المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس الخامس: ترجمة تفسير سورة النازعتت من كتاب: التفسير الميسر آيات من 27-46


طاهر جبريل دكو
_26 _December _2013هـ الموافق 26-12-2013م, 02:36 PM
أَأَنْتُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَمِ السَّمَاءُ بَنَاهَا (27)
Shin kune mafiya wahala ga halitta koko sama? (Allah) Ya ginata.
رَفَعَ سَمْكَهَا فَسَوَّاهَا (28)
Ya daukaka rufinta sa'annan Ya daidaitata.
وَأَغْطَشَ لَيْلَهَا وَأَخْرَجَ ضُحَاهَا (29)
Kuma Ya duhuntar da darenta kuma Ya fitar da hantsinta.
وَالْأَرْضَ بَعْدَ ذَلِكَ دَحَاهَا (30)
Kasa kuma, bayan haka Ya mulmulata.
أَخْرَجَ مِنْهَا مَاءَهَا وَمَرْعَاهَا (31)
Ya fitar da ruwanta daga gareta da makiyayarta.
وَالْجِبَالَ أَرْسَاهَا (32)
Duwatsu kuma Ya kafe su.
مَتَاعًا لَكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ (33)
Domin jiyar da ku dadi, hakama ga dabbobinku.

Sharhi: Yaku mutane tashinku bayan mutuwa shine mafi wahala-bisa kaddarawarku-koko halittan sama? Ya daukaka ta birbishinku kamar gini alhali rufinta yana cikin iska babu bangarenda ya kere wani kuma babu kecewa. Kuma Ya duhuntar da darenta da faduwar ranar ta, kuma Ya bayyana yininta da hasken (ranarta). Kasa kuwa Ya shimfida ta bayan halittar sama, Ya sanaya abubuwa masu amfani a cikinta, kuma Ya bubbugar da idandunan ruwa a cikinta, kuma Ya tsirar da abinda za'ayi kiwo a kansa na tsirrai a cikinta, kuma Ya tabbatar da duwatsu a cikinta domin su zamo turaku gare ta. (Allah) Mai tsarki Ya halicci wadannane duka domin amfanin ku daku da dabbobin ku. Lallai maido da halittarku ranar kiyama shi yafi sauki a wurin Allah sama da halittan wadannan abubuwan, kuma duk hakan a wurin Allah abune mai sauki.


فَإِذَا جَاءَتِ الطَّامَّةُ الْكُبْرَى (34)
To idan uwar masifu mafi girma tazo.
يَوْمَ يَتَذَكَّرُ الْإِنْسَانُ مَا سَعَى (35)
Ranar da mutum zai yi tunanin abinda ya aikata.
وَبُرِّزَتِ الْجَحِيمُ لِمَنْ يَرَى (36)
Kuma a bayyano da (wutar) Jahima ga mai gani.

Sharhi: To idan babbar alkiyama ta zo, da kuma tsanani mai girma –itace busa ta biyu (a cikin kaho) – a wannan lokacin za'a bijirar wa mutum da dukkanin ayyukansa na alkhairi da na sharri, sai ya tuna da su kuma ya ganesu, kuma a fito da jahannama fili ga duk mai gani ya ganta kiri da kiri.
فَأَمَّا مَنْ طَغَى (37)
To amma wanda yayi girman kai.
وَآثَرَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا (38)
Kuma ya zabi rayuwar Duniya.
فَإِنَّ الْجَحِيمَ هِيَ الْمَأْوَى (39)
To lallaine Jahima itace makoma.

Sharhi: Amma wanda ya kangare ga umurnin Allah, kuma ya fifita rayuwar duniya akan lahira, to lallai makoma(rsa) itace wuta.

وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِ وَنَهَى النَّفْسَ عَنِ الْهَوَى (40)
Amma wanda ya ji tsoron tsayuwa a gaban Ubangijinsa, kuma ya hana ransa (bin) son rai.
فَإِنَّ الْجَنَّةَ هِيَ الْمَأْوَى (41)
To lallaine Aljanna itace makoma.

Sharhi: kuma amma wanda ya ji tsoron tsayuwa a gaban Allah domin hisabi, kuma ya hana ransa bin mummunar son zuciya, to lallai aljanna itace mazauninsa.
يَسْأَلُونَكَ عَنِ السَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَاهَا (42)
Suna tambayarka game da tashin alkiyama, yaushene matabbatarta.
فِيمَ أَنْتَ مِنْ ذِكْرَاهَا (43)
Me ya Hadaka da ambatonta?
إِلَى رَبِّكَ مُنْتَهَاهَا (44)
Zuwaga Ubangijinka karshen al'amarinta yake.
إِنَّمَا أَنْتَ مُنْذِرُ مَنْ يَخْشَاهَا (45)
Kawai kai mai gargadine ga mai tsoronta.
كَأَنَّهُمْ يَوْمَ يَرَوْنَهَا لَمْ يَلْبَثُوا إِلَّا عَشِيَّةً أَوْ ضُحَاهَا (46)
A ranar da zasu ganta, (zasu ji) tamkar basu zauna (a Duniya) ba face maraice ko hantsinsa.

Sharhi: mushirikai suna tambayarka ya kai wannan manzon – tambayar isgilanci – game da lokacin tashin kiyama, wanda kake musu alkawari game dashi, kai baka san komai ba game dashi, a'a, makomar wannan yana ga Allah Mai girma da buwaya, kawai abinda ya shafeka game da tashin kiyama shine, kayi gargadi game da shi ga wanda yake tsoron sa. Su dai a ranar da zasu ga tashin kiyama zasu ga kamar basu zauna a duniya ba face abinda ke tsakanin azahar zuwa faduwar rana ko abinda ke tsakanin hudowar rana zuwa rabin yini.