المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : الدرسُ الثانِيَ عشَرَ: نَواقِضُ الإسلامِ


طاهر جبريل دكو
_7 _April _2013هـ الموافق 7-04-2013م, 12:01 PM
الدرسُ الثانِيَ عشَرَ: نَواقِضُ الإسلامِ

إذا عَرَفْنَا أن العَبْدَ لا يَكونُ مُسْلِمًا حتى يَشْهَدَ الشَّهادَتَيْنِ: شَهَادَةَ أن لا إلهَ إلا اللهُ، وشَهَادَةَ أن مُحَمَّدًا رسولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم، فيُوَحِّدَ اللهَ ويَتَّبِعَ الرَّسولَ، وبذلك يَكونُ مُسْلِمًا.
وعَرَفْنَا أن مُقْتَضَى شهادةِ أن لا إلهَ إلا اللهُ هو إخلاصُ العِبادةِ للهِ وَحْدَه، وأن العُبوديَّةَ مَبْناها على المَحبَّةِ والتعظيمِ والانقيادِ.
وعَرَفْنَا أن شهادةَ أن مُحمَّدًا رسولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم تَقْتَضِي مَحَبَّتَهُ وتَصْدِيقَهُ وطاعتَه.
فاعْلَمْ أنَّ مَن يَرْتَكِبْ ما يَنْقُضُ هاتينِ الشَّهادتينِ فهو خارجٌ عن دِينِ الإسلامِ كافرٌ باللهِ جل وعلا وبرسولِه، وإنْ صَلَّى وصامَ وزَعَم أنه مُسلمٌ.
ولذلك فإنَّ مَنْ ينتَفِ عنه أحَدُ هذه الأمورِ: (إخلاصِ العبادةِ للهِ جل وعلا، ومَحَبَّةِ اللهِ، وتَعْظيمِه، والانقيادِ له، ومَحَبَّةِ الرسولِ صلى الله عليه وسلم، وتَصْديقِه وطَاعتِه)؛ فقد انْتَفَى عنه إسْلامُه.
فإن كان هذا الانتفاء أصليًّا أي أنَّ العبدَ لم يقمْ بما تقتضيه الشهادتانِ في أصلِ أمرِهِ فهو كافرٌ أصليّ، فإن كان يُظْهِرُ الإسلامَ مع ذلكَ فهو منافقٌ.

… وأما من كان مسلماً قائماً بما تقتضيه الشهادتان ثم انْتَفَى عنه أحَدُ هذِهِ الأمورِ بعدَ إسلامِه فهو كَافِرٌ مُرْتَدٌّ عن دِينِ الإسلامِ.
وتكونُ الرِّدَّةُ بكلِّ أَمْرٍ قَوْلِيٍّ أو عَمَلِيٍّ أو اعْتِقاديٍّ يَلْزَمُ منه انتفاءُ حقيقةِ شَهادةِ أن لا إلهَ إلا اللهُ وأن مُحمَّدًا رَسولُ اللهِ.
وصُوَرُ النَّواقضِ التي تُخْرِجُ من مِلَّةِ الإسلامِ كثيرةٌ غيرُ مَحْصورةٍ بعَدَدٍ، لكن لها أُصولٌ جامعةٌ هي:
الناقضُ الأولُ: الإلحادُ، وهو إنكارُ وُجودِ اللهِ تعالى.
ومِن صُوَرِه:
• نِسْبةُ الخَلْقِ إلى الطَّبيعةِ.
• اعْتِقادُ قِدَمِ العَالَمِ، وهو أنَّ من المَخْلوقاتِ ما لا أَوَّلَ له في الأَزَلِ.

الناقضُ الثاني: الشِّركُ الأكبرُ، وهو اتخاذُ ندٍّ للهِ جل وعلا، وهو على أنواعٍ:
• النوعُ الأولُ: شِركُ العبادةِ، وهو صَرْفُ نوعٍ من أنواعِ العبادةِ لغيرِ اللهِ جل وعلا؛ كالدُّعاءِ أو الذَّبحِ أو النَّذرِ أو الاستعانةِ أو الاستغاثةِ أو الاستعاذةِ أو غيرِها؛ ومن صُوَرِه:
1: ما يَفْعَلُه عُبَّادُ الأوثانِ والأنبياءِ والأولياءِ من دُعائِهم من دونِ اللهِ، وطَلَبِ الشفاعةِ منهم، وقَضاءِ الحوائجِ وجَلْبِ النفعِ وكَشْفِ الضُّرِّ؛ فمَن فعَلَ ذلك فهو مُشركٌ كافرٌ، وإن زعَمَ أنه مُسلمٌ وأنه يَقولُ: (لا إلهَ إلا اللهُ) وأنه يُصلِّي ويَتصَدَّقُ ويَصومُ ويَحُجُّ ويَفْعَلُ الخَيْرَ؛ فالشِّركُ الأكبرُ مُحْبِطٌ للعَمَلِ مُنافٍ لدينِ الإسلامِ.
2: ما يَفْعَلُه السَّحَرَةُ وبعضُ مَن يَأتيهِم من الذَّبحِ لغيرِ اللهِ عز وجل والاستغاثةِ بالشياطينِ.

• النوعُ الثاني:الشِّركُ في الرُّبوبيَّةِ، ومن صُوَرِه:
1: اعتقادُ بعضِ المُشركينَ في آلهتِهم ومُعَظَّمِيهِم أنَّ لهم تَصَرُّفًا في الكَوْنِ وأنهم يَعْلَمُونَ الغَيْبَ، ويُنَزِّلونَ الغَيْثَ، ويَمْلِكونَ الرِّزقَ، ويَشْفُونَ من الأمراضِ، ويَهَبُونَ الأولادَ والأزواجَ والأموالَ، ويَكْشِفُون الضُّرَّ، ويَرْفَعُونَ البَلاءَ، ويَقْضُونَ الحَوائِجَ، ويُجِيبونَ دُعاءَ مَن يَدْعُوهم.
2: اعتقادُ المَجوسِ أنَّ للكَوْنِ خَالِقَيْنِ: النُّورَ والظُّلْمَةَ.
3: اعتقادُ بعضِ غُلاةِ الصُّوفيَّةِ والشِّيعةِ أن بعضَ مُعَظَّميهِم يَعْلَمُونَ الغَيْبَ، وأن لهم تَصَرُّفًا في الكَوْنِ، وأنهم يُجِيبونَ الدُّعاءَ ويَقْضُونَ الحَوائِجَ.

ومن الشِّرْكِ في الرُّبوبيَّةِ: الحُكْمُ بغَيْرِ ما أنْزَلَ اللهُ، فمَن حَكَمَ بغَيْرِ ما أنْزَلَ اللهُ فهو طَاغوتٌ قد جَعَلَ نَفْسَهُ شَرِيكًا للهِ في حُكْمِه.
• النوعُ الثالِثُ: شِرْكُ الطَّاعةِ؛ وهو اتِّباعُ المُعَظَّمينَ في تحليلِ الحرامِ وتَحْرِيمِ الحلالِ؛ كما يَفْعَلُهُ عُبَّادُ الطواغيتِ من طاعتِهم ومُتابَعَتِهم في تَحليلِ ما حَرَّمَ اللهُ وتَحْريمِ ما أحَلَّ اللهُ.
ومن صُوَرِه:
1: التحاكُمُ إلى الطَّواغيتِ؛ فمَن تَحاكَمَ إليهم مُرِيدًا مُختارًا فهو كافرٌ غيرُ مُؤمنٍ لقولِ اللهِ تعالى: ﴿أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ يَزْعُمُونَ أَنَّهُمْ آمَنُوا بِمَا أُنْزِلَ إِلَيْكَ وَمَا أُنْزِلَ مِنْ قَبْلِكَ يُرِيدُونَ أَنْ يَتَحَاكَمُوا إِلَى الطَّاغُوتِ وَقَدْ أُمِرُوا أَنْ يَكْفُرُوا بِهِ وَيُرِيدُ الشَّيْطَانُ أَنْ يُضِلَّهُمْ ضَلَالًا بَعِيدًا (60)﴾ [النساء: 60].
… أما مَن كانَ في بلدٍ لا يُحْكَمُ فيه بما أَنْزَلَ اللهُ واحتاجَ في رَفْعِ الظُّلمِ عنه وتمكينِه من حَقِّه إلى التَّحاكُمِ إلى بعضِ مَن يَظُنُّ فيه حِفْظَ الحَقِّ ورَفْعَ الظُّلْمِ؛ فلا يَكْفُرُ بذلك لقولِ النبيِّ صلى الله عليه وسلم لأصحابِه لَمَّا أَذِنَ لهم بالهِجْرةِ الأُولَى إلى الحَبَشةِ: ((إنَّ بأرضِ الحَبَشةِ مَلِكًا لا يُظْلَمُ أحَدٌ عندَه، فالْحَقُوا ببلادِه حتى يَجْعَلَ اللهُ لكم فَرَجًا ومَخْرَجًا مِمَّا أنتم فيه)) رواهُ البَيْهقِيُّ من حديثِ أُمِّ سَلَمَةَ بإسنادٍ حَسَنٍ.
ولم يَكُنِ النَّجاشِي قد أسْلَمَ؛ ولو حَصَلَتْ عليهم مَظْلِمَةٌ واحْتاجُوا إلى التَّحاكُمِ إليه فيها لأَنْصَفَهُم، وهذا دليلٌ على جوازِ التَّحاكُمِ إلى مَن يُعْلَمُ أن مِن شأنِه تَحَرِّيَ العَدْلِ ورَفْعَ الظُّلْمِ كما يَحْصُلُ في بعضِ البُلدانِ.
والمُسلمُ في حالِ الاضْطِرارِ والحاجةِ التي يَلْحَقُ بفواتِها حَرَجٌ غَيْرُ مُرِيدٍ للتَّحَاكُمِ إلى الطواغيتِ في حَقِيقَةِ الأَمْرِ؛ فلا يَكْفُرُ بذلك.
أما التَّحاكُمُ الذي فيه تَعَبُّدٌ لغيرِ اللهِ تعالى وتقديمُ قَرَابِينَ وسُؤالٌ للكُهَّانِ كما يَفْعَلُه بعضُ الوَثَنِيِّينَ فلا يَجوزُ بحالٍ.
2: طاعةُ عُلماءِ السُّوءِ والحُكَّامِ الطَّواغِيتِ في تَحليلِ الحرامِ البَيِّنِ حُكْمُه في الشريعةِ، وتَحْريمِ الحلالِ البَيِّنِ حُكْمُه في الشَّريعةِ.
وأفرادُ الشِّركِ وصُوَرُه كثيرةٌ جِدًّا لكنَّها راجعةٌ إلى هذه الأنواعِ الثلاثةِ.

الناقضُ الثالثُ: ادِّعاءُ بعضِخَصائصِ اللهِ في رُبُوبِيَّتِه أو أُلُوهِيَّتِه أو أسمائِه وصِفاتِه.
ومن صُوَرِ ذلك:
1: دَعوةُ بعضِ الطواغيتِ إلى عِبادةِ أنفسِهم.
2: ادِّعاءُ عِلْمِ الغَيْبِ.
3: ادِّعاءُ القُدْرَةِ على إحياءِ المَوْتَى.

الناقضُ الرَّابِعُ: ادِّعاءُ النُّبُوَّةِ
دَعْوَى النُّبُوَّةِ كُفْرٌ بإجماعِ العُلماءِ.

ومِمَّا يَلْتَحِقُ به:
• مَن يَدَّعِي مُضاهاةَ القرآنِ وأنه يَقْدِرُ عَلَى أنْ يُنْزِلَ مِثلَ ما أنزَلَ اللهُ على رُسُلِه، قال اللهُ تعالى: ﴿وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَى عَلَى اللَّهِ كَذِبًا أَوْ قَالَ أُوحِيَ إِلَيَّ وَلَمْ يُوحَ إِلَيْهِ شَيْءٌ وَمَنْ قَالَ سَأُنْزِلُ مِثْلَ مَا أَنْزَلَ اللَّهُ﴾ [الأنعام: 93].

الناقضُ الخامسُ: تكذيبُ اللهِ عز وجل وتكذيبُ رسولِه صلى الله عليه وسلم،
فمَن كَذَّبَ اللهَ ورسولَه فهو كافرٌ غيرُ مسلمٍ بإجماعِ العلماءِ.

ومن صُوَرِ هذا الناقضِ:
1: جَحْدُ ما هو مَعلومٌ من دِينِ الإسلامِ بالضَّرورةِ؛ كجَحْدِ وُجوبِ الصلاةِ أو الزكاةِ، وجَحْدِ تحريمِ الرِّبا أو الزِّنا أو أَكْلِ لحمِ الخِنْزيرِ.
2: إنكارُ شَيْءٍ من أسماءِ اللهِ تعالى وصفاتِه، بلا شُبْهةِ جَهْلٍ يُعْذَرُ بمِثْلِه ولا تَأْويلٍ.
3: إنكارُ شَيْءٍ من القرآنِ الكَريمِ.
4: ادِّعاءُ الاختلافِ والتَّناقُضِ والتحريفِ في القُرآنِ الكريمِ.
5: إنكارُ السُّنةِ النَّبويَّةِ.
6: إنكارُ البَعْثِ والجزاءِ.
7: عَدَمُ تكفيرِ مَن لا يَدِينُ بدِينِ الإسلامِ من اليَهودِ والنَّصارَى والمَجُوسِ والمَلاحِدَةِ والوَثَنِيِّينَ.
8: اعتقادُ أنَّ المَرْءَ يَسَعُه الخُروجُ عن شَريعةِ مُحَمَّدٍ صلى الله عليه وسلم كما وَسِعَ الخَضِرَ الخُروجُ عن شَرِيعَةِ مُوسَى عليه السلام.
9: استحلالُ المُحَرَّمِ المَعلومِ تَحْرِيمُه بالدليلِ الصحيحِ بلا شُبْهةٍ ولا تأويلٍ.
10: تَصْدِيقُ مَن يَدَّعِي النُّبوَّةَ.
11: دَعْوَى أن رِسالةَ النبيِّ صلى الله عليه وسلم للعَرَبِ خَاصَّةً.
12: دَعْوَى أن اللهَ تعالى يَرْضَى بأنْ يُدْعَى من دُونِه أَحَدٌ من الصالحينَ أو غَيْرِهم.
13: قَذْفُ أمِّ المؤمنينَ عائشةَ رضيَ اللهُ عنها بما برَّأَها الله مِنْه، وقذفُ سائرِ أُمَّهاتِ المُؤمِنينَ كذلك.
وكلُّ ما يَتحَقَّقُ به تَكْذيبُ اللهِ تعالى وتكذيبُ رَسولِه صلى الله عليه وسلم فهو ناقضٌ من نَواقضِ الإسلامِ، إلا أنه يَنْبَغِي التفريقُ بينَ تكذيبِ الخَبَرِ المَبْنيِّ على عدمِ العلمِ بالدليلِ أو غِيابِه عنه أو الشكِّ في ثُبوتِه أو كانَ للمُكَذِّبِ تأويلٌ في معنَى الخَبَرِ يُدْرَأُ عنه به حُكْمُ التكذيبِ، وبينَ تَكذيبِ ما عُلِمَ ثُبوتُه ومعناه، فهذا الأخيرُ ناقضٌ بلا خلافٍ بينَ أهلِ العلمِ.
وأمَّا في الأحوالِ المَذْكُورةِ قَبْلَه فلا يُحْكَمُ بكُفْرِ المُكَذِّبِ حتى تُقامَ عليه الحُجَّةُ، ويَتَبيَّنَ ثُبوتَ الخَبَرِ وصِحَّةَ مَعْناهُ.

الناقضُ السادسُ: الشَّكُّ.
الشكُّ مُنافٍ للتصديقِ الواجبِ، فمَن شَكَّ في صِدْقِ خَبَرِ اللهِ عز وجل وخَبَرِ رَسُولِه صلى الله عليه وسلم فهو كَافِرٌ غَيْرُ مُؤْمِنٍ.
والتَّكْذِيبُ والشكُّ مُنافِيَانِ للتصديقِ الوَاجِبِ.

ومن صُوَرِ هذا الناقضِ:
1: الشَّكُّ في كُفرِ مَن لا يَدِينُ بدينِ الإسلامِ.
2: الشَّكُّ في أمرِ البَعْثِ بعدَ الموتِ.
3: الشَّكُّ في ثُبوتِ القُرآنِ الكريمِ وحِفْظِه من التَّحْرِيفِ والتَّبْديلِ.

الناقضُ السابعُ: بُغْضُ اللهِ ورسولِه، وبُغْضُ دينِ الإسلامِ
البُغْضُ مُنافٍ للمَحَبَّةِ الوَاجبةِ؛ فمَن أبْغَضَ اللهَ ورسولَه أو أبْغَضَ دِينَ الإسلامِ فهو كافرٌ خارجٌ من المِلَّةِ.
ومِمَّا يَلْتَحِقُ به:
1: سَبُّ اللهِ ورسولِه وسَبُّ دينِ الإسلامِ، وتَنَقُّصُ الذَّاتِ المُقَدَّسَةِ، وتَنَقُّصُ مَقامِ النبيِّ صلى الله عليه وسلم.
2: بُغْضُ الصحابةِ رضِي الله عنهم، وسَبُّهم على وَجْهِ العُمومِ وتَكْفِيرُهم بخِلافِ مَن سَبَّ طَائِفَةً منهم لشُبْهةٍ عَرَضَتْ له فإنه يَكونُ قد ارتكَبَ مُحَرَّمًا ولكن لا يُحْكَمُ بكُفرِه.
3: بُغْضُ أَئمَّةِ الدِّينِ ورُواةِ الأحاديثِ الصحيحةِ وحَمَلةِ الشَّريعةِ على وَجْهِ العُمومِ وتَكْذيبُهم.

الناقضُ الثامنُ: الاستهزاءُ باللهِ وآياتِه ورسولِه، وهو كُفْرٌ لمُنافاتِه المَحَبَّةَ الواجبةَ والتعظيمَ الواجبَ.
ومِمَّا يَلْتَحِقُ به:
1: امْتِهانُ المُصْحَفِ.
2: الاسْتِخفافُ بأيِّ شَعيرةٍ من شَعائرِ الإسلامِ.

الناقضُ التاسعُ: اتِّخَاذُ الكُفَّارِ أولياءَ من دونِ المؤمنينَ، وهو يشملُ أمرين:
1: محبتهم في دينهم وموافقتهم عليه والرضا به.
2: مناصرة الكفار على المسلمين.
ومن صُوَرِ هذا الناقض:
1: التَّجَسُّسُ على المسلمين لصالحِ الكُفَّارِ.
2: تَهْنِئَةُ الكُفَّارِ بأعيادِهم الوَثَنِيَّةِ والكُفْريَّةِ رِضًا بما يَصْنَعُونَ من الشِّركِ والكُفْرِ باللهِ عزَّ وجلَّ، وأمَّا من شارَكَهم لِيطْعَمَ مَعهم أو يَسْتَمْتِعَ اسْتِمْتَاعًا محرَّمًا بفِسْقِهِمْ وغِنَائِهِم، وقلبُهُ منكِرٌ لِكُفْرِهِم وَشِرْكِهِم ؛ فهو على شَفَا هَلَكَةٍ ويُخْشَى عَلَيْهِ إذَا حلَّت بهم عُقُوبةٌ أن تَشْمَلَهُ مَعَهُمْ.
3: بِناءُ مَعابِدَ يُعْبَدُ فيها غيرُ اللهِ جل وعلا، أو الإعانةُ عليها كبِناءِ الكنائسِ والأَدْيرةِ والبِيَعِ وبناءِ الأَضْرِحَةِ والمَشاهِدِ التي يُدْعَى فيها غيرُ اللهِ جل وعلا.
4: مُحاربةُ حَمَلةِ الشريعةِ من العُلماءِ والدُّعاةِ والتَّضْيِيقُ عليهم قَصْدًا للتَّضْييقِ على دَعوةِ الإسلامِ.
5: العَمَلُ على تَوْهِينِ المُسلمينَ وإضعافِهم، وتَمْكِينِ الكُفَّارِ من التَّسلُّطِ على المُسلمينَ.

الناقضُ العاشرُ: التَّولِّي والإِعراضُ.
مَن تَولَّى عن طَاعةِ اللهِ ورسولِه فهو غيرُ مُسلمٍ؛ لأنه غيرُ مُنقادٍ لدينِ اللهِ تعالى؛ فهو لا يَمْتَثِلُ الوَاجباتِ ولا يَمْتَنِعُ عن المُحرَّمَاتِ إلا ما وَافَقَ هَواهُ.
ومن صُوَرِ هذا النَّاقِضِ:
1: أنْ يَرَى أنَّ طَاعَةَ اللهِ تعالى وطَاعةَ رَسُولِه لا تَلْزَمُه، وأنه لا يَجِبُ عليه امتثالُ أمرِ اللهِ تعالى وأمْرِ رَسُولِه صلى الله عليه وسلم.
2: أنْ يُعْرِضَ عن أمرِ اللهِ وأَمْرِ رَسُولِه إعراضًا كُلِّيًّا فلا يَتَفَقَّهُ في الدينِ ولا يَسْأَلُ عَمَّا يَجِبُ عليه من طاعةِ اللهِ وطَاعةِ رَسُولِه، ولا يَمْتَثِلُ الوَاجِبَاتِ، ولا يَمْتَنِعُ عن المُحَرَّمَاتِ طَاعةً للَّهِ ورسولِه.
أما مَن كانَ مُلْتَزِمًا طَاعةَ اللهِ ورسولِه ويَمْتَثِلُ مِن ذلك ما يَبْقَى به مُسْلِمًا لكنَّه يَقَعُ في بعضِ المَعاصِي فهو غيرُ كافرٍ بتلك المَعاصِي.
• ومِمَّا يَلْتَحِقُ بهذا الناقضِ: تَرْكُ الصلاةِ؛ فهي عَمُودُ الدِّينِ؛ وإذا تَرَكَها العَبْدُ تَرْكًا مُطْلَقًا فهو مُعْرِضٌ عن دِينِ اللهِ جل وعلا، قال عُمَرُ بنُ الخَطَّابِ: (مَن ضَيَّعَها فهو لِمَا سِوَاهَا أَضْيَعُ).

فَصْلٌ: وهذه النَّواقضُ تُنافِي الشَّهادَتَيْنِ مُنافاةً تَامَّةً، ومَن وَقَعَ في أَحَدِها بعدَ إسلامِه وهو عَاقِلٌ بَالِغٌ غَيْرُ مُكْرَهٍ ولا مَعْذُورٍ بشُبْهَةٍ فهو كافرٌ مُرْتَدٌّ عن دينِ الإسلامِ، فإن ماتَ على ذلك فهو خالدٌ مُخلَّدٌ في نارِ جَهنَّمَ، قال اللهُ تعالى: ﴿وَمَنْ يَرْتَدِدْ مِنْكُمْ عَنْ دِينِهِ فَيَمُتْ وَهُوَ كَافِرٌ فَأُولَئِكَ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ وَأُولَئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ﴾[البقرة: 217].
ومَن وَقَعَ في أحَدِ هذه النَّوَاقِضِ أو بَعْضِها في الباطِنِ وهو يُظْهِرُ الإسلامَ فهو من المُنافقين النِّفاقَ الأكبرَ، نُعامِلُه مُعاملةَ المُسلمين في الظَّاهِرِ، ونَكِلُ سَرِيرَتَهُ إلى اللهِ تعالى ما لم يَتَبَيَّنْ لنا منه كُفْرٌ ظَاهِرٌ.


فَصْلٌ:
والنَّوَاقِضُ على دَرَجَتَيْنِ:
الدرجةُ الأُولَى: الكُفْرُ البَوَاحُ، وهو الذي لا يَقَعُ في كُفْرِ صَاحِبِه لَبْسٌ ولا اشتباهٌ ولا يَحْتَمِلُ أنْ يَكُونَ له عُذْرٌ يُعْذَرُ به من جَهْلٍ أو تَأْوِيلٍ أو إِكْرَاهٍ.
كمَن يَنْتَسِبُ إلى غَيْرِ الإسلامِ أو يَعْبُدُ غيرَ اللهِ جل وعلا، ومَن يَسُبُّ اللهَ ورسولَه، ومَن يَسْتَهْزِئُ بالدِّينِ، ومَن يُنْكِرُ القُرْآنَ أو السُّنةَ أو يَجْحَدُ مَعْلومًا من الدِّينِ بالضَّرُورةِ معَ ظُهورِ حَالِه بعِلْمِ ذلك.
وأصحابُ هذهِ الدرجةِ يُحْكَمُ بكُفْرِهم وبأنهم من أهلِ النارِ إذا تَحَقَّقْنَا أنهم مَاتُوا على ذلك، قال اللهُ تعالى: ﴿مَا كَانَ لِلنَّبِيِّ وَالَّذِينَ آَمَنُوا أَنْ يَسْتَغْفِرُوا لِلْمُشْرِكِينَ وَلَوْ كَانُوا أُولِي قُرْبَى مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُمْ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ﴾ [التوبة: 113].
الدرجةُ الثانيةُ: ما ليسَ بكُفْرٍ بَوَاحٍ، وهو على نَوْعينِ:
النوعُ الأولُ: ما يَحْتَمِلُ أن يكونَ لصَاحِبِه ما يُعْذَرُ به من إِكْراهٍ أو ذَهَابِ عَقْلٍ أو شُبْهَةٍ من تأويلٍ أو جَهْلٍ يُعْذَرُ به ويَحْتَاجُ مَعَه إلى إقامةِ الحُجَّةِ عليه، فإنْ بَلَغَتْهُ الحُجَّةُ وعَرَفَ معناها وأصَرَّ بعدَ ما تَبَيَّنَ له الحقُّ حُكِمَ بكُفْرِه، وإن بَقِيَتِ الشُّبْهَةُ لديهِ لم يُحْكَمْ بكُفْرِه.
ولهذا امْتَنَعَ أئمَّةُ أهلِ السُّنةِ عن تَكفيرِ بعضِ أصحابِ الفِرَقِ الضالَّةِ المُنْكِرةِ لبعضِ الأسماءِ والصِّفاتِ لشُبْهةِ التأويلِ، معَ الحُكْمِ عليهم بأنهم مُبْتدِعةٌ وفُسَّاقٌ وأن الشُّبْهةَ لا تُبَرِّئُهم من المُخالفةِ لكنها تَمْنَعُ من تَكْفيرِهم.
وفي هذا النوعِ يُحْكَمُ بأنَّ العَمَل كُفْرٌ، لكن لا يُكَفَّرُ المُعَيَّنُ حتى تَتَحَقَّقَ فيه الشروطُ وتَنْتَفِي المَوَانِعُ.

النوعُ الثاني: أنْ يَكونَ الناقضُ من النواقضِ المُخْتَلَفِ فيها، ويَقَعُ للناظِرِ في ذلك شيءٌ من اللبْسِ وعَدَمِ التَّرجيحِ.
وقد اختَلَفَ أهلُ العلمِ في بعضِ النواقضِ، ومنها:
1: تَرْكُ الصَّلاةِ تَهاوُنًا وكَسَلاً من غيرِ جَحْدٍ لوُجوبِها ولا استكبارٍ عن أدائِها.
والصَّحيحُ أنَّ مَن تَرَكَها مُطْلقًا فهو كافرٌ، ومَن كانَ يُصَلِّي أحيانًا ويَتْرُكُ الصَّلاةَ أحيانًا فهو فَاسِقٌ مُتَوَعَّدٌ بالعذابِ على ما فَــرَّطَ في الفرائضِ لكنْ لا يُحْكَمُ بكُفْرِه.
وهذا القولُ وَسَطٌ بينَ قَوْلينِ:
القولُ الأولُ: أنه يَكْفُرُ بتَرْكِ صَلاةٍ وَاحِدَةٍ.
والقَوْلُ الثاني: أنه لا يَكْفُرُ وإنْ تَرَكَهَا مُطْلَقًا.
2: السِّحْرُ، وقد اختلَفَ أهلُ العلمِ في كُفْرِ مَن تَعلَّمَ السِّحْرَ وعلَّمَه ومَن يَعْمَلُ السِّحْرَ، والصوابُ أنَّ السِّحْرَ لا يَتحَقَّقُ إلا بالكُفْرِ والشِّرْكِ الأكبرِ مِن الاستغاثةِ بالشياطينِ والتَّقرُّبِ لهم بالذبحِ والنذرِ، وامتهانِ ما أمَرَ اللهُ بتعظيمِه، ولا خِلافَ بينَ أهلِ العلمِ في كُفْرِ مَن يَفْعَلُ هذه الأفعالَ.
لكن من أهلِ العلمِ مَن يُسمِّي الحِيَلَ الخَفِيَّةَ والخدَعَ البَصَرِيَّةَ سِحْرًا، ومنهم مَن يَعُدُّ التَّحَيُّلَ بسَقْيِ بعضِ العقاقيرِ المُؤثِّرةِ على عقلِ الإنسانِ ونفسِه وإدراكِه سِحْرًا، ولأجلِ ذلك لا يُكَفِّرونَ الساحرَ مُطْلقًا حتى يَسْتفسِرونَ عن سِحْرِه، فإن كان سِحْرُه بالاستغاثةِ بالشياطينِ والتَّقرُّبِ إليهم حَكَموا بكُفْرِه، وإن كان سِحْرُه بغيرِ ذلك حَكَمُوا بتعزيرِه بما يَزْجُرُه عن ذلك ولم يُكَفِّرُوه.
3: تَرْكُ الزَّكاةِ والصِّيامِ والحَجِّ، وقد ذَهَبَ بعضُ أهلِ العلمِ إلى كُفْرِ مَن تَرَكَ شَيْئًا من هذه الفَرَائِضِ، وإنْ كانَ غيرَ جَاحِدٍ لوُجوبِها، والصوابُ أنه لا يُحْكَمُ بكُفْرِ تَارِكِها إلا إذا كانَ جَاحِدًا لوُجوبِها، فيُحْكَمُ بكُفْرِه حِينَئذٍ لكونِه مُكَذِّبًا للَّهِ ولرسولِه.
وقد دَلَّت الأحاديثُ الصحيحةُ على أن تاركَ هذه الفرائضِ يُعَذَّبُ في الآخرةِ، ثم يُرَى سبيلُه إما إلى الجَنَّةِ وإما إلى النارِ، وهذا دليلٌ على عَدَمِ تَحَتُّمِ كُفْرِه.

فصلٌ: وبعضُ الأعمالِ المُخْرِجةِ من المِلَّةِ قد يَجْتَمِعُ فيها أكثرُ من ناقضٍ، فتكونُ كُفْرًا من أَكْثَرَ مِن وَجْهٍ.
مِثالُ ذلك: الذي يَحْكُمُ بغيرِ ما أنزَلَ اللهُ مُسْتَحِلاًّ ومُفَضِّلاً حُكْمَ الطَّواغيتِ على حُكْمِ اللهِ جل وعلا.
فهو كافرٌ مِن أَكْثرَ مِن وَجْهٍ:
– كافرٌ بسببِ حُكمِه بغيرِ ما أنزلَ اللهُ وجَعْلِه نفسَه شَرِيكًا للهِ في حُكْمِه.
– وكافرٌ بسببِ استحلالِه مُحرَّمًا مَعْلومَ التحريمِ بالضَّرورةِ من دِينِ الإسلامِ.
– وكافرٌ بسببِ تَكْذيبِه للهِ ولرسولِه بتَفْضيلِه حُكْمَ الطاغوتِ على حُكْمِ اللهِ جل وعلا.

ومِمَّا يَنْبَغِي أن يُعْلَمَ أن بَعْضَ الكُفَّارِ والمُرْتَدِّينَ يَقَعُونَ في أنواعٍ من النَّواقضِ، فيَقَعُ بعضُهم في الشِّركِ الأكبرِ وتكذيبِ اللهِ ورسولِه وبُغْضِ دينِ الإسلامِ ومُوالاةِ الكُفَّارِ وغيرِها من النواقضِ، وكُلَّما كانَ العبدُ أكْثَرَ وُقوعًا في هذهِ النواقضِ كانَ أعْظَمَ كُفْرًا، وكانَ عذابُه على ذلك أشَدَّ، معَ كَوْنِهم مُشتركينَ في الخُروجِ من دِينِ الإسلامِ.

فصلٌ: والكُفْرُ كُفْرانِ؛ كُفْرٌ ظَاهِرٌ، وكُفْرٌ بَاطِنٌ:
فأمَّا الكفرُ الباطنُ فهو ما يَتعلَّقُ به حالُ العبدِ فيمَا بينَه وبينَ اللهِ؛ فقد يَكونُ كافرًا في الباطِنِ بارتكابِه ما يَنْقُضُ الإسلامَ، وهو فيما يَرَى الناسُ مُظْهِرٌ للإسلامِ؛ وحينَئذٍ يكونُ مُنافِقًا يُعامَلُ مُعاملةَ المسلمين في الظاهرِ، وهو في الآخرةِ معَ الكفارِ في نارِ جَهنَّم خالدًا فيها.
ومن الناسِ مَن يَرْتَكِبُ نَاقِضًا من النواقضِ فيما يَظْهَرُ للنَّاسِ ويَكونُ له ما يُعْذَرُ به من ذَهابِ عَقْلٍ أو جَهْلٍ يُعْذَرُ بمِثْلِه، أو يَكونُ حَدِيثَ عَهْدٍ بالإسلامِ فتَجْرِي على لسانِه بعضُ أقوالِ الكُفْرِ التي اعتادَها من غيرِ أنْ يَعْتَقِدَها؛ فرُبَّما حُكِمَ بكُفْرِه في الظاهرِ وهو في الباطِنِ له ما يُعْذَرُ به.

ويُبْعَثُ الإنسانُ يومَ القيامةِ على ما ماتَ عليه من إيمانٍ وكُفْرٍ.
والأَصْلُ في الحُكْمِ بالكُفْرِ أنه إلى أهلِ العلمِ وأُولِي الأَمْرِ، وقد يُخْرَجُ عن الأصلِ
لعَوَارِضَ تَقْتَضِيها الحاجةُ وتَعَلُّقِ العَمَلِ بذلك.

ومِمَّا يَنْبَغِي التَّحْذِيرُ منه التَّسَرُّعُ في تَكْفيرِ مَن لم يَتَبيَّنْ كُفْرُه؛ لقولِ النبيِّ صلَّى الله عليه وسلم: (( إِذَا قالَ الرَّجُلُ لأخيهِ: يَا كافرُ، فقَدْ باءَ بها أحدُهمَا، فإنْ كانَ كمَا قالَ، وإلاَّ رَجَعَتْ عليهِ )) مُتَّفقٌ عليه من حديثِ ابنِ عُمَرَ رضِي الله عنهما.
وعن أَبِي ذَرٍّ رضِي الله عنه أنَّه سَمِعَ رسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم يقولُ: (( مَنْ دَعَا رَجُلاً بالكُفْرِ، أو قالَ: عَدُوَّ اللهِ، وَلَيْسَ كَذَلِكَ إلاَّ حَارَ عَلَيْهِ )). مُتَّفَقٌ عليه.
وهذا التحذيرُ هو فِيمَا يَجْرِي مَجْرَى السِّبابِ والتَّسَرُّعِ والحُكْمِ مِن غَيْرِ تَأَهُّلٍ، أما العَالِمُ المُجْتهِدُ إذا أخْطَأَ في حُكْمِه عندَ الاحتياجِ إليه وهو غَيْرُ مُفَرِّطٍ ولا مُتَّبِعٍ لِهَوى؛ فإنه مَأْجُورٌ على اجْتِهادِه وخَطَؤُه مَغْفُورٌ.

فَصْلٌ: وقدْ أجْمَعَ أهلُ العِلْمِ على وُجوبِ قَتْلِ المُرْتَدِّ لقولِ النبيِّ صلَّى اللهُ عليه وسلَّم: ((مَن بَدَّلَ دِينَهُ فَاقْتُلُوهُ)) رواهُ البُخاريُّ من حديثِ ابنِ عَبَّاسٍ رضِي الله عنهما.
ومَن مَاتَ مُرْتَدًّا فلا يُغَسَّلُ، ولا يُكَفَّنُ، ولا يُصَلَّى عليه، ولا يُدْفَنُ في مَقابِرِ المُسلمينَ، ولا يُوَرَّثُ مالُه، ولا يُدْعَى له بعدَ موتِه.
وأمَّا استتابتُه قبلَ قَتْلِه فهي من اجتهادِ الإمامِ، فإن كانَ يَرْجُو رُجوعَه للإسلامِ أو كانت لديه شُبْهَةٌ عارضةٌ ارْتَدَّ بسَبَبِها فله أن يُمْهِلَه ثلاثةَ أيَّامٍ ويَعْرِضَ عليه الرُّجوعَ للإسلامِ، فإنْ تَابَ وإلا قُتِلَ مُرْتَدًّا.
وإنْ رَأَى الإمامُ أنَّ التَّعْجِيلَ بقَتْلِه فيه مَصْلَحةٌ للمُسْلمِينَ كأنْ يَكونَ شَدِيدَ الإيذاءِ للمُسْلِمينَ بعدَ رِدَّتِه أو جَاسُوسًا عليهم أو خَشِيَ أنْ يَكُونَ في إمهالِه فِتْنةٌ وضَرَرٌ على المُسْلِمِينَ عَجَّل بقَتْلِه ما لم يَتُبْ قَبْلَ القُدْرةِ عليه.


اللهُمَّ أَحْيِنَا مُسلِمِينَ وتَوَفَّنَا مُسْلِمِينَ، وَأَلْحِقْنَا بالصَّالِحينَ، وأَجِرْنَا من خِزْيِ الدنيا وعَذَابِ الآخِرَةِ، ربَّنا إنَّك رَؤوفٌ رَحيمٌ.

طاهر جبريل دكو
_8 _April _2013هـ الموافق 8-04-2013م, 11:49 PM
Darasi na goma sha biyu: Abubuwanda ke warware Musulunci.
Idan mun fahinci cewa bawa bazai zama musulmiba har sai ya shaida da kalmomi biyuna shahada–shaidawa babu abin bawta da gaskiya sai Allah, da shaidawa Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, sai ya kadaita Allah sannan ya bi Manzon Allah (S.A.W), da wannan ne zai zama Musulmi.
Kuma mun fahimci cewa abinda shaidawa babu abin bawtawa da gaskiya sai Allah yake hukuntawa shine; tsarkake bawta ga Allah Shi kadai, kuma cewa bawta ta ginune akan soyayya da girmamawa da sallamawa.
Kuma mun fahimci cewa shaidawa Annabi Muhammadu Manzon Allah ne yana hukunta sonsa da gaskatashi da yi masa biyayya.
Sai kasani cewa, duk wanda ya aikata wani abu da zai warware wadannan kalmomi biyuna shahada, to shi fitaccene daga addinin Musulunci, wanda ya kafircewa Allah (Mai girma da dawkaka) koda kuwa yayi salla yayi azumi kuma ya riya cewa shi Musulmine.
Saboda haka duk wanda aka rasa daya daga cikin wadannan abubuwan atare dashi – tsarkake bawta ga Allah (Mai girma da dawkaka), son Allah da girmamaShi, da sallama maSa, da son Manzon Allah (S.A.W), da gaskatashi, da yi masa biyayya- hakika Musuluncinsa ya gushe daga gareshi.
Idan wannan gushewan ya kasancene daga asalinsa, wato bawa bai tsayu da abinda wadannan kalmomi biyuna shahada suke hukuntawaba tun farkon al'amarinsa, to shi kafirine na asali, idan kuma ya kasance yana bayyana Musulunci tareda hakan, to shi munafikine.
Amma wanda ya kasance Musulmi, tsayayye game da abin da Kalmomi biyuna sahada suke hukuntawa, sannan sai daya daga cikin wadannan al'amuran suka gushe daga gareshi bayan da ya kasance Musulmi, to shi kafirine riddajje daga addinin Musulunci.
Kuma ridda na iya kasancewa da kowanne daga cikin al'amura na furuci ko na aiki ko na kuduri wanda ke wajabta gushewar hakikanin shaidawa babu abin bawtawa da gaskiya sai Allah, kuma lallai Annabi Muhammadu (S.A.W).
Misalan abubuwan dake warware Musulunci wadandake fitarwa daga Addinin Musulunci suna da yawa, basu da wani adadi kididdigagge, sai dai sunada asulla da ke hadesu wadanda sune:
Abuna farko mai warwarewa: Ilhadi, shine inkarin samuwar Allah (Madawkakin Sarki)
Daga cikin misalansa:
Jingina yin halitta ga dabi'a.
Yin imani da cewa duniya batada farko, wato cewa daga cikin halittu akwai wadanda basu da fakor tun fil azan.
Abu na biyu daga cikin masu warware Musulunci: babbar shirka, itace rikon kishiya ga Allah (Mai girma da dawkaka) shima naw'uka ne:
Naw'i na farko: shirka cikin ibada, shine sarrafa wani naw'i daga naw'ukan bawta ga wanin Allah (Mai girma da dawkaka) kamar addu'a ko yanka ko bakance ko neman taimako ko neman agaji ko makamanci haka, daga cikin misalansa:
Na farko: Abinda masu bawtar gumaka da Annabawa da waliyyai ke aikatawa na rokonsu koma bayan Allah (abinda ba mai yinsa sai Allah ) da neman ceto daga garesu da neman biyan bukatu da jawo amfani da yaye cuta, to duk wanda ya aikata wannan shi mushrikine kafiri koda kuwa ya riya cewa shi Musulmine kuma yana cewa "La-ilaha- illa llahu kuma yana salla yana azumi yana sadaka yana aikin hajji kuma yana aikat alheri. Ita babbar shirka tana bata ayyuka kuma tana kore addinin Musulunci.
Abuna biyu: Abinda masu sihiri da wasu da suke zuwa wurinsu ke aikatawa na yin yanka ga wanin Allah (Mai girma da dawkaka) da neman agajin daga shedanu.
Naw'i na biyu: shirka acikin rububiyya, daga cikin misalansa:
1: اعتقادُ بعضِ المُشركينَ في آلهتِهم ومُعَظَّمِيهِم أنَّ لهم تَصَرُّفًا في الكَوْنِ وأنهم يَعْلَمُونَ الغَيْبَ، ويُنَزِّلونَ الغَيْثَ، ويَمْلِكونَ الرِّزقَ، ويَشْفُونَ من الأمراضِ، ويَهَبُونَ الأولادَ والأزواجَ والأموالَ، ويَكْشِفُون الضُّرَّ، ويَرْفَعُونَ البَلاءَ، ويَقْضُونَ الحَوائِجَ، ويُجِيبونَ دُعاءَ مَن يَدْعُوهم.
Abuna daya: Imanin da wasu daga cikin mushirikai ke dashi dangane da ababen bawtansu da wadanda suke girmamawa na cewa sunada ilimin gaibu, kuma suna sawkarda ruwan sama, kuma suna da mallakar arziki, kuma suna warkarwa daga cututtuka, kuma suna bada yaya da mata da dukiya, kuma suna yaye cuta, kuma suna tunkude bala'i, kuma suna biyan bukatu, kuma suna amsa addu'ar wanda ya rokesu.
Abuna biyu: Imanin majusawa na cewa ababen halitta sunada mahalitta biyu: Haske da duhu.
Abuna uku: Imanin wasu daga cikin masu wuce iyaka daga cikin sufaye da yan shi'a cewa wasu mutane abin darajawa acikinsu sun san gaibu, kuma cewa sunada ikon gudanarwa aciki halittu, kuma cewa suna amsa addu'a kuma su biya bukatu.
Kuma yana daga cikin shirka a rububiyya: yin hukunci da sabanin abinda Allah Ya sawkar, saboda haka duk wanda yayi hukunci da sabanin abinda Allah Ya sawkar, to shi dagutune wanda ya sanya kansa a matsayin abokin tarayya ga Allah acikin hukuncinSa.
Naw'i na uku: Shirkan da'a,wannan shine biyayya ga manya acikin halatta haram da kuma haramta halal kamar yadda masu bawtan dagutu sukeyi cikin halatta abinda Allah Ya haramta da haramta abinda Allah Ya halatta.
Daga cikin misalansa;
Na farko:Maida hukunci zuwaga dagutai. Saboda haka duk wanda ya maida hukunci zuwa garesu bisa nufi da zabi (da yarda), to shi kafirine ba muminiba, saboda fadin Allah (Madawkakin Sarki):
﴿أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ يَزْعُمُونَ أَنَّهُمْ آمَنُوا بِمَا أُنْزِلَ إِلَيْكَ وَمَا أُنْزِلَ مِنْ قَبْلِكَ يُرِيدُونَ أَنْ يَتَحَاكَمُوا إِلَى الطَّاغُوتِ وَقَدْ أُمِرُوا أَنْ يَكْفُرُوا بِهِ وَيُرِيدُ الشَّيْطَانُ أَنْ يُضِلَّهُمْ ضَلَالًا بَعِيدًا (60)﴾ [النساء: 60].
Ma'ana:"Shin baka gani ba zuwaga wadanda suke riya cewa lallai su sunyi imani da abinda aka sawkar zuwa gareka da abinda aka sawkar gabaninka suna nufin maida hukunci zuwaga dagutu alhali kuwa anyi musu umurni da cewa su kafirce masa, kuma Shedan yana nufin ya baddasune bata mai nisa. Q4ayata60.
Amma wanda ya kasance a wata kasa da ba'a hukunci acikinta da abinda Allah Ya sawkar kuma ya bukatu zuwa ga kai kara wurin wanda yake zato cewa zai kiyaye (masa) hakkinsa ya kuma kawarda zalunci, to bazai kafirta ba (don ya kai kara), saboda fadin Annabi (S.A.W) ga sahabbansa yayin da yayi musu izini da yin hijira ta farko zuwa kasar Habasha:
((إنَّ بأرضِ الحَبَشةِ مَلِكًا لا يُظْلَمُ أحَدٌ عندَه، فالْحَقُوا ببلادِه حتى يَجْعَلَ اللهُ لكم فَرَجًا ومَخْرَجًا مِمَّا أنتم فيه)) رواهُ البَيْهقِيُّ من حديثِ أُمِّ سَلَمَةَ بإسنادٍ حَسَنٍ.
Ma'ana:"Lallai akasar habasha akwai wani sarki da ba'a zaluntar kowa awurinsa. Kutafi zuwa kasarsa har sai Allah Yayi muku budi da mafita daga abinda kuke ciki" Imamul Baihaki ne ya ruwaitoshi daga hadisin Ummu Salamata da isnadi mai kyaw.
Najashi (alokacin) bai riga ya Musuluntaba. Da ace wani zalunci ya faru garesu kuma suka bukatu zuwaga kai kara zuwa gareshi dangane dashi, da zaiyi musu adalci, kuma wannan daliline gameda halaccin kai kara zuwaga wanda aka san al'amarinsa cewa shi mai kokarin yin adalcine da kawarda zalunci, kamar yadda yakke faruwa awasu kasashen.
Kuma musulmi a cikin yanayi na rashin mafita da kuma tsananin bukatuwa wanda kubucewar damar ke iya kaiwa zuwaga kuncin da za'a kai kara zuwaga dagutu batareda nufi ba a hakikanin al'amari, to bazai kafirceba da wannan.
Amma kai karanda acikinsa akwai bawta ga wanin Allah (Madawkakin Sarki) da gabatarda garawa da tambayar bokaye kamar yadda wasu masu bawtar gumaka suke aikatawa, towannan bazai taba halattaba.
Nabiyu: Biyayya ga muggan malamai da mahukunta dagutai cikin halatta haram wanda yake mai bayyanannen hukunci a shari'a.
Kuma daidaikun shirka da misalanta suna dayawa kwarai, saidai dukkansu suna komawane zuwaga wadannan naw'ukan guda uku.
Abu na uku dake warware Musulunci:Da'war (sifantuwa) da wasu (sifofi da) Allah Ya kebanta dasu, cikin ayyukanSa ko cancantan bawta ko sunayen Allah da sifofinSa.
Daga cikin misalai akan haka:
Na farko:Kiranda wasu dagutai keyi zuwaga a bawta musu.
Nabiyu:Da'awar ilimin gaibu.
Na uku:Da'awar kudura akan rayar da matattu.
Abu na huda dake warware Musulunci shine: Da'awar annabta.
Da'awar annabta kafircine da ijma'in malamai.
Daga cikin abubuwanda zasu shiga karkashinsa:
Wanda yake da'awar kishiyantar Alkur'ani, kuma yana jin cewa shi zai iya sawkar da kwatankwacin abinda Allah Ya sawkar ga ManzanninSa. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَى عَلَى اللَّهِ كَذِبًا أَوْ قَالَ أُوحِيَ إِلَيَّ وَلَمْ يُوحَ إِلَيْهِ شَيْءٌ وَمَنْ قَالَ سَأُنْزِلُ مِثْلَ مَا أَنْزَلَ اللَّهُ﴾ [الأنعام: 93].
Ma'ana:"Kuma wanene yafi zalunci samada wanda ya kirkiri karya ya jinginata ga Allah, ko kuma yace anyi wahayi gareni alhali ba'ayi masa wahayin komai ba, da wanda yace da sanu zan sawkar da kwatankwacin abinda Allah Ya sawkar". Q6ayata93.
Abu na biyar dake warware Musulunci shine: Karyata Allah (Mai girma da dawkaka) da ManzonSa (S.A.W).
Duk wanda ya karyata Allah da Manzonsa kafirine, ba Musulmibane da ijma'in malamai.
Daga cikin misalan wannan:
Na farko:Karyata wani abu dayake sananne a Musulunci, kamar karyata wajibcin salla ko zakka ko karyat haramcin riba ko zina ko cin naman Alade.
Na biyu:Inkarin wani abu daga cikin sunayen Allah (Madawkakin Sarki) da sifofinSa, batareda wata shubuha ta jahilciba wacce ake iya yin uzuri da misalinta kuma bada tawiliba.
Na uku:Inkarin wani abu daga Alkur'ani Mai girma.
Na hudu:Imani da cewa akwai sabani, da tufka da warwara, da canji acikin Alkur'ani Mai girma.
Na biyar:Inkarin sunnar Annabi (S.A.W).
Na shida:Inkarin tashin Alkiyama da sakamako.
Na bakwai: Rashin kafirta wanda baya addini da addinin Musulunci daga Yahudawa, Nasara, Majusawa, masu karyata samuwar Allah da masu bawtar gumaka.
Na takwas:Imani da cewa bawa yana da daman fita daga shari'ar Annabi Muhammadu (S.A.W) kamar yadda Khadir yasamu dammar fita daga shari'ar Annabi Musa (A.S).
Na tara: Halatta haramtaccen abu da haramcinsa yake sananne bisa ingantaccen dalili ba tareda shubuha ba ko tawili.
Na goma: Gaskata wanda yake da'awar Annabta.
Na goma sha daya:Da'awar cewa lallai Manzancin Annabi (S.A.W) zuwaga larabawane kawai.
Na goma shabiyu:Da'awar cewa lallai Allah ya yarda da a kirayi wani daga cikin salihan bayi ko waninsu (sawran mutane).
Na goma shauku:Yin kazafi ga Uwar muminai A'isha (Allah Ya kara mata yarda) da abinda Allah Ya wanketa dagashi. Hakananma yin kazafi ga sawran iyayen muminai.
وكلُّ ما يَتحَقَّقُ به تَكْذيبُ اللهِ تعالى وتكذيبُ رَسولِه صلى الله عليه وسلم فهو ناقضٌ من نَواقضِ الإسلامِ، إلا أنه يَنْبَغِي التفريقُ بينَ تكذيبِ الخَبَرِ المَبْنيِّ على عدمِ العلمِ بالدليلِ أو غِيابِه عنه أو الشكِّ في ثُبوتِه أو كانَ للمُكَذِّبِ تأويلٌ في معنَى الخَبَرِ يُدْرَأُ عنه به حُكْمُ التكذيبِ، وبينَ تَكذيبِ ما عُلِمَ ثُبوتُه ومعناه، فهذا الأخيرُ ناقضٌ بلا خلافٍ بينَ أهلِ العلمِ.
Kuma duk abinda karyata Allah (Madawkakin Sarki)da karyata ManzonSa (S.A.W) yake tabbata da aikatashi, shima wanine daga cikin abubuwa masu warware Musulunci, saidai ya kamata a banbance tsakanin karyata labarinda ya ginu akan rashin sanin dalili ko rashin bayyanan dalilin gareshi ko shakka cikin tabbatarsa ko kuma mai karyatawar yana da wani tawili acikin ma'anar hadisin wanda hukuncin karyatawa zai tashi daga kansa a sanadinsa (Wannan) ya bambanta daga karyata abinda aka san tabbatarsa da ma'anarsa, to wannan na karshen kam yana warwarewa batareda wani sabaniba atsakanin ma'abuta ilimi.
Amma cikin halayenda aka ambata kafinsa, baza'ayi hukunci da kafircin wanda ya karyataba har sai an tsayar masa da hujja kuma an bayyana masa tabbatar hadisin da ingancin ma'anarsa.
Abu na shida dake warware Musulunci shine:Shakka.
Shakka tana kore gaskatawa na wajibi, saboda haka duk wanda yayi shakka cikin gaskiyar (wani) labari (daga) Allah (Mai girma da dawkaka) da labari daga ManzonSa (S.A.W), to shi kafirne ba mumini bane.
Kuma da karyatawa da shakka suna kore gaskatawa ta wajibi.
Daga cikin misalan wannan shine:
Na daya:Shakka cikin kafircin wanda baya addini da addinin Musulunci.
Na biyu:Shakka gameda al'amarin tayarda matattu.
Na uku: Shakka cikin tabbatar Alkur'ani Mai girma da kareshi daga tahrifi da canzawa.

Abu na bakwai dake warware Musulunci shine:Kin Allah da ManzonSa, da kin Addinin Musulunci.
Shi kiyayya yana kore soyayya ta wajibi, saboda haka duk wanda yayi gaba da Allah da ManzonSa ko kuma yayi gaba da addinin Musulunci.
Daga cikin abubuwanda zasu shiga karkashinsa;
Na daya:Zagin Allah da ManzonSa da zagin addinin Musulunci, da kaskantar da Zati tsarkakakkiya, da kaskantarda matsayin Annabi (S.A.W).
Na biyu:Yin gaba da sahabbai (Allah Ya kara musu yarda) da zaginsu ta fuskar gamewa da kafirtasu, sabanin wanda ya zagi wasu daga cikinsu sakamakon wata shubuha da ta bijiro gareshi, a wannan halin mutum zai kasance ya aikata haramun saidai baza'a yi mishi hukunci da kafirciba.
Na uku:Yin gaba da malaman addini da maruwaitan hadisai ingantattu da madawka shari'a ta fuskan gamewa da karyatasu.
Abu na takwas da yake warware Musulunci: Isgilanci ga Allah da ayoyinSa da ManzonSa, kuma (wannan aikin) kafircine sakamakon cin karonsa da soyayya ta wajibi da girmamawa.
Daga cikin abubuwanda zasu shiga karkashinsa:
Na farko:Walakanta Alkur'ani mai girma.
Na biyu:Kaskantar da wani daga cikin muhimman abubuwana addinin Musulunci.
Abu na tara da yake warware Musulunci: Rikon kafirai a matsayin majibinta koma bayan muminai, wannan ya kunshi al'amura biyu:
Na farko:Kawnarsu acikin addininsu da dacewa dasu acikinsa da yarda dashi.
Na biyu:Taimakon kafirai akan Musulmai.
Daga cikin misalai akan wannan nakidin:
Na farko:Leken asirin Musulmai domin maslahohin kafirai.
Na biyu:Taya kafirai murna gameda bukukuwansu na idinsu na bawtan gumaka da kafirci bisa yarda da abinda suke aikatawa na shirka da kafircewa Allah (Mai girma da sawkaka), amma wanda yayi tarayya dasu domin yaci abinci taredasu ko kuma don yaji dan dadi na haram gameda fasikancinsu da kadekadensu, alhali zuciyarsa na kin kafircinsu da shirkansu, to shi yana cikin hadari, kuma ana jiye masa tsoron kada sa'adda ukuba zata sawka akansu ta shafeshi taredasu.
Na uku:Gina wuraren bawta da ake bawtan wanin Allah (Mai girma da dawkaka) ko kuma taimakawa akansu, kamar; gina kanisoshi da wuraren bawtan yahudawa da wuraren bawtan nasara da gina makabartu da wuraren bawta da ake kiran wanin Allah (Mai girma da dawkaka) acikinsu.
Na hudu:Yakan wadanda ke dawke da shari'ar (musulunci) daga malamai da masu kira zuwaga Allah, da kuntatawa akan da'awar Musulunci.
Na biyar:Kokarin kaskantar da Musulmi da rawnanasu, da baiwa kafirai daman yin galaba akan Musulmai.
Abu na goma mai warware Musulunci:Juya baya(ga barin addini) da bijirewa.
Wanda duk ya juya baya ga barin yiwa Allah da ManzonSa biyayya, to shi ba Musulmi bane, domin shi bai kasance mai sallamawaba ga addinin Allah (Madawkakin Sarki), don haka shi baya aikata ayyuka na wajibi, kuma baya nisantan haramtattu sai dai abinda ya dace da son zuciyarsa.
Daga cikin misalai na wannan mai warwarewan:
Na farko:Shine mutum yaga cewa yiwa Allah biyayya da yiwa ManzonSa biyayya baya lazimtansa kuma bai wajaba agareshi ya aikata umurnin Allah (Madawkakin Sarki) da umurnin ManzonSa (S.A.W).
2Na biyu:Bijrewa daga bin umurnin Allah da bin umurnin ManzonSa bijirewa ga baki daya, saboda haka baya karatu don fahimtar addini, baya tambaya gameda abinda ke kansa na wajibi gameda da'a ga Allah da ManzonSa, baya aikata ayyukan da suka wajaba agareshi kuma baya nisantan haramtattun abubuwa don da'a ga Allah da ManzonSa.
Amma wanda yake lazimtan yiwa Allah da ManzonSa biyayya kuma yana aikata gwargwadon abinda zai tabbatar dashi a Musulunci, saidai shi yana awkawa cikin sabo, to shi ba kafiri bane da wannan sabon da yakeyi.
Daga cikin abubuwanda zasu shiga karkashin wannan (abu mai warware Musuluncin): Barin salla, salla itace gimshikin addini, saboda haka idan bawa ya barta bari ga baki daya, to shi mai juya baya ne daga addinin Allah (Mai girma da dawkaka) Umar dan Khaddabi yace: Duk wanda ya iya tozartata, to saiya fi tozarta wacce ba itaba.
Fasali: Kuma wadannan abubuwan masu warware Musulunci sauna masu korewane ga kalmomi biyu na shahada (wato shaidawa babu abin bawtawa da gaskiya sai Allah, da shaidawa lallai annabi Muhammadu Manzon Allah ne) dukkanin korewa. Duk wanda ya awka cikin dayansu bayan kasancewarsa Musulmi alhali yana cikin hankalinsa, balagagge ba tareda an tilastashiba, kuma bashida wata shubuha, to shi kafirine wanda yayi ridda daga addinin Musulunci. Idan ya mutu akan haka, to shi mai dawwama ne abin dawwamarwa acikin Wutar Jahannama. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَمَنْ يَرْتَدِدْ مِنْكُمْ عَنْ دِينِهِ فَيَمُتْ وَهُوَ كَافِرٌ فَأُولَئِكَ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ وَأُولَئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ﴾[البقرة: 217].
Ma'ana:"Kuma wanda yayi ridda daga cikinku ya bar addininsa kuma ya mutu alhali yana kafiri, to wadancan ayyukansu duk sun rushe a duniya da lahira, kuma wadancan sune ma'abuta Wuta, su acikinta, masu dawwamane" Q2ayata217.
Duk wanda ya awka cikin (aikata) daya daga wadannan abubuwan masu warware Musulunci ko (ya awka cikin) wani sashi daga ciki a badininsa (wato bisa abinda ke boye azuciyarsa) alahli azahiri yana bayyana cewa shi Musulmine, to shi munafikine babban munafurci, zamu mu'amalanceshi da irin mu'amalar Musulmi a zahiri, mu kuma maida abin da ke boye game dashi zuwaga Allah (Madawkakin Sarki) matukar kafirci bai bayyana mana daga gareshi ba bayyanata azahiri.
Fasali:
Kuma abubuwa masu warware Musulunci suna kan darajojine guda biyu:
Daraja ta farko: Kafirci karara, shine wanda babu wata tantama ko rashin bayyana gameda kafircin wanada ya aikatashi, kuma babu yiwuwan ace yana da wani uzuri da za'a bashi uzuri akai na jahilci ko tawili ko tilastawa.
Kamar wanda yake nasabtuwa zuwaga wanin Musulunci ko kuma yake bawtan wanin Allah (Mai girma da dawkaka) da wanda ke zagin Allah da ManzonSa, da wanda ke yin isgilanci game da Addini da wanda ke inkarin Alkur'ani ko sunna ko yake jayayya cikin abuda yake sananne a cikin addini bisa lalura tareda bayyanan cewa yanada sani akan hakan.
To ma'abuta wannan darajar, ana hukunci da cewa sun kafirta, da kuma cewa su yan Wutane idan muka samu tabbacin cewa sun mutu akan haka. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿مَا كَانَ لِلنَّبِيِّ وَالَّذِينَ آَمَنُوا أَنْ يَسْتَغْفِرُوا لِلْمُشْرِكِينَ وَلَوْ كَانُوا أُولِي قُرْبَى مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُمْ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ﴾ [التوبة: 113].
Ma'ana:"Bai dacewa ga Annabi da wadanda sukayi imani su nemawa mushrikai gafara koda kuwa sun kasance ma'abuta kusancine bayan ya bayyana agaresu cewa lallai su ma'abuta Wutar Jahima ce. Q9ayata113.
Daraja ta biyu: Abinda bai kasance kafirci na kararaba, shima naw'ukane guda biyu:
Naw'i na farko: Abinda yake yiwuwa wanda ya aikatashi ya samu wani uzurin da za'ayi masa uzuri akai, kamr tilastawa ko gushewan hankali ko wata shubuha ta tawili ko jahilcin da zai iya zama uzuri wanda yana bukatan a tsayar masa da hujja akai, idan hujja ta isa gareshi kuma ya fahimci ma'anarta amma ya doge akan aikinsa baya gaskiya ta bayyana gareshi, to sai ayi hukunci gameda kafircinsa. Idan kuma shubuhar bata gusheba tana nan taredashi, to baza'ayi masa hukunci da kafirci ba.
Wannan shi yasa malaman Ahlu-ssunnah suka kame daga kafirta wasu daga cikin yan dariku masu inkarin wasu daga cikin sunayen (Allah) da sifofin (Sa) saboda shubuha ta tawili, tareda yin hukunci da cewa su yan bidi'ane kuma fasikaine su kuma da cewa shubuha bazata zama mafita agaresu gameda abinda sukayi na sabawa (shari'a) saidai zata hana a kafirtasu.
Acikin irin wannan ne ake hukunci da cewa aiki kafircine amma ba'a kafirta wani bisa ayyanawa har sai sharudda sun cika akansa kuma duk abubuwanda ke iya hana a kafirtashi sun kaw.
Naw'i na biyu: Shine kasancewar abunda ke warware Musuluncin yana daga cikin abubuwanda akayi sabani akansu, sai mai bincike ya awka cikin yar rudani da rashin rinjayin ra'ayi.
Hakika malamai sun yi sabani gameda wasu abubuwanda ke warware Musulunci, daga cikinsu:
Na farko:Barin salla saboda kasala da rashin kulawa ba tareda inkarin wajibcintaba kuma ba tareda girman kai ba gameda aikatata.
Ingantacciyar Magana itace, lallai wanda ya barta bari na dindindin, to ya kafirta, amma wanda yake salla a wasu lokuta kuma ya bar salla a wasu lokutan, to shi fasikine, wanda akayiwa alkawarin narkon azaba sakamakon sakacinsa cikin farillai, saidai baza'ayi hukunci da cewa ya kafirtaba.
Wannan maganar itace matsakaiciyar magana atsakanin maganganu biyu;
Maganata farko: Cewa zai kafirta da barin salla daya.
Magana ta biyu: Cewa bazai kafirtaba koda ya barta kwata kwata.
Na biyu: Sihiri, hakika malamai sunyi sabani gameda kafircin wanda ya koyi sihiri kuma ya koyardashi da wanda ke aiki da sihiri, amma ingantaccen zance shine, sihiri baya taba yiwuwa face ta hanyar kafirci da babbar shirka, kamar neman tsari daga shedanu, da neman kusanci zuwa garesu ta hanyar yanka da bakance, da walakanta abinda Allah Yayi umurni da girmamawa, kuma babu sabani tsakanin malamai gameda kafircin wanda ya aikata wadannan ayyukan.
Saidai daga cikin malamai, akwai wanda ke ambaton suddabaru da rufa ido da sunan sihiri, kuma daga cikinsu akwai wanda ke lissafa abinda wasu keyi na dabarbaru su shayarda wasu kwayoyi ko jiko dake da tasiri akan hankalin mutum da rayuwarsa da hayyacinsa da sunan sihiri, saboda haka basa kafirta masihirci kai tsaye har sai sunyi bincike gameda naw'in sihirinsa, idan sihirinsa ya kasance ta hanyar neman agaji daga shedanu da kuma neman kusanci zuwa garesune, sai suyi hukunci da cewa ya kafirta, idan kuma sihirinsa ya kasance ne ta wata hanyar dabam da wannan, sai suyi hukunci da cewa a ladabtar da shi gwargwadon ladabtarwadda zata zama masa gargadi gameda wannan aikin, amma bazasu kafirtashiba.
Na uku: Barin zakka da azumi da hajji, hakika wasu malamai sun tafi akan kafircin wanda ya bar wani abu daga cikin wadannan farillan, koda kuwa baiyi inkarin wajibcinsuba. Amma zance ingantacce shine, baza'ayi hukunci da kafircin wanda ya barsuba saidai idan ya kasance yana inkarin wajibcinsu, a wannan lokacin kam sai ayi hukunci da cewa ya kafirta saboda kasancewarsa mai karyata Allah da ManzonSa.
Kuma hakika ingantattun hadisai sunyi nuni zuwaga cewa lallai wanda ya bar wadannan farillan za'ayi mar azaba a lahira, sannan sai anuna masa hanyarsa, kodai zuwa Aljanna ko kuma zuwa Wuta, kuma wannan daliline dake nuni zuwaga rashin tabbatan kafircinsa.
Fasali: Kuma wasu daga cikin abubuwa masu fitarwa daga Addini sukan kunshi abubuwa masu warware Musulunci samada daya, saboda haka sai ya kasance kafirci ta fiskoki samada daya.
Misalin haka: Wanda ke hukunci da sabanin abinda Allah Ya sawkar kuma yana cewa yin hakan halalne kuma yana fifita hukuncin dagutu akan hukuncin Allah (Mai girma da dawkaka).
To shi kafirine ta fiskoki samada daya:
Na farko: Shi kafirine sakamakon yin hukunci da sabanin abin da Allah Ya sawkar kuma da sanya kansa amatsayin abokin tarayya ga Allah a cikin hukuncinSa.
Na biyu: Kuma shi kafirine sakamakon halattawarsa ga abinda haramcinsa a Musulunci yake sanannene bisa larura.
Na uku: Kuma shi kafirine sakamakon ya karyata Allah da ManzonSa kuma ya fifita hukuncin dagutu akan hukuncin Allah (Mai girma da dawkaka).
Kuma daga cikin abubuwanda ya kamata a sani shine, cewa lallai wasu kafirai da wadanda sukayi ridda sukan fada cikin naw'uka mabambanta na abubuwanda ke warware Musulunci, wasunsu sukan awka cikin babbar shirka da karyata Allah da ManzonSa da kin Addinin Musulunci da jibintan al'amarin kafirai da sawransu cikin abubuwa masu warware Musulunci.
Kuma duk sa'adda bawa ya faye awkawa cikin wadannan abubuwa masu warware Musuluncin zai kasance mafi tsananin kafirci, saboda haka kuwa azabarsa zata fi tsanani tareda cewa dukkaninsu sunyi tarayya acikin fita daga Musulunci.
Fasali: Kafirci naw'i biyune; kafircin zahiri da kafircin badini.
Amma shi kafircin badini shine wanda keda alaka da halin bawa tsakaninsa da Allah, mutum yana iya zama kafiri a badini sakamakon ya aikata abinda ke warware Musulunci, alhali shi a yadda mutane ke ganinsa mai bayyana Musuluncine, daga wannan lokacin zai zama munafiki kenan wanda za'a yiwa mu'amala irin ta musulmi azahiri, amma shi alahira yana tareda kafirai acikin Wutar Jahannama yana mai dawwama acikinta.
Kuma daga cikin mutane akwai wanda zai aikata wani abu wanda ke ware Musulunci ga zahiri a wurin mutane, amma kuma ya kasance yanada abinda za'ayi masa uzuri dashi kamar gushewar hankali ko jahilcin da akeyiwa mutum uzuri dashi ko kuma yakasance sabon Musuluntane shi saboda haka wasu kalmomi na kafirci daya saba dasu surika fitowa daga bakinsa batareda cewa yana imani dasuba, yana yiwuwa ayi hukunci da kafircewarsa a zahiri alhali kuma a hakikanin al'amari yanada abinda zaisa ayimasa uzuri.
Kuma ana tada Mutumne ranar kiyama bisa abinda ya mutu akai na imani ko na kafirci.
Kuma a asali yin hukunci dacewa mutum ya kafirta na malamaine da masu mulki, amma yakan iya fita daga asalin sakamakon abubuwa da zasu bijiro su hukunta bukatuwa zuwaga hakan da kuma kasancewarsa yana alaka da aiki.
Kuma yana daga cikin abinda yakamata a kiyaye, gaggawar kafirta wanda kafircinsa bai bayyanaba. Saboda fadin Annabi (S.A.W):
(( إِذَا قالَ الرَّجُلُ لأخيهِ: يَا كافرُ، فقَدْ باءَ بها أحدُهمَا، فإنْ كانَ كمَا قالَ، وإلاَّ رَجَعَتْ عليهِ )) مُتَّفقٌ عليه من حديثِ ابنِ عُمَرَ رضِي الله عنهما.
Ma'ana:"Idan mutum yace wa dan'uwansa; ya kai kafiri! To hakika daya daga cikinsu ya koma da ita (wato kalmar), idan ya kasance kamar yadda ya fada to, idan kuma bahakabane sai kalamar ta koma kansa" Buhari da Muslimne suka ruwaitoshi daga hadisin Dan Umar (Allah Ya kara musu yarda).
Kuma daga Abu Zarrin (Allah Ya kara masa yarda) yaji Manzon Allah (S.A.W) yana cewa:
(( مَنْ دَعَا رَجُلاً بالكُفْرِ، أو قالَ: عَدُوَّ اللهِ، وَلَيْسَ كَذَلِكَ إلاَّ حَارَ عَلَيْهِ )). مُتَّفَقٌ عليه.
Ma'ana:"Duk wanda ya kira wani mutum da kafirci, ko kuma yace masa; makiyin Allah alhali bahaka bane face ta koma kansa" Buhari da Muslimne suka ruwaitoshi.
Kuma wannan gargadin ya shafi abinda ke gudanane ta fuskar zagi da gaggawar yin hukunci batareda cancantaba, amma malami mujtahidi idan yayi kuskure acikin hukuncinsa ayayinda aka bukatu zuwa gareshi batareda yayi sakaciba ko bin son zuciya, to lallai za'a bashi ladan ijtihadinsa kuskurensa kuma abun gafartawane.
Fasali: Hakika malamai sunyi ijma'I akan wajabcin kasha wanda yayi ridda saboda fadin Annabi (S.A.W):
((مَن بَدَّلَ دِينَهُ فَاقْتُلُوهُ)) رواهُ البُخاريُّ من حديثِ ابنِ عَبَّاسٍ رضِي الله عنهما.
Ma'ana:"Wanda ya canza addininsa ku kasheshi" Imamul Bukharine ya ruwaitoshi daga hadisin Dan Abbas (Allah Ya kara musu yarda).
Kuma wanda ya mutu ahalin ridda, baza'a yi masa wankaba kuma baza'ayimasa likkafaniba kuma baza'a yi masa salla ba kuma baza'a binneshi a makabartan musulmiba kuma baza'a gadarda dukiyansaba kuma baza'a yimasa addu'aba bayan mutuwarsa.
Amma batun anemi ya tuba kafin a kasheshi kuma, to wannan yana komawane zuwa ga ijtihadin shugaba, idan ya kasance yana tsammanin komawarsa musulunci ko kuma yanada wata shubuha da ta bijiro masa wacce yayi riddan asanadinta, to (shugaba) ya samu dama ya jinkirta masa harna tsawon kwana uku, kuma ya bijiromasa da zancen komawa musulunci, idan ya tuba (shi kenan) idan kuma bai tubaba, sai a kasheshi alhali yana riddajje.
Idan kuma shugaba yaga cewa cikin gaggawta kasheshi akwai maslaha ga musulmi, kamar ya kasance mai tsananin cutarwa ga musulmi bayan yayi ridda, ko kuma ya zamanto akwai fitina da cutarwa ga musulmi a cikin jinkirta kasheshi, to sai yayi gaggawar kasheshi matukar bai tubaba kafin samun iko akansa.
Ya ubangijinmu Ka rayamu muna musulmai, kuma Ka kashemu muna musulmai, kuma Ka riskar damu ga salihai, kuma Ka karemu daga kaskancin Duniya da azaban Lahira, ya Ubangijinmu, lallai Kai mai tawsasawane mai jin kai.