المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : الدرسُ الحاديَ عَشَرَ: التحذيرُ من النِّفاقِ (3/3)


طاهر جبريل دكو
_7 _April _2013هـ الموافق 7-04-2013م, 11:46 AM
الدرسُ الحاديَ عَشَرَ: التحذيرُ من النِّفاقِ (3/3)

عُقوبةُ المُنافِقِ
جعَلَ اللهُ تعالى عُقوبةَ المُنافقينَ من أشْنَعِ العُقوباتِ في الدنيا والآخرةِ جَزَاءً وِفَاقًا لأعْمَالِهِم:
• فأمَّا في الدنيا فإنهم يُعاقَبُونَ بالطَّبْعِ على قُلُوبِهم وحِرْمانِهم من الفِقْهِ والعِلْمِ والهُدَى، ويُعْقِبُهم اللهُ في قُلوبِهم شَكًّا ورِيبَةً لا تُفارِقُهُم أَبَدًا، فهم من أعظمِ الناسِ حَيْرَةً وتَرَدُّدًا؛ وذلك لأنهم أرادُوا أن يُخادِعُوا اللهَ ويَخْدَعُوا المُؤْمِنينَ، فانقَلَبَ خِداعُهم عليهم، وذاقوا وَبالَ أمْرِهم وعَاقِبةَ مَكْرِهم؛ فكانوا كُلَّما عَمِلوا عَمَلاً للكيدِ للإسلامِ وأهلِه جَعَلَ اللهُ عُقوبتَه عليهم أشنعَ من حيثُ لا يَشْعُرونَ؛ فهم يَسْتَزِيدُونَ من أعمالِ الكُفْرِ والنِّفاقِ، والعُقوباتُ تَتَضاعَفُ وتَتْرَى عليهم.
قال اللهُ تعالى: ﴿فَطُبِعَ عَلَى قُلُوبِهِمْ فَهُمْ لَا يَفْقَهُونَ﴾ [المنافقون: ٣].
وقال تعالى: ﴿أُولَئِكَ الَّذِينَ اشْتَرَوُا الضَّلَالَةَ بِالْهُدَى فَمَا رَبِحَتْ تِجَارَتُهُمْ وَمَا كَانُوا مُهْتَدِينَ (16) مَثَلُهُمْ كَمَثَلِ الَّذِي اسْتَوْقَدَ نَارًا فَلَمَّا أَضَاءَتْ مَا حَوْلَهُ ذَهَبَ اللَّهُ بِنُورِهِمْ وَتَرَكَهُمْ فِي ظُلُمَاتٍ لَا يُبْصِرُونَ (17) صُمٌّ بُكْمٌ عُمْيٌ فَهُمْ لَا يَرْجِعُونَ (18)﴾ [البقرة: ١٦–١٨].
–وقال تعالى: ﴿إِنَّ الْمُنَافِقِينَ يُخَادِعُونَ اللَّهَ وَهُوَ خَادِعُهُمْ﴾ [النساء: ١٤٢]، وخَدْعُ اللهِ إيَّاهم من باب مجازاتهم بجنسِ أعمالِهم، وهو عُقوبةٌ لهم على قُبْحِ أقوالهم وأَفْعَالِهم، وسُوءِ ظَنِّهم باللهِ جل وعلا، ومُخادَعَتِهم للهِ وللذينَ آمَنوا، ومُحادَّتِهم للهِ ومُحارَبَتِهم لدينِه بمَكْرٍ وخَدِيعةٍ.
فهم بهذه الأعمالِ إنما يَخْدَعُونَ أنفسَهم كما قال تعالى: ﴿يُخَادِعُونَ اللَّهَ وَالَّذِينَ آمَنُوا وَمَا يَخْدَعُونَ إِلَّا أَنْفُسَهُمْ وَمَا يَشْعُرُونَ﴾ [البقرة: ٩]؛ فهم لا يَشْعُرونَ بأنهم يَخْدَعُون أنفسَهم؛ بل يُمَنُّون أنفسَهم الأمانِيَّ الباطلةَ، ويَجْرُونَ وَرَاءَها حتى تَغُرَّهم وتَفْتِنَهم، ويَسْتزِيدُونَ من الإثمِ والكُفْرِ والفُسوقِ والعِصْيانِ والضلالِ، ويَحْسَبُونَ أنهم يُحْسِنُونَ صُنْعًا.
وهم في كلِّ ذلك لم يَضُرُّوا إلا أنفسَهم، لم يَضُرُّوا اللهَ شيئًا ولم يَضُرُّوا رسولَه ولا المُؤمنين المُتَّبعينَ لهُدَى اللهِ جل وعلا.
–ومِمَّا يُعاقَبُونَ به في الدنيا: أنهم يُعذَّبُونَ بأموالِهم وأولادِهم حتى تَزْهَقَ أنفُسُهم، كما قالَ اللهُ تعالى: ﴿وَلَا تُعْجِبْكَ أَمْوَالُهُمْ وَأَوْلَادُهُمْ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ أَنْ يُعَذِّبَهُمْ بِهَا فِي الدُّنْيَا وَتَزْهَقَ أَنْفُسُهُمْ وَهُمْ كَافِرُونَ﴾ [التوبة: ٨٥].
–ومِمَّا يُعاقَبُونَ به أيضًا: ما يَجْعَلُه اللهُ لهم مِن البَغْضَاءِ في قُلوبِ الناسِ مهما تَوَدَّدُوا إليهم؛ وذلك لأنَّهم طَلَبُوا رِضَا الناسِ بسَخَطِ اللهِ، وآثَرُوا الحياةَ الدنيا على الآخرةِ، واتَّبَعوا ما أسْخَطَ اللهَ وكَرِهوا رِضْوانَه، وأعْرَضُوا عن اتِّباعِ هُدَى اللهِ فعَرَّضوا أنفسَهم لأنواعٍ من الخوفِ والحَزَنِ والضَّلالِ والشَّقَاءِ الذي كَتَبَه اللهُ على مَن أعْرَضَ عن اتِّباعِ هُداهُ.
وقالَ اللهُ تعالى في طائفةٍ منهم: ﴿لَا يَزَالُ بُنْيَانُهُمُ الَّذِي بَنَوْا رِيبَةً فِي قُلُوبِهِمْ إِلَّا أَنْ تَقَطَّعَ قُلُوبُهُمْ وَاللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ﴾ [التوبة: ١١٠].
قال بعضُ المُفَسِّرِينَ: ﴿إِلَّا أَنْ تَقَطَّعَ قُلُوبُهُمْ﴾ هذا استثناءٌ تَهكُّميٌّ، وهو من سُخْرِيَةِ اللهِ بهم جَزَاءً وِفاقًا على مَكْرِهم بالمؤمنين وسُخْرِيَتِهم بهم، وكَيْدِهم لهم ليُشَبِّهوا عليهم ويُضِلُّوهم عن سبيلِ الله، فكانَ من عُقوبتِهم أن ابْتُلوا بالرِّيبةِ التي لا تُفارِقُ قُلوبَهم أبدًا حتى يَلْقَوا اللهَ عز وجل.
هذا معَ ما يُصِيبُهم من العُقوباتِ الخَاصَّةِ ببَعْضِ أعمالِهم؛ فإنَّ اللهَ تعالى قد جَعَلَ لبعضِ الذُّنوبِ عُقوباتٍ خاصةً ليكونَ الجزاءُ من جِنْسِ العَمَلِ، كما قال اللهُ تعالى في طائفةٍ منهم: ﴿الَّذِينَ يَلْمِزُونَ الْمُطَّوِّعِينَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ فِي الصَّدَقَاتِ وَالَّذِينَ لَا يَجِدُونَ إِلَّا جُهْدَهُمْ فَيَسْخَرُونَ مِنْهُمْ سَخِرَ اللَّهُ مِنْهُمْ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ﴾ [التوبة: ٧٩].
فكان مِن عُقوبةِ سُخْرِيَتِهم بالمؤمنينَ أن سَخِرَ اللهُ منهم جَزَاءً وِفاقًا.
والمنافقونَ يَقَعُونَ كثيرًا في الذنوبِ التي يكونُ جَزَاؤُها من جنسِ العملِ في الدنيا قبلَ الآخرةِ، كما ورَدَ في السُّنةِ أن مَن تَتَبَّعَ عَوْرةَ مُسلمٍ تَتَبَّعَ اللهُ عَوْرتَه، ومَن ضَارَّ مُسلمًا ضَارَّه اللهُ، ومَن شاقَّ مُسلِمًا شَقَّ اللهُ عليه، ومَن خَذَلَ مُسلمًا خَذَلَه اللهُ، ومَن شَدَّدَ على المسلمين شَدَّدَ اللهُ عليه.
والمُنافقون أصحابُ مَكْرٍ سَيِّئٍ وقد قالَ اللهُ تعالى: ﴿وَلَا يَحِيقُ الْمَكْرُ السَّيِّئُ إِلَّا بِأَهْلِهِ﴾ [فاطر: ٤٣].
فهذا بيانُ شَيْءٍ مِمَّا يُصِيبُهم من العذابِ في الدنيا.

• وأما في البَرْزخِ: فإنهم إذا فارقوا هذه الحياةَ وأُدْخِلوا في قُبورِهم فإنهم في عذابٍ عظيمٍ وشَقاءٍ دائمٍ وحَسْرةٍ لا تَنْقطِعُ؛ فعن أنسِ بنِ مالكٍ رضِي الله عنه عن النبيِّ صلى الله عليه وسلم أنه قال: ((إنَّ العبدَ إذا وُضِعَ في قَبْرِه وتَولَّى عنه أصحابُه، وإنه لَيَسْمَعُ قَرْعَ نِعالِهم، أتاهُ مَلَكانِ فيُقْعدانِه فيَقولانِ: ما كُنْتَ تقولُ في الرَّجُلِ؟ لمُحمَّدٍ صلى الله عليه وسلم.
فأمَّا المُؤمنُ فيَقولُ: أشْهَدُ أنه عبدُ اللهِ ورَسولُه.
فيُقالُ له: انْظُرْ إلى مَقْعَدِكَ من النارِ قد أبْدَلَكَ اللهُ به مَقْعَدًا من الجَنَّةِ فيَرَاهما جَمِيعًا.
وأمَّا المُنافِقُ والكَافِرُ فيُقالُ له: ما كُنْتَ تَقولُ في هذا الرَّجُلِ؟
فيَقُولُ: لا أَدْرِي، كنتُ أَقولُ ما يَقولُ النَّاسُ.
فيُقالُ: لا دَرَيْتَ ولا تَلَيْتَ، ويُضْرَبُ بمَطَارِقَ من حديدٍ ضَرْبةً فيَصِيحُ صَيْحةً يَسْمَعُها مَن يليهِ غيرَ الثَّقَلينِ)) مُتَّفقٌ عليه.
معَ ما يُصِيبُهم من العُقوباتِ الخاصَّةِ على بعضِ الذنوبِ، كما صحَّ في السُّنةِ أنَّ الَّذي يَقْرَأ القُرْآنَ ويَرْفُضُهُ ويَنَامُ عن الصَّلاةِ المَكْتوبةِ يُعَذَّبُ في قَبْرِه، وكذلك الزُّناةُ وآكِلُو الرِّبا وأهلُ الغِيبَةِ والنَّميمةِ والكَذِبِ، ومانعو الزَّكاةِ والذين يُفْطِرونَ قبلَ تَحِلَّةِ فِطْرِهم، كلُّ أولئك وَرَدَتْ فيهم أحاديثُ صحيحةٌ بأنهم يُعذَّبُونَ في قُبورِهم، والمنافقون لهم النَّصِيبُ الأَوْفَرُ من هذهِ الأعمالِ.

• وأمَّا في الآخرةِ: فقد دَلَّت الأحاديثُ الصحيحةُ على أنه إذا كانَ يومُ القيامةِ، وجَمَعَ اللهُ الناسَ في مَوْقِفٍ واحدٍ لفَصْلِ القَضاءِ، ثم أَمَرَ بالكُفَّارِ إلى نَارِ جَهَنَّم بَقِيَ المُؤمنونَ والمنافقونَ وغُبَّرُ أهلِ الكتابِ في المَوْقِفِ (( فيُكْشَفُ عن سَاقٍ فلا يَبْقَى أحَدٌ كانَ يَسْجُدُ طَائِعًا في الدنيا إلا أُذِنَ له في السُّجودِ، ولا يَبْقَى أحَدٌ كانَ يَسْجُدُ رِياءً أو نِفاقًا إلا صَارَ ظَهْرُه طَبَقَةً وَاحِدَةً كُلَّما أرادَ أن يَسْجُدَ خَرَّ لِقَفَاهُ)).

وفي الحسابِ يُؤْتَى بالمُنافقِ فيُعَرِّفُه اللهُ نِعَمَهُ عليه، فيَقولُ المُنافِقُ: يا رَبِّ، آمَنْتُ بكَ وبكتابِك وبرُسُلِكَ وصَلَّيْتُ وصُمْتُ وتَصَدَّقْتُ ويُثْنِي على نفسِه بخيرٍ ما استطاعَ.
فيُقالُ له: الآنَ نَبْعَثُ شَاهِدًا عليك.
فيَتَفَكَّرُ في نفسِه مَن ذا الذي يَشْهَدُ عَلَيَّ، فيُخْتَمُ على فِيهِ، ويُقالُ لفَخِذِهِ ولَحْمِهِ وعِظَامِه: انْطِقِي.
فتَنْطِقُ فَخِذُه ولَحْمُه وعِظَامُه بعَمَلِه، وذلكَ لِيَعْذُرَ من نَفْسِه.
قال النبيُّ صلى الله عليه وسلم: ((وذَلِكَ المُنافِقُ، وذلك الذي يَسْخَطُ اللهُ عليه)).
والحديثُ في صَحِيحِ مُسلمٍ من حديثِ أبي هُرَيرةَ رضِي اللهُ عنه.

فإذا نُصِبَ الصِّراطُ على مَتْنِ جَهَنَّم وأُمِرَ بالعُبورِ عليه، وأُعْطِيَ مَن في المَوْقِفِ نُورًا على قَدْرِ أعمالِهم أُعْطِيَ المُنافِقُونَ نُورًا مِثْلَهم فِتْنَةً لهم؛ حتى إذا كانوا على الصِّراطِ طَفِئَ نورُ المنافقين وتَمَّ نورُ المُؤمِنِينَ، كما قال اللهُ تعالى: ﴿يَوْمَ تَرَى الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ يَسْعَى نُورُهُمْ بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَبِأَيْمَانِهِمْ بُشْرَاكُمُ الْيَوْمَ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ذَلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ (12) يَوْمَ يَقُولُ الْمُنَافِقُونَ وَالْمُنَافِقَاتُ لِلَّذِينَ آَمَنُوا انْظُرُونَا نَقْتَبِسْ مِنْ نُورِكُمْ قِيلَ ارْجِعُوا وَرَاءَكُمْ فَالْتَمِسُوا نُورًا فَضُرِبَ بَيْنَهُمْ بِسُورٍ لَهُ بَابٌ بَاطِنُهُ فِيهِ الرَّحْمَةُ وَظَاهِرُهُ مِنْ قِبَلِهِ الْعَذَابُ (13) يُنَادُونَهُمْ أَلَمْ نَكُنْ مَعَكُمْ قَالُوا بَلَى وَلَكِنَّكُمْ فَتَنْتُمْ أَنْفُسَكُمْ وَتَرَبَّصْتُمْ وَارْتَبْتُمْ وَغَرَّتْكُمُ الْأَمَانِيُّ حَتَّى جَاءَ أَمْرُ اللَّهِ وَغَرَّكُمْ بِاللَّهِ الْغَرُورُ (14) فَالْيَوْمَ لَا يُؤْخَذُ مِنْكُمْ فِدْيَةٌ وَلَا مِنَ الَّذِينَ كَفَرُوا مَأْوَاكُمُ النَّارُ هِيَ مَوْلَاكُمْ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ (15)﴾ [الحديد: ٢–١٥]

وأما عَذَابُهم في نارِ جَهَنَّم فهو العَذابُ المُهِينُ الأليمُ والوبيلُ المُقِيمُ، كَتَبَ اللهُ لهم الدَّرْكَ الأسْفَلَ فيها، فهم مِن أشَدِّ أهلِ النارِ عَذابًا.
قال اللهُ تعالى: ﴿إِنَّ الْمُنَافِقِينَ فِي الدَّرْكِ الْأَسْفَلِ مِنَ النَّارِ وَلَنْ تَجِدَ لَهُمْ نَصِيرًا﴾ [النساء: ١٤٥].
وهم بسَبَبِ كُفْرِهم الباطِنِ ومُوالاتِهم للكُفَّارِ جَمَعَهم اللهُ بالكافرينَ في نارِ جَهَنَّم كما قال تعالى: ﴿إِنَّ اللَّهَ جَامِعُ الْمُنَافِقِينَ وَالْكَافِرِينَ فِي جَهَنَّمَ جَمِيعًا﴾[النساء: ١٤٠].
وقال تعالى: ﴿وَعَدَ اللَّهُ الْمُنَافِقِينَ وَالْمُنَافِقَاتِ وَالْكُفَّارَ نَارَ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا هِيَ حَسْبُهُمْ وَلَعَنَهُمُ اللَّهُ وَلَهُمْ عَذَابٌ مُقِيمٌ﴾ [التوبة: ٦٨].

طاهر جبريل دكو
_7 _April _2013هـ الموافق 7-04-2013م, 11:48 AM
Darasi na shadaya: Gargadi gameda munafurci 3\3
Ukubar munafuki.
Allah (Madawkakin Sarki) Ya sanya ukubar munafukai daga mafi munin ukubobi aDuniya da Lahira sakamako kwatankwacin ayyukansu.
Amma (sakamakonsu) a Duniya, lallai su za'ayi musu ukuba da sanya toshiya a zukatansu, da kuma haramta musu fahimta da ilimi da shiriya. Kuma Allah zai gadar musu da shakka a zukatansu da kokwanto bazata rabu dasu ba har abada. Saboda haka sune mafiya rudani da kai komo acikin Mutane, wannan kuwa (ya kasancene) saboda sunyi nufin yin yawdara ga Allah kuma su yawdari muminai, sai yawdararsu ta koma kansu. Kuma suka dandani azaba game da al'amarinsu da ukuba gameda makircinsu, sai suka kasance duk sa'adda suka aikata wani aiki don kaidi ga Musulunci da ma'abutansa, sai Allah Ya sanya ukubarSa aknsu mafi muni ta inda basuyi tsammaniba, saboda haka su suna cikin neman karine cikin ayyukan kafirci da munafurci, ukuba kuma tana ninninkuwa akansu wata bayan wata. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿فَطُبِعَ عَلَى قُلُوبِهِمْ فَهُمْ لَا يَفْقَهُونَ﴾ [المنافقون: ٣].
Ma'ana:"Sai aka sanya toshiya akan zukatansu, saboda haka basa fahimta" Q63ayata3.
Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
وقال تعالى: ﴿أُولَئِكَ الَّذِينَ اشْتَرَوُا الضَّلَالَةَ بِالْهُدَى فَمَا رَبِحَتْ تِجَارَتُهُمْ وَمَا كَانُوا مُهْتَدِينَ (16) مَثَلُهُمْ كَمَثَلِ الَّذِي اسْتَوْقَدَ نَارًا فَلَمَّا أَضَاءَتْ مَا حَوْلَهُ ذَهَبَ اللَّهُ بِنُورِهِمْ وَتَرَكَهُمْ فِي ظُلُمَاتٍ لَا يُبْصِرُونَ (17) صُمٌّ بُكْمٌ عُمْيٌ فَهُمْ لَا يَرْجِعُونَ (18)﴾ [البقرة: ١٦–١٨].
Ma'ana:"Wadannan sune wadanda suka sayi bata da shiriya, sai fatawcinsu bai yi riba ba kuma basu kasance masu shiryuwa ba (16) Misalinsu shine misalin wanda ya hura wuta, yayin da ta haska abinda ke gefensa (na abin tsoro) sai Allah Ya tafiyar da haskensu kuma Ya barsu acikin duffai basu gani (17) Kurame, bebaye, makafi saboda haka basu komowa (18). Q2ayata16-18.
Kuma (Allah Madawkakin Sarki) Yace:
–وقال تعالى: ﴿إِنَّ الْمُنَافِقِينَ يُخَادِعُونَ اللَّهَ وَهُوَ خَادِعُهُمْ﴾ [النساء: ١٤٢]،
Ma'ana:"Lallai ne munafukai suna yin yawdara ga Allah alhali kuwa Shi ne mai yawdararsu. Q4ayata142.
Kuma yawdarar da Allah Yake musu Yana babin yi musu sakamakone da jinsin ayyukansu, sakamakone akan munin maganganunsu da ayyukansu, da mummunan zatonsu gameda Allah (Mai girma da dawkaka) da yawdararsu ga Allah kuma ga wadanda sukayi imani, da kiyayyarsu ga Allah da yakan addininSa da makirci da yawdara.
Da wadannan ayyukan, lallai su yawdarar kansu kawai sukeyi kamar yadda Allah (Madawkwkin Sarki) Yace:
﴿يُخَادِعُونَ اللَّهَ وَالَّذِينَ آمَنُوا وَمَا يَخْدَعُونَ إِلَّا أَنْفُسَهُمْ وَمَا يَشْعُرُونَ﴾ [البقرة: ٩]؛
Ma'ana:"Suna yin yawdara ga Allah da wadanda sukayi imani, alhali basu yawdarar kowa face kawukansu kuma basu sakankancewa" Q2ayata9.
Saboda haka su basu sakankancewa cewa lallai su suna yawdarar kawukansune. A'a suna yiwa kawukansu burace buracenema nakarya kuma suna gudana abayansa har sai ya rudesu kuma ya fitinesu. Kuma suna karuwa cikin zunubi da kafirci da fasikanci da sabon (Allah) da bata kuma suna tsammanin cewa kyawtata aiki sukeyi.
Su acikin haka baki dayay basu cutar kowa face kawukansu, basu cutar da Allah da komai ba, kuma basu cutar ManzonnSa da komai ba hakanan ma muminai mabiya shiriyar Allah (Mai girma da dawkaka).
Daga cikin abubuwanda za'ayi musu ukuba dasu a Duniya, lallai za'ayi musu azaba da dukiyoyinsu da yayansu har sai rayukansu sun fice. Kamar yadda Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَلَا تُعْجِبْكَ أَمْوَالُهُمْ وَأَوْلَادُهُمْ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ أَنْ يُعَذِّبَهُمْ بِهَا فِي الدُّنْيَا وَتَزْهَقَ أَنْفُسُهُمْ وَهُمْ كَافِرُونَ﴾ [التوبة: ٨٥].
Ma'ana:"Kuma kada dukiyoyinsu da yayansu subaka shi'awa, abin sani kawai, Allah Yana nufinne yayi musu azaba dasu a cikin duniya kuma rayukansu su fita alhali kuwa suna kafirai. Q9ayata85.
Daga cikin abubuwanda za'a yi musu azaba dashi harwa yaw, abin da Allah zai sanya musu na kiyayya a zukatan mutane duk yadda suka kai da neman soyayyarsu, wannan kuwa ya faru dasune domin sun nemi yardar mutane da fushin Allah, kuma sun fifita rayuwar duniya akan lahira, kuma sun bi abinda ke fusata Allah kuma sunki yardanSa, sun kawar da kai daga bin shiriyar Allah sakamakon haka sai suka bijirar da kawukansu ga naw'uka na tsoro da bakinciki da bata da shakiyanci wanda Allah Ya rubuta ga wanda ya kawar da kai daga bin shiriyarSa.
Kuma Allah (Madawkakin Sarki) Yace gameda wata jama'a daga cikinsu:

﴿لَا يَزَالُ بُنْيَانُهُمُ الَّذِي بَنَوْا رِيبَةً فِي قُلُوبِهِمْ إِلَّا أَنْ تَقَطَّعَ قُلُوبُهُمْ وَاللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ﴾ [التوبة: ١١٠].
Ma'ana:"Gininsu wanda suka gina bazai gushe ba yana zama shakka a zukatansu har sai zukatansu sun yayyanke (wato har su mutu) kuma Allah masanine mai hikima.Q9ayata110.
Wani daga cikin malaman tafsiri yace: (fadin) " har sai zukatansu su yayyanke" wanna togaciyace ta isgilanci (garesu), yana daga cikin isgilancin Allah a agaresu sakamako tamkar da aikin su, saboda makircin su ga muminai da isgilancinsu garesu da kaidinsu garesu, domin su sanya musu shubuha kuma su batardasu daga tafarkin Allah.
Saboda haka ya kasance daga ukubarsu an jarrabesu da shakka bazai rabu da zukatansu ba har abada, har su sadu da Allah (Mai girma da dawkaka)
Wannan shine abinda zai faru dasu daga ukubobi kebantattu sakamako gameda wasu daga cikin ayyukansu domin lallai hakika Allah (Madawkakin Sarki) Ya sanya ukubobi na musamman ga wasu zunubbai don yazama sakamako daga jinsin aiki.
Allah (Madawkakin Sarki) Yace gameda wata jama'a daga cikinsu (munafukai):
﴿الَّذِينَ يَلْمِزُونَ الْمُطَّوِّعِينَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ فِي الصَّدَقَاتِ وَالَّذِينَ لَا يَجِدُونَ إِلَّا جُهْدَهُمْ فَيَسْخَرُونَ مِنْهُمْ سَخِرَ اللَّهُ مِنْهُمْ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ﴾ [التوبة: ٧٩].
Ma'ana:"Wadanda suke aibanta masu yin alheri daga muminai a cikin dukiyoyin sadaka da wadanda basu samuba face iyakar kokarinsu, sai suna yi musu isgili. Allah Yana yin isgili garesu kuma suna da azaba mai radadi. Q9ayata79.
Sai ya kasance daga cikin ukubarsu sakamakon isgilancinsu ga muminai, Allah Yayi isgili garesu. Sakamako mai dacewa.
Kuma munafukai suna yawan fadawa acikin zunubban da sakamakonsu ke kasancewa daga jinsin aikin(su) a duniya kafin kiyama, kamar yadda yazo acikin sunna cewa; lallai wanda ya bibiyi al'awrar Musulmi Allah zai bibiyi al'awrarsa, kuma wanda ya cutar da Musulmi Allah zai cutar dashi, kuma wanda ya tsanantawa Musulmi Allah zai tsananta masa, kuma wanda ya tabarda Musulmi Allah zai tabar dashi, kuma wanda ya takurawa Musulmi Allah zai takura masa.
Kuma su munafukai ma'abuta makircine mummuna, hakika Allah Yace:
﴿وَلَا يَحِيقُ الْمَكْرُ السَّيِّئُ إِلَّا بِأَهْلِهِ﴾ [فاطر: ٤٣].
Ma'ana:"Kuma makirci mummuna baya gewayewa face ga mutanensa" Q35ayata43.
Wannan shine bayanin wani abu da zai samesu a duniya.

Amma (abinda zai samesu) a barzahu kuwa, lallai su idan suka rabu da wannan rayuwar kuma aka shigar dasu cikin kabur buransu, lallai suna cikin azaba mai girma da tabewa dawwamamme da dan danasani wanda bashida iyaka.
Daga Anas dan Malik (Allah Ya karamasa yarda) daga Annabi (S.A.W) lallai yace:
((إنَّ العبدَ إذا وُضِعَ في قَبْرِه وتَولَّى عنه أصحابُه، وإنه لَيَسْمَعُ قَرْعَ نِعالِهم، أتاهُ مَلَكانِ فيُقْعدانِه فيَقولانِ: ما كُنْتَ تقولُ في الرَّجُلِ؟ لمُحمَّدٍ صلى الله عليه وسلم.
فأمَّا المُؤمنُ فيَقولُ: أشْهَدُ أنه عبدُ اللهِ ورَسولُه.
فيُقالُ له: انْظُرْ إلى مَقْعَدِكَ من النارِ قد أبْدَلَكَ اللهُ به مَقْعَدًا من الجَنَّةِ فيَرَاهما جَمِيعًا.
وأمَّا المُنافِقُ والكَافِرُ فيُقالُ له: ما كُنْتَ تَقولُ في هذا الرَّجُلِ؟
فيَقُولُ: لا أَدْرِي، كنتُ أَقولُ ما يَقولُ النَّاسُ.
فيُقالُ: لا دَرَيْتَ ولا تَلَيْتَ، ويُضْرَبُ بمَطَارِقَ من حديدٍ ضَرْبةً فيَصِيحُ صَيْحةً يَسْمَعُها مَن يليهِ غيرَ الثَّقَلينِ)) مُتَّفقٌ عليه.
Ma'ana:"lallai bawa idan aka saka shi acikin kabarinsa kuma abokansa suka juya suka tafi suka barshi, alhali shi yana jin karan takalmansu, sai Mala'iku biyu su zo masa, saisu zawnar dashi, sannan sai suce:" Me ka kasance kana fadi gameda Mutumin? –ga (Annabi ) Muhammadu (S.A.W).
Amma mumini shikam zaice: Na shaida cewa shi bawan Allah ne kuma Manzon Allah ne.
Sai ace masa:"kayi dubi zuwaga mazawninka a cikin wuta Allah Ya canza makashi da wani mazawni acikin aljanna. Sai ya gansu baki daya.
Amma shiko munafuki da kafiri, sai ace masa:"Me ka kasance kana fadi gameda wannan Mutumin?
Sai yace; ban saniba, ni na kasancene ina fadin abinda mutane ke fadi.
Sai ace; baka saniba kuma baka bi wanda ya saniba? Sai a dakeshi da guduma ta bakin karfe duka daya, sai yatsala ihu duk wanda ke kusa dashi zaijishi banda aljani da mutum. Bukhri da Muslimne suka ruwaitoshi.
tareda abin da zai samesu na ukubobi na musamman saboda wasu zunubbai nasu, kamar yadda ya inganta a sunna cewa wanda yake karanta kur'ani sannan yayi watsi dashi kuma yake bacci gabarin sallar farilla, to za'ayi masa azaba a kabarinsa. Hakanan mazinata da masu cin riba da masu giba da annamimanci da karya da masu hana zakka da wadanda ke karya azumi kafin lokacin buda bakinsu yayi. Duk wadannan, ingantattun hadisai sunzo akansu cewa za'ayi musu azaba acikin kaburburansu. Munafukai kuwa suna da kaso mafi girma cikin wadannan ayyukan.
A lahira kuwa, hakika ingantattun hadisai sunyi nuni zuwaga cewa, idan alkiyama ta tsaya kuma Allah Ya tara mutane matattara daya domin hukunci a tsakaninsu, sannan Yayi umurni da kafirai aka kaisu Wutar Jahannama, muminai da munafukai da sawran Ahlul kitabi zasu sawra a filin kiyama. Sai a yaye kwawri, sa'annan babu wanda zai sawra cikin wadanda suka kasance suna sujjada anan duniya don biyayya (ga Allah) face anyi musu izini da yin sujjada, kuma babu wani daya kasance yana yin sujjada don riya ko munafurci face gadon bayansa ya koma dabaki guda (wato ya sandare) duk sa'adda yayi nufin yin sujjada sai ya fadi akan keyarsa.
A cikin hisabi kuwa za'a taho da munafuki sai Allah Ya tunatar dashi ni'imominSa akansa, sai munafukin yace; Ya Ubangijina, nayi imani daKai, kuma nayi imani da littafinKa da kuma ManzanniKa, nayi salla kuma nayi azumi kuma nayi sadaka, saiya yabi kansa da alheri gwargwadon iyawarsa.
Sai ace masa; yanzu zamu tayarda mai yin sheda akanka.
Sai yayi tunani acikin ransa (yace yanzu) waye zaiyi sheda agareni? Sai a sanya toshiya a bakinsa, kuma acewa cinyarsa da namansa da kashinsa; kuyi magana.
Sai cinyarsa da namansa da kashinsa suyi Magana game da ayyukansa, wannan kuwa saboda a yanke masa hanzarine bisa kansa. Annabi (S.A.W) yace:
((وذَلِكَ المُنافِقُ، وذلك الذي يَسْخَطُ اللهُ عليه)).
Ma'ana:"To wannan shinne munafuki, wannan shine wanda Allah zaiyi fushi dashi"
Hadisin yana cikin sahihu Muslim daga hadisin Abu Huraira (Allah Ya kara masa yarda).
Saboda haka idan aka sanya siradi akan Jahannama kuma akayi umurni da ketarawa ta kansa, kuma aka baiwa wadanda ke filin kiyama haske gwargwadon ayyukansu, suma munafukai za'a basu haske kwatan kwacinsu don ya zama fitina garesu, har sai sun kasance akan siradi sai a dawke hasken munafukai, hasken muminai kuma ya kamala. Kamar yadda Allah Yace:
﴿يَوْمَ تَرَى الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ يَسْعَى نُورُهُمْ بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَبِأَيْمَانِهِمْ بُشْرَاكُمُ الْيَوْمَ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ذَلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ (12) يَوْمَ يَقُولُ الْمُنَافِقُونَ وَالْمُنَافِقَاتُ لِلَّذِينَ آَمَنُوا انْظُرُونَا نَقْتَبِسْ مِنْ نُورِكُمْ قِيلَ ارْجِعُوا وَرَاءَكُمْ فَالْتَمِسُوا نُورًا فَضُرِبَ بَيْنَهُمْ بِسُورٍ لَهُ بَابٌ بَاطِنُهُ فِيهِ الرَّحْمَةُ وَظَاهِرُهُ مِنْ قِبَلِهِ الْعَذَابُ (13) يُنَادُونَهُمْ أَلَمْ نَكُنْ مَعَكُمْ قَالُوا بَلَى وَلَكِنَّكُمْ فَتَنْتُمْ أَنْفُسَكُمْ وَتَرَبَّصْتُمْ وَارْتَبْتُمْ وَغَرَّتْكُمُ الْأَمَانِيُّ حَتَّى جَاءَ أَمْرُ اللَّهِ وَغَرَّكُمْ بِاللَّهِ الْغَرُورُ (14) فَالْيَوْمَ لَا يُؤْخَذُ مِنْكُمْ فِدْيَةٌ وَلَا مِنَ الَّذِينَ كَفَرُوا مَأْوَاكُمُ النَّارُ هِيَ مَوْلَاكُمْ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ (15)﴾ [الحديد: 1٢–١٥]
Ma'ana:" Ranar da zaka ga muminai maza da muminai mata haskensu na tafiya gaba garesu da kuma dama garesu, (ana cemusu,) bushararku a yaw, itace Aljanna, koramu na gudana a karkashinsu, suna masu dawwama acikinsu, wannan shine rabo mai girma (12) Ranar da munafukai maza da munafukai mata ke cewa wadanda suka yi imani, ku dubo mu muyi makamashi daga haskenku. Sai ace (musu), ku koma bayan ku domin ku nemo wani haske. Sai a buga wata Katanga da takeda wani kyawre, a ta cikinsa nan rahama take, kuma a bayansa ta wajensa azaba take (13) Suna kiransu, "ashe bamu kasance taredaku ba? Sai suce "ii (mnu kasance tare) saidai ku kun fitini kawukanku kuma kunyi zaman jiran wata musiba kuma kunyi shakka kuma burace burace sun rudeku har said a al'amarin Allah yazo muku kuma mai rudi ya rudeku game da Allah (14) To ayaw baza'a karbi fansa daga gareku ba kuma baza'a karba ba daga wadanda suka kafirta. Makomarku itace Wuta, itace mafi dacewa daku, tir da makoma idan ta kasance Wuta (15) Q57ayata12-15..
Amma azabarsu acikin Wutar Jahannama, itace azaba ta wulakanci, kuma mai radadi, kuma mai tsanani tabbatacciya, Allah Ya wajabta musu (shiga) magan gara mafi zurfi acikinta, saboda haka suna daga cikin wadanda keda azaba mafi tsanani acikin yan Wuta. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿إِنَّ الْمُنَافِقِينَ فِي الدَّرْكِ الْأَسْفَلِ مِنَ النَّارِ وَلَنْ تَجِدَ لَهُمْ نَصِيرًا﴾ [النساء: ١٤٥].
Ma'ana:"Lallai munafukai suna cikin magangara mafi zurfi daga Wuta, kuma bazaka sama musu wani mai taimakoba" Q4ayata145.
Su sakamakon boyayyar kafircinsu da jibintarsu ga al'amarin kafirai, sai Allah Ya hadasu da kafirai acikin Wutar Jahannama. Kamar yadda Yace:
﴿إِنَّ اللَّهَ جَامِعُ الْمُنَافِقِينَ وَالْكَافِرِينَ فِي جَهَنَّمَ جَمِيعًا﴾[النساء: ١٤٠].
Ma'ana:"Lallai Allah mai tara munafukai da kafirai ne a cikin Jahannama baki daya. Q4ayata140.
Kuma Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَعَدَ اللَّهُ الْمُنَافِقِينَ وَالْمُنَافِقَاتِ وَالْكُفَّارَ نَارَ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا هِيَ حَسْبُهُمْ وَلَعَنَهُمُ اللَّهُ وَلَهُمْ عَذَابٌ مُقِيمٌ﴾ [التوبة: ٦٨].
Ma'ana:" Allah Yayi alkawarin Wutar Jahannama ga munafukai maza da munafukai mata da kafirai, suna masu dawwama acikinta. Itce mai isarsu. Kuma Allah Ya tsine musu. Kuma suna da wata azaba tabbatacciya. Q9ayata68.