تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس الثالث: ترجمة تفسير سورة النبإ من كتاب: التفسير الميسر آيات من 17-40


طاهر جبريل دكو
_26 _December _2013هـ الموافق 26-12-2013م, 12:34 AM
إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ كَانَ مِيقَاتًا (17)
Lallaine ranar rarrabewa ta kasance abin kayyadewa lokaci.
يَوْمَ يُنْفَخُ فِي الصُّورِ فَتَأْتُونَ أَفْوَاجًا (18)
Ranar da za'ayi busa acikin kaho, sai kuzo jama'a jama'a.

Sharhi: lallai ranar raba gardama tsakanin halittu-shine ranan kiyama- ya kasance lokacine kuma mau'idine iyakantacce ga na farko da na karshe, ranar da mala'ika zaiyi busa a cikin kaho, domin sanar da tashin kiyama, sai ku taho al'umma al'umma, kowace al'umma tana tareda shugabanta.
وَفُتِحَتِ السَّمَاءُ فَكَانَتْ أَبْوَابًا (19)
Kuma aka bude sama sai ta kasance kofofi.
Sharhi: kuma aka bude sama, sai ta kasance ma'abuciyar kofofi masu yawa domin saukar mala'iku.
وَسُيِّرَتِ الْجِبَالُ فَكَانَتْ سَرَابًا (20)
Kuma aka tafiyar da duwatsu, sai suka kasance (kamar) ruwan kawalwalniya.
Sharhi: kuma a sheke duwatsu bayan kafuwarsu, sai su kasance kamar ruwan kawalwalniya.

إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتْ مِرْصَادًا (21)
Lallaine jahannama ta kasance madakata.
لِلطَّاغِينَ مَآبًا (22)
Ga masu ketare iyakoki, ta zama makoma.
لَابِثِينَ فِيهَا أَحْقَابًا (23)
Suna masu zama a cikinta zamunna.
لَا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرْدًا وَلَا شَرَابًا (24)
Basu dandanar wani sanyi acikinta, kuma basu dandanar wani abin sha.
إِلَّا حَمِيمًا وَغَسَّاقًا (25)
Face tafasashshen ruwa da diwa.
جَزَاءً وِفَاقًا (26)
Sakamako mai dacewa.
Sharhi: lallai jahannama a wannan ranar ta kasance tana dakon kafirai wadanda aka tanadar da ita dominsu, makoma ga kafirai suna masu zama acikinta zamunna masu bibiyan juna basu yankewa, basu cin wani abu da zai sanyaya zafin wutan sa'ir a garesu, haka kuma basu da wani abin sha da zai magance musu kishi, sai dai ruwan zafi da diwan yan wuta, ana musu sakamako da wannan sakamakon na adalci dai dai da ayyukansu da suka kasance suna aikatawa a duniya.


إِنَّهُمْ كَانُوا لَا يَرْجُونَ حِسَابًا (27)
Lallaine su sun kasance basu tsammani wani hisabi.
وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا كِذَّابًا (28)
Kuma suka karyata gameda ayoyinmu karyatawa.
وَكُلَّ شَيْءٍ أَحْصَيْنَاهُ كِتَابًا (29)
Alhali ko wane abu mun kididdigeshi a rubuce.
فَذُوقُوا فَلَنْ نَزِيدَكُمْ إِلَّا عَذَابًا (30)
Saboda haka ku dandana, domin bazaMu kara muku komai ba face azaba.
Sharhi: lallai su sun kasance basu tsoron ranar hisabi, saboda haka basuyi aiki domintaba, kuma sun karyata gameda abinda manzanni suka zo musu dashi karyatawa, alhali Mu komai da komai Mun sanshi kuma Mun rubutashi a lauhul mahfuzu, saboda haka ku dandani sakamakon aikinku ya ku kafirai! bazaMu taba kara muku ba face azaba a kan azabarku.
إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ مَفَازًا (31)
Lallaine masu takawa sunada wani wurin samun babban rabo.
حَدَائِقَ وَأَعْنَابًا (32)
Lambuna da inabi.
وَكَوَاعِبَ أَتْرَابًا (33)
Da cikakkun yan mata tsarar juna.
وَكَأْسًا دِهَاقًا (34)
Da kofunan giya cikakku.
لَا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا كِذَّابًا (35)
Basu jin yasashshiyar magana a cikinta kuma basu jin karyatawa.

Sharhi: lallai wadanda suke tsoron Ubangijinsu kuma suke kyawawan ayyuka suna da rabo na shiga aljanna, lallai sunada manyan gonaki da inabi masu yawa, kuma sunada yan mata masu kananan shekaru masu tsayayyun nonna tsaran juna, kuma suna da kofuna cikakku na giya, a cikin wannan aljannan basu jin mummunar magana, kuma sashinsu baya Karyata sashi.
جَزَاءً مِنْ رَبِّكَ عَطَاءً حِسَابًا (36)
Domin sakamako daga Ubangijinka, kyuta mai yawa.
رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا الرَّحْمَنِ لَا يَمْلِكُونَ مِنْهُ خِطَابًا (37)
Ubangijin sammai da kasa da abinda ke tsakaninsu, Mai rahama, basu mallakar (wata dama) ta yin magana daga gareshi.
يَوْمَ يَقُومُ الرُّوحُ وَالْمَلَائِكَةُ صَفًّا لَا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنْ أَذِنَ لَهُ الرَّحْمَنُ وَقَالَ صَوَابًا (38)
Ranar da Ruhi (wato mala'ika Jibrilu) da mala'iku zasu tsaya a cikin sahu, basu magana sai wanda Allah Ya masa izini, kuma ya fadi abinda yake daidai.
ذَلِكَ الْيَوْمُ الْحَقُّ فَمَنْ شَاءَ اتَّخَذَ إِلَى رَبِّهِ مَآبًا (39)
Wancan shine yini na gaskiya. Saboda haka, wanda yaso ya riki makoma zuwaga Ubangijinsa.
Sharhi: duk wadannan (ni'imomin) nasune saboda sakamako da falala da kyauta mai yawa daga Allah, wacce ta wadacesu. Ubangijin sammai da kasa da abin dake tsakaninsu, Mai rahamar duniya da lahira, basu mallakar dammar tambayarSa face cikin abinda Yayi musu izini. Ranarda Jibrilu (amincin Allah Ya tabbata a gareshi) zai tashi, da mala'iku suna masu yin sahu, basu yin ceto face ga wanda Mai rahama Yayi musu izini cikin cetonsa, kuma ya fadi gaskiya da datacciyar magana. Wannan itace ranata gaskiya, wacce babu kokwanto cikin kasancewarta, saboda haka, wanda yaso kubuta daga wahalhalun ta sai ya riki makoma zuwaga Ubangijinsa da kyakkyawan aiki.
إِنَّا أَنْذَرْنَاكُمْ عَذَابًا قَرِيبًا يَوْمَ يَنْظُرُ الْمَرْءُ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ وَيَقُولُ الْكَافِرُ يَا لَيْتَنِي كُنْتُ تُرَابًا (40)
Lallaine Munyi muku gargadi gameda azaba makusanciya, ranar da mutum ke dubi zuwaga abinda hannayensa biyu suka aikata, kuma kafiri yace; kaitona inama da na kasance turbaya.
Sharhi: lallai Mu Mun gargadeku gameda azabar ranar karshe wacce take kusa, wacce ko wane mutum zai ga abinda ya aikata na alkhairi ko na sharri, ko zunubbanda ya tara, kafiri kuma zai daura cewa; kaitona! inama da na kasance turbaya, saboda wahalhalun hisabi.