المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس العاشر: ترجمة تفسير سورة المطففين من كتاب: التفسير الميسر آيات من 1- 17


طاهر جبريل دكو
_28 _December _2013هـ الموافق 28-12-2013م, 02:04 AM
وَيْلٌ لِلْمُطَفِّفِينَ (1)
Bone ya tabbata ga masu tauye ma'auni.
الَّذِينَ إِذَا اكْتَالُوا عَلَى النَّاسِ يَسْتَوْفُونَ (2)
Wadanda suke idan suka auna daga mutane suna cika ma'auni.
وَإِذَا كَالُوهُمْ أَوْ وَزَنُوهُمْ يُخْسِرُونَ (3)
Kuma idan zasu aunar musu da mudu ko zasu gwada musu da sikeli sai su tauye.
أَلَا يَظُنُّ أُولَئِكَ أَنَّهُمْ مَبْعُوثُونَ (4)
Ashe wadancan basu yi yakini cewa lallai su za'a tadasu ba?

Sharhi: azaba mai tsanani ta tabbata ga masu tauye mudu da sikeli, wadanda idan suka sayi abinda ake aunawa da mudu ko wanda ake gwadawa da sikeli daga mutane sai su cika wa kansu ma'auni, amma idan zasu sayar ga mutane da abinda ake aunawa da mudu ko wanda ake gwadawa da sikeli sai su tauye mudu da sikeli, to ina kuma ga wanda ke sacesu ko kuma ya kwacesu kuma ya cuci mutane gameda kayansu? Lallai shi yafi cancantan shiga azaba samada masu tauye mudu da sikeli. Shin masu tauye ma'aunin nan basu yarda cewa Allah ta'ala zai tashesu bane kuma Yayi musu hisabi akan ayyukansu?
لِيَوْمٍ عَظِيمٍ (5)
Domin wani yini mai girma.
يَوْمَ يَقُومُ النَّاسُ لِرَبِّ الْعَالَمِينَ (6)
Yinin da mutane ke tashi zuwa ga Ubangijin halittu.

Sharhi: tayar dasu zai kasancene a wani yini mai tsananin tashin hankali, ranar da mutane zasu tsaya a gaban Allah, sai Yayi musu hisabi akan (ayyukansu) kadan da mai yawansa, alhali su a cikinsa suna masu kankan da kai ga Allah Ubangijin talikai.
كَلَّا إِنَّ كِتَابَ الْفُجَّارِ لَفِي سِجِّينٍ (7)
A'aha! Lallaine littafin fajirai tabbas yana cikin sijjin.

وَمَا أَدْرَاكَ مَا سِجِّينٌ (8)
Mai ya sanar da kai abinda ake cewa sijjin?
كِتَابٌ مَرْقُومٌ (9)
Littafine rubutacce.


Sharhi: tabbas hakika makoman fajirai kuma mazauninsu yana cikin kuntataccen wuri, kuma me ya sanar da kai wannan kuncin? Lallai shi wani kurkuku ne wanda azabarsa take dauwamammiya kuma azaba mai radadi, kuma shine aka rubuta musu komawa gareshi, rubutaccene an riga an gama dashi, baza'ayi kari a cikinsaba kuma baza a rageba.
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِلْمُكَذِّبِينَ (10)
Bone ya tabbata a ranar nan ga masu karyatawa.
الَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوْمِ الدِّينِ (11)
Wadanda suke karyatawa game da ranar sakamako.
وَمَا يُكَذِّبُ بِهِ إِلَّا كُلُّ مُعْتَدٍ أَثِيمٍ (12)
Kuma babu mai karyatawa gareshi face dukkan mai ketare haddi mai yawan zunubi.
إِذَا تُتْلَى عَلَيْهِ آيَاتُنَا قَالَ أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ (13)
Idan ana karatun ayoyinMu akansa sai yace tatsuniyoyin mutanen farkone.
كَلَّا بَلْ رَانَ عَلَى قُلُوبِهِمْ مَا كَانُوا يَكْسِبُونَ (14)
A'aha! Ba haka, abinda suka kasance suna aikatawa dai yayi tsatsa a cikin zukatansu.
كَلَّا إِنَّهُمْ عَنْ رَبِّهِمْ يَوْمَئِذٍ لَمَحْجُوبُونَ (15)
A'aha! Hakika su daga Ubangijinsu – a wannan ranan- wadanda ake shamakancewane.
ثُمَّ إِنَّهُمْ لَصَالُو الْجَحِيمِ (16)
Sa'annan lallai ne su masu shiga cikin jahima ne.
ثُمَّ يُقَالُ هَذَا الَّذِي كُنْتُمْ بِهِ تُكَذِّبُونَ (17)
Sa'annan ace; wannan shine abinda kuka kasance kuna karyatawa game dashi.

Sharhi: azaba mai tsanani a wannan ranar ya tabbata ga masu karyatawa, wadanda suke karyatawa game da aukuwan ranar sakamako, kuma babu mai karyatawa gamedashi face duk wani azzalumi mai yawan sabo. Idan aka karanta ayoyin Alkur'ani akan sa sai yace; wadannan karairayi ne na mutanen farko. Al'amarin ba kamar yadda suke riyawa bane, a'a, shidai (Alkur'ani) maganan Allah ne kuma wahayinSa zuwa ga annabinSa, kawai abinda ya toshe zukatansu ya hanasu gaskatawa shine abinda suke aikatawa na yawan zunubbai. Al'amarin ba kamar yadda kafirai suke riyawa bane, a'aha! Su dai a ranar kiyama ababen kangewa ne daga barin ganin Ubangijinsu, kuma a cikin wannan ayar akwai dalili na ganin muminai ga Ubangijinsu a cikin aljanna. Sa'annan su (kafirai bayan nan) masu shiga wata ne su ana dandana musu zafinta, sannan sai ace musu wannan shine sakamakon da kuka kasance kuna karyatawa.