تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس الثامن: ترجمة تفسير سورة التكوير من كتاب: التفسير الميسر


طاهر جبريل دكو
_28 _December _2013هـ الموافق 28-12-2013م, 12:43 AM
إِذَا الشَّمْسُ كُوِّرَتْ (1)
Idan rana aka shafe haskenta.
وَإِذَا النُّجُومُ انْكَدَرَتْ (2)
Kuma idan taurari suka watse.
وَإِذَا الْجِبَالُ سُيِّرَتْ (3)
Kuma idan aka tafiyar da duwatsu.
وَإِذَا الْعِشَارُ عُطِّلَتْ (4)
Kuma idan rakuma masu cikin (wata goma goma) aka kyale su babu makiyayi.
وَإِذَا الْوُحُوشُ حُشِرَتْ (5)
Kuma idan aka tattara dabbobin daji.
وَإِذَا الْبِحَارُ سُجِّرَتْ (6)
Kuma idan aka maida tekuna wuta.
وَإِذَا النُّفُوسُ زُوِّجَتْ (7)
Kuma idan aka hada rayuka da masu kama dasu (a halayya)
وَإِذَا الْمَوْءُودَةُ سُئِلَتْ (8)
Kuma idan aka tambayi wacce aka turbudeta da rai.
بِأَيِّ ذَنْبٍ قُتِلَتْ (9)
Saboda wani laifi aka kashe ta?
وَإِذَا الصُّحُفُ نُشِرَتْ (10)
Kuma idan aka watsa takardun ayyuka (ga masu su).
وَإِذَا السَّمَاءُ كُشِطَتْ (11)
Kuma idan aka fede sama.
وَإِذَا الْجَحِيمُ سُعِّرَتْ (12)
Kuma idan aka hura jahima.
وَإِذَا الْجَنَّةُ أُزْلِفَتْ (13)
Kuma idan aka kusanto da aljanna.
عَلِمَتْ نَفْسٌ مَا أَحْضَرَتْ (14)
Rai ya san abinda ya halartar (a wannan ranan).


Sharhi: idan aka nade rana kuma hasken ta ya gushe, kuma idan taurari suka waste kuma annurinsu ya dushe, kuma idan aka tafiyar da duwatsu daga doron kasa kuma suka kasance kura shekakkiya, kuma idan aka yi banza da rakuma masu ciki, kuma idan aka tara namun daji wuri guda suka gauraya da juna saboda Allah Ya dau fansa ga sashinsu akan sashi, kuma idan aka kyasta tekuna sai suka kama da wuta suna masu ci da wuta duk da girman da suke dashi, kuma idan aka hada rayuka da ire irensu (muminai da muminai kafirai da kafirai), kuma idan jaririyar da aka binne ta da ranta aka tambaye ta –tambayar da zai dadada mata rai kuma ya bakanta ran wanda ya binneta- wani lefi tayi aka binneta? Kuma idan aka bijiroda littattafan ayyuka, kuma idan aka jaye sama daga inda take, kuma idan aka kunna wuta kuma aka bunka ta, kuma idan aljanna -gidan ni'ima-aka kusanto da ita ga yayanta masu takawa, idan wadannan abubuwan suka faru, rai zai taradda abinda ya gabatar na alheri ko sharri.
فَلَا أُقْسِمُ بِالْخُنَّسِ (15)
To ina rantsuwa da taurari masu buya (a lokacin yini).
الْجَوَارِ الْكُنَّسِ (16)
Masu gudu suna bacewa.
وَاللَّيْلِ إِذَا عَسْعَسَ (17)
Da dare idan ya bada baya.
وَالصُّبْحِ إِذَا تَنَفَّسَ (18)
Da safiya idan ta numfasa.
إِنَّهُ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ (19)
Lallaine shi (Alkur'ani) tabbas maganar wani manzo ne mai girma (Jibrilu).
ذِي قُوَّةٍ عِنْدَ ذِي الْعَرْشِ مَكِينٍ (20)
Ma'abucin karfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.
مُطَاعٍ ثَمَّ أَمِينٍ (21)
Wanda ake yiwa da'a ne a can amintacce. ( wato shugaban mala'iku)

Sharhi: Allah madaukaki Yayi rantsuwa da taurarin da haskensu ke buya da rana wadanda suke gudu suna buya a ckin hanyoyinsu, da kuma dare idan ya gabato da duhunsa, da safiya idan haskenta ya bayyana, lallai Alkur'ani isarwa ne na wani manzo mai girma-shine Jibrilu (A.S)- ma'abucin karfi cikin zartas da abinda aka umurceshi dashi, ma'abucin matsayi madaukaki a wurin Allah, mala'iku suna yi masa da'a, amintaccene shi gameda abinda yake saukowa dashi (na wahayi).
وَمَا صَاحِبُكُمْ بِمَجْنُونٍ (22)
Kuma abokinku ba mahaukaci bane.

وَلَقَدْ رَآهُ بِالْأُفُقِ الْمُبِينِ (23)
Kuma lallaine ya ganshi (wato Jibrilu) a cikin sararin sama mabayyani.
وَمَا هُوَ عَلَى الْغَيْبِ بِضَنِينٍ (24)
Kuma shi ga gaibi (wato abinda ake masa wahayi) ba mai rowa bane.
وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَيْطَانٍ رَجِيمٍ (25)
Kuma shi (Alkur'ani) ba maganar wani shedani bane la'ananne.

Sharhi: Muhammadun da kuka sani dai ba mahaukaci bane, kuma hakika Muhammadu ya ga Jibrilu- wanda yake zuwa masa da sako - akan surarsa ta hakika wacce Allah Ya halicceshi akai, (ya ganshi) a bangaren gabashi a kusurwa mai girma a (garin) Makka, wannan shine ganin farko wacce ta kasance a kogon Hira. Kuma Muhammadu ba marowaci bane game da isarda wahayi, kuma wannan Alkur'anin ba maganar shedani bane jefaffe, korarre daga rahamar Allah, a'a shi dai maganan Allahne kuma wahayinSa.
فَأَيْنَ تَذْهَبُونَ (26)
Shin ina zaku tafine?
إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِلْعَالَمِينَ (27)
Lallai ne shi (Alkur'ani) ba komai bane face gargadi ga talikai.
لِمَنْ شَاءَ مِنْكُمْ أَنْ يَسْتَقِيمَ (28)
Ga wanda ya so daga cikin ku ya shiriya.
وَمَا تَشَاءُونَ إِلَّا أَنْ يَشَاءَ اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ (29)
Kuma baza kuso ba sai dai idan Allah Ubangijin talikai Ya so.

Sharhi: To ina hankulanku zasu kaikune cikin karyata Alkur'ani bayan wadannan hujjojin yankakku? (Alkur'ani) bai kasanceba face wa'azi daga Allah ga dukkanin mutane, ga duk wanda yaso - daga cikin ku- yayi istikama akan gaskiya da imani, kuma bazaku so yin istikamar ba kuma baku da iko akan hakan face da kaddarawar Allah Ubangijin dukkanin halittu.