طاهر جبريل دكو
_25 _December _2013هـ الموافق 25-12-2013م, 11:59 PM
(أعوذ بالله من الشيطان الرجيم)
Ma'ana:"Ina neman tsarin Allah daga shedan jefaffe"
(Sharhi):Allah Madaukakin sarki Ya shar'anta wa duk wani makarancin Akur'ani mai girma daya nemi tsarin Allah daga shedan jefaffe, Allah tsarkakakke Yace:
فَإِذَا قَرَأْتَ الْقُرْآَنَ فَاسْتَعِذْ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ
Ma'ana:Idan zaka karanta Akur'ani ka nemi tsarin Allah daga shedan jefaffe" wannan kuwa ya kasancene saboda Alkur'ani shiriyane ga mutane kuma warakane ga abinda ke cikin zukata, shedan kuma shine sababin dukkanin sharrurruka da bace bace. Sai Allah Ya umurci dukkanin mai karatun Alkur'ani da cewa ya nemi kariya daShi daga shedan jefaffe da waswasinsa da rundunarsa.
Kuma malamai sunyi ijma'i akan cewa isti'aza bata daga cikin (ayoyin) Alkur'ani mai girma, shi yasa ma ba'a rubutataba a cikin Alkur'nan da aka rubuta.
Ma'anar: «أعوذ بالله» shine: ina neman mafaka kuma ina rikon Allah kariya Shi kadai.
Ma'anar «من الشيطان» daga kowane mai yawan girman kai mai yawan kangara daga aljannu da mutane wanda zai kawar da ni daga yiwa Ubangijina biyayya da karanta littafinSa.
Ma'anar «الرجيمِ» wato korarre daga rahamar Allah.
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ (1)
Ma'ana: Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai.
(Sharhi): Suratul fatiha an ambacetane da wannan sunan saboda da itane ake bude Alkur'ani mai girma, kuma ana ambatonta da Almathani saboda karantata da akeyi a cikin kowace raka'a, kuma tana da wasu sunayen na dabam.
An fara karanta Alkur'anine da sunan Allah domin neman taimakonSa, (lafazin) (اللهِ) (kuwa) sunane ga Uban giji (Allah) - Mai yawan Albarka da daukaka- abin bauta bisa cancanta, sabanin waninSa. Kuma Shine sunan Allah (Madaukaki) mafi kebantuwa gareShi ba'a ambaton wani da shi koma bayanSa (tsarki ya tabbata gareShi)
Ma'anar (الرَّحْمَنِ) (wato) ma'abucin gamammiyar Rahama, wanda rahamarSa ta yalwaci dukkanin halittu
Ma'anar (الرَّحِيمِ) (wato mai yawan jin kai) ga muminai. Wadannan sunaye ne guda biyu daga cikin sunayen Allah (madaukaki) wadanda suke kunsheda tabbatar da sifan Rahama ga Allah(madaukaki) kamar yadda yake dacewa da girmanSa.
الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ (2)
Ma'ana:"Dukkan godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai (2)
(Sharhi):Wannan yabone ga Allah da dukkanin sifofinSa wadanda dukkansu sifofi ne na kamala, kuma yabone gareShi game da ni'imominSa na fili da na boye, wanda ya shafi duniya da lahira. A cikin (wannan ayar) akwai umurnin (Allah) ga bayinSa na su gode maSa, shine wanda ya cancanci (godiya) Shi kadai, Shine kadai wanda Ya kagi halitta, kuma wanda Yake tsayuwa akan gudanar da al'amuransu, wanda Yake Mai reno ga dukkanin halittunSa da ni'imominSa ga waliyyanSa kuma da imani da kyakkyawan aiki.
الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ (3)
Ma'ana:"Mai rahama Mai jinqai (3)
(Sharhi) Ma'anar (الرَّحْمَنِ) (wato) ma'abucin gamammiyar Rahama, wanda rahamarSa ta yalwaci dukkanin halittu. Ma'anar (الرَّحِيمِ) (wato mai yawan jin kai) ga muminai. Wadannan sunayene guda biyu daga cikin sunayen Allah (madaukaki).
مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ (4)
Ma'ana:" Mamallakin ranan sakamako (4)
(Sharhi) Shi (Allah) tsarkakakken (sarki) Shi kadai yakeda mulkin ranar alkiyama, (shi wannan ranan ) shine ranan sakamako akan ayyuka. Kuma cikin karatun musulmi ga wannan ayar akowace raka'a daga sallolinsa (akwai) tunatarwa gareshi game da ranar karshe, kuma akwai kwadaitarwa gare shi akan yin tanadi na kyawawan ayyuka da kuma kamewa daga sabo da munanan ayyuka.
إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ (5)
Ma'ana:" Kai kaxai muke bautawa kuma Kai kaxai muke neman taimakon Ka (5)
(Sharhi) wato: lallai mu muna kebance Ka da bauta Kai kadai, kuma muna neman taimako daga gare Ka Kai kadai cikin dukkan al'amuran mu, saboda dukkan al'amura a hannunKa suke, babu wanda ke mallakan koda kwayar zarra daga ciki.
Kuma a cikin wannan ayar akwai dalili kan cewa lallai bai halatta ga bawa ya aiwatar da wani nau'i na bauta ba kamar; addu'a, neman agaji, yanka da dawafi face ga Allah Shi kadai. Kuma a cikin (bautar Allah Shi kadai) akwai warakar zuciya daga cutar ratayuwa ga wanin Allah. Kuma (waraka ne) daga riya da jiji da kai da girman kai.
اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ (6)
Ma'ana:" Ka shiryar da mu zuwa ga hanya madaidaiciya (6)
(Sharhi): Ka nuna mana kuma Ka shiryar da mu kuma Ka datar damu zuwa ga tafarki madaidaici, kuma Ka tabbatar da mu akan sa har mu sadu da Kai, wannan shine musulunci wanda shine bayyanannen tafarki wanda ke sadarwa zuwa ga yardan Allah kuma izuwa ga aljannarSa wanda manzonSa kuma annabinSa na karshe (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) yayi kira zuwa gareshi. Saboda haka babu wata hanya da bawa (zai bi) ya rabauta face dauwama a kansa (wato wannan tafarkin)
صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا الضَّالِّينَ (7)
Hanyar wadanda Kayi ni'ima a garsu ba ta wadanda aka yiwa fushi ba kuma ba ta batattu ba (7)
(Sharhi) ma'ana: tafarkin wadanda kayi ni'ima a garesu daga annabawa da siddikai da shahidai da salihai, domin sune ma'abuta shiriya da istikama, kada Ka sanya mu daga cikin wadanda suka shiga tafarkin wadanda akyi wa fushi. Wadanda suka fahimci gaskiya amma basu yi aiki da itaba, wadanda sune yahudawa da (duk) wanda yake kan aiki irin nasu. Batattu kuma sune wadanda basu samu shiriya ba sakamakon jahilcin su saboda haka sai suka bata daga tafarki (na gaskiya) wadannan kuwa sune nasara da (duk) wanda ya bi hanyarsu.
A cikin wannan addu'ar akwai waraka ga zuciyar musulmi daga cutar jayayya da (gaskiya) da jahilci da bata, kuma (a cikin sa) akwai abinda ke nuna cewa ni'ima mafi girma - ba tareda togewaba - itace ni'imar musulunci. Don haka duk wanda ya (kasance na gaba cikin sanin gaskiya da aiki dashi, to shine ya fi cancantan kasancewa akan tafarki madaidaici. Kuma babu shakka sahabban manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) su suka fi dacewa da hakan a cikin mutane bayan annabawa (aminci ya tabbata a garesu) saboda haka ayar tana nuni zuwaga falalarsu, da girman matsayinsu (Allah Ya kara musu yarda).