تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس التاسع: ترجمة تفسير سورة الانفطار من كتاب: التفسير الميسر


طاهر جبريل دكو
_28 _December _2013هـ الموافق 28-12-2013م, 01:10 AM
إِذَا السَّمَاءُ انْفَطَرَتْ (1)
Idan sama ta tsage.
وَإِذَا الْكَوَاكِبُ انْتَثَرَتْ (2)
Kuma idan taurari suka waste.
وَإِذَا الْبِحَارُ فُجِّرَتْ (3)
Kuma idan aka fashe tekuna.
وَإِذَا الْقُبُورُ بُعْثِرَتْ (4)
Kuma idan aka tone kaburbura.
عَلِمَتْ نَفْسٌ مَا قَدَّمَتْ وَأَخَّرَتْ (5)
Rai ya san abinda ya gabatar da abinda ya jinkirtar.

Sharhi: Idan sama ta tsage, kuma tsarinta ya rikice, kuma taurari suka warwatse, kuma idan Allah Ya fasa tekuna wani ya shiga cikin wasu sai ruwan cikinsu ya tsiyaye, kuma idan aka bulluko kaburbura ta hanyar tayarda wadanda ke cikinsu, a wannan lokacin duk wani rai zai san dukkanin ayyukansa, abin da ya gabatar daga ciki da abin da ya jinkirta kuma a saka masa gameda su.
يَا أَيُّهَا الْإِنْسَانُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ الْكَرِيمِ (6)
Ya kai mutum meye ya rudeka gameda Ubangijinka mai karimci?
الَّذِي خَلَقَكَ فَسَوَّاكَ فَعَدَلَكَ (7)
Wanda Ya halittaka sa'annan Ya daidaitaka.
فِي أَيِّ صُورَةٍ مَا شَاءَ رَكَّبَكَ (8)
A cikin kowace irin sura Yaso ya ginaka akanta.

Sharhi: Ya kai mutumin dake Karyatawa gameda tashin kiyama, meya rudeka ka (har ka kafircewa) Ubangijinka mai yawan kyauta mai yawan alheri? Wanda Ya cancanci godiya da biyayya, ashe ba Shine Ya halicceka ba, sa'annan Ya daidaita halittarka, sa'annan Ya daidaitaka, kuma Ya ginaka ta yadda zaka iya aiwatar da ayyukanka, cikin kowace sura Yaso zai halittaka?

كَلَّا بَلْ تُكَذِّبُونَ بِالدِّينِ (9)
A'aha! Ba hakaba, kuna karyatawane gameda sakamakon.
وَإِنَّ عَلَيْكُمْ لَحَافِظِينَ (10)
Kuma lallaine akanku hakika akwai masu tsaro.
كِرَامًا كَاتِبِينَ (11)
Masu daraja marubuta.
يَعْلَمُونَ مَا تَفْعَلُونَ (12)
Suna sanin abinda kuke aikatawa.

Sharhi: Al'amarin ba kamar yadda kuke fadi bane cewa lallai ku bautarku ga wanin Allah bisa cancantane, a'aha kudai kuna karyatawane game da ranr hisabi da sakamako, kuma akwai mala'iku masu tsaro a kanku, masu daraja a wurin Allah masu rubata abinda aka wakiltasu ga kididdigeshi, babu wani abu dake kubuce musu daga cikin ayyukanku, suna sanin abinda kukeyi na alheri ko na sharri.
إِنَّ الْأَبْرَارَ لَفِي نَعِيمٍ (13)
Lallaine masu da'a ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.


Sharhi: Lallai masu takawa wadanda suke tsaye akan bada hakkokin Allah da hakkokin bayinSa tabbas suna cikin ni'ima.
وَإِنَّ الْفُجَّارَ لَفِي جَحِيمٍ (14)
Kuma lallaine fajirai tabbas suna cikin jahim.
يَصْلَوْنَهَا يَوْمَ الدِّينِ (15)
Zasu shigeta a ranar sakamako.
وَمَا هُمْ عَنْهَا بِغَائِبِينَ (16)
Kuma su ba masu fakuwa bane daga gareta.

Sharhi: Lallai fajirai wadanda suka yi karanta cikin bada hakkokin Allah da hakkokin bayinSa tabbas suna cikin jahim, balbalinta zai rika shafansu ranar sakamako, kuma su ba wadanda ke iya buya bane daga azabar jahannama, ba da fitaba, kuma ba da mutuwaba.
وَمَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ (17)
Kuma mai ya sanar da kai abinda ake cewa ranar sakamako?
ثُمَّ مَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ (18)
Sa'annan mai ya sanar da kai abinda ake cewa ranar sakamako?
يَوْمَ لَا تَمْلِكُ نَفْسٌ لِنَفْسٍ شَيْئًا وَالْأَمْرُ يَوْمَئِذٍ لِلَّهِ (19)
Rana ce da wani rai baya mallakan komai ga wani rai, al'amari a wannan ranan, ga Allah dai yake.

Sharhi: Kuma mai ya sanar da kai girman ranar hisabi? Sa'annan mai ya sanar da kai girman ranar hisabi? Ranar hisabi babu wanda keda ikon amfanar da wani. Al'amari a wannan ranar na Allah ne Shi kadai wanda babu wani mai galaba dake iya galaba akanSa, kuma babu wani mai tilastawan dake iya tilastaShi, kuma babu mai jayayya daShi.