المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس الأول: مقدمات مهمة في طلب العلم


عبد الله الداخل
_9 _November _2013هـ الموافق 9-11-2013م, 09:33 AM
مقاصد الدرس الأول
· المقصد الأول: بيان شدة الحاجة إلى الهداية، وأنها لا تكون إلا بالعلم الصحيح، وأن إهمال العلم يعرّض صاحبَه لخطر الضلال.
· المقصد الثاني: بيان عداوة الشيطان للإنسان وحرصه على إضلاله.
· المقصد الثالث: بيان فضل العلم، والتحذير من العلم الذي لا ينفع.
· المقصد الرابع: بيان معالم المنهج الصحيح لطلب العلم، والميزان الذي توزن به طرق طلب العلم.
· المقصد الخامس: بيان المنهج المقترح لدراسة العقيدة.
· المقصد السادس: بيان أهمية دراسة سير المجدّدين.
· المقصد السابع: ترجمة الإمام المجدد محمد بن عبد الوهاب رحمه الله.
· المقصد الثامن: التعريف برسالة ثلاثة الأصول وأدلتها.
===========================================================================

الشرح

الحاجة إلى الهداية
· لا نجاة للعبد ولا للأمة إلا بما يهديهم الله عز وجل به كما قال الله عز وجل في الحديث القدسي: [يَا عِبَادِي كُلُّكُمْ ضَالٌّ إِلَّا مَنْ هَدَيْتُهُ فَاسْتَهْدُونِي أَهْدِكُمْ] رواه مسلم من حديث أبي ذر رضي الله عنه.
o وهذا يشمل جميع ما يحتاجون إلى الهداية فيه، والهداية أصلها العلم.
· أول وصية وصى الله بها الناس عند بدء هذه الحياة الدنيا ما تضمنه قوله تعالى: ﴿قُلْنَا اهْبِطُوا مِنْهَا جَمِيعًا فَإِمَّا يَأْتِيَنَّكُمْ مِنِّي هُدًى فَمَنْ تَبِعَ هُدَايَ فَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ﴾[البقرة: 38].
· وقد ضمن الله تعالى لمن اتبع هداه أن لا يخاف ولا يحزن، وأن لا يضل ولا يشقى، وأن يخرجه من الظلمات إلى النور وأن يهديه سبل السلام وأن ينجيه مما يخاف، وهذا وعد صادق للفرد والأمة.
o قال الله تعالى: ﴿فمن تبع هداي فلا يضلّ ولا يشقى﴾ [البقرة: 38]، وقال: ﴿إِنَّ هَذَا الْقُرْآنَ يَهْدِي لِلَّتِي هِيَ أَقْوَمُ﴾[الإسراء: 9]، وقال: ﴿يهدي به الله من اتبع رضوانه سبل السلام ويخرجهم من الظلمات إلى النور بإذنه ويهديهم إلى صراط مستقيم﴾[المائدة: 16].
· ونحن قد جاءنا أعظمُ الهدى وهو القرآن الكريم خير كتاب أُنزِل، وبعث إلينا نبيُّنا محمد صلى الله عليه وسلم وهو خير نبي أرسل، أحسن الهدي هديه كما ثبت في الحديث الصحيح: (إن أحسن الهدي هدي محمد) وقال الله تعالى عن القرآن: ﴿إِنَّ هَذَا الْقُرْآنَ يَهْدِي لِلَّتِي هِيَ أَقْوَمُ﴾[الإسراء: 9].
o لهذا كانت هذه الأمة خير أمة أخرجت للناس، لأنها أعظم الأمم هداية.
· الهداية مبناها على العلم الصحيح، واتباع رضوان الله عز وجل بطاعة أمره وتصديق وعده والحذر من طاعة الشيطان وحزبه كما قال الله تعالى: ﴿وَمِنَ النَّاسِ مَنْ يُجَادِلُ فِي اللَّهِ بِغَيْرِ عِلْمٍ وَيَتَّبِعُ كُلَّ شَيْطَانٍ مَرِيدٍ (3) كُتِبَ عَلَيْهِ أَنَّهُ مَنْ تَوَلَّاهُ فَأَنَّهُ يُضِلُّهُ وَيَهْدِيهِ إِلَى عَذَابِ السَّعِيرِ (4)﴾[الحج: 3، 4].
· تولّي الشيطان يكون باتباع خطواته، وتصديق ما يعدّ به ويمنّي، وفعل ما يزيّنه من المعاصي كما قال الله تعالى: ﴿وَمَنْ يَتَّخِذِ الشَّيْطَانَ وَلِيًّا مِنْ دُونِ اللَّهِ فَقَدْ خَسِرَ خُسْرَانًا مُبِينًا (119) يَعِدُهُمْ وَيُمَنِّيهِمْ وَمَا يَعِدُهُمُ الشَّيْطَانُ إِلَّا غُرُورًا﴾[النساء: 119، 120].
· أخبر الله تعالى أن أعداءه أولياء للشياطين، وأن الناس حزبان: حزب مع الله وحزب مع الشياطين، وقال: ﴿وَإِنَّ الشَّيَاطِينَ لَيُوحُونَ إِلَى أَوْلِيَائِهِمْ لِيُجَادِلُوكُمْ وَإِنْ أَطَعْتُمُوهُمْ إِنَّكُمْ لَمُشْرِكُونَ﴾[الأنعام: 121].
· العداوة الحقيقية بين الإنسان والشيطان قضية كبيرة بينها الله عز وجل لنا أتم بيان، قال الله تعالى: ﴿وَلَا تَتَّبِعُوا خُطُوَاتِ الشَّيْطَانِ إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُبِينٌ﴾ [الأنعام: 142].
· وبيَّنها النبي صلى الله عليه وسلم بيانا شافيا، بل جاء في صحيح مسلم من حديث جابر بن عبد الله الأنصاري رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه قال: ((إن الشيطان يحضر أحدكم عند كل شيء من شأنه)).
· مِنْ شأن الشيطان حرصه على الإضلال كما قال الله تعالى حكاية عن موسى عليه السلام، قَالَ ﴿هَذَا مِنْ عَمَلِ الشَّيْطَانِ إِنَّهُ عَدُوٌّ مُضِلٌّ مُبِينٌ﴾[القصص: 15]، وقال تعالى: ﴿أَلَمْ أَعْهَدْ إِلَيْكُمْ يَا بَنِي آدَمَ أَنْ لَا تَعْبُدُوا الشَّيْطَانَ إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُبِينٌ (60) وَأَنِ اعْبُدُونِي هَذَا صِرَاطٌ مُسْتَقِيمٌ (61) وَلَقَدْ أَضَلَّ مِنْكُمْ جِبِلًّا كَثِيرًا أَفَلَمْ تَكُونُوا تَعْقِلُونَ (62)﴾[يس: 60-62]، جبلاً: أي خلقاً كثيراً كانوا مجبولين على الفطرة الصحيحة التي فطر الله الناس عليها.
· من آمن بالله واتبع هداه عصمه الله من كيد الشيطان وكفاه وأغناه ﴿أليس الله بكاف عبده﴾[الزمر: 36].
· يحتاج المؤمن إلى اتباع هدى الله في كبير الأمور وصغيرها وحاجته إلى الهداية أعظم من حاجته إلى الطعام والشراب والنفَس؛ لأن فوزه بالثواب ونجاته من العذاب متوقف على الهداية.
· المهتدون يتفاضلون في الهداية تفاضلاً عظيماً ولذلك أمر الله المسلمين أن يسألوه الهداية مراراً كثيرة في اليوم الواحد فلا تصح صلاة مسلم لا يدعو فيها بدعاء ﴿اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ﴾[الفاتحة: 6].
· ما يعترض الإنسان من عوارض الفتن والمحن والشرور والمعاصي والهموم والأحزان والجهل والشك والحيرة وغيرها هي من الظلمات التي وعد الله المؤمنين أن يخرجهم منها.
· لم يترك الله أمراً يحتاج الناس إلى بيانه إلا بيَّنه لهم بما أنزل في كتابه الكريم وبما أرسل به نبيَّه صلى الله عليه وسلم، فقد أكمل الله الدين وأتمه كما قال تعالى: ﴿الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا﴾ [المائدة: 3].
· لما اجتمع الناس في أعظم جمع في حياة النبي صلى الله عليه وسلم في حجة الوداع قال لهم في خطبة الوداع العظيمة: (( وقد تركت فيكم ما لن تضلوا بعده إن اعتصمتم به كتاب الله وأنتم تسألون عني فما أنتم قائلون قالوا نشهد أنك قد بلغت وأديت ونصحت وقال بإصبعه السبابة يرفعها إلى السماء وينكتها إلى الناس اللهم اشهد اللهم اشهد ثلاث مرات ))رواه مسلم من حديث جابر.
· في مستدرك الحاكم وسنن البيهقي وغيرهما من حديث أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه قال: (( إني قد تركت فيكم شيئين لن تضلوا بعدهما: كتاب الله وسنتي ولن يتفرقا حتى يردا علي الحوض )). صححه الألباني.
فضل طلب العلم
· طلب العلم من أفضل القربات إلى الله تعالى.
· العلم أصل كل عبادة، وبيان ذلك أن كل عبادة يؤديها العابد لا تقبل إلا إذا كانت خالصة لله تعالى وعلى سنة النبي صلى الله عليه وسلم، ومعرفة ذلك تستدعي قدراً من العلم.
· معرفة ما يحبه الله وما يكرهه إجمالاً وتفصيلاً لا تكون إلا بالعلم.
· الناس متفاضلون في العلم تفاضلاً كبيراً كما قال الله تعالى: ﴿وَفَوْقَ كُلِّ ذِي عِلْمٍ عَلِيمٌ﴾[يوسف: 76]، وكلما كان الإنسان أكثر علماً بما ينفع كان أكثر فضلاً.
· تواترت الأدلة ببيان فضل العلم وأهله، وفضل طلبه، ورُتِّب على ذلك من الثناء العظيم والثواب الجزيل في القرآن الكريم والسنة النبوية ما يجعل المؤمن حرياً بأن يكون حريصاً على نيل هذا الفضل العظيم مجتهداً في طلبه.
· قال الله تعالى: ﴿يَرْفَعِ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا مِنْكُمْ وَالَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ دَرَجَاتٍ﴾[المجادلة: 11]، فأسند الرفع إليه جل وعلا وتكفل به، والله لا يخلف وعده.
· قال الله تعالى: ﴿إِنَّمَا يَخْشَى اللَّهَ مِنْ عِبَادِهِ الْعُلَمَاءُ﴾[فاطر: 28]، وقال: ﴿قُلْ هَلْ يَسْتَوِي الَّذِينَ يَعْلَمُونَ وَالَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ﴾[الزمر: 9]، وقال: ﴿وَقُلْ رَبِّ زِدْنِي عِلْمًا﴾[طه: 114].
·في الصحيحين من حديث معاوية بن أبي سفيان رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رسول الله صلى الله عليه وسلم: (( مَنْ يُرِدِ اللهُ بِهِ خَيْراً يُفَقِّهْهُ في الدِّينِ )).
· التفقّه في الدين يشمل جميع أبوابه في الاعتقاد والأحكام والأخلاق والآداب والتزكية والجزاء وغيرها.
· عن أَبي هريرة رضي الله عنه: أنَّ رسول الله صلى الله عليه وسلم قَالَ: ((وَمَنْ سَلَكَ طَرِيقاً يَلْتَمِسُ فِيهِ عِلْماً سَهَّلَ اللهُ لَهُ طَرِيقاً إِلَى الجَنَّةِ)) رواه مسلم.
· عن أَبي موسى الأشعري رضي الله عنه قَالَ: قَالَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم:
(( مَثَلُ مَا بَعَثَنِي الله بِهِ مِنَ الهُدَى وَالعِلْمِ كَمَثَلِ غَيْثٍ أصَابَ أرْضاً؛ فَكَانَتْ مِنْهَا طَائِفَةٌ طَيِّبةٌ قَبِلَتِ المَاءَ فَأَنْبَتَتِ الكَلأَ، وَالعُشْبَ الكَثِيرَ، وَكَانَ مِنْهَا أجَادِبُ أمْسَكَتِ المَاءَ، فَنَفَعَ اللهُ بِهَا النَّاسَ، فَشَرِبُوا مِنْهَا وَسَقَوْا وَزَرَعُوا، وَأَصَابَ طَائِفَةً مِنْهَا أُخْرَى إنَّمَا هِيَ قِيعَانٌ؛ لا تُمْسِكُ مَاءً وَلاَ تُنْبِتُ كلأً، فَذلِكَ مَثَلُ مَنْ فَقُهَ في دِينِ اللهِ، وَنَفَعَهُ مَا بَعَثَنِي اللهُ بِهِ، فَعَلِمَ وَعَلَّمَ، وَمَثَلُ مَنْ لَمْ يَرْفَعْ بِذلِكَ رَأسَاً، وَلَمْ يَقْبَلْ هُدَى اللهِ الَّذِي أُرْسِلْتُ بِهِ)). متفقٌ عَلَيْهِ.
· عن أبي الدرداء رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: (( مَنْ سَلَكَ طَرِيقاً يَبْتَغِي فِيهِ عِلْماً سَهَّلَ اللهُ لَهُ طَريقاً إِلَى الجَنَّةِ، وَإنَّ المَلاَئِكَةَ لَتَضَعُ أجْنِحَتَهَا لِطَالِبِ العِلْمِ رِضاً بِمَا يَصْنَعُ، وَإنَّ العَالِمَ لَيَسْتَغْفِرُ لَهُ مَنْ فِي السَّماوَاتِ وَمَنْ فِي الأرْضِ حَتَّى الحيتَانُ في المَاءِ، وَفضْلُ العَالِمِ عَلَى العَابِدِ كَفَضْلِ القَمَرِ عَلَى سَائِرِ الكَوَاكِبِ، وَإنَّ العُلَمَاءَ وَرَثَةُ الأنْبِيَاءِ، وَإنَّ الأنْبِيَاءَ لَمْ يَوَرِّثُوا دِينَاراً وَلاَ دِرْهَماً وَإنَّمَا وَرَّثُوا العِلْمَ، فَمَنْ أَخَذَهُ أَخَذَ بحَظٍّ وَافِرٍ )). رواه أَبُو داود والترمذي.
o ذكر ابن عبد البر في التمهيد أن استغفار الملائكة دليل على أن الله يغفر له إن شاء الله، وقال: (ألا ترى أن طلب العلم من أفضل الأعمال وإنما صار كذلك والله أعلم لأن الملائكة تضع أجنحتها له بالدعاء والاستغفار)ا.هـ.
· أدرك أئمة الهدى من علماء الأمة هذه الحقيقة فاجتهدوا في تعلّم العلم وتعليمه وصبروا على ما أصابهم حتى تبوؤوا المكانة التي رفع الله بها ذكرهم وأعلى شأنهم فكانوا أئمة الدين وأولياء رب العالمين، وآثارهم في بيان فضل العلم مذكورة مشهورة.
· روى عبد الرزاق عن معمر عن الزهري أنه قال: (ما عُبِدَ اللهُ بمثل الفقه).
· قال مطرف بن عبد الله بن الشخِّير: (فضل العلم أحب إليَّ من فضل العبادة، وخير دينكم الورع) رواه الإمام أحمد في الزهد.
· قال سفيان الثوري: (ما أعلم عملاً أفضلَ من طلب العلم وحفظه لمن أراد الله به خيراً) رواه الدارمي.
· وروى ابن عبد البر في جامع بيان العلم وفضله عن عبد الله بن المبارك أنه قال: قال لي سفيان الثوري: (ما يُرادُ الله عزَّ وجل بشيء أفضل من طلب العلم، وما طلب العلم في زمان أفضل منه اليوم)ا.هـ.
· نحن اليوم إنما نتعلم مما ورّثه لنا أئمة الهدى من العلم رواية ودراية؛ فعنهم نتلقى مسائل الاعتقاد، وعنهم نتلقى مسائل الفقه، وعنهم نتلقى معرفة صحيح الحديث من ضعيفه ومن تقبل روايته ومن ترد، وعنهم نتلقى الأخلاق الفاضلة والتزكية والسلوك.
· من صفات العلماء الربانيين أن يجدهم طالب العلم فيما يَحتاج إليه من أبواب الدين أئمةً يقتدى بهم ويتلقى عنهم العلم والهدي.
· روى البيهقي بإسناده إلى الربيع بن سليمان المرادي أنه قال: سمعت الشافعي يقول: (ليس بعد أداء الفرائض شيء أفضلَ من طلب العلم، قيل له: ولا الجهاد في سبيل الله؟ قال: ولا الجهاد في سبيل الله عز وجل).
·وقال مهنا بن يحيى السلمي: قلت: لأحمد بن حنبل ما أفضل الأعمال؟ قال: (طلب العلم لمن صحت نيته) قلت: وأي شيء تصحيح النية؟ قال: ينوي يتواضع فيه وينفي عنه الجهل).
· نقل ابن هانئ في مسائله عن الإمام أحمد أنه قال: (العلم لا يعدله شيء).
· نقل النووي في المجموع اتفاق السلف على أن الاشتغال بالعلم أفضلُ من الاشتغال بنوافل الصوم والصلاة والتسبيح ونحو ذلك من نوافل عبادات البدن.
· صنَّف العلماءُ في فضل العلم وأهله مصنفات عظيمة النفع جليلة القدر، وأفرد له بعضهم أبواباً في بعض كتبهم فأفرد البخاري في صحيحه كتاب العلم وضمنه باباً في فضل العلم، وكذلك فعل الإمام مسلم وأبو داوود والترمذي والنسائي والدارمي وغيرهم كثير.
· وممَّن أفرد فضل العلم بالتصنيف: أبو نعيم الأصبهاني، وأبو العباس المُرْهِبي (أحمد بن علي، من شيوخ أبي نعيم)، وابن عبد البر، وابن القيّم، وابن رجب، وغيرهم.
· لا توجد أمة من الأمم اعتنت بتعلم أحكام دينها كعناية هذه الأمة المباركة؛ فإنها قد بلغت فيه غاية لم تبلغها أمة من الأمم قبلها، واختصها الله فيه بخصائص.
التحذير من العلم الذي لا ينفع
· مما ينبغي أن يُعلم أنَّ العلم منه نافع وغير نافع، وقد استعاذ النبي صلى الله عليه وسلم من علم لا ينفع؛ فعن زيد بن أرقم رضي الله عنه قال: كان من دعاء النبي صلى الله عليه وسلم: (( اللهم إني أعوذ بك من علم لا ينفع، ومن قلب لا يخشع، ومن نفس لا تشبع ومن دعوة لا يستجاب لها )) رواه مسلم.
· وعن جابر رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: (( سلوا الله علماً نافعاً، وتعوذوا بالله من علم لا ينفع ))رواه ابن ماجة.
o التعوذ من العلم الذي لا ينفع دليل على أن فيه شراً يجب التحرز منه.
· ينبغي لطالب العلم أن يعتني بالعلم الذي ينفعه في دينه ودنياه، ويحفظ وقته مما لا ينفعه.
· (العلم الذي لا ينفع) فسّر بتفسيرين: أحدهما: العلوم الضارة، والآخر: عدم الانتفاع بالعلوم النافعة في أصلها لسبب أفضى به إلى الحرمان من بركة العلم.
· من العلوم الضارة: السحر والتنجيم والكهانة وعلم الكلام والفلسفة وغيرها.
· العلوم التي لا تنفع كثيرة ومن أبرز علاماتها مخالفة مؤداها لهدي الكتاب والسنة؛ فكل علم تجده يصد عن طاعة الله أو يزين معصية الله أو يؤول إلى تحسين ما جاءت الشريعة بتقبيحه أو تقبيح ما جاءت الشريعة بتحسينه فهو علم غير نافع.
· الفضول قد يدفع المتعلّم إلى القراءة في ما لا ينفع؛ فيعرّض نفسه للافتتان وهو ضعيف الآلة في العلم.
· قال الله تعالى: ﴿فليحذر الذين يخالفون عن أمره أن تصيبهم فتنة أو يصيبهم عذاب أليم﴾[النور: 63].
· افتتن بعض المتعلّمين بعلم الكلام بعد أن كانوا في عافية منه، وسبب ذلك مخالفة هدى الله تعالى، واتباع غير سبيل المؤمنين.
المنهجية في طلب العلم
· مناهج طلب العلم كثيرة متنوعة؛ لكن لها أصول جامعة ينبغي أن لا يخرج عنها طالب العلم؛ وإلا أضاع وقته وجهده.
· كلّ من أراد أن يتعلّم صنعة من الصنائع فلا بدّ له أن يصحب أستاذاً فيها يتعلّم منه، ويقوّمه إذا أخطأ؛ حتى يشتدّ عوده في تلك الصنعة.
· من تلبّس بلباس أهل العلم وتحدث بلسانهم واستعمل شيئاً من أدواتهم وهو ولم يسلك سبيلهم في تحصيله ورعايته فليس من أهل العلم، وإنما هو جاهل متعالم لا يوثق به ولا يأتمنه من يعرف حاله، بل ما أسهل ما يبيِّن الامتحان كذبَه وادّعاءه.
· المناهج الصحيحة في التعلم تجتمع في أربعة أمور: الإشراف العلمي، والتدرج، والنَّهمة في التعلم، والوقت الكافي.
· يؤخذ العلم شيئاً فشيئاً؛ على مرّ الأيام والليالي؛ بالنهمة والمواصلة والصبر تحت إشراف علمي من عالمٍ بصير بطرق التعلم حتى يجتاز الطالب مرحلة المتوسطين في طلب العلم.
· من أراد أن يكون عالماً وهو لم يسلك طريقة أهل العلم في التعلم فإنه لا يحصل مراده؛ فإن تكلّم في العلم وتصدر مع ذلك فهو جاهل متعالم ضرره أكبر من نفعه.
· سلوك المنهج الصحيح في طلب العلم يفيد طالب العلم في حفظ وقته وجهده ويعرِّفه بمعالم كل علم فيأتيه من بابه ويتعلمه على وجهه الصحيح؛ فإن سار فيه وصل ونجح، وإن تذبذب وانقطع لم يصل فيه إلى ما كان يأمل.
· مسارات طلب العلم لدى العلماء متعددة إلا أن لها ثوابت محددة تجمعها، وهي أن كل علم يؤخذ عن أهله ولكل علم مصادره التي ينهل منها العلماء، وأن طالب العلم يحتاج إلى من يرشده بادئ الأمر حتى يصلب عوده ويشتد، فيعرف ما يأتي وما يذر.
المنهج المقترح لدراسة العقيدة
· تعلم علم العقيدة يسير ولله الحمد، وإذا سار فيه طالب العلم سيراً صحيحاً، اختصر على نفسه كثيراً من الجهد والوقت.
· من المهمّ لطالب علم العقيدة أن يدرس مسائلها بتأنّ وتؤدة، وأن يحرص على حسن فهم المسائل وحفظ أدلتها، ويتعرّف على منهج أهل السنة في تلك المسائل.
· لو مكث الطالب في الباب الواحد أياماً حتى يضبطه جيداً لما كان كثيراً، لأن الرسوخ في فهمه يعينه على حسن فهم ما بعده من الأبواب.
· الأصل في منهج دراسة العقيدة حديث جبريل الطويل، وفي آخره قال النبي صلى الله عليه وسلم: (هذا جبريل أتاكم يعلمكم أمر دينكم)، وفيه مراتب الدين الثلاثة: الإسلام والإيمان والإحسان، وفيه: أشراط الساعة.
· وأوّل ركن من أركان الإسلام: الشهادتان، وبهما يدخل العبد في دين الإسلام؛ فلذلك كان أوّل ما يجب على العبد أن يتعلمّه: التوحيد.
o في الصحيحين من حديث ابن عباس رضي الله عنهما أن النبي صلى الله عليه وسلم لما بعث معاذ بن جبل إلى اليمن قال له: (( إنك تقدم على قوم أهل كتاب فليكن أول ما تدعوهم إليه عبادة الله)). وفي رواية في صحيح البخاري: (( فليكن أول ما تدعوهم إلى أن يوحدوا الله)).
· اخترنا لكم في البداية رسالة ثلاثة الأصول وأدلتها لأنها تضمنت حديث جبريل، وإلا لو درس الطالب متناً آخر يفي بهذا المقصد التعليمي لكفاه إن شاء الله.
· إذا درس طالب العلم شهادة أن لا إله إلا الله دراسة جيدة عرف معنى التوحيد وأقسامه وواجباته وآدابه وما يقدح فيه، وعرف معنى العبادة التي يجب إفراد الله تعالى بها، وأنواعها، وأحوال دخول الشرك في العبادة وما يعتبر شركاً وما ليس بشرك، إلى غير ذلك من المسائل المهمة التي دلت عليها كلمة التوحيد العظيمة.
· وإذا درس شهادة أن محمداً رسول الله صلى الله عليه وسلم دراسة جيدة عرف معنى المتابعة وشروطها وواجباتها وآدابها وعرف معنى البدعة وحكمها، وعرف ما ينقض الشهادتين، وعرف مقتضى شهادة أن محمداً رسول الله صلى الله عليه وسلم من طاعة أوامره واجتناب نواهيه وتصديق أخباره وقبول أحكامه، واعتقاد أن هديه أحسن الهدي في الأمور كلها، وأن محبته مقدمة على محبة النفس والأهل والولد، وعرف أن ما ينافي تحقيق هذه الشهادة فهو مخرج عن دين الإسلام والعياذ بالله.
· الشهادتان أصل الإسلام ومفتاح الدخول فيه، فارتكاب أيِّ أمرٍ ينقضُهما يعدُّ ناقضاً من نواقض الإسلام.
· ثم بعد ذلك ينتقل إلى دراسة مراتب الدين فيدرس أركان الإسلام ومنها الشهادتان، وأركان الإيمان وركن الإحسان.
· غالب مسائل الاعتقاد التي يذكرها الأئمة في كتبهم ترجع إلى أركان الإيمان الستة، حتى إن بعض الأئمة يرتب الكلام في أبواب الاعتقاد على ترتيب أركان الإيمان.
·يوصَى طالب العلم في المرحلة الأولى بدراسة ثلاثة الأصول وأدلتها أو ما يقوم مقامها مما فيه بيان مراتب الدين وشرح التوحيد وكتاب مختصر في شرح أسماء الله الحسنى.
·وفي المرحلة التالية: كتاب التوحيد والعقيدة الواسطية أو ما يقوم مقامهما.
· وفي المرحلة التي تليها: كشف الشبهات، ونواقض الإسلام، والعقيدة الطحاوية والفتوى الحموية والرسالة التدمرية أو ما يقوم مقام هذه الكتب.
· وفي المرحلة التي تليها يقرأ في كتب الاعتقاد المسندة وما كتبه شيخ الإسلام ابن تيمية وتلميذه ابن القيم وغيرهما ممن كتب في الاعتقاد.
· وفي المرحلة التي تليها يوسّع الطالب قراءاته في العقيدة، وليعتنِ بكتب الأئمة المجدّدين في كلّ قرن وما اعترض دعواتهم من فتن الملل والنحل.
· ينبغي أن يُعلم أن المهم هو تحقيق هذه المقاصد التعليمية؛ وأمّا المفاضلة بين المتون والكتب التي تعتني بهذه الموضوعات فهي مما يدخله الاجتهاد واختلاف المسالك، وإذا عرف الطالب المقصود لم ينشغل بمسألة التفضيل بين الكتب والمتون والتذبذب بينها بل كان همّه مجتمع على فهم هذه الموضوعات المهمة ودراسة مسائلها جيداً.
· لا يحسن بطالب العلم الجاد أن يقف كثيراً عند كل ألفاظ المتون حتى يكاد يعربها لأن الإغراق في جزئيات المسائل الجانبية يشغله عن فهم المقصود الذي لأجله يدرس تلك المتون، ويشتت ذهنه ويضعف تركيزه.
· اعتنِ بهذه المسألة جيداً، ولتكن عنايتك متوجهة لفهم المقاصد أولاً، ثم ما تحصِّله بعد ذلك من العلم فهو خير على خير.
· مَنْ فقِه ذلك سهل عليه أن يدرس في الفنّ الواحد متوناً كثيرة، لأنه إذا درس متناً منها فهم مقاصده ومسائله فإذا قرأ متناً آخر في ذلك العلم كانت عنايته متوجهة إلى معرفة ما فيه من زيادة علم، ولم يكن واقفاً عند رسوم الألفاظ.
· تنوّع الاطلاع يحتاجه طالب العلم لكن بعد أن يضبط أصلاً في كل علم.
· من كان يدرس متناً ولا يتمه ثم ينتقل إلى متن آخر وينقطع فإنه يبقى مغبوناً في وقته وجهده محروماً من بلوغ مأموله إلى أن يعاود العزيمة الصادقة فيجتهد في تحصيل العلم على وجهه الصحيح.
· مراعاة التدرج ومتابعة الطلب مهمة جداً لطالب العلم فهي المنهجية الصحيحة في التعلم.
· هذه المتون التي اخترناها لكم هي على سبيل الاجتهاد في التفضيل، وإلا لو درس الطالب كتباً أخرى تعتني بتلك الموضوعات وفهم مقاصدها فإنه يكون قد أتى على المطلوب.
· من ابتلي بمخالطة أصحاب ملّة من الملل أو نِحْلَة من النحل أو تيّار فكري فليعتن بقراءة ما كتبه أهل العلم عنها قراءة جيّدة؛ لأن تعامله معهم فتنة توجب له التيقظ ومعرفة الهدى فيما يعاملهم به.
أهمية دراسة الدعوات الإصلاحية:
· مما يعين على فهم العقيدة فهماً حسناً قراءة تاريخ الدعوات الإصلاحية وسير المجددين من الأئمة.
· القراءة في سير المجددين وكتبهم تعين على فهم دعوة الإسلام كما ينبغي وتُعرِّفُ طالب العلم بما اعترض القائمين عليها من محن وابتلاءات، وما جرت به سنة الله تعالى من نصر من ينصر دينه وجعل العاقبة لأوليائه.
· من أهم فوائد دراسة سير المجدّدين وقراءة كتبهم:
o 1: التعرف على أسباب نجاح دعوة المجددين وانتفاع الناس بها.
o 2: التعرف على أنواع مكائد أعداء الدين في المكر بها لردها وإجهاضها وتنفير الناس منها.
o 3: التعرف على مناهج الأئمة في معالجة هذا الأمر، وما كان هديهم في مواجهة تلك التحديات من أعداء الداخل والخارج، من المنافقين والكافرين.
o تآمر الكفار والمنافقين على محاربة دعوة الإسلام الصحيحة يتجدد ويتنوّع في كل عصر.
o غالب مكائد الأعداء ترجع إلى أنواع إذا ضبطها طالب العلم ودرسها جيدا فهم كثيرا من مسائل الدعوة المعاصرة، وتكشفت له بعض مكائد أعداء الدين اليوم.
o من تأمَّل سِيَر أئمة الدين من المجددين الكبار وغيرهم وجد منهم عناية بارزة بسير الأئمة قبلهم، ومن قرأ كتبهم وجد استشهادهم بحوادث جرت للأئمة قبلهم أمراً ظاهراً.
· هذه المادة لا يحتاج فيها طالب العلم إلى متن يدرسه، لكن ينبغي له أن يقرأ في هذا العلم أو في هذه المادة التاريخية شيئا فشيئا من كتب السير والتراجم وما جمع في سير بعض المجددين من المؤلفات المفردة الخاصة، يقرأ سيرهم قراءة المعتني بفقه أسباب نجاح الدعوة وما كان يعترضهم من عقبات وصعوبات وكيف تصدوا لمكائد الأعداء؟
· المقصد الذي يكون في نفس القارئ عند القراءة مهم جداً في انتفاعه من الكتاب، فالقراءة بغرض الثقافة قد تفيد الطالب في توسيع مداركه وازدياده من المعرفة، لكنها قد لا توصله إلى فقه ما تُنصر به الدعوة وكيف يكون إمدادها وحسن التدبير لها.
· أوَّل ما ينبغي دراسته في ذلك سيرة إمام المجددين صلى الله عليه وسلم، فقد جعل الله سيرته وهديه نبراساً للأئمة ومشكاة يقتبسون منها الهدي القويم في الملمات والشدائد التي تمر بهم، بل قلَّ أن يمر على عالم موقف من مكيدة الأعداء إلا وجد له أصلاً في سيرة النبي صلى الله عليه وسلم.
· ثم يدرس سير المجددين بعده من علماء الصحابة والتابعين ومن تبعهم بإحسان إلى عصرنا هذا.
· وقد روى أبو داوود والحاكم في مستدركه وصححه عن أبي هريرة رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: (( إن الله يبعث لهذه الأمة على رأس كل مائة سنة من يجدد لها دينها ))والحديث صححه جماعة من أهل العلم.
· روى الخطيب البغدادي في تاريخه عن الإمام أحمد أنه قال: (إن الله يقيِّضُ للناس في كل رأس مائة سنة مَن يعلمهم السنن وينفي عن رسول الله صلى الله عليه وسلم الكذب فنظرنا فإذا في رأس المائة عمر بن عبد العزيز وفي رأس المائتين الشافعي).
o لفظ (مَن) في الحديث يحتمل الواحدَ والجماعةَ؛ فقد يقوم بالتجديد واحد، وقد يقوم به جماعة، وقد نص على ذلك جماعة من أهل العلم.
o رُوِي عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه قال: ((يحمل هذا العلم من كل خلف عدوله، ينفون عنه تحريف الغالين، وانتحال المبطلين، وتأويل الجاهلين)) وهذا الحديث روي من حديث أبي أمامة وأبي هريرة وابن عباس وغيرهم وطرقه فيها ضعف بيـِّن.
o هذا الحديث مختلف في تصحيحه وتضعيفه، نُقِل عن الإمام أحمد أنه صححه، وصححه ابن القيم رحمه الله باعتبار تعدد طرقه،ومن أهل العلم من ضعفه ومنهم من حسنه، لكن معناه صحيح.
o يؤيده ما في الصحيحين من حديث عبد الله بن عمرو بن العاص رضي الله عنهما قَالَ: سَمعْتُ رسولَ اللهِ صلى اللهُ عليهِ وَسَلَّمَ يقولُ: (( إِنَّ اللهَ لا يقبضُ العِلمَ انتِزَاعًا يَنتزِعُهُ مِن العِبَادِ، ولَكِنْ يَقْبضُ العِلمَ بقبضِ العُلَمَاءِ حَتى إِذا لَمْ يُبْقِ عَالِمًا اتَّخَذَ الناسُ رءوسًا جُهالاً فَسُئِلُوا فأَفتوا بغيرِ علمٍ فضَلُّوا وَأَضَلُّوا )).
o هذا الحديث يدلك على أن حاجة الناس إلى العلم ماسة وضرورية، لأنهم بحاجة إلى السؤال، فإن وجدوا عالماً سألوه وإن لم يجدوا اتخذوا رءوساً جهالاً فسئلوهم، فالحاجة إلى السؤال باقية.
o ينبغي لطلاب العلم أن يفقهوا هذه المسألة جيدا؛ وهو أنهم اليوم طلاب، وغداً تحتاجهم الأمة؛ فينبغي لهم أن يتأصلوا بالعلم المفيد حتى إذا كانوا في السن والقدر الذي يؤهلهم للإفتاء والتعليم والدعوة إلى الله عز وجل على بصيرة كانوا من خير من يقوم بهذا الأمر.
o قال عبدالله بن عمر رضي الله عنه في أواخر حياته: ( لو كنت أعلم أنكم تحتاجون إليَّ لتفقَّهتُ لكم) وهو من فقهاء الصحابة رضي الله عنه لكنه أراد أن يزداد من التفقه لأجل أن ينفعهم ويزداد من الخير بنشر العلم النافع.
كلام العلماء في تعيين المجددين كثير وفيه اختلاف كبير، لكن من المجددين من عرف لهم كبير أثرهم في الأمة ولهم دعواتهم الإصلاحية الظاهرة ومن أشهر هذه الدعوات دعوة شيخ الإسلام ابن تيمية رحمه الله، ودعوة شيخ الإسلام محمد بن عبد الوهاب رحمه الله.
ترجمة المؤلف رحمه الله
· هو شيخ الإسلام محمد بن عبد الوهاب بن سليمان التميمي.
· ولد فِي بلدة العُيَينةِ من قرى نجد، سنة 1115هـ.
· نشأ نشأةً صالِحة فحفظ القرآن قبل بلوغه عشر سنين، وتتلمذ على والده قاضي العيينة.
· ظهرت عليه أمارات النبوغ من حدّة الذهن وقوة الحفظ وحسن الفهم وعلو الهمة.
· قرأ على صغر سنه كتباً كثيرة في التفسير والحديث والاعتقاد والفقه وغيرها.
· رحل في طلب العلم إلى الحرمين والأحساء والبصرة والزبير.
· كان سريع الكتابة حادّ الذكاء قوي الحفظ جادًّا مقبلاً على العلم والعمل.
· أقبل على كتب شيخ الإسلام ابن تيمية وتلميذه ابن القيم ففهم مقاصدها واختصر بعضها.
· أَسِفَ لما آل إليه حال الناس من غربة الدين وانتشار الشرك والجهل حتى عُبدت الأشجار والأحجار والقبور والجن.
· اتفق مع أمير الدرعية محمد بن سعود على الدعوة إلى التوحيد ونصرة الدين بالحجة والسنان، وتبايعا على ذلك.
· أقام مدرسة لتعليم التوحيد وعلوم الشريعة وألَّفَ لهم المناهج ورتَّبَ لهم الدروس فوفد إليه طلاب العلم وانتشرت دعوة الشيخ المباركة.
· كاتَبَ الشيخ العلماءَ والأمراءَ والوجهاء وأقام الحجج وكشف الشُّبَه.
· استجاب لدعوة الشيخ طائفة من الناس وأيدوه وناصروه، واستنكف آخرون وعادوه وآذوه، واجتهدوا في تنفير الناس عنه ورميه بالعظائم.
· رُفعت راية الجهاد بعد عام 1158هـ ففتح الله لهم القلوب والبلاد وأعلى الله كلمته ونصر أولياءه ودحض الشرك وأهله.
· كان الشيّخ متوليّا أمانة بيت المال وأمور السلم والحرب،وفي عام 1188هـ تركهما وانقطع للعبادة والتعليم إلى أن توفاه الله عز وجل في الدرعية سنة 1206 هـ فرحمه الله رحمة واسعة وألحقه بالصالحين، وجمعنا به في مقعد صدق عند مليك مقتدر.
رسالة ثلاثة الأصول وأدلتها
· المؤلف له رسالة أخرى باسم: (الأصول الثلاثة) أكثر اختصاراً من هذه الرسالة مطبوعة ضمن مجموع مؤلفاته، حذف منها بعض العبارات، وحديث جبريل الطويل.
· رسالتا المسائل الأربع والمسائل الثلاث أُلحقتا برسالة ثلاثة الأصول، وليست منها في الأصل كما نبه إلى ذلك شيخنا الشيخ عبد الله بن جبرين رحمه الله.
o كان هذا التصرف سبباً مباركاً في كثرة تدريس هاتين الرسالتين الوجيزيتن النافعتين.
· هذا الدليل هو لشرح رسالة (ثلاثة الأصول وأدلتها)، وهذه الرسالة مشهورة متداولة وقد طبعت كثيراً وشرحها كثير من أهل العلم في بلادنا، بل جعلوها من أول ما يبدؤون به تعليم العقيدة.
· والأصول الثلاثة: هي معرفة الله ومعرفة نبيه صلى الله عليه وسلم ومعرفة دين الإسلام بالأدلة.
· كان الشيخ رحمه الله يكرر تأليف هذه الرسالة ويلقنها للعامة، وفي بعض نسخها اختلاف يسير وموضوعها واحد.
o منها رسالة باسم (الأصول الثلاثة) طبعت من دون المسائل الأربع والمسائل الثلاث وليس فيها حديث جبريل الطويل وبينها وبين هذه النسخة اختلاف يسير.
o ومنها رسالة أكثر اختصاراً باسم (أصول الدين الثلاثة) أدخل في بعضها ألفاظاً عامية ليقربها للعامة.
o من تلاميذ الشيخ والمعتنين بتدريس هذه الأصول الثلاثة من اختصرها وصاغها بأسلوب السؤال والجواب كما فعل ذلك الشيخ: عبد العزيز بن محمد أبو حبيب الشثري وعلق عليها حاشية يسيرة وأسمى كتابه (المصقول في التعليق على مختصر ثلاثة الأصول) وقد اعتنى بنشرها حفيده الشيخ سعد بن ناصر الشثري حفظه الله.
· هذه الرسالة غلب عليها اسم (ثلاثة الأصول) حتى صار علماً عليها.
· هذه الإضافة (ثلاثة الأصول) صحيحة فصيحة، وهي مستعملة في نجد إلى اليوم.
o قال المبرد في المقتضب: (تقول: هذه ثلاثة أثوابٍ؛ كما تقول: هذا صاحب ثوبٍ؛ فإن أردت التعريف قلت: هذه ثلاثة الأثواب، كما تقول: هذا صاحب الأثواب؛ لأن المضاف إنما يعرفه ما يضاف إليه فيستحيل هذه الثلاثة الأثواب؛ كما يستحيل هذا الصاحب الأثواب، وهذا محال في كل وجه، ألا ترى أن ذا الرمة لما أراد التعريف قال:

أمنزلتي مَيٍّ سلامٌ عليكما...هل الأزمن اللائي مضين رواجع
وهل يرجع التسليم أو يدفع البكا...ثلاث الأثافي والرسوم البلاقع

وقال الفرزدق:

ما زال مُذْ عَقَدَتْ يداهُ إزارَه...ودنا فأدرك خمسة الأشبار

فهذا لا يجوز غيره)ا.هـ.
o ذكر الحريري في "أوهام الخواص" أنهم يقولون: ما فعلت الثلاثة الأثواب؛ فيعرّفون الاسمين ويضيفون الأول منهما إلى الثاني؛ قال: (والاختيار أن يعرّف الأخير من كل عدد مضاف، فيقال: ما فعلت ثلاثة الأثواب؟ وفيم انصرفت ثلاثمائة الدرهم؟).
· الأصول جمع أصل وهو ما يُبنى عليه، وسميت ثلاثة الأصول بهذا الاسم لأنه الدين مبني على معرفتها.
أهمية رسالة ثلاثة الأصول وأدلتها
· كان الشيخ يلقّن الطلبة والعامة هذه الرسالة ليدرسوها ويحفظوها ويعقلوا معانيها.
· الأصول الثلاثة هي: معرفة العبد ربه جل وعلا، ومعرفة نبيه صلى الله عليه وسلم، ومعرفة دين الإسلام بالأدلة.
· هذه الأصول الثلاثة هي المسائل الثلاث التي يسأل عنها العبد في قبره: من ربك؟ وما دينك؟ ومن نبيك؟
· عن البراء بن عازب رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: (إن الميتَ ليسمع خَفْق نعالهم إذا وَلَّوْا مدبرين حين يقال له: يا هذا، مَنْ ربُّك ؟ وما دِينُك ؟ ومن نَبِيُّكَ ؟). رواه أبو داوود وغيره.
· جميع مسائل الدين ترجع إلى هذه الأصول الثلاثة.

طاهر جبريل دكو
_28 _November _2013هـ الموافق 28-11-2013م, 01:12 PM
DARASI NA DAYA MUHIMMIYAR MUKADDIMA AKAN NEMAN ILIMI

MANUFOFIN DARASI NA DAYA
Manufa ta daya: bayani gameda tsananin bukatuwa zuwaga shiriya, da cewa lallai (ita shiriya) bata samuwa face ta hanyar ingantaccen ilimi, da kuma cewa yin sakaci da (neman) ilimi yana bijiradda mai yin sa ga hadari wanda shine bata.
Manufa ta biyu:bayani gameda adawan shedan ga mutum da kwadayinsa na batar dashi.
Manufa ta uku: bayani gameda falalan ilimi da gargadi game da ilimi mara anfani.
Manufa ta hudu: bayani game da alamomin hanyar neman ilimi ta kwarai da mizanin da ake auna hanyoyin neman ilimi.
Manufa ta biyar:bayani game da hanyar da ake bada shawara ga (mai neman ilimin) akida ya rika.
Manufa ta shida: bayani gameda muhimmancin karanta tarihin mujaddadai.
Manufa ta bakwai: tarjaman shugaba mujaddadi Muhammadu dan Abdulwahhab Allah Yayi masa rahama.
Manufa ta takwas: bayani gameda risalar thalathatul usul da dalilansa.

SHARHI
BUKATUWA ZUWA GA SHIRIYA
Babu tsira ga bawa hakanan ma ga al'umma face da abinda Allah (mai girma da buwaya) Yake shiryar dasu dashi, kamar yadda Allah(mai girma da buwaya) Ya fadi a cikin hadisin kudusi:
((يَا عِبَادِي كُلُّكُمْ ضَالٌّ إِلَّا مَنْ هَدَيْتُهُ فَاسْتَهْدُونِي أَهْدِكُم))
Ma'ana:" Yaku bayiNa dukkaninku batattune saidai wanda Na shiryar dashi saboda haka ku nemi shiriyaTa In shiryar daku" imamu Muslimne ya ruwaitoshi daga hadisin Abu Zarrin (Allah Ya kara masa yarda).
Kuma wannan zai kunshi dukkanin abinda suke bukatan shiriya a cikinsa, asalin shiriya kuwa shine ilimi. Farkon wasiyyaar da Allah Yayi ga mutane a farkon wannan rayuwar ta duniya itace abinda ke kunshe acikin fadin Allah (madaukaki)
﴿قُلْنَا اهْبِطُوا مِنْهَا جَمِيعًا فَإِمَّا يَأْتِيَنَّكُمْ مِنِّي هُدًى فَمَنْ تَبِعَ هُدَايَ فَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ﴾ [البقرة: 38]
Ma'ana:"Mukace ku sauka daga gareta gaba daya, to idan shiriya tazo muku daga gareNi, duk wanda yabi shiriyaTa to babu tsoro garesu kuma bazasuyi bakin cikiba" Q 2: ayata 38.
Hakika Allah (madaukaki)Ya lamuncewa duk wanda yabi shiriyarSa da cewa kada ya ji tsoro kuma ba zaiyi bakin cikiba, bazai bataba kuma bazai tabeba, kuma zai fiddashi daga duffai zuwa haske, kuma zai shiryar dashi tafarkin aminci kuma zai tseratar dashi daga abinda yake tsoro. Wannan alkawari ne na gaskiya ga daidaiku da al'umma. Allah (madaukaki) Yace:
فَمَنِ اتَّبَعَ هُدَايَ فَلَا يَضِلُّ وَلَا يَشْقَى [طه 123]
Ma'ana:"Duk wanda yabi shiriyaTa to bazai bataba kuma bazai tabeba" Q20ayata123. Kuma Allah Yace:
إِنَّ هَذَا الْقُرْآنَ يَهْدِي لِلَّتِي هِيَ أَقْوَمُ [الإسراء 9]
Ma'ana:"Lallai wannan Alkur'anin Yana shiryarwa zuwaga (hanya) wacce itace mafi daidai" Q17ayata9. Kuma Yace:
يَهْدِي بِهِ اللَّهُ مَنِ اتَّبَعَ رِضْوَانَهُ سُبُلَ السَّلَامِ وَيُخْرِجُهُمْ مِنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ بِإِذْنِهِ وَيَهْدِيهِمْ إِلَى صِرَاطٍ مُسْتَقِيمٍ [المائدة 16]
Ma'ana:" Allah Yana shiryar da wand ya bi yardansa Dashi (Alkur'ani) zuwa ga hanyoyin aminci, kuma Yana fitar dasu daga duffai zuwa haske da izininSa, kuma Yana shiryar dasu zuwa ga tafarki madaidaici" Q5ayata16.
Kuma mu hakika mafi girmar shiriya tazo mana, itace Alkur'ani mai girma, mafi alherin littafin da aka saukar, kuma aka aiko mana Annabinmu Muhammadu (s.a.w) kuma shine mafi falala cikin dukkanin Annabawanda aka aiko, mafi kyawun shiriya kuma, (iatce) shiriyarsa kamar yadda ya tabbata acikin ingantaccen hadisi:
((إن أحسن الهدي هدي محمد))
Ma'ana:"Lallai mafi kyawun shiriya, shiriyar Muhammadu"kuma Allah Yace: – gameda Alkur'ani-
إِنَّ هَذَا الْقُرْآنَ يَهْدِي لِلَّتِي هِيَ أَقْوَمُ [الإسراء 9]
Ma'ana:"Lallai wannan Alkur'anin Yana shiryarwa zuwaga (hanya) wacce itace mafi daidai" Q17ayata9.
Wannan ne yasa wannan al'ummar tafi sauran al'ummu alkhairi saboda tafisu shirya. Shirya ta ginune akan ingantaccen ilimi, da bin yardan Allah (mai girma da buwaya) ta hanyar bin abubuwanda Yayi umurni dasu da gaskata alkawarinSa da nisantan biyayya ga shedan da jama'arsa kamar yadda Allah Yace:

وَمِنَ النَّاسِ مَنْ يُجَادِلُ فِي اللَّهِ بِغَيْرِ عِلْمٍ وَيَتَّبِعُ كُلَّ شَيْطَانٍ مَرِيدٍ (3) كُتِبَ عَلَيْهِ أَنَّهُ مَنْ تَوَلَّاهُ فَأَنَّهُ يُضِلُّهُ وَيَهْدِيهِ إِلَى عَذَابِ السَّعِيرِ [الحج 3و4]
Ma'ana:" Akwai daga cikin mutane wanda yake yin musu gameda sha'anin Allah bada wani ilimi ba, kuma yana biyar ko wane shedani mai taurin kai (3) an wajabta masa cewa duk wanda ya jibince shi, to lallai ne sai ya batar da shi kuma ya shiryar da shi zuwa azabar sa'ir (4) Q22ayata3da4.
Jibintan shedan yakan kasancene ta hanyar bibiyar tafarkinsa, da gaskata abinda yake alkawartawa kuma yake burantawa, da kuma aikata abinda yake kawatawa na ayyukan sabon (Allah) kamar yadda Allah (madaukaki) Yace:
وَمَنْ يَتَّخِذِ الشَّيْطَانَ وَلِيًّا مِنْ دُونِ اللَّهِ فَقَدْ خَسِرَ خُسْرَانًا مُبِينًا (119) يَعِدُهُمْ وَيُمَنِّيهِمْ وَمَا يَعِدُهُمُ الشَّيْطَانُ إِلَّا غُرُورًا [النساء 119و120]
Ma'ana:"Kuma wanda ya riki shedan majibinci koma bayan Allah, to hakika ya bata bata bayyananniya (119) yana yi musu alkawari kuma yana sanya musu buri, alhali shedan baya yi musu wa'adin komai face rudi" Q4ayata119 da120.
Allah (madaukaki) Ya bada labarin cewa lallai makiyanSa masoyane ga shedan, kuma mutane sun kasu zuwa kungiyoyi biyu; kungiyar da take tare da Allah, da kungiyar da take tareda shedanu, kuma Yace:
وَإِنَّ الشَّيَاطِينَ لَيُوحُونَ إِلَى أَوْلِيَائِهِمْ لِيُجَادِلُوكُمْ وَإِنْ أَطَعْتُمُوهُمْ إِنَّكُمْ لَمُشْرِكُونَ [الأنعام 121]
Ma'ana:"Kuma lallai ne shedanu suna yin ishara ga masoyansu domin suyi jayayya daku, kuma idan kuka yi musu da'a hakika lallai ku mushirikaine" Q6ayata121.
Adawa ta hakika tsakanin mutum da shedan babban al'amari ne da Allah (mai girma da buwaya) Ya bayyana shi garemu mafi cikan bayani. Allah (madaukaki) Yace:
وَلَا تَتَّبِعُوا خُطُوَاتِ الشَّيْطَانِ إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُبِينٌ [الأنعام 142]
Ma'ana:"Kuma kada ku bi hanyoyin shedan, lallai shi agareku makiyine mai bayyananniyar kiyayya" Q6ayata142.
Kuma Annabi (s.a.w) yayi bayaninsa bayani mai warkarwa, bahaka kawai bama, yazo cikin sahihu muslim daga hadisin Jabir dan Abdullahi Al'ansari (Allah Ya kara musu yarda) daga Annabi (s.a.w) lallai yace:
((إن الشيطان يحضر أحدكم عند كل شيء من شأنه))
Ma'ana:"Lallai shedan yana halartowa dayan ku ayayin da yake komai cikin sha'aninsa"

Yana daga sha'anin shedan, kwadayinsa gameda batarwa kamar yadda Allah (madaukaki)Ya fadi yana mai hakaito mana (kissar Annabi) Musa (Amincin Allah Ya tabbata agareshi):
هَذَا مِنْ عَمَلِ الشَّيْطَانِ إِنَّهُ عَدُوٌّ مُضِلٌّ مُبِينٌ [القصص 15]
Ma'ana:"Wannan aikin shedanne, lallai shi makiyine mai batarwa mabayyani" Q28ayata15. Kuma (madaukaki) Yace:
أَلَمْ أَعْهَدْ إِلَيْكُمْ يَا بَنِي آدَمَ أَنْ لَا تَعْبُدُوا الشَّيْطَانَ إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُبِينٌ (60) وَأَنِ اعْبُدُونِي هَذَا صِرَاطٌ مُسْتَقِيمٌ (61) وَلَقَدْ أَضَلَّ مِنْكُمْ جِبِلًّا كَثِيرًا أَفَلَمْ تَكُونُوا تَعْقِلُونَ (62) [يس 60-62]
Ma'ana:"Ashe banyi muku umurni na alkawari ba ya ku yayan Adam? Cewa kada ku bauta wa shedan, lallai shi makiyine agareku mai bayyananniyar kiyayya (60) kuma ku bauta miNi, wannan itace hanya madaidaiciya (61) kuma lallai (shedan) ya batar da jama'a da masu yawa daga cikinku baku kasance masu hankaltaba?(62) Q36ayata60-62.
(Ma'anar) jama'a da yawa: (wato) halitta masu yawa wadanda aka haliccesu akan fidira ingantacciya wacce Allah Ya halicci mutane akai, wanda yayi imani kuma yabi shiriyarSa (wato Allah) sai Allah Ya kareshi daga kaidin shedan ya iyar masa ya kuma wadatar dashi.
أليس الله بكاف عبده [الزمر 36]
Ma'ana:"Ashe Allah bai zama mai isa ga bawansaba"Q39ayata36.
Mumini yana bukatan bin shiriyar Allah cikin dukkan al'amura babba da karami kuma bukatuwarsa zuwaga shiriya tafi girma samada bukatuwarsa zuwaga abinci da abinsha da nunfashi, saboda rabautansa da sakamako da kubutarsa daga azaba ya dogarane akan shiriya.
Shiryayyu sunada fifiko atsakaninsu fifiko mai girma, shi yasa Allah Ya umurci musulmai da cewa su rokeshi shiriya sau adadi mai yawa a kowane yini, sbaoda haka sallar musulmi bata inganta in baiyi addu'a acikin taba yace:
اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ [الفاتحة 6]
Ma'ana:"Ka shiryar damu hanya madaidaiciya"Q1ayata6.
Abinda ke bijirowa mutum na fitintinu da jarrabawa da sharrurruka da kurakurai da bakin ciki da tashe tashen hankali da jahilci da shakka da dimuwa da wanin haka duk suna daga cikin duffan da Allah Yayi alkawarin fitarda muminai daga ciki. Allah bai bar wani al'amari ba wanda mutane ke bukatan bayani game dashi face Yayi bayanin shi garesu da abinda Ya saukar acikin littafinSa kuma abinda Ya aiko manzonSa (s.a.w) dashi. Hakika Allah Ya kammala addini kuma Ya cikatashi kamar yadda Allah (madaukaki) Yace:
الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا [المائدة 3]
Ma'ana:"Ayau Na kamala muku addininku kuma na cika ni'imata agareku kuma Na yarda da musulunci ya zama addini agreku" Q5ayata3.
Yayin da mutane suka taru a taro mafi girma arayuwar Annabi (s.a.w) a hajjin bankwana, yace musu a hudubar bankwanan nan mai girma.
((وقد تركت فيكم ما لن تضلوا بعده إن اعتصمتم به، كتاب الله، وأنتم تسألون عني، فما أنتم قائلون؟» قالوا: نشهد أنك قد بلغت وأديت ونصحت، فقال: بإصبعه السبابة، يرفعها إلى السماء وينكتها إلى الناس «اللهم، اشهد، اللهم، اشهد» ثلاث مرات)) رواه مسلم من حديث جابر.
Ma'ana:"Hakika acikinku na bar abinda bazaku taba bataba matukar kunyi riko dashi, littafin Allah. Kuma za'a tambayeku game dani menene zaku fadi? Sai sukace: mun shaida cewa lallai kai hakika ka isar (da manzanci) kuma ka sauke (amana) kuma kayi nasiha, saiya daga dan yatsansa manuniya yana dagata sama sannan yana nuni da ita ga mutane yana cewa:"ya Allah Ka shaida ya Allah Ka shaida, har sau uku" Muslimne ya ruwaitoshi daga hadisin Jabir.
Yazo a cikin almustadrak na Hakim da sunan na Baihaki da waninsu, daga hadisin Abuhuraira (Allah Ya kara masa yarda) daga Annabi (s.a.w) yace:
(( إني قد تركت فيكم شيئين لن تضلوا بعدهما: كتاب الله وسنتي ولن يتفرقا حتى يردا علي الحوض )). صححه الألباني.
Ma'ana:"Lallai ni na bar abu biyu a cikinku baza ku bataba a bayansu, littafin Allah da sunnata, kuma bazasu taba rabuwaba har sai sun gangara zuwa gareni a tafkin" Albani ya ingantashi.

FALALAN NEMAN ILIMI
Neman ilimi yana daga cikin mafi girman ayyukan dake kusantarwa zuwa ga Allah (madaukaki).
Ilimi shine tushen duk wata ibada, abin nufi da haka shine, dukkanin bautanda mai bauta zai gabatar baza a karbetaba har sai ta kasance tsarkakakkiya ga Allah (madaukaki) kuma bisa sunnar Annabi (s.a.w) kuma sanin wannan yana bukatan wani gwargwado na ilimi.
Sanin abinda Allah Yake so da abinda Yake ki a jumlace da fassale baya yuwuwa saida ilimi.
Mutane sunada fifiko a cikin ilimi fifiko mai girma, kamar yadda Allah Yace:
وَفَوْقَ كُلِّ ذِي عِلْمٍ عَلِيمٌ [يوسف: 76]،
Ma'ana:"Kuma a sama da kowane ma'abucin sani akwai masani" Q12ayata76.
Duk sa'adda bawa ya kasance mafi sani gameda abu mai anfani, zai kasance mafi falala.
Dalilai sun yawita wani bayan wani gameda falalan ilimi da ma'abutansa da falalan nemansa, kuma dalilai daga Alkur'ani da sunnonin Annabi sunzo da yabo mai girma da lada mai kauri wanda zai sa mumini ya zama mai kwadayin samun wannan falalan mai girma kuma mai kokari wurin nemansa. Allah (madaukaki) Yace:

يَرْفَعِ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا مِنْكُمْ وَالَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ دَرَجَاتٍ [المجادلة: 11]،
Ma'ana:"Allah Yana daukaka wadanda sukayi imani daga cikinku da wadanda aka bawa ilimi darajoji" Q58ayata11.
SaiYa jingina daukakawar zuwa gareShi kuma Ya dauki nauyin hakan kuma Allah baYa saba alkawarinSa. Allah (madaukaki) Yace:

إِنَّمَا يَخْشَى اللَّهَ مِنْ عِبَادِهِ الْعُلَمَاءُ [فاطر: 28]
Ma'ana:"Kawai malamai ne ke tsoron Allah daga cikin bayinSa" Q35ayata28. Kuma Yace:
قُلْ هَلْ يَسْتَوِي الَّذِينَ يَعْلَمُونَ وَالَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ [الزمر: 9]
Ma'ana:"Kace shin wadanda suka sani zasuyi daidai da wadanda basu saniba? Q39ayata9.
وَقُلْ رَبِّ زِدْنِي عِلْمًا [طه: 114]
Ma'ana:"Kuma kace ya Ubangiji Ka kara mini ilimi" Q19ayata114.
A cikin sahihul Bukhari da Muslim daga hadisin Mu'awiya dan Abu Sufiyanu (Allah Ya kara musu yarda) yace; lallai Manzon Allah (s.a.w) yace:
((من يرد الله به خيرا يفقهه في الدين))
Ma'ana:"Wanda Allah ke nufinsa da alhri, Yana bashi fahimta a cikin addini".
Fahimtan addini ya game dukkanin babukansa, na akida da hukunce hukunce da dabi'u da ladubba da tsarkin zuciya da sakamako da waninsu.
Daga Abu Huraira (Allah Ya kara masa yarda) yace: lallai Manzon Allah (s.a.w) yace:
((ومن سلك طريقا يلتمس فيه علما، سهل الله له به طريقا إلى الجنة)) رواه مسلم.
Ma'ana:"Kuma wanda ya shiga wata hanya yana neman ilimi a cikinta, Allah zai sauwake masa hanya da ita – hanyar neman ilimin- wata hanya zuwa Aljanna" Muslim ne ya ruwaitoshi.
Daga Abu Musa Al'ash'ari (Allah Ya kara masa yarda) yace: Annabi (s.a.w) yace:

((مثل ما بعثني الله به من الهدى والعلم، كمثل الغيث الكثير أصاب أرضا، فكان منها نقية، قبلت الماء، فأنبتت الكلأ والعشب الكثير، وكانت منها أجادب، أمسكت الماء، فنفع الله بها الناس، فشربوا وسقوا وزرعوا، وأصابت منها طائفة أخرى، إنما هي قيعان لا تمسك ماء ولا تنبت كلأ، فذلك مثل من فقه في دين الله، ونفعه ما بعثني الله به فعلم وعلم، ومثل من لم يرفع بذلك رأسا، ولم يقبل هدى الله الذي أرسلت به)) متفقٌ عَلَيْهِ.
Ma'ana:"Misalin abinda Allah Ya aikoni dashi na shiriya da ilimi, kamar misalin ruwan samane mai yawa daya sauka akan kasa, daga cikinta akwai tsaftatacciya wacce ta karbi ruwan sai ta tsirar da abincin dabbobi da ciyayi masu yawa, daga cikinta kuma akwai wacce ta kasance fako (wacce take iya rike ruwa) ta rike ruwa sai Allah Ya anfanar da mutane, sai suka sha kuma suka shayar dashi kuma sukayi noma. Sai ya sauka akan wani sashi –na kasa-wacce ta kasance fako bata rike ruwa kuma bata yabanya. Wannan shine misalin wanda yayi fahimta cikin addinin Allah kuma ya anfana da abinda Allah Ya aikoni dashi, yayi karatu kuma ya karantar, da kuma wanda yayi ko in kula da wannan" Bukhari da Muslimne suka ruwaitoshi.
Daga Abuddarda'i (Allah Ya kara masa yarda) yace: naji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa:
(( مَنْ سَلَكَ طَرِيقاً يَبْتَغِي فِيهِ عِلْماً سَهَّلَ اللهُ لَهُ طَريقاً إِلَى الجَنَّةِ، وَإنَّ المَلاَئِكَةَ لَتَضَعُ أجْنِحَتَهَا لِطَالِبِ العِلْمِ رِضاً بِمَا يَصْنَعُ، وَإنَّ العَالِمَ لَيَسْتَغْفِرُ لَهُ مَنْ فِي السَّماوَاتِ وَمَنْ فِي الأرْضِ حَتَّى الحيتَانُ في المَاءِ، وَفضْلُ العَالِمِ عَلَى العَابِدِ كَفَضْلِ القَمَرِ عَلَى سَائِرِ الكَوَاكِبِ، وَإنَّ العُلَمَاءَ وَرَثَةُ الأنْبِيَاءِ، وَإنَّ الأنْبِيَاءَ لَمْ يَوَرِّثُوا دِينَاراً وَلاَ دِرْهَماً وَإنَّمَا وَرَّثُوا العِلْمَ، فَمَنْ أَخَذَهُ أَخَذَ بحَظٍّ وَافِرٍ )). رواه أَبُو داود والترمذي.
Ma'ana:"Wanda ya shiga wata hanya yana neman ilimi acikinta, Allah zai sauwake masa hanya zuwa gidan aljanna, kuma lallai mala'iku suna sauke fukafukansu domin nuna yarda da abida yake aikatawa, kuma lallai malami duk abinda ke cikin sama da kasa suna roka masa gafara harda kifi a cikin ruwa, kuma falalan malami akan mai bauta kamar falalar wata ce akan sauran taurari, kuma lallai su malamai magada Annabawane, kuma lallai su Annabawa basu gadar da dinari ko dirhami ba, kawai sun gadar da ilimi ne, duk wanda yayi riko dashi yayi riko da kaso cikakke" Abu Dawuda da Tirmizi ne suka ruwaitoshi.
Ibnu Abdil barri ya anbata a cikin littafinsa Attamhid yana mai cewa; neman gafarar mala'iku (ga dalibin ilimi) daliline dake nuna cewa insha Allahu Allah zai gafarta masa. Kuma yace; baka ganiba cewa shi neman ilimi yana daga cikin ayyuka mafi girma? Kuma hakan ya kasancene kawai –Allah Shine mafi sani-saboda mala'iku na sauke fukafukansu gareshi tareda yi masa addu'a da istigfari.
Jagororin shiriya daga malaman al'umma sun riski wannan hakikar, sai suka zage dantse wurin neman ilimi da karantar dashi kuma suka yi hakuri akan abinda ke samunsu har saida suka samu matsayinda Allah Ya daukaka anbatonsu kuma Ya daukaka sha'aninsu, sai suka kasance shugabanni a cikin addini kuma waliyyan Ubangijin talikai, maganganunsu kuma gameda falalan neman ilimi ambataccene kuma shahararre.
Kuma Abdurrazzak ya ruwaito daga Ma'amar daga Zuhuri lallai yace: "ba'a bautawa Allah da abinda ya kai fikihu ba, Mudarrif bnu Abdillahi bnu Shshikhkhir yace:" falalar ilimi tafi soyuwa agareni bisa ga falalar ibada, kuma mafi alherin addininku shine tsantseni" Ahmad ne ya ruwaitoshi a cikin (littafin) zuhudu.
Sufiyanu Ththauri yace:" ban san wani aiki da yafi neman ilimi da haddaceshi falala ba, ga wanda Allah ke nufinsa da alheri" Darimi ne ya ruwaitoshi.
Kuma Ibnu Abdilbarri ya ruwaito a cikin (littafinsa) jami'u bayanil ilmi wa fadlihi daga Abdullahi Ibnul Mubarak yace: Sufiyanu Ththauri yace mini:"ba'a taba nufin Allah da wani abu da yafi falala samada neman ilimi, kuma babu wani zamani da neman ilimi ya fi falala a cikinsa kamar yau"
Mu ayau muna koyon iliminmu ne daga abinda malaman mu na shiriya suka gado mana na ilimi riwaya da fahimta, saboda haka daga garesu muke daukan mas'alolin akida, kuma daga garesu muke daukan mas'alolin fikihu, kuma daga garesu muke samun ilimin sanin ingantaccen hadisi daga mai rauninsa da kuma wanda za'a karbi riwayarsa daga wanda ba'a karba daga gareshi. Kuma daga garesu muke daukan halayen kwarai da tsarkake zuciya da dabi'u.
Daga cikin sifofin malamai rabbaniyyai, shine dalibin ilimi ya taraddasu jagorori ababen koyi a cikin abubuwanda yake bukata daga babukan ilimi kuma ana daukan ilimi da shiriya daga wurinsu.
Imamul Bayhaki ya ruwaito da isnadinsa zuwaga Rabi'u binu Sulaiman Almuradi yace; naji Shafi'i yana cewa:"bayan farilla babu wani abinda ya fi neman ilimi falala. Sai akace har jihadi saboda Allah? Yace; har jihadi saboda Allah (mai girma da buwaya).
Mihna binu Yahya Assulami yace: nace wa Ahmad binu Hanbali: wani aikine yafi falala? Sai yace: "neman ilimi ga wanda niyyarsa ta kyautata" nace: menene kyautata niyya? Sai yace: yayi niyyar tawalu'u a cikinsa kuma da kore wa kansa jahilci"
Ibnu Hani'i ya nakalto daga cikin tanbayoyin da yayi ga Imamu Ahmad lallai yace:"ilimi ba abinda yake daidai dashi"
Imamu Nnawawi ya nakalto a cikin (littafinsa) -Almajmu'u- ittifakin magabata akan cewa shagaltuwa da ilimi yafi falala sama da shagaltuwa da nafilfilun azumi da sallah da tasbihi da makamancin haka daga nafilfilun ibada na gangan jiki.
Malamai sun rubuta littattafai masu girma masu matukar anfani akan falalan ilimi da (falalan) ma'abutansa, wasunsu kuma sun ware masa babuka a cikin wasu daga littattafansu. Imamul Bukhari ya ware kitabul ilmi a cikin sahihinsa sai ya sanya babi gameda falalan ilimi, hakanan ma Imamu Muslim da Abu Dawuda da Tirmizi da Nasa'i da Darimi da wasunsu da yawa.
Daga cikin wadanda suka ware littafi musamman don bayani gameda falalan ilimi, akwai Abu Nu'aim Al'asbahani, da Abul Abbas Almurhibi Ahmad bin Aliyu, daga cikin malaman Abu Nu'aim, da Ibnu Abdilbarri, da Ibnulkayyim, da Ibnu Rajab da wasunsu.
Ba'a taba samun wata al'umma ba data kula da ilimin addininta kamar kulawar wannan al'ummar mai albarka, domin ita hakika takai wani matsayi da babu wata al'ummar da ta kai gareshi kafin ita, kuma Allah Ya kebance ta da wasu sifofi na musamman.
GARGADI GAMEDA ILIMI MARA ANFANI
Daga cikin abinda ya kamata a sani shine, lallai ilimi daga cikinsa akwai mai anfani akwai mara anfani, hakika Annabi (s.a.w) ya nemi tsari daga ilimi mara anfani.
Daga Zaidu binu Arkam (Allah Ya kara masa yarda) yace: yana daga cikin addu'ar Annabi (s.a.w):
(( اللهم إني أعوذ بك من علم لا ينفع، ومن قلب لا يخشع، ومن نفس لا تشبع ومن دعوة لا يستجاب لها )) رواه مسلم.
Ma'ana:"Ya Ubangijina, lallai ni ina neman tsarinKa daga ilimi mara anfani, da zuciya da bata da natsuwa, da rai wanda baya koshi, da addu'ar da ba'a amsarta" Muslimne ya ruwaitoshi.
Daga Jabir (Allah Ya kara masa yarda) yace: Manzon Allah (s.a.w) yace:
(( سلوا الله علماً نافعاً، وتعوذوا بالله من علم لا ينفع ))رواه ابن ماجة.

Ma'ana:" Ku roki Allah ilimi mai anfani, kuma ku nemi tsarin Allah daga ilimi mara anfani" Ibnu Maja ne ya ruwaitoshi.
Neman tsari daga ilimi mara anfani daliline da yake nuna cewa cikin sa akwai sharri wanda ya wajaba a kiyaye.
Ya kamata ga dalibi ya kula da ilimin da zai anfaneshi a cikin addininsa da duniyarsa kuma ya kiyaye lokacinsa daga abinda ba zai anfaneshiba.
Ilimi mara anfani an fassarashi da tafsirai biyu; daya daga ciki; ilmummuka masu cutarwa, dayan kuma rashin anfanuwa da ilmummuka masu anfani a asalinsu sakamakon wani sababi da ya zama masa sanadin haramtuwa daga albarkan ilimi kamr ilmummuka masu cutarwa; sihiri, da bugun kasa, da bokanci, ilmul kalam, da falsafa da waninsu.
Ilmummuka marasa anfani suna da yawa, daga mafi bayyanan alamominsu shine ya zama abinda yake kaiwa gareshi yana sabawa shiriyar Alkur'ani da sunna, saboda haka duk iliminda ka samu yana kangiya daga yiwa Allah da'a, ko kuma yana kawata sabon Allah, ko yana kaiwa ga kyautata abinda shari'a tazo da munanashi, ko munana abinda shari'a tazo da kyautata shi, to wannan ilimi ne mara anfani.
Raran (lokaci) yakan sa mai neman ilimi ya karanta abinda ba azi anfaneshiba, sakamakon haka sai ya bijiradda kansa ga fitinuwa alhali shi mai raunine a cikin ilimi. Allah (madaukaki) Yace:
فَلْيَحْذَرِ الَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنْ أَمْرِهِ أَنْ تُصِيبَهُمْ فِتْنَةٌ أَوْ يُصِيبَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ [النور: 63]
Ma'ana:"To wadanda ke sabawa umurnin sa suyi hattara kada wata fitina ta samesu ko kuma wata azaba mai radadi" Q24ayata63.
Wasu daga cikin daliban ilimi sun fitinu da ilmul kalam bayan sun kasance kubutattu daga gareshi, kuma sababin haka shine sabawa shiriyar Allah (madaukaki) da kuma bin tafarkin da bata muminai ba.
HANYOYIN NEMAN ILIMI
Hanyoyin neman ilimi suna da yawa kuma sun bambanta, sai dai suna da asulla da ke hadesu wadanda bai kamata dalibin ilimi ya fita daga cikin su ba, inba haka ba kuma sai ya sha wahalar banza kuma ya bata lokacinsa.
Duk wanda yake nufin ya koyi wata sana'a daga cikin sana'o'i babu makawa gareshi sai ya abuci masani a cikinta wanda zai koya daga gareshi kuma ya sashi a hanya idan yayi kuskure har sai ya samu kwarewa akan wannan sana'ar.
Wanda ya tufatu da tufafin malamai, yayi Magana irin tasu, yayi aiki da wani abu daga abubuwansu alhali shi bai shiga tafarkinsu ba game da nemansa da kula dashi to shi baya daga cikin ma'abuta ilimi, kawai shi jahiline mai da'awar malanta ba'a yarda dashi kuma duk wanda ya san halinsa bazai aminta da shi ba, a'a (irin wannan) cikin sauki jarrabawa ke bayyana karyarsa da da'awarsa ta karya.
Hanyoyin kwarai a neman ilimi sun tattarune a cikin abubuwa hudu; kulawa ta ilimi, tadarruji (wato fara neman ilimi daga na kasa zuwa na sama), himma cikin neman ilimi da wadataccen lokaci.
Ilimi ana daukansane kadan kadan yau da gobe cikin dare da yini tareda himma ta dindindin da hakuri karkashin kula ta ilimi na malami masani gameda hanyoyin neman ilimi har sai dalibi ya wuce marhalan yan tsakatsaki a cikin neman ilimi. Wanda duk yake son ya zama malami amma bai shiga tafarkin ma'abuta ilimi ba a cikin neman ilimi, to lallai bazai cimma burinsa ba, idan tareda hakan yayi magana cikin (al'amarin) ilimi kuma ya gabatar da kansa to shi jahiline mai karyar ilimi cutarwarsa tafi anfanarwansa.
Rikon ingantacciyar hanya a cikin neman ilimi yana fa'idantadda dalibin ilimi wurin (takaita masa wahala) da kiyaye lokacinsa kuma ya sanar dashi alamomin kowane ilimi, saboda haka sai ya shigo masa ta mashigansa kuma ya koyeshi tafuska ingantacciya, idan ya tafi akai sai ya kai ga bukata kuma ya ci nasara. Amma idan ya yita inda inda ya kuma yanke, to ba zai cimma burinsa ba.
Mashiga ta neman ilimi a wurin malamai yana da yawa, sai dai suna da ka'idoji iyakantattu dake hadesu, sune; kowane ilimi ana daukansane daga ma'abutansa, kuma kowane ilimi yana da masdaroinsa wanda daga ciki malamai ke ciroshi, kuma mai neman ilimi yana bukatan wanda zai shiryarda shi tun daga farkon al'amari har zuwa kashin bayansa yayi karfi (a cikin neman ilimi) sai ya san abinda zai dauka da abinda zai bari.
HANYAR DA AKE BADA SHAWARI GA MAI KARATUN AKIDA YA RIKA
Alhamdu lillahi, shi ilimin akida koyonsa abu ne mai sauki. Idan dalibin ilimi ya tafi akansa tafiya mai kyau zai takaitawa kansa wahalhalu masu yawa da lokaci.
Daga cikin abubuwa mafiya muhimmanci ga dalibin ilimin akida shine, ya karanta mas'alolinta sannu sannu cikin nutsuwa, kuma ya kwadaitu zuwaga kyakkyawar fahimta ga mas'aloli da haddace dalilansu, kuma ya san akidar ahlu-ssunna a cikin wadannan mas'alolin.
Da dalibi zai tsaya a babi guda na tsawon kwanaki don yaga cewa ya fahimce shi da kyau da wannan dadewan bai baci ba, saboda zurfafawa cikin fahimtansa zai taimaka masa wurin fahimtar abinda ke biye dashi na babuka.
Asali gameda hanyar da za'abi don koyon ilimin akida shine hadisin Jibrilu mai tsayinnan, akarshensa Annabi (s.a.w) yace:
((هذا جبريل أتاكم يعلمكم أمر دينكم))،
Ma'ana:"Wannan Jibirilu ne ya taho domin ya karantar daku al'amarin addininku" a cikinsa akwai (anbaton) martabobi uku na addini; musulunci, imani da ihsani. Kuma a cikinsa akwai (anbaton) alamomin tashin alkiyama
Kuma rukunin farko daga rukunnan musulunci shine shahadu guda biyu (wato La'ilaha illa llahu Muhammadun rasulullahi) kuma da sune bawa ke shiga addinin musulunci, shi yasa abu na farko daya wajaba ga bawa ya fara dadshi shine, karatun tauhidi.
Yazo cikin sahihul Bukhari da Muslim daga hadisin Ibnu Abbas (Allah Ya kara musu yarda) yace lallai Annabi (s.a.w) yayinda ya tura Mu'azu dan Jabal zuwa (kasar) Yaman, yace masa:
(( إنك تقدم على قوم أهل كتاب فليكن أول ما تدعوهم إليه عبادة الله)). وفي رواية في صحيح البخاري: (( فليكن أول ما تدعوهم إلى أن يوحدوا الله)).
Ma'ana:" Lallai kai zaka tafine zuwaga wasu jama'a ma'abuta littafi, saboda haka abu na farko da zaka kirasu zuwa gareshi ya kasance bautan Allah" a wata riwayar " saboda haka abu na farko da zaka kirasu zuwa gareshi ya kasance kadaita Allah" sahihul Bukhari.
Mun zaba muku risalar thalathatul usul da dalilanta ne afarko saboda ta kunshi hadisin Jibril, amma, da dalibi zai karanta wani matani wanda zai biya bukata gameda wannan manufar ta karantarwa da zai wadatar in Allah Yarda.
Idan dalibin ilimi ya karanci la'ilaha illa llahu karatu mai kyau, to zai fahimci ma'anar tauhidi da karkasuwansa, da wajibansa da ladubbansa da abinda ke illatashi, kuma ya fahimci ma'anar ibada wacce ya wajaba a kadaita Allah (madaukaki) a ckinta, da nau'ukanta da yadda shirka ke shiga cikin ibada, da abinda ake la'akari dashi a matsayin shirka da abinda ba shirkaba da wanin wadannan (ab ubuwan) cikin muhimman mas'alolin da kalmar tauhidi ke nuni zuwa garesu.
Idan ya karanci shahadatu anna Muhammadan rasulullahi karatu mai kyau, sai ya san ma'anar mutaba'a (wato bautan Allah akan karantarwan Annabi (s.a.w)) da sharuddanta da wajibanta da ladubbanta, kuma zai san ma'anar bidi'a da hukuncinta da abinda ke warware shahadunnan biyu. Kuma zai san abinda shahadatu anna Muhammadan rasulullahi ke hukuntawa na bin umurninsa da nisantan abubuwanda yayi hani da gaskata maganganunsa da karban hukunce hukuncensa da kudurce cewa shiriyarsa itace mafi kyawun shiriya cikin komai, kuma sonsa shine abin gabatarwa akan son kai da iyalai da yaya. Kuma zai san cewa duk abinda ke kore tabbatuwan wadannan shahadun guda biyu, to yana fitarwa daga addinin musulunci. Allah Ya tsaremu.
Shahadunnan guda biyu sune asalin addinin musulunci, kuma mabudin shiga cikinsa. Saboda haka ana kirga aikata duk wani abu da yake warwaresu daga cikin abubuwa masu warware musulunci.
Sannan bayannan sai ya kaura zuwaga karatu akan martabobin addini, sai ya karanta rukunnan musulunci wanda daga cikinsu akwai shahadunnan guda biyu, da rukunnan imani, da rukunin ihisani.
Galibin mas'aloli na akida da malamai ke anbato a cikin littattafansu yana komawane zuwaga rukunnan imani guda shida, harma wani daga cikin malamai yana rattaba maganganu a cikin babukan akida bisa tartibin rukunnan imani.
Kuma ana yiwa dalibin dake marhalar farko wasiyya da cewa ya karanta (littafin) thalathatul usul da dalilansa ko kuma abinda ke iya maye gurbinsa gameda abinda ke cikinsa.
Bayani gameda martabobin addini, da sharhin tauhidi, da littafi takaitacce a kan sharhin sunayen Allah kyawawa.
A cikin marhalar da ke biye; (ana wasiyya da karanta) kitabu-ttauhidi da akidatul wasidiyya ko abinda zai maye gurbinsu.
A marhalar da ke biye kuma; kashfu-shshubuhat, nawakidul Islam, akidatu-ddahawiyya da fatawal hamawiyya, risalatu-ttadmuriyya ko abinda ke iya maye gurbin wadannan littattafan.
A marhalar da ke biye kuma; yayi karatu a cikin littattafan akida masu isnadi da abubuwanda Shaikhul islam Ibnu taimiyya da dalibinsa Ibnul kayyim suka rubuta da wanin su daga wadanda suka yi rubutu akan akida.
A marhalar da ke biye kuma; sai dalibi ya fadada karatunsa a cikin akida kuma ya bada kula ga littattafan malamai mujaddadai a cikin kowane karni da bubuwan da suka ci karo da da'awarsu daga fitintinun addinai da darikoki.
Ya kamata a san cewa muhimmin abu shine tabbatarda wadannan manufofin na karantarwa amma yin mukarana tsakanin wadannan matanoni da littattafan don gano wanda yafi kula da wadannan maudu'an abune da ijtihadi zai shiga cikinsa, kuma hanyoyi sun bambanta. Kuma idan dalibi ya san manufan to ba zai shagaltu da matsalan fifitawa tsakanin littattafai da matanoni ba, da kai komo tsakaninsu, a'a himmarsa kawai zata tattaru ne kawai akan fahimtan wadannan muhimman maudu'an da karanta mas'alolinsu da kyau.
Baya kyautuwa ga dalibin ilimi mai yi da gaske ya tsaya sosai akan dukkanin lafuzzan matanoni har sai ya nemi kaiwa ga li'irabinsu, saboda zurfafawa cikin sassan mas'aloli na gefe zai shagaltar dashi daga fahimtan manufanda a sanadinsa ne yake karatun wadannan matanonin, kuma zai rarraba masa hankali ya raunana tarkizinsa.
Ka kula kwarai da wannan mas'alar, kuma kulawarka ta kasance ta fuskanta zuwa ga fahimtan manufofi a karon farko, sannan abinda zaka samu na ilimi bayan nan, wannan alkhairine akan alkhairi.
Duk wanda ya fahimci wannan, zaiyi sauki gareshi ya karanta matanoni masu yawa a fanni daya. Saboda idan ya karanta matani guda daga cikinsu, zai fahimci makasudinsa da mas'alolinsa, idan ya karanta wani matani a cikin wannan ilimin, to kulawarsa zata koma kan sanin abinda ke cikinsa na Karin ilimi kuma bazai tsaya akan lafuzza kawai ba.
Dalibi yana bukatan duba littattafai mabanbanta, amma sai ya kiyaye asali cikin ko wane ilimi. Duk wanda ya kasance yana karatun wani matani amma baya gamashi sai ya kaura zuwa wani matanin, to wannan zai yi asaran lokacinsa da wahalarsa kuma wanda aka haramtawa isa ga burinsa, har sai ya sake himma ta gaskiya kuma ya kara kwazo wurin neman ilimi akan ingantacciyar fuska.
La'akari da tadarruji da cigaba cikin neman ilimi abune mai matukar muhimmanci ga dalibin ilimi, wannar itace ingantacciyar hanya ta neman ilimi. Wadannan matanonin wadanda muka zaba muku, kawai a babin ijtihadi ne cikin fifitawa (tsakaninsu) amma da dalibi zai karanta wasu littattafan da suke bada muhimmanci ga wadannan maudu'an kuma ya fahimci wadannan manufofin, sai ya kai ga bukata.
Duk wanda aka jarrabeshi da cudanya da ma'abuta wani addini daga wadannan addinan ko wata darika daga wadannan darikokin ko kuma hargowar fikirori, to sai ya nemi agaji ta hanyar karanta abubuwanda ma'abuta ilimi suka rubuta gameda shi karatu mai kyau, saboda mu'amalarsa da su (wato addinai da darikoki) fitinace da zata wajabta masa ya kasance a fadake kuma ya san shiriya cikin abinda yake mu'amala dasu a cikinsa.
MUHIMMANCIN KARANTA (TARIHIN) DA'AWAR KAWO GYARA
Daga cikin abinda yake taimakawa wurin fahimtar akida fahimta mai kyau, karanta tarihin da'awar (da malamai sukayi) don kawo gyara, da tarihin mujaddadai daga cikin malamai.
Karanta tarihin mujaddadai da littattafansu yana taimakawa wurin fahimtan da'awar musulunci kamar yadda ya kamata, kuma yana sanar da dalibin ilimi abubuwan da suka bijiro ga wadanda suka tsayu akan da'awar na; bala'o'i da jarrabawowi, da abinda sunnar Allah ta tafi akai na taimakon duk wanda ya taimaki addininSa da kuma sanya kyakkyawan karshe ga waliyyanSa.
KADAN DAGA CIKIN MUHIMMAN FA'IDOJIN KARANTA TARIHIN MUJADDADAI DA LITTATTAFANSU.
Na daya: sanin sabubban cin nasarar da'awar mujaddadai da anfanan mutane da ita.
Na biyu: sanin nau'uka (dabamdabam) na kaidin makiya addini na kulle kullen makirci don maida da'awar, da batata, da koran mutane daga gareta.
Na uku: Sanin hanyoyin da malamai sukabi domin magance wannan al'amarin, da abinda ya kasance shiriyarsu domin fuskantar wadannan kalubalen daga makiya na cikin (gida) da na waje daga munafukai da kafirai.
Temakekeniyan kafirai da munafukai akan yakan da'awar musulunci ingantacciya cikin sabuntuwa da caccanzuwa yake a kowane zamani.
Galibin kaidin makiya yana komawane zuwa ga (wasu) nau'uka, idan dalibin ilimi ya kiyayesu kuma ya karancesu da kyau zai fahimci matsalolin da'awa masu yawa a wannan zamanin. Kuma wasu daga cikin kaidojin makiya a yau su bayyana gareshi.
Duk wanda ya lura da tarihin manyan malamai mujaddadai da wasunsu zai tarar cewa kulawarsu da tarihin malamai magabata abune da yake a fili.
Wannan maudu'in (wato tarihin mujaddadai) dalibin ilimi baya bukatan wani matani (na musamman) da zai karanta, saidai ya kamata ya karanta littattafan tarihi da tarjamomin da (littattafanda) aka tara tarihin wasu mujaddadai a cikinsa daga wallafe wallafen da aka ware musamman (domin haka). Ya karanta tarihansu karatun mai lura da fahimtan sababin cin nasarar da'awarsu, da abubuwanda suka bijiro musu na matsaloli da wahalhalu, da hanyar da suka bi don magance kaidin makiya.
Manufar da ya kamata ta kasance a ran makaranci a yayin karatu abune mai matukar mhuimmanci a cikin anfanuwarsa daga littafi, saboda haka karatu da nufin samun wayewar kai yakan iya anfanan dalibi cikin fadada fahimtarsa da karin sani, sai dai akwai yiwuwan bazai iya kai shi ga fahimtar abin da da'awa zata ci nasara dashi ba, da kuma yadda za'a fadada da'awa a kuma kyautata ta.
Farkon abin karantawa daga cikin haka shine siran shugaban mujaddadai Annabi (s.a.w) hakika Allah Ya sanya siransa da shiriyarsa fitila mai haske ga malamai wacce suke samun shiriya daga gareta mikakkiya yayinda suka fada cikin fitintinu da tsanani, bama haka kawaiba zaiyi wuya wani abu na kaidin abokan gaba ya faru da wani malami face ya sama masa asali daga siran Annabi (s.a.w).
Sannan sai ya karanta tarihin mujaddadai na bayansa daga malamai cikin sahabbai da tabi'ai da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa wannan zamanin namu.
Kuma hakika Abu Dawuda ya ruwaito da Hakim a cikin almustadrak dinsa kuma ya ingantashi daga hadisin Abu Huraira (Allah Ya kara masa yarda) yace: lallai Annabi (s.a.w) yace:
(( إن الله يبعث لهذه الأمة على رأس كل مائة سنة من يجدد لها دينها ))
Ma'ana:"Lallai a farkon ko wane shekara dari Allah Yana tayar da wanda zai sabuntawa wannan al'ummar addininta" hadisin da yawa daga cikin malamai sun ingantashi.
Khadibul Baghdadi ya ruwaito a cikin (littafinsa na) tarihi daga imamu Ahmad yace:"Lallai Allah yana huwace wa mutane wanda zai koyar dasu sunnoni kuma ya korewa manzon Allah karya farkon ko wane shekara dari, da muka duba shekara dari na farko sai ga Umar dan Abdul'aziz, a kan shekara dari biyu kuma sai ga Shafi'i.
Cewa (da Annabi yayi) a cikin hadisin "wanda" yana iya nufin mutum daya kuma yana iya nufin jama'a, saboda haka akwai yiwuwan mutum daya ya tsayu da aikin jaddada addini, kuma akwai yiwuwan jama'a (masu yawa) su tsayu akansa. Hakika malamai da yawa sun nassanta haka.
An ruwaito daga Annabi (s.a.w) lallai yace:
((يحمل هذا العلم من كل خلف عدوله، ينفون عنه تحريف الغالين، وانتحال المبطلين، وتأويل الجاهلين))
Ma'ana:" Adilai na cikin ko wace (jama'a) mai mayewa su su suke daukan wannan ilimin, suna kore jirkitawar masu wuce gona da iri, kwashe kwashen mabarnata da tawilin jahilai" hadisin an ruwaito shi daga haisin Abu Umama da Abu Huraira da Ibnu Abbas da waninsu kuma a cikin hanyoyin sa akwai rauni bayyananne, hadisin anyi sabani gameda ingantashi ko raunanashi. An nakalto daga Imamu Ahmad cewa ya ingantashi, kuma Ibnul Kayyim (Allah Yayi masa rahama) shima ya ingantashi saboda la'akari da yawan hanyoyinsa, kuma daga cikin malamai akwai wadanda suka raunanashi daga cikinsu kuma akwai wanda yace hadisine hasan, saidai ma'anansa ingantaccene.
(hadisin) zai karfafa da abida yazo cikin sahihul Bukhari da Muslim daga hadisin Abdullahi bin Amr binil Aas (Allah Ya kara musu yarda) yace: naji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa:
«إن الله لا يقبض العلم انتزاعا ينتزعه من العباد، ولكن يقبض العلم بقبض العلماء، حتى إذا لم يبق عالما اتخذ الناس رءوسا جهالا، فسئلوا فأفتوا بغير علم، فضلوا وأضلوا»
Ma'ana:"Lallai Allah baYa dauke ilimi ta hanyar zareshi daga bayi zarewa, saidai Yana dauke ilimi ne da daukan (ran) malamai har sai (ta kaiga cewa) babu wanda ya rage masani, sai mutane su riki jagorori jahilai, sai ayi musu tambaya, sai su bada fatawa ba tareda ilimiba, da haka sai su bata kuma su batar"
Wannan hadisin yana nuna maka cewa bukatan mutane zuwaga ilimi (bukatace) babba ta dole, saboda su suna bukatan suyi tanbaya, idan suka samu malami sai su tanbayeshi, idan kuma basu samu ba sai su riki jagorori jahilai, sai su tanbayesu, saboda haka bukatar tambaya tana nan.
Ya kamata daliban ilimi su fahimci wannar mas'alar da kyau, dlili kuwa shine, a yau su dalibaine gobe kuma al'umma zata bukacesu, saboda haka ya kamata su samu ilimi mai anfani saboda idan suka kai shekaru da matsayin da zai basu dammar yin fatawa da karantarwa da kira zuwaga Allah (mai girma da buwaya) bisa basira, sai su kasance daga mafiya alkhairin wadanda zasu tsayu da wannan al'amarin (wato kira zuwaga Allah da karantarwa da fatawa).
Abdullahi dan Umar (Allah Ya kara masu yarda)- akarshen rayuwarsa- yace:" Da nasan cewa zaku bukatu zuwa gareni, dana koyi fikihu dominku" tareda cewa shi yana daga cikin fakihai na sahabbai (Allah Ya kara musu yarda) amma nufinisa shine, daya kara kaimi wurin neman ilimin saboda ya anfanar dasu kuma ya samu karin alkhairi saboda yada ilimi mai anfani.
Maganganun malamai gameda ayyana mujaddadai suna da yawa kuma akwai sabani mai girma, saidai daga cikin mujaddadai akwai wadanda ake ganin tasirinsu a cikin al'umma kuma suna da da'awarsu ta kawo gyara wacce take afili. Daga cikin mafiya shaharan wadannan da'awar, da'war shekhul Islam ibnu Taimiyya (Allah Yayi masa rahama) da da'war shekhul Islam Muhammadu bnu Abdilwahhab (Allah Yayi masa rahama)
TARJAMAN MAWALLAFIN (ALLAH YAYI MASA RAHAMA)
Shine shehin musulunci Muhammadu dan Abdilwahhab dan Sulaiman Attamimi (wato dan kabilar banu tamim)
An haifeshi a garin Uyaina daga cikin garurwan Najad shekarata 1115 bayan hijira.
Ya tashi tashi mai kyau inda ya haddace Alkur'ani kafin ya kai shekaru goma, kuma yayi dalibta a gaban mahaifinsa alkalin (garin) Uyaina.
Alamun bunkasa ta kaifin kwakwaiwa da karfin hadda da kyakkyawar fahimta da karfin himma sun fara bayyana a gareshi.
Tareda karancin shekarunsa ya karanta littattafai masu yawa a tafsiri da hadisi da akida da fikihu da waninsu. Yayi tafiye tafiye don neman ilimi zuwa Makka da Madina da Ahsa'i da Basra da Zubair. Ya kasance mai saurin rubutu mai kaifin basira mai karfin hadda mai yi da gaske mai kifuwa akan ilimi da aiki (dashi) ya kifu akan littattafan shaikhul islam Ibnu Taimiyya da dalibinsa Ibnul Kayyim sai ya fahimci manufofin su ya kuma yi talkhisin wasunsu.
Yayi bakin ciki gameda yadda halin mutane ya koma, ta yadda addini ya zama bako shirka da jahilci suka yadu har saida aka bautawa bishiyoyi da duwatsu da kaburbura da Aljannu.
Yayi ittifaki da shugaban Dir'iyya Muhammadu binu Su'ud akan kira zuwaga tauhidi da taimakon addini ta hanyar hujja da makami kuma suka yiwa juna mubaya'a akan haka.
Ya kafa makaranta domin karantar da tauhidi da ilmummuka na shari'a, ya kuma shirya musu manhaji ya tsara musu darussa, sai daliban ilimi suka dungumo zuwa gareshi, sai da'awar malam mai albarka ta yadu.
Malam yayi rubutu zuwa ga malamai da shuwagabanni da manyan gari ya tsayar da hujja ya yaye shubuha. Wasu jama'a sun amsa da'awar malam suka karfafeshi kuma suka taimakeshi, wasu kuma suka kyamaci (da'awar) suka yi adawa dashi kuma suka cutardashi, kuma suka yi kokari wurin kore mutane daga gareshi da jifansa da munanan kalamai.
An daga tutan jihadi bayan shekara ta 1158 bayan hijira, sai Allah Ya bude musu zukata da garuruwa, sai Allah Ya daukaka kalmarSa Ya kuma taimaki waliyyanSa Ya kuma bata shirka da ma'abutanta.
Malam ya kasance shine mai alhakkin kulawa da baitul mali da al'amuran musulmi da yaki. A shekarata 1188 bayan hijira kuma sai ya barsu ya dukufa akan ibada da karantarwa har Allah (mai girma da buwaya) Ya karbi rayuwarsa a garin Dir'iyya shekara ta 1206 bayan hijira. Allah Yayi masa rahama yalwatacciyar rahama ya riskar dashi ga salihai ya kuma hadamu dashi a mazauni na gaskiya a wurin sarki mai cikakken kudura.
RISALAR THALATHATUL'USUL
Mawallafin yana da wata risalar mai suna Al'usulu-thathalathatu tafi zama takaitacciya samada wannan risalar da aka buga wacce take kunshe a cikin majamu'an littattafansa, ya goge wasu ibarori da hadisin Jibril mai tsayinnan.
Rasaloli biyu Almasa'ilul arba'atu da Almasa'ilu-ththalathatu an riskar dasu ga risalar thalathatul usul kamar yadda malaminmu Abdullahi binu Jibrin (Allah Yayi masa rahama) yayi tanbihi akai. Wannan tasarrufin ya zama sababi mai albarka na yawan karantadda wadannan rasalolin guda biyu takaitattu masu anfani.
Wannan jagoran na sharhin thalathatul -usulne da dalilanta, kuma wannan risalar mashhuriyace kuma tana nan tana jujjuyawa a hanun jama'a, an buga ta bugu da dama kuma malamai da yawa a kasashenmu sun yi sharhinta, bama haka kawai ba, sun sanyata farkon abinda suke farawa dashi cikin karantar da akida.
Kuma Al'usulu ththalathatu (wato asali guda uku) sune: sanin Allah da sanin AnnabinSa (s.a.w) da sanin addinin musulunci da dalilai.
Malam –Allah Yayi masa rahama- ya kasance yana maimaita ta'alifin wannan littafin kuma yana lakkanata ga gama garin mutane, kuma a wasu nuskhokhinta akwai sabani kadan amma maudu'insu daya ne.
Daga cikinsu akwai risala mai suna Al'usulu-thathalathatu an bugata ba tareda Almasa'ilul arba'atu da Almasa'ilu- thathalathatu ba kuma a cikinta babu hadisin Jibril mai tsayin nan, tsakaninta da wannan nuskhar akwai dan sabani kadan.
Daga cikinsu akwai risalar da duk tafisu kankanta da sunan Usuluddin-Athathalathatu ya shigarda lafuzza na ammiyya a cikin wasunsu saboda gama garin mutane su fahimta.
Daga cikin daliban malam akwai wadanda suka bawa karantar da wannan (littafin) -Al'usulu-thathalathatu -kula akwai wanda yayi talkhisinta ya sigantata da uslubin tambaya da amsa, kamar yadda Ashshekh Abdul'aziz bin Muhammad Abu Habib Ashshathri yayi kuma yayi dan ta'aliki a hashiya ya anbaceta da suna Almasqul fitta'liqi ala thalathati l'usul, hakika jikansa Ashshekh Sa'ad bin Nasir Ashshathri – Allah Ya kareshi- ya kula da yadata.
Wannan risalar sunan -thalathatu l'usulu yayi galaba akanta har aka wayi gari ya zama sunanta na yanka.
Wannan idafar -thalathatu l'usulu – ingantacciyace kuma ta dace da fasaha, kuma ana aiki da ita a Najad har zuwa yau.
Almubarrid yace – a cikin littafinsa mai suna almuqtadab ; "kakan ce:" (هذه ثلاثة أثوابٍ) ma'ana: wadannan tufafine guda uku', kamar yadda kakance; (هذا صاحب ثوبٍ) ma'ana; 'wannan ma'abucin tufane', idan kana nufin (magana ne akan) sanannen abu, sai kace:( (هذه ثلاثة الأثواب ma'ana;'wadannan sune tufafin guda uku' kamar yadda zaka ce; ( هذا صاحب الأثواب) ma'ana;'wannan shine ma'abucin tufafin' daomin shi mudaf (wato kalmarda aka jinginata ga wata kalma) kawai kalmarda take jinginuwa gareta ita take mai da ita ma'arifa (wato sananniya) saboda haka bai taba yiwuwa kace: (هذه الثلاثة الأثواب) kamar yadda bai taba yiwuwa kace: (الصاحب الأثواب) wannan bai taba yiwuwa ko ta wace fuska (wato a harshen larabci baya taba yiwuwa a mai da sunaye biyu dukkanin su ma'arifa –ma'ana da sigar sanannu- alhali alakar dake tsakaninsu alakace ta mudafun da mudafun ilaihi, ma'ana kalmar da aka jingina da wacce aka jingina zuwa gareta, saboda haka wacce aka jingina ta zama sananniya –wato ma'arifa- sakamakon jinginuwarta ga sananniya don haka bata bukatan a bata sigar ma'arifa). Shin baka ga ma'abucin (littafinnan mai suna) Arrumah yayin da yayi nufin ta'arifi cewa yayi:


أمنزلتي مَيٍّ سلامٌ عليكما...هل الأزمن اللائي مضين رواجع
وهل يرجع التسليم أو يدفع البكا...ثلاث الأثافي والرسوم البلاقع

Alfarazdak kuma yace:

ما زال مُذْ عَقَدَتْ يداهُ إزارَه...ودنا فأدرك خمسة الأشبار
Saboda haka wanin wannan bai halattaba.
Alhariri ya anbata acikin (littafinsa mai suna) Auhamul khawas cewa lallai suna cewa (ما فعلت الثلاثة الأثواب) sai suna yin ta'arifin sunaye biyu suna jingina daya zuwaga ta biyu, yace; zababben (ra'ayi) shine yin ta'arifin na karshensu daga cikin adadi na (kalmomi) da aka jingina, sai ace;
(ما فعلت ثلاثة الأثواب؟ وفيم انصرفت ثلاثمائة الدرهم؟)
(lafazin) Al'usul jam'ine na asali shine abinda ake gini akansa (wato tushe) kuma an ambaci (wannan risalar) ne thalathatu l'usulu saboda akan fahimtansu ake gina addini.
MUHIMMANCIN THALATHATUL'USUL DA DALILANSA
Malam ya kasance yana lakkanawa dalibai da gama garin (mutane) wannan risalar saboda suyi dirasan ta kuma su haddace ta kuma su fahimci ma'anonin ta.
Asaligudauku sune sanin bawa ga Ubangijinsa (mai girma da daukaka) da sanin AnnabinSa (s.a.w) da sanin Addinin musulunci da dalilai.
Wadannan Asulla guda uka sune tanbayoyin da ake yiwa bawa a cikin kabarinsa; wanene Ubangijinka? Menene addininka? Wanene Annabinka?
Daga Albara' bin Azib (Allah Ya kara musu yarda) yace; lallai Annabi (s.a.w) yace:
(إن الميتَ ليسمع خَفْق نعالهم إذا وَلَّوْا مدبرين حين يقال له: يا هذا، مَنْ ربُّك ؟ وما دِينُك ؟ ومن نَبِيُّكَ ؟). رواه أبو داوود وغيره
Ma'ana:"Lallai mamaci yana jin karan takalmansu idan suka juya bayan suna komawa ayayin da akece masa; ya kai wannan wanene Ubangijinka? Menene addininka? Wanene Annabinka? Abu Dawuda da waninsa ne ya ruwaitoshi
Dukkanin mas'alolin addini yana komowa ne zuwaga wadannan asullan guda uku.