تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس التاسع: التَّحْذِيرُ من النِّفاقِ (1/3)


طاهر جبريل دكو
_5 _April _2013هـ الموافق 5-04-2013م, 02:16 PM
الدرس التاسع: التَّحْذِيرُ من النِّفاقِ (1/3)

النِّفاقُ هو: مُخالفةُ الظاهرِ للباطِنِ، وهو على قِسْمينِ:
· نِفاقٌ أكْبَرُ مُخْرِجٌ عن مِلَّةِ الإسلامِ.
· ونِفاقٌ أصْغَرُ لا يُخْرِجُ من المِلَّةِ.

- أما النِّفاقُ الأَكْبَرُ فهو إِظْهَارُ الإِسْلامِ وإِضْمَارُ الكُفْرِ.
- وأَمَّا النِّفاقُ الأصْغَرُ فهو أن يَكونُ لدَى العبدِ بعضُ خِصالِ المُنافِقِينَ التي لا تُخْرِجُ من المِلَّةِ لذاتِها كالكَذِبِ في الحديثِ وإخلافِ الوَعْدِ وخيانةِ الأمانةِ والفُجورِ في الخُصومةِ والغَدْرِ بالعَهْدِ؛ وهذه الخصالُ سُمِّيت نِفاقًا لما فيها من مُخادعةٍ ومُخالفةِ ظَاهِرِ الشَّخْصِ لباطِنِه.

وأصحابُ النِّفاقِ الأكبرِ المُخْرِجِ من المِلَّةِ على صِنْفَيْنِ:
الصِّنْفُ الأوَّلُ: مَن لم يُسْلِمْ على الحقيقةِ، وإنما أظْهَرَ الإسلامَ خَدِيعةً ومَكْرًا ليَكِيدَ الإسلامَ وأهْلَه، ولِيَأْمَنَ على نفسِه من القتلِ والتعزيرِ وإنكارِ المسلمين عليه، وهو في الباطنِ لا يُؤمِنُ باللهِ ولا باليومِ الآخِرِ.
قال اللهُ تعالى: ﴿وَمِنَ النَّاسِ مَنْ يَقُولُ آمَنَّا بِاللَّهِ وَبِالْيَوْمِ الْآخِرِ وَمَا هُمْ بِمُؤْمِنِينَ (8) يُخَادِعُونَ اللَّهَ وَالَّذِينَ آمَنُوا وَمَا يَخْدَعُونَ إِلَّا أَنْفُسَهُمْ وَمَا يَشْعُرُونَ﴾[البقرة: ٨–٩].
وقال تعالى: ﴿إِذَا جَاءَكَ الْمُنَافِقُونَ قَالُوا نَشْهَدُ إِنَّكَ لَرَسُولُ اللَّهِ وَاللَّهُ يَعْلَمُ إِنَّكَ لَرَسُولُهُ وَاللَّهُ يَشْهَدُ إِنَّ الْمُنَافِقِينَ لَكَاذِبُونَ (1) اتَّخَذُوا أَيْمَانَهُمْ جُنَّةً فَصَدُّوا عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ إِنَّهُمْ سَاءَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ﴾ [المنافقون: ١–٢].

الصِّنْفُ الثاني: مَن يَرْتَدُّ بعدَ إسلامِه بارتكابِه ما يَنْقُضُ الإسلامَ ويُخْرِجُ من المِلَّةِ مع إظهارِه للإسلامِ، ومنهم مَن يُعْلَمُ بكُفْرِه وانْسِلاخِه من الدِّينِ، ومنهم مَن يَحْسَبُ أنه يُحْسِنُ صُنْعًا.
ويَكْثُرُ في أهلِ هذا الصِّنْفِ التَّردُّدُ والتَّذَبْذُبُ والشكُّ؛ لأنهم يَعْمَلُون ببَعْضِ أعمالِ المسلمين ويَقَعُونَ في أعمالِ الكُفْرِ والتَّكْذيبِ.
قال اللهُ تعالى:﴿إِنَّ الْمُنَافِقِينَ يُخَادِعُونَ اللَّهَ وَهُوَ خَادِعُهُمْ وَإِذَا قَامُوا إِلَى الصَّلَاةِ قَامُوا كُسَالَى يُرَاءُونَ النَّاسَ وَلَا يَذْكُرُونَ اللَّهَ إِلَّا قَلِيلًا (142) مُذَبْذَبِينَ بَيْنَ ذَلِكَ لَا إِلَى هَؤُلَاءِ وَلَا إِلَى هَؤُلَاءِ وَمَنْ يُضْلِلِ اللَّهُ فَلَنْ تَجِدَ لَهُ سَبِيلًا﴾ [النساء: ١٤٢–١٤٣].
وقال تعالى: ﴿وَمَا مَنَعَهُمْ أَنْ تُقْبَلَ مِنْهُمْ نَفَقَاتُهُمْ إِلَّا أَنَّهُمْ كَفَرُوا بِاللَّهِ وَبِرَسُولِهِ وَلَا يَأْتُونَ الصَّلَاةَ إِلَّا وَهُمْ كُسَالَى وَلَا يُنْفِقُونَ إِلَّا وَهُمْ كَارِهُونَ﴾ [التوبة: ٥٤].
فوُقُوعُهم في أعمالِ الكُفْرِ باللهِ وبرُسولِه مَانِعٌ من قَبُولِ أعمالِهم؛ فإنَّ اللهَ تعالى لا يَقْبَلُ من كافرٍ عَمَلاً.
وكَسَلُهم عندَ القيامِ للصلاةِ وكَرَاهَتُهم للإنفاقِ في سبيلِ اللهِ دَلِيلٌ على أنهم لم يُصَدِّقوا بوَعْدِ اللهِ ولم يَرْجُوا لقاءَه.
وقِلَّةُ ذِكْرِهم للهِ سَبَبُه أنهم يَذْكُرونَ اللهَ بألسنتِهم رِياءً ونِفاقًا وقُلُوبُهم غَيْرُ مُحِبَّةٍ لدينِ اللهِ تعالى؛ فهم بذلك مُذَبْذَبونَ مُتَرَدِّدونَ ليسوا كالكُفَّارِ ظَاهِرًا وبَاطِنًا، ولا مِن المؤمنين ظاهرًا وباطنًا.
قال ابنُ كثيرٍ: (ومنهم مَن يَعْتريهِ الشكُّ، فتَارَةً يَمِيلُ إلى هؤلاءِ، وتَارَةً يَمِيلُ إلى أولئكَ ﴿كُلَّمَا أَضَاءَ لَهُمْ مَشَوْا فِيهِ وَإِذَا أَظْلَمَ عَلَيْهِمْ قَامُوا﴾ [البقرة: ٢٠]، الآية) ا.هـ.
قال عبدُ اللهِ بنُ عُمَرَ رضِي الله عنهما سَمِعتُ النبيَّ صلى الله عليه وسلم يقولُ: ((مَثَلُ المُنافِقِ كمَثَلِ الشَّاةِ العَائِرَةِ بينَ الغَنَمَيْنِ تَعِيرُ إلى هذه مَرَّةً وإلى هذه مَرَّةً)). رواه مسلمٌ
وفي روايةٍ في مُسندِ الإمامِ أحمدَ: ((تَعِيرُ إلى هذهِ مَرَّةً وإلى هذه مَرَّةً، لا تَدْرِي أهذه تَتَّبِعُ أم هذه؟!)).

وقد بيَّنَ اللهُ تعالى في كتابِه الكريمِ، وبيَّنَ النبيُّ صلَّى اللهُ عليهِ وَسَلَّمَ فِي سُنَّتِهِ المُطهَّرةِ أعمالَ المنافقينَ وخِصالَهم وعلاماتِهم وعُقوباتِهم في الدنيا والآخِرَةِ، وأحْكَامَ مُعامَلَتِهم، وما يَجِبُ على المُؤمنِ من الحَذَرِ من النِّفاقِ والمنافقين؛ فهم ألدُّ الأعداءِ وأعْظَمُهم خَطَرًا، وقد قالَ اللهُ تعالى فيهم: ﴿هُمُ الْعَدُوُّ فَاحْذَرْهُمْ﴾ [المنافقون: ٤].
فيَجِبُ على المُؤمِنِ أن يَحْذَرَ من كَيْدِهم ومَكْرِهم، ويَحْذَرَ من الاغترارِ بما يُزَيِّنُونَ من أعمالِ الكفرِ والفُسوقِ والعِصْيانِ، ويَحْذَرَ من التَّخَلُّقِ بأخلاقِهم والاتصافِ بصِفَاتِهم.

والمنافقونَ من الصِّنْفِينِ مُتفاوِتونَ في نِفاقِهم فبَعْضُهم أعْظَمُ نِفاقًا وكُفْرًا من بَعْضٍ:
– فمنهم المَارِدُونَ على النِّفاقِ، وهم شَدِيدُو العَداوةِ والكَيْدِ للإسلامِ والمسلمين، الذين يَترَبَّصونَ بالمسلمين الدَّوائِرَ، ويَسْعَوْنَ للفِتْنةِ بينَهم وتَوْهينِهم، وتَهْويلِ شَأْنِ الكُفَّارِ وتَمْكينِهم؛ فلذلك يَبُثُّونَ الشائعاتِ والأكاذيبَ والأراجِيفَ، ويُثِيرونَ الشُّبُهاتِ، ويُزَيِّنونَ الشَّهواتِ، ويُشِيعونَ الفَوَاحِشَ، ويُؤْذُونَ المسلمين في أنفسِهم وأعراضِهم بطُرقٍ ماكرةٍ ومكائِدَ دَنِيئَةٍ، ويَسْعَوْنَ للتَّضْيِيقِ عليهم في أمورِ دِينِهم ودُنْياهم بما يَسْتَطِيعونَ.
ويُنَفِّرونَ من الدَّعْوةِ إلى اللهِ والجهادِ في سبيلِه والأمرِ بالمعروفِ والنَّهْيِ عن المُنْكَرِ، ويُسَمُّونَ ما يَقُومونَ به من الفَسادِ والإفسادِ إصلاحًا، ويَصِفُونَ المؤمنين بالسَّفَهِ والجَهْلِ وقِلَّةِ المَعْرفةِ.
ويَنْفِرونَ من تَحْكِيمِ الشَّريعةِ، ويُرِيدُونَ أن يَتحاكَمُوا إلى الطاغوتِ، ويُبْغِضُونَ المُجاهِدِينَ في سبيلِ اللهِ ومَن يَنْصُرُ الإسلامَ والمسلمين.
قال النبيُّ صلى الله عليه وسلم: ((آيةُ الإيمانِ حُبُّ الأنصارِ، وآيةُ النِّفاقِ بُغْضُ الأنصارِ)) متفق عليه من حديثِ أنسِ بنِ مالكٍ رضِي الله عنه.
فلأَجْلِ أنَّ الأنصارَ نَصَرُوا الدِّينَ كان بُغْضُ مَن أبْغَضَهم عَلامةً بَيِّنَةً على نفاقِه.
ويَجْمَعُ وَصْفَ أعمالِ المنافقينَ أنَّهم يَأْمُرونَ بالمُنْكَرِ ويَنْهَوْنَ عن المَعْروفِ ويَقْبِضُونَ أَيْدِيَهُم.
ومن عَلاماتِ هؤلاء أنَّهم إذا أصابَ المُؤمنين بَلاءٌ ومِحْنَةٌ سَرَّهم ذلك وفَرِحوا به، وشَمِتوا بالمُؤْمِنينَ، وإذا أصابَ المؤمنين خَيْرٌ ونَصْرٌ ورِفْعَةٌ ساءَهم ذلك.
ولذلك كانَ من أَعْظَمِ صِفاتِهم وألصقِها بهم أنهم يَتَّخِذُونَ الكافرينَ أولياءَ مِن دُونِ المؤمنين، ويُفْضُون إليهم بعَوْراتِ المُسلمين، ويُحَرِّضُونَهم على حَرْبِهم والتَّسلُّطِ عليهم، ويَسْتَنْصِرُونَ بهم على ذلك.
قال اللهُ تعالى: ﴿بَشِّرِ الْمُنَافِقِينَ بِأَنَّ لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا (138) الَّذِينَ يَتَّخِذُونَ الْكَافِرِينَ أَوْلِيَاءَ مِنْ دُونِ الْمُؤْمِنِينَ أَيَبْتَغُونَ عِنْدَهُمُ الْعِزَّةَ فَإِنَّ الْعِزَّةَ لِلَّهِ جَمِيعًا (139) وَقَدْ نَزَّلَ عَلَيْكُمْ فِي الْكِتَابِ أَنْ إِذَا سَمِعْتُمْ آَيَاتِ اللَّهِ يُكْفَرُ بِهَا وَيُسْتَهْزَأُ بِهَا فَلَا تَقْعُدُوا مَعَهُمْ حَتَّى يَخُوضُوا فِي حَدِيثٍ غَيْرِهِ إِنَّكُمْ إِذًا مِثْلُهُمْ إِنَّ اللَّهَ جَامِعُ الْمُنَافِقِينَ وَالْكَافِرِينَ فِي جَهَنَّمَ جَمِيعًا (140) الَّذِينَ يَتَرَبَّصُونَ بِكُمْ فَإِنْ كَانَ لَكُمْ فَتْحٌ مِنَ اللَّهِ قَالُوا أَلَمْ نَكُنْ مَعَكُمْ وَإِنْ كَانَ لِلْكَافِرِينَ نَصِيبٌ قَالُوا أَلَمْ نَسْتَحْوِذْ عَلَيْكُمْ وَنَمْنَعْكُمْ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ فَاللَّهُ يَحْكُمُ بَيْنَكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَلَنْ يَجْعَلَ اللَّهُ لِلْكَافِرِينَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ سَبِيلًا (141)﴾ [النساء: ١٣٨–١٤١].
وهذه الأعمالُ المَذْكورةُ هي لأصنافٍ من المنافقين؛ فمنهم مَن يَقَعُ في أكثرِها، ومنهم مَن يَقَعُ في شَيْءٍ منها، وكلُّ مَن أظْهَرَ الإسلامَ وارْتَكَبَ ما يخرجُ بهِ من مِلَّةِ الإِسْلامِ فهو مُنافِقٌ كَافِرٌ.
– ومن المُنافِقِينَ مَن هو مُتَرَدِّدٌ بينَ الإسلامِ والكُفْرِ، فتَارَةً يَعْمَلُ أعمالَ المسلمين ظاهِرًا وباطِنًا، وتَارَةً يَرْتَكِبُ ما يَخْرُجُ به من دينِ الإسلامِ، فهو مُتَذَبْذِبٌ مُتَرَدِّدٌ، لم يُخْلِصْ دينَهُ للهِ، ولم يَثْبُتْ قَدَمُه فِي الإسلامِ، ولم يُصَدِّقْ بوَعْدِ اللهِ.
وهؤلاء يُبَيِّنُ الابتلاءُ حالَهُم ويَكْشِفُ عَوَارَهم ونِفَاقَهُم، ويُعاقَبُون بالطَّبْعِ على قُلوبِهم، وبالرِّيبةِ والشَّكِّ والتَّردُّدِ في أحوالِهم وأعمالِهم، وذلك لأنهم عَرَفوا الحقَّ فلم يَتَّبِعوه، ووَعَظَهم اللهُ فلم يَسْتَجِيبُوا لمَوَاعِظِه ولم يَتَّبِعوا هُداه، ولم يكن لَدَيْهم يَقِينٌ بصِدْقِ وَعْدِ اللهِ وَوَعْدِ رَسُولِه، وغَلَبَ على قُلوبِهم التَّعَامِي عن هُدَى اللهِ، وإيثارُ الحياةِ الدنيا، واتباعُ ما تَهْوَى الأَنْفُسُ.
قال الله تعالى: ﴿ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ آَمَنُوا ثُمَّ كَفَرُوا فَطُبِعَ عَلَى قُلُوبِهِمْ فَهُمْ لَا يَفْقَهُونَ﴾ [المنافقون: ٣].
وقال تعالى: ﴿إِنَّ الَّذِينَ آَمَنُوا ثُمَّ كَفَرُوا ثُمَّ آَمَنُوا ثُمَّ كَفَرُوا ثُمَّ ازْدَادُوا كُفْرًا لَمْ يَكُنِ اللَّهُ لِيَغْفِرَ لَهُمْ وَلَا لِيَهْدِيَهُمْ سَبِيلًا (137) بَشِّرِ الْمُنَافِقِينَ بِأَنَّ لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا﴾ [النساء: ١٣٧–١٣٨].
وأهلُ هذا الصِّنْفِ من المنافقين يَقَعُونَ في أعمالٍ كُفْريَّةٍ مُخرِجةٍ عن المِلَّةِ؛ كمُوالاةِ الكُفَّارِ في الفِتَنِ والشدائدِ، والاستهزاءِ بالدِّينِ وسَبِّ اللهِ ورسولِه، والنُّفورِ من تَحْكيمِ الشريعةِ، وإرادةِ تَحْكيمِ الطَّاغوتِ، والتكذيبِ بوَعْدِ اللهِ، ونحوِ ذلك من الأعمالِ والأقوالِ والاعتقاداتِ التي تُخْرِجُ صاحبَها من مِلَّةِ الإسلامِ.

والعبدُ قد يَكْفُرُ بكلمةٍ يَقولُها، كما قال اللهُ تعالى في المنافقين: ﴿يَحْلِفُونَ بِاللَّهِ مَا قَالُوا وَلَقَدْ قَالُوا كَلِمَةَ الْكُفْرِ وَكَفَرُوا بَعْدَ إِسْلَامِهِمْ﴾ [التوبة: ٧٤]؛ فهؤلاء كفروا بكلمةٍ قالوها بعدما كانوا مسلمين.
وقال حُذيفةُ بنُ اليَمَانِ رضِي الله عنه: (إنْ كانَ الرجُلُ لَيَتكَلَّمُ بالكلمةِ على عهدِ رسولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم فيَصِيرُ مُنافِقًا، وإنِّي لأَسْمَعُها من أَحَدِكم في المَقْعَدِ الوَاحِدِ أَرْبَعَ مَرَّاتٍ.
لَتَأمُرُنَّ بالمعروفِ ولَتَنْهَوُنَّ عن المُنْكَرِ، ولَتَحَاضُنَّ على الخيرِ، أو لَيُسْحِتَنَّكُمُ اللهُ جميعًا بعذابٍ، أو لَيُؤَمِّرَنَّ عليكم شِرارَكم، ثم يَدْعو خِيارُكم فلا يُسْتجابُ لكم). رواه أحمدُ وابنُ أبي شَيْبَةَ.
وعن أبي هُريرةَ رضِي اللهُ عنه عن النبيِّ صلى الله عليه وسلم قال: ((إنَّ العَبْدَ لَيَتَكَلَّمُ بالكَلِمَةِ مِن رِضْوَانِ اللهِ لا يُلْقِي لها بَالاً يَرْفَعُهُ اللهُ بها دَرَجاتٍ، وإنَّ العبدَ لَيَتكَلَّمُ بالكلمةِ من سَخَطِ اللهِ لا يُلْقِي لها بَالاً يَهْوِي بها في جَهَنَّمَ)). رواه البخاريُّ.
وعن عَلْقمةَ بنِ وَقَّاصٍ الليثيِّ عن بِلالِ بنِ الحارِثِ المُزنِيِّ رضِي الله عنه أن رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قال: ((إنَّ الرَّجُلَ لَيتكَلَّمُ بالكلمةِ من رِضْوانِ اللهِ ما كانَ يَظُنُّ أن تَبْلُغَ ما بَلَغَتْ، يَكْتُبُ اللهُ له بها رِضْوَانَهُ إلى يومِ يَلْقَاهُ، وإنَّ الرَّجُلَ لَيَتَكَلَّمُ بالكلمةِ مِن سَخَطِ اللهِ ما كانَ يَظُنُّ أنْ تَبْلُغَ ما بَلَغَتْ، يَكْتُبُ اللهُ له بها سَخَطَهُ إلى يومِ يَلْقَاهُ)). رواه مالكٌ في المُوَطَّإِ، وأحمدُ في مُسْندِه، وزادَ: (فكانَ عَلْقَمَةُ يَقولُ: كَمْ مِن كَلامٍ مَنَعَنِيهِ حَدِيثُ بِلالِ بنِ الحَارِثِ).
ورَوَى البَيْهقِيُّ عن مُحمَّدِ بنِ عَمْرِو بنِ عَلْقَمَةَ بنِ وَقَّاصٍ أنه قال: كانَ رَجُلٌ بَطَّالٌ يدخُلُ على الأُمراءِ فيُضْحِكُهم، فقال له جَدِّي: (وَيْحَكَ يا فُلانُ، لِمَ تَدْخُلُ على هؤلاءِ فتُضْحِكُهم؟! فإني سَمِعتُ بلالَ بنَ الحارِثِ المُزنِيَّ صَاحِبَ رسولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم يُحدِّثُ...) فذكَرَ الحديثَ.
فخَطَرُ اللسانِ عَظِيمٌ، وشأنُ الكَلامِ كَبِيرٌ، ومَن عدَّ كَلامَه من عَمَلِه احْتَرَزَ في مَنْطِقِهِ، وظَهَرَتْ عليه أماراتُ التَّقْوَى؛ فإن العبدَ إذا تَهاوَنَ في مَنطقِهِ مع رِقَّةِ دِيانتِه لم يَأْمَنْ أن يَتكَلَّمَ بكلمةٍ تُوجِبُ له سَخَطَ اللهِ ومَقْتَهُ، أو يَتَكَلَّمَ بكلمةٍ يَكْفُرُ بها ويَخْرُجُ بها من دينِ الإسلامِ، والعياذُ باللهِ.
وهذا الأمرُ يَكْثُرُ وُقوعُه عندَ الفِتَنِ ولا سِيَّما في آخِرِ الزمانِ كما في الصحيحين من حديثِ أبي هُريرةَ رضِي الله عنه أن رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قال: ((بَادِرُوا بالأعمالِ فِتَنًا كقِطَعِ الليلِ المُظْلمِ، يُصبِحُ الرَّجُلُ مُؤمِنًا ويُمْسِي كَافِرًا، ويُمْسِي مُؤْمِنًا ويُصْبِحُ كافِرًا، يَبِيعُ دِينَهُ بعَرَضٍ من الدُّنْيَا)).
نسألُ اللهَ السلامةَ والعافيةَ، وأن يُجِيرَنا من أسبابِ سَخَطِه وعقابِه.
ولذلك اشْتَدَّ خَوْفُ الصحابةِ والتابعين من الوُقوعِ في شيءٍ من أعمالِ المُنافِقينَ.
قال البخاريُّ في صحيحِه: (قال ابنُ أبي مُلَيْكَةَ: أدْرَكْتُ ثَلاثِينَ من أصحابِ النبيِّ صلى الله عليه وسلم كلُّهم يَخافُ النِّفاقَ على نَفْسِه، ما منهم أَحَدٌ يَقولُ إنَّه على إيمانِ جِبْريلَ ومِيكائِيلَ.
ويُذْكَرُ عن الحَسَنِ: ما خَافَهُ إلا مُؤمِنٌ، ولا أَمِنَهُ إلا مُنافِقٌ).
قال زَيْدُ بنُ وَهْبٍ: (ماتَ رَجُلٌ من المُنافِقِينَ فلم يُصَلِّ عليه حُذَيفةُ، فقال له عُمَرُ: أَمِنَ القَوْمِ هو؟
قال: نعم.
فقال له عُمَرُ: باللهِ منهم أنا؟
قال: لا، ولن أُخْبِرَ به أحَدًا بَعْدَكَ). رواه ابن أبي شيبة.
وحُذيفةُ بنُ اليَمَانِ رضِي الله عنه كانَ قد أسَرَّ إليه النبيُّ صلى الله عليه وسلم بأسماءِ المنافقين، وهو من أعلمِ هذه الأُمَّةِ بأحوالِ المنافقين وأحكامِهم وأعمالِ النِّفاقِ، وكان الصحابةُ يَعْرِفونَ له قَدْرَه في ذلك، ولذلك كانَ عُمَرُ يَرْقُبُه إذا قُدِّمت جِنازةٌ، فإن رأى حُذيفةَ لا يُصَلِّي عليها لم يُصَلِّ عليها، واستنابَ مُن يُصَلِّي عليها، لئلا يُفْشِيَ سِرَّ رسولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم.

طاهر جبريل دكو
_5 _April _2013هـ الموافق 5-04-2013م, 02:17 PM
Darasi na tara: Gargadi gameda munfurci 1/3
Munafurci shine sabawan zahiri ga badini, kuma ya kasu kasha biyu:
Babban munafurci wanda ke fitarwa daga Addinin Musulunci.
Da karamin Munafurci wanda baya fitarwa daga Addinin Musulunci.
Amma shi babban munafurci, shine bayyana Musulunci da boye kafirci.
Amma shiko karamin munafurci, shine samun wasu daga cikin dabi'una munafukai tareda bawa wadanda basu fitarwa daga Addini da karan kansu. Kamar karya acikin zance, saba alkawari, cin amana, fajirci cikin husuma da yawdara. Wadannan dabi'un ankirasu munafurcine saboda abinda ke cikinsu na ha'inci da sabanin dake tsakanin zahirin bawa da badininsa.
Ma'abuta babban munafurci mai fitarwa daga Addini sun kasu zuwa simfi biyu:
Simfi na farko:Wanda dama asali bai musuluntaba bisa hakika, kawai ya bayyana musuluncine don yawdara da makirci, don yayiwa musulunci da musulmi zagon kasa. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَمِنَ النَّاسِ مَنْ يَقُولُ آمَنَّا بِاللَّهِ وَبِالْيَوْمِ الْآخِرِ وَمَا هُمْ بِمُؤْمِنِينَ (8) يُخَادِعُونَ اللَّهَ وَالَّذِينَ آمَنُوا وَمَا يَخْدَعُونَ إِلَّا أَنْفُسَهُمْ وَمَا يَشْعُرُونَ﴾[البقرة: ٨–٩].
Ma'ana:"Kuma daga cikin mutane akwai wanda ke cewa; "munyi imani da Allah da ranar karshe," alhali kuwa suba ba muminai bane (8) Suna yawdara ga Allah da masu imani, alhali basu yawdari kowa ba face kawukansu, kuma basu sakankancewa (9) Q2ayata8 da9. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:

﴿إِذَا جَاءَكَ الْمُنَافِقُونَ قَالُوا نَشْهَدُ إِنَّكَ لَرَسُولُ اللَّهِ وَاللَّهُ يَعْلَمُ إِنَّكَ لَرَسُولُهُ وَاللَّهُ يَشْهَدُ إِنَّ الْمُنَافِقِينَ لَكَاذِبُونَ (1) اتَّخَذُوا أَيْمَانَهُمْ جُنَّةً فَصَدُّوا عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ إِنَّهُمْ سَاءَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ﴾ [المنافقون: ١–٢].
Ma'ana:"Idan munafukai sukazo gareka sai su dora cewa; "mun shaida cewa kai Manzon Allah ne, kuma Allah Ya san cewa kai ManzonSa ne, kuma Allah Ya shaida cewa munafukai makaryatane (1) Sun riki rantse rantsensu a matsayin garkuwa garesu sai suka kange daga tafarkin Allah. Lallai abinda sukeyi ya munana. (2) Q63ayata1da2.

Sinfi na biyu:Wanda zaiyi ridda bayan kasancewarsa Musulmi, ta hanyar aikata abinda ke warware Musulunci kuma ya fitar (da maiyinsa) daga Addini, tareda bayyana Musulunci. Daga cikinsu akwai wanda ake sanin kafircinsa da zarewarsa daga Addini. Daga cikinsu kuma akwai wanda yake zaton cewa shi mai kyawtata aikine.
Taraddudi da kai komo da shakka yana yawaita acikin ma'abuta wannan simfin, saboda suna aiwatar da wasu daga cikin ayyukan Musulmi kuma sukan awka cikin wasu ayyukan kafirci da karyatawa. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿إِنَّ الْمُنَافِقِينَ يُخَادِعُونَ اللَّهَ وَهُوَ خَادِعُهُمْ وَإِذَا قَامُوا إِلَى الصَّلَاةِ قَامُوا كُسَالَى يُرَاءُونَ النَّاسَ وَلَا يَذْكُرُونَ اللَّهَ إِلَّا قَلِيلًا (142) مُذَبْذَبِينَ بَيْنَ ذَلِكَ لَا إِلَى هَؤُلَاءِ وَلَا إِلَى هَؤُلَاءِ وَمَنْ يُضْلِلِ اللَّهُ فَلَنْ تَجِدَ لَهُ سَبِيلًا﴾ [النساء: ١٤٢–١٤٣].
Ma'ana:"Lallai munafukai sunyin yawdara ga Allah alhali kuwa Shine ke yawdararsu, idan suka tashi zuwaga salla sai su tashi suna masu kasala suna yin riya ga mutane, kuma basu ambaton Allah face dan kadan (142) Suna kaikawo takanin haka, basa nan basa can. Kuma duk wanda Allah Ya batar, baka taba sama masa hanya (143) Q4ayata142 da143.
Kuma Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَمَا مَنَعَهُمْ أَنْ تُقْبَلَ مِنْهُمْ نَفَقَاتُهُمْ إِلَّا أَنَّهُمْ كَفَرُوا بِاللَّهِ وَبِرَسُولِهِ وَلَا يَأْتُونَ الصَّلَاةَ إِلَّا وَهُمْ كُسَالَى وَلَا يُنْفِقُونَ إِلَّا وَهُمْ كَارِهُونَ﴾ [التوبة: ٥٤].
Ma'ana:" Kuma ba abinda ya hana a karbi sadakokinsu daga garesu face lallai su sun kafirce da Allah da ManzonSa kuma basa zuwa salla face suna masu kasala kuma basa ciyarwa face suna masu ki. Q9ayata54.
Saboda haka fadawarsu cikin ayyukan kafircewa Allah da ManzonSa shine ya hana akarbi ayyukansu. Domin lallai Allah (Madawkakin Sarki) baYa karban wani aiki daga kafiri.

Kuma kasalarsu ayayin tashi zuwaga salla da kyamatarsu gameda ciyarwa don dawkaka Kalmar Allah daliline akan cewa lallai basu gaskata alkawarin Allah ba kuma basu fatan saduwa da Allah.
Karanci ambatonsu ga Allah sababinsa shine, sun kasance suna ambaton Allah ne da harsunan su don riya, alhali zukatansu basa son Addinin Allah (Madawkakin Sarki) da wannan sai suka kasance masu kai komo basa nan basa can, basuyi kama da kafiraiba [wadanda kafircinsu yake] ta zahiri da badini, kuma basa daga cikin Muminai [masu imani zahiri da badini].
Ibnu Kathir yace:"Daga cikinsu akwai wanda shakka ke bijiro masa, wani lokacin saiya karkata zuwaga wadancan wani lokacin kuma saiya karkata zuwaga wadannan
﴿كُلَّمَا أَضَاءَ لَهُمْ مَشَوْا فِيهِ وَإِذَا أَظْلَمَ عَلَيْهِمْ قَامُوا﴾ [البقرة: ٢٠]، الآية) ا.هـ.
Ma’ana:"Duk sa'adda aka haska musu, sai suyi tafiya acikinsa idan kuma haske ya dawke musu saisu dakata" Q2ayata20.
Abdullahi dan Umar (Allah Ya kara musu yarda) yace: naji manzon Allah (S.A.W) yana cewa:
((مَثَلُ المُنافِقِ كمَثَلِ الشَّاةِ العَائِرَةِ بينَ الغَنَمَيْنِ تَعِيرُ إلى هذه مَرَّةً وإلى هذه مَرَّةً)). رواه مسلمٌ
Ma'ana:"Misalin muafuki shine misalin batacciyar akuya da take kai komo a tsakanin garke biyu na tumaki, wani lokacin tabi wadannan wani lokacin kuma tabi wadannan. Imamu Muslimne ya ruwaitoshi.
A wata riwayar a cikin musnad din Imamu Ahmad yace:
((تَعِيرُ إلى هذهِ مَرَّةً وإلى هذه مَرَّةً، لا تَدْرِي أهذه تَتَّبِعُ أم هذه؟!)).
Ma'ana:"Wani lokacin taje zuwaga wadannan, wani lokacin kuma ta tafi zuwaga wadannan, batasani ba, wai shin wadannan zatabine ko wadancan.

Kuma hakia Allah (Madawkakin Sarki) Ya bayyana acikin littafinSa mai girma, kuma Manzon Allah (S.A.W) ma ya bayyana - acikin sunnoninsa tsarkaka- ayyukan munafukai da dabi'unsu da alamominsu da ukubobinsu anan Duniya da ranan gobe, da hukunce hukuncen mu'amala dasu da abin da yake wajaba ga mumini ya kiyaye gameda munafurci da munafukai. Domin sune miyagun makiya mafiya hadari. Allah Ya fadi gamedasu yace:
﴿هُمُ الْعَدُوُّ فَاحْذَرْهُمْ﴾ [المنافقون: ٤].
Ma'ana:"Sune makiyan, kagujesu. Q63ayata4.
Saboda haka ya wajaba ga Mumini ya kiyayi kaidinsu da makircinsu kuma ya kiyayi ruduwa daga abinda suke kawatawa daga ayyukan kafirci da fasikanci da sabon Allah. Kuma ya guji dabi'antuwa da dabi'unsu da sifantuwa da sifofinsu.
Kuma munafukai cikin wadannan simfi biyun sunada fifiko atsakaninsu gameda munafurcinsu, saboda haka sashinsu sunfi sashi munafurci da kafirci.
Daga cikinsu akawai makangara cikin munafurci, kuma su masu tsananin adawane da kaidi ga Musulunci da Musulmai, wadanda suke yiwa Musulmai kulle kulle, kuma suke kai kawo wurin kunna wutar fitina atsakaninsu da kaskantar dasu, da kambama matsayin kafirai da samar musu da dama, don hakane suke yayata jita jita da karairayi da labarin kanzon kurege. Kuma suna yada shubuhohi (wato abubuwa masu rudani), kuma suke kawata sha'awa, kuma suke warwatsa ayyukan alfasha, kuma suke cutarda Musulmai cikin rayuwarsu da mutuncinsu ta makiran hanyoyi da munanan kaidoji, kuma suke iyakacin kokarinsu na ganin cewa sun kuntata musu cikin al'amuransu na Addini da Duniya da duk abinda suke iyawa.
Kuma suna korewa daga kira zuwaga Allah da Jihadi don dawkaka KalmarSa, da umurni dakyakkyawa da hani ga mummuna, kuma suna ambaton aikin da sukeyi na barna da barnatarwa da sunan gyara, kuma suna sifanta muminai da wawta da jahilci da karancin sani.
Kuma suna korewa daga hukunci da shari'a suna nufin su rika dawkaka hukunci zuwaga dagutu, kuma suna kin masu jihadi don dawkaka Kalmar Allah da duk mai taimakon Musulunci da Musulmai. Annabi (S.A.W) yace:
((آيةُ الإيمانِ حُبُّ الأنصارِ، وآيةُ النِّفاقِ بُغْضُ الأنصارِ)) متفق عليه من حديثِ أنسِ بنِ مالكٍ رضِي الله عنه.
Ma'ana:"Alamar imani shine son Ansar [wato sahabbai mutanen Madina] kuma alamar munafurci shine kin Ansar" Bukari da Muslim ne suka ruwaitoshi daga hadisin Anas dan Malik (Allah Ya kara masa yarda).
Saboda taimakonda Ansar suka yiwa Addinine yasa kiyayyan wanda ya kisu yake zama alama gameda munafurcin sa.
Kuma ayyukan munafukai da sifofinsu ya tattara cikin kasancewarsu suna umurni da mummuna suna hani ga kyakkyawa kuma suna kankame hannuwansu [wato suna rowa]
Kuma yana daga cikin alamomin wadannan [munafukai] kasancewar idan bala'i da jarrabawa suka shafi Muminai, sai ya faranta musu rai kuma suji dadin hakan kuma suyi madalla da [musibar da ta shafi] muminai. Idan kuma alheri da budi da dawkaka ta sami Muminai, sai ya bakanta mus rai.
Wannan shi yasa mafi girman sifansu kuma mafi damfaruwa dasu, kasancewarsu suna rikon kafirai majibinta koma bayan Muminai, kuma suna tona asirin Musulmai awurin su, kuma suna zaburadda su akan yakarsu da mulkansu kuma suna neman agajinsu akan yin hakan. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿بَشِّرِ الْمُنَافِقِينَ بِأَنَّ لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا (138) الَّذِينَ يَتَّخِذُونَ الْكَافِرِينَ أَوْلِيَاءَ مِنْ دُونِ الْمُؤْمِنِينَ أَيَبْتَغُونَ عِنْدَهُمُ الْعِزَّةَ فَإِنَّ الْعِزَّةَ لِلَّهِ جَمِيعًا (139) وَقَدْ نَزَّلَ عَلَيْكُمْ فِي الْكِتَابِ أَنْ إِذَا سَمِعْتُمْ آَيَاتِ اللَّهِ يُكْفَرُ بِهَا وَيُسْتَهْزَأُ بِهَا فَلَا تَقْعُدُوا مَعَهُمْ حَتَّى يَخُوضُوا فِي حَدِيثٍ غَيْرِهِ إِنَّكُمْ إِذًا مِثْلُهُمْ إِنَّ اللَّهَ جَامِعُ الْمُنَافِقِينَ وَالْكَافِرِينَ فِي جَهَنَّمَ جَمِيعًا (140) الَّذِينَ يَتَرَبَّصُونَ بِكُمْ فَإِنْ كَانَ لَكُمْ فَتْحٌ مِنَ اللَّهِ قَالُوا أَلَمْ نَكُنْ مَعَكُمْ وَإِنْ كَانَ لِلْكَافِرِينَ نَصِيبٌ قَالُوا أَلَمْ نَسْتَحْوِذْ عَلَيْكُمْ وَنَمْنَعْكُمْ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ فَاللَّهُ يَحْكُمُ بَيْنَكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَلَنْ يَجْعَلَ اللَّهُ لِلْكَافِرِينَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ سَبِيلًا (141)﴾ [النساء: ١٣٨–١٤١].
Ma'ana:"Kayiwa munafukai albishir da cewa lallai suna da azaba mai radadi (138) Wadanda ke rikon kafirai masoya koma bayan muminai. Shin suna neman dawkakane daga garesu? Dawkaka dukkaninta ta Allah ce (139) Kuma hakika an sawkar gareku acikin Littafin cewa idan kuka ji ayoyin Allah ana kafircewa dasu kuma anayin izgilanci dasu, kada ku zawana taredasu har sai sun kutsa cikin wani labarin dabam dashi.[in ba hakaba kuwa] Lallai kuma kamarsu kuke. Lallai Allah zai hada munafukai da kafirai acikin Jahannama baki daya (140) Wadannan da suke jirandako gameda ku, idan budi ya kasance gareku daga Allah, sai suce ashe bamu kasance taredakuba? Idan kuma wani kaso ya kasance daga kafirai, sai suce ashe bamu rinjayekuba kuma muka tsareku daga muminai? Kuma Allah zai yi hukunci a tsakaninku ranar Kiyama. Kuma Allah bazai sanya tafarkiba ga kafirai akan muminai(141). Q4ayata 139-141.
Kuma wadannan ayyukan da aka ambata na wani simfine daga munafukai. Daga cikinsu (munafukan) akwai wanda ke awkawa cikin mafi yawansu (wato wadannan ayyukan), daga cikinsu kuma akwai wanda ke awkawa cikin wasunsu, kuma duk wanda ya bayyana Musulunci amma ya aikata abinda zai fita daga Addinin Musulunci dashi, to shi munafukine kafiri.
Daga cikin munafukai akwai wanda ke kai komo tsakanin Musulunci da kafirci, wani lokaci ya aikata ayyukan Musulmi azahiri da badini, wani lokacin kuma ya aikata abinda zai fita daga Addinin Musulunci da aikatashi, saboda haka shi mai fuska biyu ne mai kai komo bai tsarkake Addininsa bag a Allah, kuma duddugensa bai tabbataba a Musulunci, kuma bai gaskataba gameda alkawarin Allah.
Kuma wadannan, jarrabawa tana bayyana halinsu ta yaye al'awrarsu da munafurcinsu, kuma ana musu ukuba da sanya murfi akan zukatansu da kokwanto da shakka da taraddudi cikin halayyensu da ayyukansu wannan kuma ya farune saboda sun fahimci gaskiya amma basu bitaba, kuma Allah Yayi musu wa'azi amma basu amsa maSa ba gameda wa'azinSa kuma basu bi shiriyarSaba, basu kasance sunada yakini ba gameda alkawarin Allah da alkawarin ManzonSa, kuma makanta ta ganganci tayi galaba akan zukatansu daga shiriyar Allah, da fifita rayuwar Duniya da soye soyen zuciya. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ آَمَنُوا ثُمَّ كَفَرُوا فَطُبِعَ عَلَى قُلُوبِهِمْ فَهُمْ لَا يَفْقَهُونَ﴾ [المنافقون: ٣].
Ma'ana:Wannan ya kasancene saboda sunyi imani sannan suka kafirce, sai aka sanya rufi akan zukatansu, saboda haka basu fahimta" Q63ayata3. Kuma Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
: ﴿إِنَّ الَّذِينَ آَمَنُوا ثُمَّ كَفَرُوا ثُمَّ آَمَنُوا ثُمَّ كَفَرُوا ثُمَّ ازْدَادُوا كُفْرًا لَمْ يَكُنِ اللَّهُ لِيَغْفِرَ لَهُمْ وَلَا لِيَهْدِيَهُمْ سَبِيلًا (137) بَشِّرِ الْمُنَافِقِينَ بِأَنَّ لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا﴾ [النساء: ١٣٧–١٣٨].
Ma'ana:"Lallai wadanda suka yi imani sannan kuma suka kafirta sannan kuma sukayi imani sannan kuma suka kafirta sannan kuma suka kara kafirci, [wadannan] Allah bai kasance Yana gafarta musu ba kuma bazai shiryar dasu ba zuwaga tafarki (137) Kayi albishir ga munafukai cewa lallai suna da wata azaba mai radadi (138). Q4ayata137 da 138.
Kuma ma'abuta wannan sinfin daga munafukai suna fadawa cikin ayyukan kafirci masu fitarwa daga Addini, kamar jibintar kafirai a halin fitintinu da halin tsanani, da isgilanci da addini , da zagin Allah da ManzonSa, da kange Mutane daga yin hukunci da shari'a, da nufin maida hukunci ga dagutu, da karyatawa gameda alkawarin Allah da makamantan haka daga ayyuka da maganganu da kudurce kudurce wadanda suke fidda ma'abucinsu daga Addinin Musulunci.
Kuma yakan iya kafirta da furta kalma daya. Kamar yadda Allah Yace gameda munafukai:
﴿يَحْلِفُونَ بِاللَّهِ مَا قَالُوا وَلَقَدْ قَالُوا كَلِمَةَ الْكُفْرِ وَكَفَرُوا بَعْدَ إِسْلَامِهِمْ﴾ [التوبة: ٧٤]؛
Ma'ana:"Suna rantsuwa da Allah cewa basu fadaba, alhali sun riga sun furta kalma ta kafirci kuma sun kafirta bayan Musuluncinsu. Q9ayata74.
Wadannan sun kafirta da kalma daya da suka fada bayan sun kasance Musulmi.
Huzaifa dan Yaman (Allah Ya kara musu yarda) yace:" Mutum yakan yi furuci da kalma daya a zamanin Manzon Allah (S.A.W) saiya kasance munafuki, lallai ni nakan ji irynta daga dayanku a wuri guda saw hudu.
Lallai kuyi umurni da kyakkyawa kuma lallai kuyi hani daga abinki, kuma lallai ku karfafa juna akan alheri ko Allah Ya awkar muku da azaba baki dayanku ko a shugabantadda ashararun cikinku akanku sannan zababbun cikinku su yi addu'a baza'a amsa mukuba.
Daga Abu Huraira (Allah Ya kara masa yarda) daga Annabi (S.A.W) yace:
((إنَّ العَبْدَ لَيَتَكَلَّمُ بالكَلِمَةِ مِن رِضْوَانِ اللهِ لا يُلْقِي لها بَالاً يَرْفَعُهُ اللهُ بها دَرَجاتٍ، وإنَّ العبدَ لَيَتكَلَّمُ بالكلمةِ من سَخَطِ اللهِ لا يُلْقِي لها بَالاً يَهْوِي بها في جَهَنَّمَ)). رواه البخاريُّ.
Ma'ana:"Lallai bawa yakan furta kalma ta yardan Allah bai bata muhimmanci, sai Allah Ya dawkakashi darajoji asanadinta, lallai wani bawan kuma yakan furta wata kalma da ke jawo fushin Allah, bai bata muhimmanci, zai fada cikin Jahannama a sanadinta" Imamul Bukharine ya ruwaitoshi.
Daga Alqama dan Wakkas Allaithi (Allah Ya kara masa yarda) yace; lallai Manzon Allah (S.A.W) yace:
((إنَّ الرَّجُلَ لَيتكَلَّمُ بالكلمةِ من رِضْوانِ اللهِ ما كانَ يَظُنُّ أن تَبْلُغَ ما بَلَغَتْ، يَكْتُبُ اللهُ له بها رِضْوَانَهُ إلى يومِ يَلْقَاهُ، وإنَّ الرَّجُلَ لَيَتَكَلَّمُ بالكلمةِ مِن سَخَطِ اللهِ ما كانَ يَظُنُّ أنْ تَبْلُغَ ما بَلَغَتْ، يَكْتُبُ اللهُ له بها سَخَطَهُ إلى يومِ يَلْقَاهُ)). رواه مالكٌ في المُوَطَّإِ، وأحمدُ في مُسْندِه، وزادَ: (فكانَ عَلْقَمَةُ يَقولُ: كَمْ مِن كَلامٍ مَنَعَنِيهِ حَدِيثُ بِلالِ بنِ الحَارِثِ).
Ma'ana:"Lallai mutum yakan furta kalma ta yardan Allah baya zaton takai matsayinda takai, sai Allah Ya rubuta masa yardansa asanadinta har tashin alkiyama, kuma lallai mutum yakan furta kalma ta fushin Allah baya zaton ta kai matsayinda takai, sai Allah Ya rubuta masa fushinSa asanadinta har zuwa tashi Alkiyama" Imamu Malik ne ya ruwaitoshi acikin Muwadda, da Imamu Ahmad acikin Musnad ya kara da cewa: Alqama ya kasance yana cewa:" Maganganu nawane hadisin Bilal dan Harithu ya hanani fada?
Imamul Baihaqi ya ruwaito daga Muhammad dan Amr dan Alqama dan Wakkas lallai yace:"Akwai wani mutum zawna gari banza yakan shiga ga sarakuna yana basu dariya, sai kakana yace masa"kaicon ka, meyasa kake shiga wurin wadannan kake basu dariya? Domin ni naji Bilal dan Harith Almuzani sahabin Manzon Allah (S.A.W) yana cewa:"… sai ya ambaci wacan hadisin.
Saboda haka hadarin harshe abune mai girma, kuma sha'anin Magana babbane, duk wanda yayi la'akari da maganarsa a matsayin aikinsa, zaiyi taka tsantsan cikin furucinsa, kuma alamun takawa zasu bayyana agareshi, domin lallai bawa idan yayi sakaci cikin maganarsa tareda rawnin addininsa, bazai amintaba daga furuci da wata kalma da zata wajabta masa fushin Allah da kiyayyarSa. Ko kuma yayi furuci da wata kalmarda zai kafirta asanadinta kuma ya fice a sanadinta daga Addinin Musulunci. Allah Yayi mana tsari.
Kuma wannan al'amarin faruwarsa na yawaita a lokacin fitintinu musamman ma a karshen zamani. Kamar yadda yazo acikin Sahihai biyu na Bukahri da Muslim daga hadisin Abu Huraira (Allah Ya kara masa yarda) yace Manzon Allah (S.A.W) yace:
((بَادِرُوا بالأعمالِ فِتَنًا كقِطَعِ الليلِ المُظْلمِ، يُصبِحُ الرَّجُلُ مُؤمِنًا ويُمْسِي كَافِرًا، ويُمْسِي مُؤْمِنًا ويُصْبِحُ كافِرًا، يَبِيعُ دِينَهُ بعَرَضٍ من الدُّنْيَا)).
Ma'ana:"Ku gabatar da ayyukan (kwarai) kafin wasu fitintinu su kasance. masu kama da yankin dare mai duhu, Mutum zai wayi gari yana mumini amma a yammaita yana kafiri, wani kuma zai yammaita yana mumini amma sai ya wayi gari yana kafiri, ya saida addininsa da wani dan abin rayuwar duniya".
Muna rokon Allah aminci ad afuwa da kuma Ya karemu daga abubuwanda ke sabbaba fushinSa da ukubarSa.
Shiyasa tsoron sahabbai da tabi'ai ya tsananta gameda fadawa cikin wani abu daga ayyukan munafukai.
Imamul Bukhari yace acikin sahihinsa: Ibnu Abi Mulaika yace: na riski talatin daga sahabban Annabi (S.A.W) kowannensu yana jiye wa kansa tsoron munafurci, babu daya daga cikinsu dayake cewa shi yana kan imani daidai dana Jibrilu da Mika'ilu.
Kuma ana ruwaitowa daga Alhasan [yana cewa]: babu mai tsoronsa (wato fadawa cikin munafurci) face mumini, kuma babu mai [jin cewa ya] aminta daga gareshi face munafuki.
Zaidu dan Wahab yace: wani mutum ya mutu daga cikin munafukai, Huzaifa baiyi masa salla ba, sai Umar yace masa; daga mutanen yakene?
Sai [Huzaifa] yace; ee!
Sai Umar yace masa, don Allah ina cikinsu?
[Huzaifa] Yace; a'a, kuma bazan kara bawa wani labariba bayan ka. Ibnu Abi- Shaibane ya ruwaitoshi.
Kuma huzaifa dan Yaman, Annabi (S.A.W) ya riga ya radanta masa sunayen munafukai, kuma yana daga cikin mafiya ilimi acikin al'ummannan game da halayen munafukai da hukunce hukuncensu da ayyukan munafurci, sahabbai sun kasance suna bashi matsayinsa awannan janibin, shiyasa Umar yake dakonsa idan aka gabatarda matacce, idan yaga Huzaifa baiyi masa salla ba, shima baya masa salla, saiya sanya wani ya na'ibanceshi akan yi masa salla, saboda kada ya fitar da sirrin Mazon Allah (S.A.W).