المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس الثاني: ترجمة تفسير سورة النبإ من كتاب: التفسير الميسر آيات من1-16


طاهر جبريل دكو
_26 _December _2013هـ الموافق 26-12-2013م, 12:25 AM
بسم الله الرحمن الرحيم

عَمَّ يَتَسَاءَلُونَ (1)
Akan me suke tambayan juna?
عَنِ النَّبَإِ الْعَظِيمِ (2)
Akan muhimmin labarinnan mai girma.
الَّذِي هُمْ فِيهِ مُخْتَلِفُونَ (3)
Wanda suke sabawa juna a ciknsa.

Sharhi: game da wani abune sashin kafiran kuraishawa ke tambayan sashi? Suna tambayan junane game da labarinnan mai girman sha'ani, wanda yake labartawa game da tashin Alkiyama wanda kafiran kuraishawa suka yi shakka game da shi kuma suka karyata shi.
كَلَّا سَيَعْلَمُونَ (4)
A'aha! Zasu sani

ثُمَّ كَلَّا سَيَعْلَمُونَ (5)
Sannan a'aha zasu sani.

Sharhi: Al'amarin ba kamar yadda wadannan mushirikan suke riyawa bane, da sannu wadannan mushirikan zasu ga karshen karyatawarsu, kuma abinda Allah zai yi da su rananr kiyama zai bayyana garesu sannan zasu samu tabbaci game da hakan kuma gaskiyar abinda Muhammadu (s.a.w) ya zo da shi na Alkur'ani da tashin Alkiyama ya tabbata a garesu. Wannan kasheji ne kuma bayani ne gameda narkon azaba garesu.
أَلَمْ نَجْعَلِ الْأَرْضَ مِهَادًا (6)
Ashe baMu sanya kasa shimfida ba?

Sharhi: Ashe baMu sanya kasa faffada ba gareku kamar shimfida?

وَالْجِبَالَ أَوْتَادًا (7)
Da duwatsu a matsayin turaku (ga kasa)?
Sharhi: da duwatsu dogaye saboda kada kasa ta motsa daku?
وَخَلَقْنَاكُمْ أَزْوَاجًا (8)
Kuma Muka halittaku maza da mata.

Sharhi: Muka halittaku bibbuyu, jinsin maza da jinsin mata?
وَجَعَلْنَا نَوْمَكُمْ سُبَاتًا (9)
Kuma Muka sanya baccinku ya zama hutu (gareku).

Sharhi: kuma Mun sanya baccinku ya zama hutu ga jikkunanku, acikinsa kuke samun natsuwa da sukuni.
وَجَعَلْنَا اللَّيْلَ لِبَاسًا (10)
Kuma Muka sanya dare (ya zama) sutura?

Sharhi: kuma Mun sanya dare a matsayin tufafi da duhunsa yake suturceku ya lullubeku kamar yadda tufafi ke suturce wanda ya tufatu da shi.
وَجَعَلْنَا النَّهَارَ مَعَاشًا (11)

Kuma muka sanya yini (yazama) lokacin neman abinci ?
Sharhi: kuma Muka sanya yini ya zama lokacin rayuwa gareku, kuna fadi tashi a cikinsa saboda neman abinda zaku rayu dashi, kuna kokari cikinsa don anfanin kanku?
وَبَنَيْنَا فَوْقَكُمْ سَبْعًا شِدَادًا (12)
Kuma Muka gina sammai bakwai masu karfi a samanku?

Sharhi: kuma Mun gina sammai bakwai gini mai aminci halitta mai nagrta babu tsatstsagewa a gareshi kuma babu kekkecewa?
وَجَعَلْنَا سِرَاجًا وَهَّاجًا (13)
Kuma Muka sanya fitila mai tsananin haske (rana)?

Sharhi: kuma Muka sanya rana fitila kunnanniya mai haske?
وَأَنْزَلْنَا مِنَ الْمُعْصِرَاتِ مَاءً ثَجَّاجًا (14)
Kuma muka saukar daga cikakkun giragizai, ruwa mai yawan zuba.

لِنُخْرِجَ بِهِ حَبًّا وَنَبَاتًا (15)
Domin mu fitar da kwaya da tsiri game da shi?
وَجَنَّاتٍ أَلْفَافًا (16)
Da lambuna masu (itatuwa) ma'abuta lillibniya?

Sharhi: kuma Mun saukar da ruwa mai kwaranya da yawa daga giragizai masu ruwa, saboda Mu tsirar da kwaya na abinda mutane suke rika abinci da ciyayi da dabbobi ke ci, da gonaki wadanda sashinsu ke ruhuwa kan sashi saboda yawan rassansu?