طاهر جبريل دكو
_26 _December _2013هـ الموافق 26-12-2013م, 03:13 PM
فَلْيَنْظُرِ الْإِنْسَانُ إِلَى طَعَامِهِ (24)
To mutum yayi dubi mana zuwaga abincinsa.
أَنَّا صَبَبْنَا الْمَاءَ صَبًّا (25)
Lallaine Mu mun zubo da ruwa zubowa.
ثُمَّ شَقَقْنَا الْأَرْضَ شَقًّا (26)
Sa'annan Muka tsatstsage kasa tsatstsagewa.
فَأَنْبَتْنَا فِيهَا حَبًّا (27)
Sai Muka tsirar da tsirrai a cikinta.
وَعِنَبًا وَقَضْبًا (28)
Da inabi da danyun ganyaye (da ake yanka lokaci lokaci).
وَزَيْتُونًا وَنَخْلًا (29)
Da zaitun da (itacen) dabino.
وَحَدَائِقَ غُلْبًا (30)
Da lambuna masu yawan itatuwa.
وَفَاكِهَةً وَأَبًّا (31)
Da yayan itatuwa na marmari da makiyaya ta dabbobi.
مَتَاعًا لَكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ (32)
Domin jin dadinku ku da dabbobinku.
Sharhi: Saboda haka mutum yayi la'akari da yadda Allah Ya halitta masa abincinsa wanda shine madogarar rayuwarsa? Ta yadda Muka (wato Allah) zubo da ruwa a kasa zubowa, sa'annan Muka tsatstsagata da abinda Muka fitar daga cikinta na kwayoyi ma bambanta, sai muka tsiradda kwaya daga cikinta, da inabi da abincin dabbobi, da zaitun da dabinnai, da lambuna masu manyan manyan itatuwa, da yayan itatuwa da ciyayi da kuke ni'imtuwa dasu daku da dabbobinku.
فَإِذَا جَاءَتِ الصَّاخَّةُ (33)
To idan mai toshe kunnuwa (wato busa ta biyu) tazo.
يَوْمَ يَفِرُّ الْمَرْءُ مِنْ أَخِيهِ (34)
Ranar da mutum yake gudun dan'uwansa.
وَأُمِّهِ وَأَبِيهِ (35)
Da uwarsa da ubansa.
وَصَاحِبَتِهِ وَبَنِيهِ (36)
Da matar sa da yayan sa.
لِكُلِّ امْرِئٍ مِنْهُمْ يَوْمَئِذٍ شَأْنٌ يُغْنِيهِ (37)
Ga kowane mutum daga cikin su a ranar nan akwai wani sha'ani da ya isheshi.
Sharhi: To idan karar (busan kaho) na tashin kiyama tazo ranar kiyama –wacce kunnuwa ke toshewa saboda tsananinta (kararta), ranan da - saboda musibansa- mutum ke gudun dan'uwansa, da mahaifiyarsa da mahaifinsa, da matarsa da yayansa. Ga kowane daya daga cikinsu akwai wani sha'anin da zai hanashi shagaltuwa da waninsa awannan ranar.
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ مُسْفِرَةٌ (38)
Wasu fuskoki a ranar nan masu haskene.
ضَاحِكَةٌ مُسْتَبْشِرَةٌ (39)
Masu dariyane masu bushara.
وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ عَلَيْهَا غَبَرَةٌ (40)
Wasu fuskoki a ranar nan akwai kura akansu.
Sharhi: fuskokin yan Aljanna a wannan ranar suna walkiya, suna cikin farin ciki da annashuwa. Fuskokin yan wuta kuma zasu yi duhu suyi baki.
تَرْهَقُهَا قَتَرَةٌ (41)
Kaskanci zai lullubesu.
أُولَئِكَ هُمُ الْكَفَرَةُ الْفَجَرَةُ (42)
Wadannan sune kafirai fajirai.
Sharhi: kaskanci zai rufesu, wadannan da aka sifanta da wannan sifan sune wadanda suka kafirce wa ni'imomin Allah, kuma suka karyata ayoyinSa, kuma suka yi kasadan aikata fajirci da wuce iyaka cikin aikata abinda Allah Ya hana.