ (26)
Karshen kurbinta Almiskine, kuma a cikin wannan sai masu rige rige suyita rige rige.
وَمِزَاجُهُ مِنْ تَسْنِيمٍ (27)
Kuma gaurayenta daga tasnim yake.
عَيْنًا يَشْرَبُ بِهَا الْمُقَرَّبُونَ (28)
Wani marmarone wanda mukarrabai ke sha daga gareshi.
Sharhi: lallai masu gaskiya da biyayya suna cikin aljanna suna morewarsu, suna kan gadaje suna kallon Ubangijinsu, da abinda Ya tanadar musu na alkhairai, kuma kana ganin damshi na ni'ima a fusakunsu, ana shayar dasu daga giya tsaftatacciya wacce aka rufe kokunansu, karsheta kamshin almiskine, (saboda haka) sai masu rige rige suyi tserereniya akan wannan dauwamammiyar ni'imar. Kuma wannan abinshan (wato giyar) kayan hadinta wanda ake cakuda ta dashi, wani marmarone daga cikin aljanna ana kiransa » Tasnim« saboda daukakansa, wani marmarone da aka tanadeshi domin makusanta ga Allah (wato muminai) su sha daga gareshi kuma suji dadi dashi.
إِنَّ الَّذِينَ أَجْرَمُوا كَانُوا مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا يَضْحَكُونَ (29)
Lallaine wadanda suka kafirta sun kasance (a duniya) suna yiwa wadanda sukayi imani dariya.
وَإِذَا مَرُّوا بِهِمْ يَتَغَامَزُونَ (30)
Kuma idan suka wuce ta inda suke, saisu rika zundensu.
وَإِذَا انْقَلَبُوا إِلَى أَهْلِهِمُ انْقَلَبُوا فَكِهِينَ (31)
Kuma idan suka juya zuwaga iyalansu sai su tafi suna farin ciki (game da abinda sukayi)
وَإِذَا رَأَوْهُمْ قَالُوا إِنَّ هَؤُلَاءِ لَضَالُّونَ (32)
Kuma idan sun gansu, sai suce; lallai wadannan batattune.
وَمَا أُرْسِلُوا عَلَيْهِمْ حَافِظِينَ (33)
Alhali kuwa ba'a aikosuba domin su zama masu tsaro akansu.
Sharhi: lallai wadanda suka kafirta sun kasance a duniya suna isgilanci ga muminai, idan suka wuce ta inda suke, sai su rika zundensu saboda isgilanci, idan kuma suka koma (wato su kafiran) ga iyalansu da abokansu sai su rika dariya suna shashewa saboda abinda sukayi ga muminai na isgilanci, kuma idan wadannan kafiran suka ga sahabban Annabi Muhammad (s.a.w) alhali sun bi gaskiya sai suce; lallai wadannan dimautattune game da binsu ga Muhammadu (s.a.w) kuma (dai) ba'a aiko wadannan kafiran domin su zama masu sa ido ba akan sahabban (Annabi) Muhammadu (s.a.w).
فَالْيَوْمَ الَّذِينَ آمَنُوا مِنَ الْكُفَّارِ يَضْحَكُونَ (34)
Ta ayau (wato ranan kiyama) wadanda sukayi imani suke yiwa kafirai dariya.
Sharhi: to ranar kiyama da sannu wadanda suka gaskata Allah da manzonSa kuma sukayi aiki da shari'arSa suma zasuyi isgilanci ga kafirai kamar yadda kafiran suka yi musu isgilanci a duniya.
عَلَى الْأَرَائِكِ يَنْظُرُونَ (35)
Akan karagu sonata kallo.
هَلْ ثُوِّبَ الْكُفَّارُ مَا كَانُوا يَفْعَلُونَ (36)
Shin an sakawa kafirai gameda abinda suka kasance suna aikatawa?
Sharhi: bisa gadaje na alfahari muminai zasu rika kallon abinda Allah Ya basu na karama da ni'ima a cikin aljanna, mafi girma daga haka shine ganin Allah mai karimci. To shin an sakawa kafirai da jinsin aikinsu sakamako mai dacewa da abinda suka kasance suna aikatawa a duniya na sharrurruka da zunubbai? (amsar itace); na'am da sannu za'a sakanta musu sakamako mafi cika kuma mafi adalcinsa.