تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس العاشر: التَّحذيرُ من النِّفاقِ (2/3)


طاهر جبريل دكو
_5 _April _2013هـ الموافق 5-04-2013م, 02:22 PM
الدرس العاشر: التَّحذيرُ من النِّفاقِ (2/3)

وسبيلُ السلامةِ والبَراءةِ من النفاقِ هو اتِّباعُ هُدَى اللهِ جلَّ وعلا، كما قالَ اللهُ تعالى في المنافقين: ﴿وَلَوْ أَنَّهُمْ فَعَلُوا مَا يُوعَظُونَ بِهِ لَكَانَ خَيْرًا لَهُمْ وَأَشَدَّ تَثْبِيتًا (66) وَإِذًا لَآَتَيْنَاهُمْ مِنْ لَدُنَّا أَجْرًا عَظِيمًا (67) وَلَهَدَيْنَاهُمْ صِرَاطًا مُسْتَقِيمًا (68) وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَالرَّسُولَ فَأُولَئِكَ مَعَ الَّذِينَ أَنْعَمَ اللَّهُ عَلَيْهِمْ مِنَ النَّبِيِّينَ وَالصِّدِّيقِينَ وَالشُّهَدَاءِ وَالصَّالِحِينَ وَحَسُنَ أُولَئِكَ رَفِيقًا (69) ذَلِكَ الْفَضْلُ مِنَ اللَّهِ وَكَفَى بِاللَّهِ عَلِيمًا (70)﴾[النساء: ٦٦–٧٠].
وبهذا تَعْلَمُ أن المنافقين إنما خَسِروا الخُسْرانَ العَظِيمَ بسببِ إعراضِهم عن هُدَى اللهِ، فإنهم خَسِروا رِضْوانَ اللهِ عزَّ وجلَّ وفَضْلَه ورحمتَه وثوابَه العظيمَ ومُرافقةَ الأنبياءِ والصِّدِّيقينَ والشُّهداءِ والصالحين، ووَقَعُوا في شَرِّ أعمالِهم من تكذيبِهم للهِ ورسولِه، وسُوءِ ظَنِّهم باللهِ، واتباعِهم لما يَسْخَطُه اللهُ، وكَرَاهِيَتِهم لِمَا يُحِبُّه ويَرْضاهُ، وسَعْيِهم في مُحارَبةِ دينِ اللهِ بأقوالِهم وأعمالِهم، وتَوَلِّيهم للكافرين من أهلِ الكتابِ والمُشركين، ومُظاهرتِهم لهم على المسلمين، وإيذائِهم للمؤمنين؛ فاسْتَحَقُّوا العذابَ الشديدَ على إِجْرَامِهِم.
قال اللهُ تعالى: ﴿وَيُعَذِّبَ الْمُنَافِقِينَ وَالْمُنَافِقَاتِ وَالْمُشْرِكِينَ وَالْمُشْرِكَاتِ الظَّانِّينَ بِاللَّهِ ظَنَّ السَّوْءِ عَلَيْهِمْ دَائِرَةُ السَّوْءِ وَغَضِبَ اللَّهُ عَلَيْهِمْ وَلَعَنَهُمْ وَأَعَدَّ لَهُمْ جَهَنَّمَ وَسَاءَتْ مَصِيرًا﴾ [الفتح: ٦].
وقال تعالى: ﴿ذَلِكَ بِأَنَّهُمُ اتَّبَعُوا مَا أَسْخَطَ اللَّهَ وَكَرِهُوا رِضْوَانَهُ فَأَحْبَطَ أَعْمَالَهُمْ﴾ [محمد: ٢٨].
وهم بسَبَبِ مُخالفةِ ظَواهِرِهم لبَواطِنِهم وَقَعُوا في أعمالٍ قَبِيحةٍ ذَمِيمةٍ، من الكَذِبِ والغَدْرِ والخِيانةِ والفُجورِ وإخلافِ الوَعْدِ، وكانت هذه من أخلاقِهم التي يُعْرَفُون بها.

وأعمالُ المنافقين على صِنْفينِ:
الصِّنْفُ الأولُ: أعمالٌ كُفْريَّةٌ مَن وَقَعَ فيها فهو كَافِرٌ باللهِ جل وعلا، خارجٌ من دينِ الإسلامِ، وإن صَلَّى وصام وزَعَم أنه مُسلِمٌ.
وذلك مِثْلُ: تَكْذيبِ اللهِ ورسولِه، والبُغْضِ والسبِّ والاستهزاءِ باللهِ وآياته ورسولِهِ، وتَوَلِّي الكافرينَ ومُناصَرَتِهم على المسلمين.
فهذه الأعمالُ ونَحْوُها هي من نَواقِضِ الإسلامِ، فمَن وَقَعَ فيها فهو غَيْرُ مُؤْمِنٍ باللهِ جل وعلا، بل هو كَافِرٌ خارجٌ عن دينِ الإسلامِ؛ فإن كان يُظْهِرُ الإسلامَ فهو مُنافِقٌ النِّفَاقَ الأَكْبَرَ.
وهذا الصِّنْفُ يُسَمِّيهِ بعضُ أهلِ العلمِ النِّفاقَ الاعتقاديَّ، وذلك بسببِ انطواءِ القلبِ على الكفرِ، وإلا فإن القلبَ المؤمنَ لا تَصْدُرُ منه هذه الأعمالُ والأقوالُ الكُفريَّةُ، وليسَ مُرادُهم حَصْرَ أعمالِ النِّفاقِ الأَكْبَرِ في الأمورِ الاعتقاديَّةِ.


الصِّنْفُ الثاني: أعمالٌ وخِصالٌ ذَمِيمةٌ، وهي وإنْ لم تَكُنْ مُكَفِّرةً لذاتِها إلا أنَّها لا تَجْتَمِعُ إلا في المُنافِقِ الخالِصِ، وعلى المؤمن أن يَحْذَرَ منها لئلا تَكونَ فيه خَصْلةٌ من خِصالِ النفاقِ، وهي التي بَيَّنَها النبيُّ صلى الله عليه وسلم بقولِه: ((آيةُ المُنافِقِ ثلاثٌ إذا حدَّثَ كَذَبَ، وإذا وَعَدَ أخْلَفَ، وإذا اؤتُمِنَ خَانَ)). متفق عليه من حديثِ أبي هُريرةَ رضِي الله عنه.
وفي روايةٍ لمسلمٍ: ((آيةُ المُنافقِ ثلاثٌ وإنْ صلَّى وصام وزَعَمَ أنه مُسلِمٌ)).
وفي روايةِ أحمدَ: ((ثلاثٌ إذا كُنَّ في الرجُّلِ فهو المُنافِقُ الخَالِصُ...)) الحديثَ، بنحوِه.
وفي الصحيحين من حديثِ عبدِ اللهِ بنِ عَمْرِو بنِ العاصِ رضِي اللهُ عنهما قال: قال رسولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم: ((أَرْبَعٌ مَن كُنَّ فيه كانَ مُنافِقًا خالصًا، ومَن كانت فيه خَلَّةٌ منهنَّ كانتْ فيه خَلَّةٌ من نفاقٍ حتى يَدَعَها: إذا حدَّثَ كَذَبَ، وإذا عاهَدَ غَدَرَ، وإذا وَعَدَ أخْلَفَ، وإذا خاصَمَ فَجَرَ)).
فالذي يَكُونُ من شَأْنِهِ إنه إذا حَدَّث كَذَب وإذا وَعَدَ أَخْلَفَ وإذا اؤتُمِنَ خانَ فهو مُنافِقٌ خَالِصٌ، و(إذا) غيرُ الغائِيَّةِ تَدُلُّ على التَّكْرَارِ والكَثْرَةِ، وهذا يُخْرِجُ مَن يَقَعُ منه شيءٌ من ذلك على وَجْهِ القِلَّةِ والنُّدْرَةِ، فيَكونُ قد أَذْنَبَ ذَنْبًا وأتَى عَمَلاً من أعمالِ المنافقين، لكنَّهُ لا يَصِيرُ بذلك مُنافِقًا أو صَاحِبَ خَصْلةٍ من خِصالِ النِّفاقِ حتى يَكونَ ذلك من شأنِه الذي يَعْتادُه أو يُعْرَفُ عنه.

فصل: في مَن يَكونُ في قلبِه إيمانٌ ونِفاقٌ
أما النفاقُ الأكبرُ فإنه لا يَجتمِعُ مع الإيمانِ، بل صاحبُه كافرٌ باللهِ جل وعلا، وإن صلَّى وصام وزَعَمَ أنه مسلمٌ؛ لأن الكُفْرَ مُحْبِطٌ لجَميعِ العملِ، والإيمانُ والكفرُ الأكبرُ لا يَجْتمعانِ، قال اللهُ تعالى: ﴿وَمَنْ يَكْفُرْ بِالْإِيمَانِ فَقَدْ حَبِطَ عَمَلُهُ وَهُوَ فِي الْآَخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ﴾ [المائدة: ٥].
وأما النفاقُ الأصغرُ الذي لا يُخرِجُ من المِلَّةِ فقد يكونُ في قَلْبِ المُسلمِ بَعْضُ خِصالِه كما دَلَّ عليه حديثُ عبدِ اللهِ بنِ عَمْرِو بنِ العاصِ المُتقَدِّمُ.
وفي صَحيحِ مُسلمٍ من حديثِ أَبي هُريرةَ رضِي الله عنه قالَ: قالَ رسولُ الله صلى الله عليه وسلم: ((مَن ماتَ ولَم يَغْزُ، ولَمْ يُحدِّثْ نفسَهُ بالغَزْوِ ماتَ على شُعبةٍ مِنَ النفاقِ)) رواه مسلمٌ.
وقال حُذيفةُ بنُ اليَمَانِ رضِي الله عنه: (القُلوبُ أربعةٌ:
– قَلْبٌ مُصْفَحٌ فذلك قَلْبُ المنافقِ.
– وقَلْبٌ أَغْلَفُ فذاك قلبُ الكافرِ.
– وقَلْبٌ أجْرَدُ كأنَّ فيه سِراجًا يُزهِرُ فذلك قَلْبُ المؤمنِ.
–وقَلْبٌ فيه نِفاقٌ وإيمانٌ؛ فمَثَلُه مَثَلُ قَرْحةٍ يَمُدُّها قَيْحٌ وَدَمٌ، ومَثَلُه مَثَلُ شَجَرةٍ يَسْقِيها ماءٌ خَبِيثٌ وطَيِّبٌ؛ فأيُّهما غَلَبَ عليها غَلَبَ). رواه ابن أبي شيبة في المصنَّفِ وفي كتابِ الإيمانِ وقد صَحَّحَهُ الألبانيُّ، وأُعِلَّ بالانقطاعِ، ومعناه صحيح.
والقَلْبُ المُصْفَحُ هو القَلْبُ المَائِلُ.
وقال عَلِيُّ بنُ أبي طَالِبٍ رضِيَ اللهُ عنهُ: (الإيمانُ يَبْدَأُ لُمْظَةً بيضاءَ في القلبِ، كُلَّما ازدادَ الإيمانُ ازدادت بَياضًا حتى يَبْيَضَّ القلبُ كلُّه، وإن النِّفاقَ يَبْدَأُ لُمْظَةً سوداءَ في القلبِ فكلما ازدادَ النفاقُ ازدادت حتى يَسْوَدَّ القلبُ كلُّه). رواه ابنُ أبي شَيْبةَ في كتابِ الإيمانِ، والبيهقيُّ في شُعب الإيمانِ.
والُّلمْظَةُ هي كالنُّقْطةِ الصغيرةِ.

والمقصودُ أنَّ المسلمَ قد يكونُ لديهِ نِفاقٌ يَكْثُرُ ويَقِلُّ بحَسَبِ مَبْلَغِ إيمانِه وطاعتِه للهِ جل وعلا؛ فمنهم مَن يَكونُ فيه شَوَائِبُ من نِفاقٍ فتَقَعُ منه الكَذْبةُ والكَذْبتانِ ويَقَعُ منه إخلافُ الوَعْدِ أحيانًا ونحوُ ذلك.

ومنهم مَن يَكْثُرُ منه الوقوعُ في هذه الأعمالِ مع قِلَّةِ ذِكْرِ اللهِ وكَثْرَةِ تَجاوُزِ حُدودِ اللهِ بانتهاكِ الحُرماتِ والتفريطِ في الوَاجباتِ والانكبابِ على الشهواتِ والاغترارِ بالشُّبهاتِ؛ فيكونُ في قلبِه نفاقٌ كثيرٌ وإيمانٌ قليلٌ، حتى إن من المسلمين مَن لا يَكادُ يُصلِّي إلا على عَجَلةٍ مع تأخيرِه للصلاةِ إلى وقتِ الكَراهةِ وإساءتِه في أدائِها، كما في صحيحِ مسلمٍ من حديثِ أنسِ بنِ مالكٍ رضِي الله عنه قال: سمعتُ رسولَ الله صلى الله عليه وسلم يقول: ((تلكَ صلاةُ المنافقِ، يَجْلِسُ يَرْقُبُ الشمسَ حتى إذا كانتْ بينَ قَرْنَي الشيطانِ قامَ فنَقَرَهَا أَربعًا لا يذكُرُ اللهَ فيها إِلا قليلاً)). رواه مسلمٌ
فهذا مِمَّن غَلَبَ على قَلْبِه النفاقُ حتى استحَقَّ أن يُسمَّى مُنافقًا، معَ وُجودِ إيمانٍ في قلبِه مَنَعَه من تَرْكِ الصلاةِ مُطْلقًا.

ويَكْثُرُ في أهلِ هذا الصِّنفِ الوُقوعُ في الرِّياءِ الأصغرِ والتسميعِ وما يُحْبِطُ بعضَ الأعمالِ كالمَنِّ والإيذاءِ في النَّفَقةِ، وطَلَبِ الدنيا بعَمَلِ الآخرةِ، وانتهاكِ الحُرُماتِ في الخَلَواتِ.
وأهلُ هذا الصِّنفِ على خَطَرٍ عَظِيمٍ أنْ يُؤدِّيَ بهم هذا التَّهاوُنُ إلى الانسلاخِ من دِينِ اللهِ عز وجل، ومَن ماتَ منهم على هذا النِّفاقِ معَ وُجودِ إيمانٍ في قلبِه؛ فإنَّه من أهلِ الكَبائرِ المُتَوعَّدِينَ بالعَذابِ الشديدِ، لكنه لا يَخْلُدُ في النارِ لبَقاءِ إسْلامِه، وقد صَحَّ عن النبيِّ صلى الله عليه وسلم أنه قالَ: ((يَدْخُلُ أهلُ الجنةِ الجنةَ، وأهلُ النَّارِ النَّارَ، ثم يقولُ اللهُ تعالى: أَخْرِجوا مَن كانَ في قلبِه مِثْقالُ حَبَّةٍ مِن خَرْدَلٍ من إيمانٍ؛ فيُخْرَجونَ منها قد اسْوَدُّوا؛ فيُلْقَونَ في نَهَرِ الحَياةِ؛ فيَنْبُتونَ كمَا تَنْبُتُ الحِبَّةُ في جانبِ السَّيْلِ، ألَمْ تَرَ أنَّهَا تَخْرُجُ صَفْرَاءَ مُلْتَوِيَةً؟)) رواه البخاريُّ من حديثِ أبي سَعِيدٍ الخُدْريِّ رضِي الله عنه.

أمَّا مَن ارتَكَبَ نَاقِضًا من نَوَاقِضِ الإسْلامِ كالاستهزاءِ بالدِّينِ وسَبِّ اللهِ ورَسُولِه ومُوالاةِ الكُفَّارِ على المُسلمينَ فهو كافرٌ خارجٌ من الإسلامِ قد انسلَخَ الإيمانُ من قلبِه، والعياذُ باللهِ.

فصلٌ: في تَوْبَةِ المُنافِقِ
إذا تَابَ المُنافِقُ قَبْلَ موتِه وأصْلَحَ عَمَلَهُ واعْتَصَمَ باللهِ وأخلَصَ دينَه للَّهِ عز وجل فتَوْبَتُه صحيحةٌ مَقْبولةٌ، قال اللهُ تعالى: ﴿إِنَّ الْمُنَافِقِينَ فِي الدَّرْكِ الْأَسْفَلِ مِنَ النَّارِ وَلَنْ تَجِدَ لَهُمْ نَصِيرًا (145) إِلَّا الَّذِينَ تَابُوا وَأَصْلَحُوا وَاعْتَصَمُوا بِاللَّهِ وَأَخْلَصُوا دِينَهُمْ لِلَّهِ فَأُولَئِكَ مَعَ الْمُؤْمِنِينَ وَسَوْفَ يُؤْتِ اللَّهُ الْمُؤْمِنِينَ أَجْرًا عَظِيمًا (146) مَا يَفْعَلُ اللَّهُ بِعَذَابِكُمْ إِنْ شَكَرْتُمْ وَآَمَنْتُمْ وَكَانَ اللَّهُ شَاكِرًا عَلِيمًا (147)﴾ [النساء: ١٤٥– ١٤٧].
وكذلك المسلمُ الذي يكونُ فيه بعضُ خِصالِ النفاقِ إذا تابَ منها وترَكَ تلك الخَصْلَةَ تابَ اللهُ عليه، وبَرِئَ من النِّفَاقِ.

وفي هذه المَسْألةِ لُغْزٌ ظَرِيفٌ أَوْرَدَهُ حُذَيْفَةُ بنُ اليَمانِ رضِي الله عنه على طُلاَّبِ حَلْقَةِ عبدِ اللهِ بنِ مَسعودٍ رضِي الله عنه؛ فإنه وَقَفَ عليهم وعبدُ اللهِ بنُ مَسْعودٍ حاضِرٌ فسلَّم عليهم ثم قالَ: (لَقَدْ أُنْزِلَ النِّفَاقُ على قَوْمٍ خَيْرٍ مِنْكُمْ!!)
فتَبَسَّمَ عبدُ اللهِ بنُ مَسْعودٍ وعَرَفَ مُرادَهُ.
وقال أصحابُه: سُبحانَ اللهِ؛ إنَّ اللهَ عز وجل يقولُ: ﴿إِنَّ الْمُنَافِقِينَ فِي الدَّرْكِ الْأَسْفَلِ مِنَ النَّارِ﴾ [النساء: ١٤٥]!!
ثم لَمَّا تَفرَّقَ المَجْلسُ قال حُذيفةُ للأسودِ بنِ يَزِيدَ النَّخَعِيِّ وهو أحَدُ أصْحَابِ ابنِ مَسعودٍ: (لقد أُنزِلَ النفاقُ على قَوْمٍ كانوا خَيْرًا مِنْكم، ثم تَابوا فتابَ اللهُ عليهم).
وفي روايةٍ فقالَ: (إنَّهم لَمَّا تَابوا كانوا خَيْرًا مِنْكم).
وهو يَقْصِدُ بهم بَعْضَ الذين كانوا مُنافقينَ على عهدِ رسولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم، ثم تابوا وأصْلَحُوا وأحْسَنُوا إسلامَهم فكانوا بأجرِ الصُّحبةِ والجهادِ معَ رسولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم خَيْرًا مِمَّن جَاءَ بعدَهم مِن التَّابِعِينَ.
وهذه القِصَّةُ أَخْرَجَها البخاريُّ في صحيحِه.

فصلٌ: ويَجِبُ على المُؤْمنينَ أن يَعْمَلُوا بما يُنْجِيهِم مِن خِصالِ النِّفاقِ وأعمالِ المُنافقينَ، ومن ذلك تَكْرَارُ التوبةِ والاستغفارِ، ورعايةُ حُدودِ اللهِ، وتعظيمُ أوامرِه، والبراءةُ من الشِّركِ وأهلِه، وإقامةُ الصلاةِ وإيتاءُ الزكاةِ، والنَّصِيحةُ للهِ ولرسولِه ولكتابِه ولأئِمَّةِ المسلمينَ وعامَّتِهم.
ومن ذلك: مَحبَّةُ الجهادِ في سبيلِ اللهِ، وتَحْديثُ النَّفْسِ بذلك.
ومن ذلك: الأمرُ بالمعروفِ، والنَّهْيُ عن المُنْكَرِ، والتواصي بالحقِّ، والتواصي بالصبرِ، والتحاضُّ على طَعامِ المِسْكينِ والإنفاقُ في سبيلِ اللهِ إيمانًا واحْتسابًا.
فمَن فعَلَ ذلك كان بَرِيئًا من النفاقِ.
وفي المُسندِ وغيرِه من حديثِ عُمَرَ بنِ الخَطَّابِ رضِي الله عنه أن النبيَّ صلى الله عليه وسلم قال: ((مَنْ سَرَّتْهُ حَسَنَتُهُ وسَاءَتْهُ سَيِّئَتُهُ فهو مُؤْمِنٌ)).
فمَن وقَعَ في ذَنْبٍ وَسَاءَهُ الذَّنْبُ فهو عَلامةٌ على صِحَّةِ إيمانِه، وأَرْجَى أن يَتُوبَ ويَسْتَغْفِرَ ويَسْتَعْتِبَ، ومَن فَرِحَ بمَعْصيتِه وسَرَّتْهُ سَيِّئَتُهُ كانَ ذلك أمارةً على نفاقٍ في قلبِه.
وفي سُننِ التِّرمذيِّ من حديثِ أبي هُريرةَ رضِي الله عنه قال: قال رسولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم: «خَصْلَتَانِ لا تَجْتمعانِ في مُنافِقٍ: حُسْنُ سَمْتٍ، وفِقْهٌ في الدِّينِ». صَحَّحَه الألبانيُّ.

طاهر جبريل دكو
_6 _April _2013هـ الموافق 6-04-2013م, 11:28 AM
Gargadi gameda munafurci 2/3

Tafarkin tsira da kubuta daga munafurci shine, bin hanyar Allah (Mai girma da dawkaka) kamar yadda Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَلَوْ أَنَّهُمْ فَعَلُوا مَا يُوعَظُونَ بِهِ لَكَانَ خَيْرًا لَهُمْ وَأَشَدَّ تَثْبِيتًا (66) وَإِذًا لَآَتَيْنَاهُمْ مِنْ لَدُنَّا أَجْرًا عَظِيمًا (67) وَلَهَدَيْنَاهُمْ صِرَاطًا مُسْتَقِيمًا (68) وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَالرَّسُولَ فَأُولَئِكَ مَعَ الَّذِينَ أَنْعَمَ اللَّهُ عَلَيْهِمْ مِنَ النَّبِيِّينَ وَالصِّدِّيقِينَ وَالشُّهَدَاءِ وَالصَّالِحِينَ وَحَسُنَ أُولَئِكَ رَفِيقًا (69) ذَلِكَ الْفَضْلُ مِنَ اللَّهِ وَكَفَى بِاللَّهِ عَلِيمًا (70)﴾[النساء: ٦٦–٧٠].
Ma'ana:"Kuma da dai lallai su sun aikata abinda ake yi musu gargadi dashi, hakika, daya kasance mafi alheri garesu, kuma mafi tsanani ga tabbatarwa (66) Kuma da Mun shiryar dasu tafarki madaidaici (67)Kuma a sa'annan, hakika da Mun basu lada mai yawa daga gunMu (68) Kuma duk wadanda sukayi da'a ga Allah da Manzon Sa, to wadannan suna tareda wadanda Allah Yayi ni'ima a kansu daga Annabawa da siddikai da shahidai. Kuma wadannan sun kyawtatu ga zama abokan tafiya (69) Wancan falalar daga Allah take, kuma Allah Ya isa zama masani (70) Q4ayata 66-70.
Kuma da wannan ne zaka san cewa lallai munafukai sunyi hasarane hasara mai girma sakamakon kawar da kai daga shiriyar Allah, domin sunyi hasarar yardan Allah (Mai girma da dawkaka) da falalarSa da rahamarSa da sakamakonSa mai girma da abuta da Annabawa da Siddikai da Shahidai da Salihai. Kuma sun awka cikin mafi sharrin ayyukansu, kamar karyata Allah da ManzonSa, da mummunan zatonsu ga Allah da bibiyarsu ga abinda ke jawo fushin Allah, da kiyayyansu ga abinda [Allah] Yakeso kuma Yake yarda dashi, da kokarinsu wurin yaki da addinin Allah da maganganunsu da ayyukansu, da jibintansu ga kafirai daga ma'abuta littafi da mushirikai, da taimaka musu akan Musulmai, da cutarwarsu ga muminai, saboda hakane suka cancanci matsanancin azaba akan sabonsu. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَيُعَذِّبَ الْمُنَافِقِينَ وَالْمُنَافِقَاتِ وَالْمُشْرِكِينَ وَالْمُشْرِكَاتِ الظَّانِّينَ بِاللَّهِ ظَنَّ السَّوْءِ عَلَيْهِمْ دَائِرَةُ السَّوْءِ وَغَضِبَ اللَّهُ عَلَيْهِمْ وَلَعَنَهُمْ وَأَعَدَّ لَهُمْ جَهَنَّمَ وَسَاءَتْ مَصِيرًا﴾ [الفتح: ٦].
Ma'ana:"Kuma Yayi azaba ga munafukai maza da munafukai mata da mushirikai maza da mushirikai mata, masu munana zato ga Allah, muguwar musiba mai kewayewa ta tabbata a kansu, kuma Allah Yayi fushi dasu kuma Ya la'ancesu, kuma Yayi musu tattalin Jahannama, kuma ta munana ta zama makoma [agaresu] Q48ayata6.
Kuma (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿ذَلِكَ بِأَنَّهُمُ اتَّبَعُوا مَا أَسْخَطَ اللَّهَ وَكَرِهُوا رِضْوَانَهُ فَأَحْبَطَ أَعْمَالَهُمْ﴾ [محمد: ٢٨].
Ma'ana:"Wannan, domin lallai su sunbi abinda ya fusatar da Allah, kuma sunki yardarSa, saboda haka saiya bata ayyukansu. Q47ayata28.
Kuma su, sakamakon sabanin zahirinsu ga badininsu sai suka fada cikin ayyuka munana abar zargi, daga karya, yawdara da cin amana da fajirci da saba alkawari, wadannan kuma sun kasance dabi'unsu da aka sansu dasu.
Ayyukan munafukai sun kasu zuwa sinfi biyu:
Sinfi na farko: Ayyuka na kafirci, wanda ya awka cikinsu ya kafirce wa Allah (Mai girma da dawkaka), ya fice daga addinin Musulunci koda kuwa yayi salla yayi azumi kuma ya riya cewa shi Musulmine.
Wannan kuwa misalinsa shine:Karyata Allah da ManzonSa. Da kiyayya da zagi da isgilanci ga Allah da ayoyinSa da ManzonSa, da jibintan al'amarin kafirai da taimakonsu akan Musulmai.
Wadannan ayyukan da makamantansu suna cikin abubuwan dake warware Musulunci, saboda haka duk wanda ya fada acikinsu, to shi ba mai imani da Allah bane, shi kafirine fitacce daga addinin Musulunci, idan kuma ya kasance yana bayyana Musulunci, to shi munafukine munafurci mai girma.
Wannan sinfin wasu daga cikin malami suna kiransa munafurcin kuduri. Wannan saboda damfaruwar zuciya ce akan kafirci, amma in bahaka ba ai lallai irin wadannan ayyukan da maganganun na kafirci, basu fitowa daga zuciya mai imani.
Kuma manufar su [malamai] ba itace iyakance ayyukan babban munafurci cikin ayyukan zuciya kawai ba.


Sinfi na biyu: Ayyuka da dabi'u ababen zargi, wadannan duk da cewa basu kaisu kafirtar ba akaran kansu, saidai [su ayyukane] da basu tattaruwa sai ga cikakken munafuki, kuma ya wajaba ga mumini ya kiyayesu saboda kada wata dabi'a daga cikin dabi'un munafurci ta kasance atare dashi, sune wadanda Annabi (S.A.W) ya bayyanasu cikin fadinsa:
((آيةُ المُنافِقِ ثلاثٌ إذا حدَّثَ كَذَبَ، وإذا وَعَدَ أخْلَفَ، وإذا اؤتُمِنَ خَانَ)). متفق عليه من حديثِ أبي هُريرةَ رضِي الله عنه.
Ma'ana:"Alamomin munafuki ukune, idan yayi Magana sai yayi karya, idan yayi alkawari sai ya saba kuma idan aka amince dashi sai yayi ha'inci". Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi daga hadisin Abu Huraira (Allah Ya kara masa yarda).
A wata riwayar ta Imamu Muslim yace:
((آيةُ المُنافقِ ثلاثٌ وإنْ صلَّى وصام وزَعَمَ أنه مُسلِمٌ)).
Ma'ana:"Alamomin munafiki guda ukune, koda kuwa yayi salla yayi azumi kuma ya riya cewa shi Musulmine".
A riwayar Imamu Ahmad [yace]:
((ثلاثٌ إذا كُنَّ في الرجُّلِ فهو المُنافِقُ الخَالِصُ...)) الحديثَ، بنحوِه.
Ma'ana:"[Abubuwa] uku idan suka kasance a tattare da mutum, to shi munafukine cikakke…" zuwa karshen hadisin makamancin wancan.
A cikin sahihul Bukhari da shihu Muslim daga hadisin Abdullah dan Amru dan Aas (Allah Ya kara musu yarda) yace, Manzon Allah (S.A.W) Yace:
((أَرْبَعٌ مَن كُنَّ فيه كانَ مُنافِقًا خالصًا، ومَن كانت فيه خَلَّةٌ منهنَّ كانتْ فيه خَلَّةٌ من نفاقٍ حتى يَدَعَها: إذا حدَّثَ كَذَبَ، وإذا عاهَدَ غَدَرَ، وإذا وَعَدَ أخْلَفَ، وإذا خاصَمَ فَجَرَ)).
Ma'ana:"[Abubuwa] hudu duk wanda suka kasance tattare dashi, to ya kasance cikakken munafuki, wanda kuma wata dibi'a daga cikinsu ta kasance tare dashi, to akwai wata dabi'a ta munafurci taredashi har sai ya barta, idan yayi maga yayi karya, kuma idan akayi alkawari dashi, sai yayi yawdara, idan kuma yayi alkawari sai ya saba, idan kuma akayi husuma dashi, sai yayi fajirci".
Saboda haka duk wanda sha'ninsa ya kasance idan yayi maga zaiyi karya, idan yayi alkawari zai saba, kuma idan aka bashi amana zaiyi ha'inci, to shi cikakken munafikine, lafazin 'idha' baya nufin iyakancewa, sai dai yana nufin maimaicine, wannan zai fidda [mutumin] da wani abu daga cikin haka yake karancin faruwa dashi. Sai ya kasance ya aikata aikin zunubi kuma ya zakke ga aiki daga cikin ayyukan munafukai. Sai dai shi bazai zama munafuki ba da aikata wannan ko ma'abucin wata dabi'a ta munafurci har sai hakan ya kasance daga cikin sha'aninsa daya saba dashi ko kuma aka sanshi dashi.
Fasali: cikin [bayani gameda] wanda imani da munafurci zasu kasance acikin zuciyarsa.
Babban munafurci kam, lallai shi baya haduwa da imani. A’a ma’abucinsa ya kafirce wa Allah (Mai girma da dawkaka) koda kuwa yayi salla yayi azumi kuma ya riya cewa shi Musulmine. Saboda kafirci yana rusa ayyuka baki daya. Imani da babban kafirci kuma basa taba haduwa. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَمَنْ يَكْفُرْ بِالْإِيمَانِ فَقَدْ حَبِطَ عَمَلُهُ وَهُوَ فِي الْآَخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ﴾ [المائدة: ٥].
Ma'ana:"Kuma wanda ya kafirce da imani , to hakika aikinsa ya baci kuma shi a lahira yana daga cikin masu hasara" Q5ayata5.
Amma karamin munafurci wanda baya fitarwa daga Addini, hakika wani sashi na dabi'unsa kan iya kasancewa a zuciyar mumini, kamar yadda hadisin daya gabata na Abdullahi dan Amru dan Aas yayi nuni zuwa gareshi.
Acikin sahihu Muslim daga hadisin Abuhuraira (Allah Ya kara masa yarda) yace, Manzon Allah (S.A.W) yace:
((مَن ماتَ ولَم يَغْزُ، ولَمْ يُحدِّثْ نفسَهُ بالغَزْوِ ماتَ على شُعبةٍ مِنَ النفاقِ)) رواه مسلمٌ.
Ma'ana:"Duk wanda ya mutu baiyi yaki ba kuma buranta wa kansa yin yaki ba, to ya mautu akan wani reshe na munafurci". Imamu Muslimne ya ruwaitoshi.
Kuma Huzaifa dan Yaman (Allah Ya karamasa yarda) yace:"Zukata naw'uka hudune:
-Zuciya lullubabbiya, wannar itace zuciyar munafuki.
- Zuciya rufaffiya, wannar itace zuciyar kafiri.
-Zuciya sumbulalliya kamar kace fitilace acikinta mai hake, wannar itace zuciyar mumini.
-Zuciyar da acikinta akwai munafurci da imani, misalinta kamar misalign kurjine wanda yake zubarda diwa da jini, kuma misalinta shine misalin bishiyar da ruwan kazanta da ruwa mai tsafta ke shayar da ita, duk wanda yayi galaba akanta shi zaiyi rinjaye" Ibnu Abi- Shaiba ne ya ruwaitoshi acikin (littafinsa) Almusannaf acikin kitabul iman kuma Albani ya ingantashi amma ance yanada illata tsinkewar isnadi saidai ma'anarsa ingantaccene.
Zuciya lullubabbiya ko yababbiya, itace karkatacciya.
Aliyu dan Abu Dalib (Allah Ya kara masa yarda) yace:" Imani yakan fara ne alhali yana wani digon fari acikin zuciya, duk sa'adda imani ya karu, sai digon ya kara fari har zuciya ta zama fara dukkaninta, shi kuma munafurci yana farawane dabakin digo acikin zuciya, duk sa'adda munafurci ya karu sai ya kara bakantuwa har sai zuciyar ta bakance baki dayanta" Ibnu Abi- Shaiba ne ya ruwaitoshi acikin (littafinsa) Almusannaf acikin kitabul iman da Al –Baihaki acikin shu'abul iman.
(Lafazin "Allamzatu" – acikin maganar Sayyidina Ali- tana nufin) dan kankanin digo.
Abin nufi shine, munafurci yakan iya kasancewa tareda mumini, yawansa da karantansa ya dogara ga matsayin imaninsa da da'arsa ga Allah (Mai girma da dawkaka), daga cikinsu akwai wanda akesamun wani gawraye daga gawrayen munafurci taredashi, sai yayi karya daya ko biyu, wanin karon kuma ya saba alkawari da makamancin haka.
Daga cikinsu kuma akwai wanda yake yawaita fadawa cikin ireiren wadannan ayyukan, tareda karantawa cikin ambaton Allah, da yawan ketare iyakokin Allah ta hanyar keta alfarmar haramtattun al'amura da sakaci cikin wajibai, da kifuwa akan abubuwan shi'awa, da ruduwa da shubuhohi, sai yakasance acikin zuciyarsa akwai munfurci mai yawa da imani dan kadan, harma akan samu daga cikin Musulmi akwai wanda yake baya yin salla face cikin gaggawa tareda jinkirta sallar har zuwa lokacin karhanci da munanawarshi acikin aiwatar da ita. Kamar yadda yazo acikin sahihu Muslim daga hadisin Anas dan Malik (Allah Ya kara masa yarda) yace, naji Manzo Allah (S.A.W) yana cewa:

((تلكَ صلاةُ المنافقِ، يَجْلِسُ يَرْقُبُ الشمسَ حتى إذا كانتْ بينَ قَرْنَي الشيطانِ قامَ فنَقَرَهَا أَربعًا لا يذكُرُ اللهَ فيها إِلا قليلاً)). رواه مسلمٌ
Ma'ana:"Wannan itace sallar munafuki, zai zawna yana jiran rana har sai ta kasance tsakanin kahonnin shedan guda biyu, sai ya tashi yayi tsatstsagensu guda hudu, baya ambaton Allah acikinsu face dan kadan" Imamu Muslim ne ya ruwaitoshi.
Wannan yana faruwane ga wanda munafurci yayi galaba acikin zuciyarsa kuma ya cancanci a akirashi munafuki, tare samuwan wani imani azuciyarsa wanda ya hanashi barin salla baki daya.
Fadawa cikin karamar riya da jiyarwa na yawaita acikin ma'abuta wannan sinfin, da abinda ke bata wasu ayyuka kamar gori da cutarwa cikin sadaka, da neman duniya da aikin lahira, da keta alfarmar haramtattun abubuwa ayayin da suka kadaita.
To ma'abuta wannan sinfin suna cikin hadari mai girma. Wannan sakacin na iya kaisu ga fita daga addinin Allah (Mai girma da dawkaka) kuma duk wanda ya mutu daga cikinsu akan wannan munafurcin tareda samuwar wani sashi na imani azuciyarsa, to lallai yana cikin yan kaba'ira, wadanda akayiwa alkawarin matsanancin azaba, saidai shi bazai dawwamaba acikin wuta sakamakon wanzuwar Musuluncinsa, kuma ya inganta daga Annabi (S.A.W) lallai yana cewa:
((يَدْخُلُ أهلُ الجنةِ الجنةَ، وأهلُ النَّارِ النَّارَ، ثم يقولُ اللهُ تعالى: أَخْرِجوا مَن كانَ في قلبِه مِثْقالُ حَبَّةٍ مِن خَرْدَلٍ من إيمانٍ؛ فيُخْرَجونَ منها قد اسْوَدُّوا؛ فيُلْقَونَ في نَهَرِ الحَياةِ؛ فيَنْبُتونَ كمَا تَنْبُتُ الحِبَّةُ في جانبِ السَّيْلِ، ألَمْ تَرَ أنَّهَا تَخْرُجُ صَفْرَاءَ مُلْتَوِيَةً؟)) رواه البخاريُّ من حديثِ أبي سَعِيدٍ الخُدْريِّ رضِي الله عنه.
Ma'ana:"Yan Aljanna zasu shiga Aljanna yan Wutama zasu shiga wuta, sa'annan Allah (Madawkakin Sarki)Yace:" kufitarda wanda acikin zuciyarsa akwai misalign kwayar komayya na imani, sai a fitardasu alhali sun riga sunyi baki, sai a jefasu cikin kogin rayuwa, saisu tsira kamar yadda kwaya ke tsira a gafen kogi mai gudana, shin bakaganiba tana fita da lawnin yalo kuma lankwasashshiya?" Imamul Bukharine ya ruwaitoshi daga hadisin Abu Sa'idin Alkhudri (Allah Ya kara masa yarda)
Amma wanda ya aikata wani abu daga cikin abubuwa masu warware Musulunci, kamar isgilanci da addini, zagin Allah da Manzonsa, jibinta kafirai da taimakonsu akan Musulmai, to shi kafirine wanda ya fita daga Musulunci, hakika imani ya sabule daga zuciyarsa. Allah Yayi mana tsari.
Fasali: game da tuban Munafiki.
Idan munafiki ya tuba kafin mutuwarsa kuma ya kyawtata ayyukansa ya kuma yi riko ga Allah ya tsarkake addininsa ga Allah (Mai girma da dawkaka) to tubarsa ingantacciyace karbabbiya. Allah (Madawkakin Sarki) yace:
﴿إِنَّ الْمُنَافِقِينَ فِي الدَّرْكِ الْأَسْفَلِ مِنَ النَّارِ وَلَنْ تَجِدَ لَهُمْ نَصِيرًا (145) إِلَّا الَّذِينَ تَابُوا وَأَصْلَحُوا وَاعْتَصَمُوا بِاللَّهِ وَأَخْلَصُوا دِينَهُمْ لِلَّهِ فَأُولَئِكَ مَعَ الْمُؤْمِنِينَ وَسَوْفَ يُؤْتِ اللَّهُ الْمُؤْمِنِينَ أَجْرًا عَظِيمًا (146) مَا يَفْعَلُ اللَّهُ بِعَذَابِكُمْ إِنْ شَكَرْتُمْ وَآَمَنْتُمْ وَكَانَ اللَّهُ شَاكِرًا عَلِيمًا (147)﴾ [النساء: ١٤٥– ١٤٧].
Ma'ana:"Lallai munafukai suna cikin mafi zurfin magangara daga Wuta, kuma bazaka taba sama musu wani mataimakiba (145) Saidai wadanda suka tuba kuma suka kyawtata kuma suka nemi mafaka ga Allah kuma suka tsarkake addininsu ga Allah, to wadannan suna tareda muminai, kuma da sannu Allah zai bawa muminai lada mai girma (146) Menene Allah zai amfana dashi cikin yi muku azaba in kuka gode kuma kuka yi imani? Kuma lallai Allah Ya kasance mai godiya Masani (147). Q4ayata145-147.
Kuma hakanan Musulmin daya kasance tare dashi akwai wata dabi'a ta munafurci idan ya tuba Allah zai karbi tubansa kuma zai barranta daga munafurci.
Acikin wannar matsalar akwai wasa kwakwalwa mai ban dariya wanda Huzaifa dan Yaman (Allah Ya kara masu yarda) ya bijiro dashi ga daliban tsangayar Abdullahi dan Mas'ud (Allah Ya kara masa yarda), lallai ya tsaya akansu alhali Abdullahi dan Mas'udu yana nan, sai yayi musu sallama sannan yace:"hakika an sawkarda munafurci akan wasu mutane da suka fiku alheri" sai Abdullahi dan Mas'udu yayi murmushi ya kuma fahimci manufarsa.
Dalibansa sukace; tsarki ya tabbata ga Allah, lallai Allah (Mai girma da dawkaka) Yana cewa:
﴿إِنَّ الْمُنَافِقِينَ فِي الدَّرْكِ الْأَسْفَلِ مِنَ النَّارِ﴾ [النساء: ١٤٥]!!
Ma'ana:"Lallai munafukai suna cikin magangara mafi zurfi daga cikin Wuta" Q4ayat145.
Sannan bayan an waste daga tsangayar, sai Huzaifa yaceda Aswad dan Yazid Annakha'i daya daga cikin daliban Abdullahi dan Mas'ud:" hakika an sawkarda munafurci akan wasu mutane da suka fiku alheri sannan sai suka tuba sai Allah Ya karbi tubansu".
a wata riwayar yace:"Lallai su yayin da suka tuba sai suka kasance mafiya alkhairi daga ku"
Yana nufin wasu daga cikin wadanda suka kasance munafukai a zamanin Manzon Allah (S.A.W) sannan sai suak tuba kuma suka gyara kuma suka kyawtata musuluncinsu, sai suka kasance ) mafiya alheri sama da wadanda suka zo abayansu daga tabi'ai albarkacin ladan abuta da Annabi da jihadi tareda Annabi (S.A.W
Kuma wannar kisser Imamul Bukhari ya ruwaitota acikin sahihinsa.

Fasali: Kuma ya wajaba ga muminai suyi aikin da zai kubutar dasu daga dabi'un munafurci da ayyukan munafukai, daga cikin haka akwai mai maita tuba da neman gafara da kiyaye dokokin Allah da girmama umurce umurcenSa da barranta daga shirka da ma'abutanta da tsaida salla da bada zakka da nasiha ga Allah da ManzonSa da littafinSa da shugabannin Musulmai da gama garinsu.
Daga cikin haka:Akawi son jihadi saboda Allah da kuma kwadaitarwa rai game da hakan.
Kuma daga cikin haka akwai umurni da kyakkyawa da hani ga mummuna da yiwa juna wasiyya da gaskiya da yiwa juna wasiyya da hakuri da kwadaitar da juna akan ciyar da miskini da ciyarwa saboda Allah bisa imani da neman lada.
Duk wanda ya aikata haka zai kasance barrantacce daga munafurci
Yazo acikin musnad da waninsa daga hadisin Umar dan Khaddabi (Allah Ya kara masa yarda) lallai manzon Allah yace:
((مَنْ سَرَّتْهُ حَسَنَتُهُ وسَاءَتْهُ سَيِّئَتُهُ فهو مُؤْمِنٌ)).
Ma'ana:"Duk wanda kyakyyawan aikinsa ya faranta masa rai kuma mummunan aikinsa ya bakanta masa rai, to shi muminine"
Saboda haka duk wanda ya fada cikin wani zunubi kuma zunubin ya bakanta masa rai to wannan alamace ta ingancin imaninsa, kuma akwai kyakkyawan tsammanin cewa zai tuba kuma ya nemi gafara kuma ya nemi yarda, wanda kuma yayi farin ciki da sabonsa kuma mummunan aikinsa ya faranta masa rai, to wannan alamace ta dake nuni zuwaga munafurci a cikin zuciyarsa.
A cikin sunanu- Attirmidhi daga hadisin Abu Huraira (Allah Ya kara masa yarda) yace; Manzon Allah (S.A.W) yace:
«خَصْلَتَانِ لا تَجْتمعانِ في مُنافِقٍ: حُسْنُ سَمْتٍ، وفِقْهٌ في الدِّينِ». صَحَّحَه الألبانيُّ.
Ma'ana:"Sifofi biyu basu haduwa ga munafuki. Kyakkyawar dabi'a da fahimtar addini" kuma Albani ya ingantashi.