طاهر جبريل دكو
_26 _December _2013هـ الموافق 26-12-2013م, 12:49 AM
بسم الله الرحمن الرحيم
وَالنَّازِعَاتِ غَرْقًا (1)
Ina rantsuwa da mala'iku masu fisgar rayukan (kafirai) da karfi.
وَالنَّاشِطَاتِ نَشْطًا (2)
Da (mala'iku) masu zare rayukan (muminai) cikin sauki da nashadi.
وَالسَّابِحَاتِ سَبْحًا (3)
Da (mala'iku) masu sauka daga sama suna haurawa –da umurnin Allah- kamar suna iyo.
فَالسَّابِقَاتِ سَبْقًا (4)
Sa'annan (da mala'iku) masu tseretsere wurin zartas da umurnin Allah
فَالْمُدَبِّرَاتِ أَمْرًا (5)
Sa'annan (da mala'iku) masu dabbara al'amuran (duniya) da umurnin Allah.
يَوْمَ تَرْجُفُ الرَّاجِفَةُ (6)
Ranar da mai girgiza abubuwa (wato busan kaho na farko) zata girgiza.
تَتْبَعُهَا الرَّادِفَةُ (7)
Mai biyarta (busa ta biyu) tana biye.
Sharhi: Allah (Madaukaki) Ya rantse da mala'iku masu fisgan rayukan kafirai fisga mai tsanani, da mala'ikun da suke daukan rayukan muminai cikin sauki da nashadi, da mala'ikun da suke iyo ayayin saukowarsu daga sama da haurawarsu zuwa gareta, sannan sai mala'ikun da suke rige rige wurin zartas da umurnin Allah, sannan mala'ikun da suke zartas da abin da Allah Ya wakiltasu akai game da gudanar da sha'anin kaunu (wato Duniya da abinda Allah ya kaddara a cikinta mai kyau da mara kyau).- Kuma baya halatta ga wani mahaluki yayi rantsuwa da wanin (Allah) mahaliccinsa, idan ko ya aikata haka, to yayi shirk- lallai za'a tada halittu kuma za'ayi musu hisabi a ranar da kasa zata girgiza saboda busa ta farko (a cikin kaho) busa ta matarwa, busa ta biyu ma tana biye da ita wacce itace busa ta rayarwa.
قُلُوبٌ يَوْمَئِذٍ وَاجِفَةٌ (8)
Wasu zukata a wannan ranar suna tsaurace.
أَبْصَارُهَا خَاشِعَةٌ (9)
Alhali idanunsu na cikin kaskanci.
Sharhi: Zukatan kafirai a wannan ranar zata kasance cikin rashin nutsuwa saboda tsananin tsoro, idandunansu kuma kaskantattu saboda wahalhalun da suke gani.
يَقُولُونَ أَإِنَّا لَمَرْدُودُونَ فِي الْحَافِرَةِ (10)
Suna cewa; ashe lallai za'a iya mayar damu a kan al'amarin farko?
أَإِذَا كُنَّا عِظَامًا نَخِرَةً (11)
Ashe idan muka zama kasusuwa rududdugaggu?
قَالُوا تِلْكَ إِذًا كَرَّةٌ خَاسِرَةٌ (12)
Sukace; wancan kam, komawace tababbiya.
Sharhi: wadannan masu karyatawa gameda tashin alkiyama suka ce; yanzu ana iya maidamu zuwaga halin da muka kasance a cikinsa na rayuwa a kan kasa bayan mutuwarmu? Yanzu ana iya dawo da mu bayan mun kasance kasusuwa rududdugaggu? Sai sukace; wannan dawowar tamu-inma har ta yiwu – zata kasance tababbiya makaryaciya.
فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَةٌ وَاحِدَةٌ (13)
To ita tsawa guda ce kawai.
فَإِذَا هُمْ بِالسَّاهِرَةِ (14)
Sai kawai gasu a bayan kasa.
Sharhi: kawai busace kwaya daya (a cikin kaho) sai gasu nan rayayyu akan kasa bayan da sun kasance a cikinta.
هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ مُوسَى (15)
Shin labarin Musa ya zo maka?
Sharhi: shin labarin Musa ya zo maka ya kai wannan Annabin? Yayin da Ubangijinsa Ya kirashi a cikin kwari mai tsarki mai albarka (Duwa)
إِذْ نَادَاهُ رَبُّهُ بِالْوَادِ الْمُقَدَّسِ طُوًى (16)
A lokacinda Ubangijinsa Ya kirayeshi a cikin kwari mai tsarki (wato) Duwa?
اذْهَبْ إِلَى فِرْعَوْنَ إِنَّهُ طَغَى (17)
Ka tafi zuwaga Fir'auna, lallaine shi ya ketare haddi.
فَقُلْ هَلْ لَكَ إِلَى أَنْ تَزَكَّى (18)
Sai kace masa ko zakaso ka tsarkaka?
وَأَهْدِيَكَ إِلَى رَبِّكَ فَتَخْشَى (19)
Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin kaji tsoronSa?
Sharhi: sai Yace masa: ka tafi zuwa ga Fir'auna, lallai shi ya kai makura a cikin sabon (Allah) sai kace masa; shin kana da bukatan ka tsarkake ranka daga nakasa kuma kayi masa ado na imani, kuma in shiryar da kai zuwa ga yiwa Ubangijinka da'a, domin kaji tsoronSa kuma ka kiyaye dokokinSa?
فَأَرَاهُ الْآيَةَ الْكُبْرَى (20)
Sai Ya nuna masa ayar nan mafi girma?
فَكَذَّبَ وَعَصَى (21)
Sai ya karyata kuma ya saba (umurni)
ثُمَّ أَدْبَرَ يَسْعَى (22)
Sa'annan ya juya baya yana tafiya da sauri.
Sharhi: sai (Annabi) Musa ya nuna wa Fir'auna alamomi masu girma: Sanda da Hanu, sai Fir'auna ya karyata Annabin Allah Musa (Amincin Allah su tabbata a gareshi) ya kuma sabawa Ubangijinsa (Mai girma da buwaya) sannan ya juya baya yana mai kauda kai daga yin imani kuma yana mai yin fito na fito da Annabi Musa .
فَحَشَرَ فَنَادَى (23)
Sai yayi gayya, sa'annan yayi kira.
فَقَالَ أَنَا رَبُّكُمُ الْأَعْلَى (24)
Sai yace; nine ubangijinku mafi daukaka.
فَأَخَذَهُ اللَّهُ نَكَالَ الْآخِرَةِ وَالْأُولَى (25)
Saboda haka sai Allah Ya kamashi, domin azaba gameda (maganar sa ta) karshe da ta farko.
إِنَّ فِي ذَلِكَ لَعِبْرَةً لِمَنْ يَخْشَى (26)
Lallaine a cikin wannan hakika akwai abin kula ga wanda yake tsoron Allah.