المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس السادس: ترجمة تفسير سورة عبس من كتاب: التفسير الميسر آيات من1 -23


طاهر جبريل دكو
_26 _December _2013هـ الموافق 26-12-2013م, 03:09 PM
عَبَسَ وَتَوَلَّى (1)
Ya daure fuska kuma ya juya baya.
أَنْ جَاءَهُ الْأَعْمَى (2)
Saboda makaho ya je masa.
Sharhi: Canjin fuska da tsumewa ya bayyana a fuskar Annabi (s.a.w) kuma ya kauda kai saboda makahonnan Abdullahi binu Ummi Maktum ya zo masa yana mai neman shiriya, alhali Annabi ya shagaltu da kiran manyan kuraishawa zuwa ga musulunci.
وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّهُ يَزَّكَّى (3)
To me ya sanar da kai cewa wata kila shine zai tsarkaka?
أَوْ يَذَّكَّرُ فَتَنْفَعَهُ الذِّكْرَى (4)
Ko kuma ya fadaka sai fadakarwar ta amfaneshi?

Sharhi: kuma me ya sanar da kai hakikanin al'amarinsa? Tana yiwuwa ransa ta tsaftata da wannan tambayar tasa, kuma ta tsarkaka, ko ya kara samun wa'aztuwa da la'akari.
أَمَّا مَنِ اسْتَغْنَى (5)
Amma wanda ya wadatu (da dukiya ga barin yin imani)
فَأَنْتَ لَهُ تَصَدَّى (6)
Sai gashi kai gare shi kake fuskanta.
وَمَا عَلَيْكَ أَلَّا يَزَّكَّى (7)
Kuma babu wani laifi a akanka don shi bai tsarkakaba.

Sharhi: Amma wanda ya wadatu daga shiriyarka, kai shi kake bijirowa kuma maganarsa kake sauraro? To menene akanka na laifi don bai tsarkakaba daga kafircinsa?
وَأَمَّا مَنْ جَاءَكَ يَسْعَى (8)
Kuma amma wanda yazo maka yana gaggawa.
وَهُوَ يَخْشَى (9)
Alhali shi yana jin tsoron Allah.
فَأَنْتَ عَنْهُ تَلَهَّى (10)
Kai kuma ka shagaltu ga barinsa.
كَلَّا إِنَّهَا تَذْكِرَةٌ (11)
A'aha! Wannan tunatarwace.
فَمَنْ شَاءَ ذَكَرَهُ (12)
Saboda haka wanda yaso ya tunaShi (Allah).
فِي صُحُفٍ مُكَرَّمَةٍ (13)
Cikin wasu littattafai ababen girmamawa.
مَرْفُوعَةٍ مُطَهَّرَةٍ (14)
Ababen daukakawa kuma ababen tsarkakewa.
بِأَيْدِي سَفَرَةٍ (15)
A cikin hanun mala'iku marubuta.
كِرَامٍ بَرَرَةٍ (16)
Masu daraja kuma masu da'a ga Allah.

Sharhi: Amma wanda yake burin saduwa da kai alhali yana tsoron Allah, kada yayi karanta cikin neman shiriya, to kai ga barinsa kake shagaltuwa? Al'amarin ba kamar yadda ka aikata bane – ya kai wannan manzon- lallai wannan surar wa'azince gareka da kuma duk wanda yaso wa'aztuwa. Saboda haka, wanda yaso sai ya ambaci Allah kuma yayi koyi da wahayinSa, wannan wahayin – wanda shine Akur'ani – yana cikin wasu littattafai ababen girmamawa ababen darajawa, mai matsayi madukaki, tsarkakakke daga dauda da kari da ragi, a hannun wasu mala'iku marubuta, masu kai komo tsakanin Allah da halittansa, (mala'ikun) halittune masu daraja, da dabi'unsu da ayyukansu da'a ne, tsarkaka.
قُتِلَ الْإِنْسَانُ مَا أَكْفَرَهُ (17)
An la'anci mutum (wato kafiri) kayi mamakin kafircinsa.
مِنْ أَيِّ شَيْءٍ خَلَقَهُ (18)
Daga wani abu (Allah) Ya halicceshi?
مِنْ نُطْفَةٍ خَلَقَهُ فَقَدَّرَهُ (19)
Daga digon maniyyi Ya halicceshi sa'annan Ya kaddarashi.
ثُمَّ السَّبِيلَ يَسَّرَهُ (20)
Sa'annan hanyarsa ta fita (daga cikin mahaifiyarsa) Ya saukake masa ita.
ثُمَّ أَمَاتَهُ فَأَقْبَرَهُ (21)
Sa'annan Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.
ثُمَّ إِذَا شَاءَ أَنْشَرَهُ (22)
Sa'annan idan ya so (raya shi) zai raya shi.
كَلَّا لَمَّا يَقْضِ مَا أَمَرَهُ (23)
A'aha! Bai idar da abinda (Allah) Ya umurceshi ba.

Sharhi: An la'anci mutum kafiri kuma an azabtar dashi, kayi mamakin tsananin kafircewarsa da Ubangijinsa, shin bai ga abinda Allah Ya halittashi daga gareshi bane a karon fari? Ya halicceshine daga wani ruwa dan kadan wanda shine maniyyi, sa'annan Ya kaddarashi mataki mataki, sannan Ya bayyana masa hanyar alheri da ta sharri, sa'annan Ya kasheshi kuma Ya sanya masa wuri da za'a binneshi a cikinsa. Sa'annan idan subahanahu Yaso sai Ya rayashi, kuma Ya tasheshi bayan mutuwa saboda hisabi da sakamako. Al'amarin dai ba kamar yadda kafiri yake fadi bane kuma yake aikatawa, domin bai zartas da abinda Allah Ya umurceshi dashi ba, na imani da aiki cikin yi maSa biyayya.