تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس الثامن: التحذيرُ من الشِّركِ وبَيانُ أنواعِه


طاهر جبريل دكو
_4 _April _2013هـ الموافق 4-04-2013م, 12:19 AM
الدرس الثامن: التحذيرُ من الشِّركِ وبَيانُ أنواعِه

قال اللهُ تعالى: ﴿وَاعْبُدُوا اللَّهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا﴾ [النساء: ٣٦].
وقال تعالى: ﴿إِنَّ الشِّرْكَ لَظُلْمٌ عَظِيمٌ﴾ [لقمان: ١٣].
وقال تعالى: ﴿إِنَّهُ مَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ حَرَّمَ اللَّهُ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ وَمَأْوَاهُ النَّارُ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنْصَارٍ﴾ [المائدة: ٧٢].
وقال تعالى: ﴿إِنَّ اللَّهَ لَا يَغْفِرُ أَنْ يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَلِكَ لِمَنْ يَشَاءُ وَمَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا بَعِيدًا﴾ [النساء: ١١٦].
وعن عبدِ اللهِ بنِ مَسعودٍ رضِي الله عنه قال: سألتُ رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم: أيُّ الذَّنْبِ أعْظَمُ؟
قال: ((أنْ تَجْعَلَ للهِ نِدًّا وهو خَلَقَكَ)). متفق عليه.
وعن جابرِ بنِ عبدِ اللهِ رضِي الله عنه قال:قال رسولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم: ((مَن لَقِيَ اللهَ لا يُشْرِكُ به شَيْئًا دخَلَ الجَنَّةَ، ومَن لَقِيَهُ يُشْرِكُ به دخَلَ النَّارَ)). رواه مسلمٌ.
والشِّرْكُ هو: عبادةُ غيرِ اللهِ تعالى، فمَن دعا معَ اللهِ أحَدًا – دُعاءَ مسألةٍ أو دُعاءَ عبادةٍ– فهو مُشركٌ كافرٌ؛ قد جَعَلَ للهِ شَرِيكًا ونِدًّا في عبادتِه؛ واللهُ تعالى لا يَرْضَى أن يُشْرَكَ معَه أحَدٌ في عبادتِه، لا نَبِيٌّ مُرسَلٌ، ولا مَلَكٌ مُقرَّبٌ، ولا غيرُهما؛ فالعبادةُ حَقٌّ للهِ وحدَه، قال اللهُ تعالى:﴿إِنِ الْحُكْمُ إِلَّا لِلَّهِ أَمَرَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ﴾ [يوسف: ٤٠].
وقال تعالى: ﴿قُلْ أَرَأَيْتُمْ شُرَكَاءَكُمُ الَّذِينَ تَدْعُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ أَرُونِي مَاذَا خَلَقُوا مِنَ الْأَرْضِ﴾ [فاطر: ٤٠].
وقال تعالى: ﴿وَمَنْ يَدْعُ مَعَ اللَّهِ إِلَهًا آَخَرَ لَا بُرْهَانَ لَهُ بِهِ فَإِنَّمَا حِسَابُهُ عِنْدَ رَبِّهِ إِنَّهُ لَا يُفْلِحُ الْكَافِرُونَ﴾ [المؤمنون: ١١٧].
فمَن دعا من دُونِ اللهِ نِدًّا فهو مُشرِكٌ.
والشِّرْكُ هو أعْظَمُ ذَنبٍ عُصِيَ اللهُ به، وهو أعْظَمُ ما نَهَى اللهُ عنه، وهو أكبرُ الكبائرِ، وأعظمُ الظُّلمِ، وهو نَقْضٌ لعهدِ اللهِ وميثاقِه، وخيانةٌ لأعظمِ الأماناتِ وأكبرِ الحُقوقِ، وهو حقُّ اللهِ عز وجل فيما خَلَقَ الخَلْقَ لأجلِه، وهو عبادتُه وَحْدَه لا شريكَ له.
فلا جَرَمَ كان عِقابُه أعظمَ العِقابِ في الدنيا والآخرةِ:
فأما في الدنيا فمَقْتُ اللهِ وسَخَطُه كما قال تعالى: ﴿إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا يُنَادَوْنَ لَمَقْتُ اللَّهِ أَكْبَرُ مِنْ مَقْتِكُمْ أَنْفُسَكُمْ إِذْ تُدْعَوْنَ إِلَى الْإِيمَانِ فَتَكْفُرُونَ﴾[غافر: ١٠].
معَ ما يُصِيبُهم في الدنيا من عُقوباتِ ما كَسَبتْ أيدِيهم بسَبَبِ إعراضِهم عن هُدَى اللهِ من الضلالِ والشقاءِ، والخوفِ والحَزَنِ، الحَيْرَةِ والشكِّ، والاضطرابِ والمعيشةِ الضَّنْكِ، وإنْ مُتِّعوا في الدنيا مَتاعًا قليلاً إلى أجلٍ فهو عليهم عذابٌ ووَبَالٌ، قال اللهُ تعالى: ﴿لَا يَغُرَّنَّكَ تَقَلُّبُ الَّذِينَ كَفَرُوا فِي الْبِلَادِ (196) مَتَاعٌ قَلِيلٌ ثُمَّ مَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ وَبِئْسَ الْمِهَادُ﴾ [آل عمران: ١٩٦–١٩٧].
وقال تعالى: ﴿وَمَنْ كَفَرَ فَلَا يَحْزُنْكَ كُفْرُهُ إِلَيْنَا مَرْجِعُهُمْ فَنُنَبِّئُهُمْ بِمَا عَمِلُوا إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ (23) نُمَتِّعُهُمْ قَلِيلًا ثُمَّ نَضْطَرُّهُمْ إِلَى عَذَابٍ غَلِيظٍ﴾ [لقمان: ٢٣–٢٤].
وقال تعالى: ﴿وَمَنْ كَفَرَ فَأُمَتِّعُهُ قَلِيلًا ثُمَّ أَضْطَرُّهُ إِلَى عَذَابِ النَّارِ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ (126)﴾ [البقرة: ١٢٦].
وأما في الآخرةِ فإنهم من حِينِ قَبْضِ أرواحِهم وهم في عَذابٍ شَديدٍ مُتتابِعٍ بسببِ لَعْنةِ اللهِ لهم؛ إذ تُنْزَعُ أرواحُهم نَزْعًا شديدًا يُعذَّبون به، ويُعذَّبون بالفَزَعِ من هَوْلِ المَطْلَعِ، ورُؤْيَةِ ملائكةِ العذابِ، ويُعذَّبُونَ في قُبورِهم عذابًا شديدًا، ويُعذَّبونَ إذا بُعِثوا بأهوالِ يومِ القيامةِ وبالفَزَعِ الأكبرِ، ويُعذَّبون بطُولِ المَوقِفِ ودُنُوِّ الشمسِ منهم في يومٍ كانَ مِقْدارُه خمسين ألفَ سنةٍ، ويُعذَّبُون في العَرَصاتِ ثم يَكُونُ مَصِيرُهم إلى نارِ جَهَنَّم خَالِدِينَ فيها أبَدًا، لا يُخَفَّفُ عنهم من عَذَابِها، وما هم منها بمُخْرَجِين.
قال اللهُ تعالى: ﴿إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا وَمَاتُوا وَهُمْ كُفَّارٌ أُولَئِكَ عَلَيْهِمْ لَعْنَةُ اللَّهِ وَالْمَلَائِكَةِ وَالنَّاسِ أَجْمَعِينَ (161) خَالِدِينَ فِيهَا لَا يُخَفَّفُ عَنْهُمُ الْعَذَابُ وَلَا هُمْ يُنْظَرُونَ (162)﴾ [البقرة: ١٦١–١٦٢].
وقال تعالى: ﴿وَالَّذِينَ كَفَرُوا لَهُمْ نَارُ جَهَنَّمَ لَا يُقْضَى عَلَيْهِمْ فَيَمُوتُوا وَلَا يُخَفَّفُ عَنْهُمْ مِنْ عَذَابِهَا كَذَلِكَ نَجْزِي كُلَّ كَفُورٍ (36) وَهُمْ يَصْطَرِخُونَ فِيهَا رَبَّنَا أَخْرِجْنَا نَعْمَلْ صَالِحًا غَيْرَ الَّذِي كُنَّا نَعْمَلُ أَوَلَمْ نُعَمِّرْكُمْ مَا يَتَذَكَّرُ فِيهِ مَنْ تَذَكَّرَ وَجَاءَكُمُ النَّذِيرُ فَذُوقُوا فَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ نَصِيرٍ (37)﴾ [فاطر: ٣٦–٣٧].
وقال تعالى: ﴿إِنَّ اللَّهَ لَعَنَ الْكَافِرِينَ وَأَعَدَّ لَهُمْ سَعِيرًا (64) خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا لَا يَجِدُونَ وَلِيًّا وَلَا نَصِيرًا (65) يَوْمَ تُقَلَّبُ وُجُوهُهُمْ فِي النَّارِ يَقُولُونَ يَا لَيْتَنَا أَطَعْنَا اللَّهَ وَأَطَعْنَا الرَّسُولَا (66) وَقَالُوا رَبَّنَا إِنَّا أَطَعْنَا سَادَتَنَا وَكُبَرَاءَنَا فَأَضَلُّونَا السَّبِيلَا (67) رَبَّنَا آَتِهِمْ ضِعْفَيْنِ مِنَ الْعَذَابِ وَالْعَنْهُمْ لَعْنًا كَبِيرًا (68)﴾ [الأحزاب: ٦٤–٦٨].
ومِمَّا يدُلُّ على عَظيمِ خَطَرِ الشِّرْكِ ووُجوبِ الحَذَرِ منه، أنَّ مَن أشْرَكَ باللهِ من بعدِ إسلامِه حَبِطَ عَمَلُه وكانَ من الكافرين الخاسرين، كأنه لم يَعْمَلْ من قبلُ شيئًا، فاللهُ لا يَقْبَلُ من مُشركٍ عملاً.
قال اللهُ تعالى: ﴿وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الْآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ﴾ [آل عمران: ٨٥].
وقال تعالى: ﴿وَلَقَدْ أُوحِيَ إِلَيْكَ وَإِلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكَ لَئِنْ أَشْرَكْتَ لَيَحْبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ الْخَاسِرِينَ (65) بَلِ اللَّهَ فَاعْبُدْ وَكُنْ مِنَ الشَّاكِرِينَ (66)﴾ [الزمر: ٦٥–٦٦].
وقال تعالى بعدَ ما ذكَرَ الأنبياءَ في سُورةِ الأنعامِ وأثْنَى عليهم: ﴿وَمِنْ آَبَائِهِمْ وَذُرِّيَّاتِهِمْ وَإِخْوَانِهِمْ وَاجْتَبَيْنَاهُمْ وَهَدَيْنَاهُمْ إِلَى صِرَاطٍ مُسْتَقِيمٍ (87) ذَلِكَ هُدَى اللَّهِ يَهْدِي بِهِ مَنْ يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ وَلَوْ أَشْرَكُوا لَحَبِطَ عَنْهُمْ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ (88)﴾ [الأنعام: ٨٧–٨٨].
فالأنبياءُ – على صَلاحِهم وشَرَفِهم وقُرْبِهم من اللهِ تعالى وعظيمِ مَحَبَّتِه لهم – لا يُغْفَرُ لهم الشركُ باللهِ جل وعلا لو وقَعَ منهم، وقد عَلِمْنا أنَّ اللهَ تعالى قد عَصَمَهم من الشركِ، فغيرُ الأنبياءِ أَوْلَى بهذا الحُكْم، وقد أبْقَى اللهُ لنا هذا الخِطابَ يُتْلَى علينا لِنَتَدَبَّرَهُ ونَتأمَّلَهُ، ونَفْهَم منه عَظِيمَ جُرْمِ الشِّركِ.

والشِّرْكُ على قِسْمَينِ:
أحَدُهما: الشِّرْكُ الأَكْبَرُ: ويَكونُ في الرُّبوبِيَّةِ والأُلوهيَّةِ:
أما الشِّرْكُ الأكْبَرُ في الرُّبوبيَّةِ فهو: اعْتقادُ شَرِيكٍ للهِ تعالى في أفعالِه من الخَلْقِ والرَّزقِ والمُلْكِ والتَّدْبيرِ.
وأمَّا الشِّرْكُ الأَكْبَرُ في الألوهيَّةِ فهو: دُعاءُ غيرِ اللهِ تعالى دُعاءَ مسألةٍ أو دُعاءَ عِبادَةٍ
ويكونُ الشركُ الأكبرُ بالقلبِ والقولِ والعملِ.

فمِثالُ الشركِ الأكبرِ القَلْبِيِّ: اعتقادُ أنَّ للأوثانِ تَصَرُّفًا في الكَوْنِ، وأنها تَعْلَمُ الغَيْبَ، وتَنْفَعُ وتَضُرُّ، ومَحَبَّةُ الأوثانِ والتَّوكُّلُ عليها والاستعانةُ بها كلُّ ذلك من العباداتِ القَلْبيَّةِ التي لا يَجوزُ صَرْفُها لغيرِ اللهِ عز وجل، فمَن صَرَفَها لغيرِ اللهِ تعالى فهو مُشركٌ كَافِرٌ

ومثالُ الشِّرْكِ بالقَوْلِ: دُعاءُ الأوثانِ من دُونِ اللهِ، والأقوالُ الكُفْريَّةُ التي يَكونُ فيها تَعْظيمٌ للأوثانِ ومَدْحٌ لها، وافتراءُ الكَذِبِ على اللهِ.

ومِثالُ الشركِ بعَمَلِ الجَوَارحِ: الذَّبْحُ لغَيْرِ اللهِ، والنَّذْرُ له، والسُّجودُ له.
والشِّرْكُ الأكبرُ مُخْرِجٌ عن مِلَّةِ الإسلامِ، ومَن ماتَ ولم يَتُبْ منه لم يَغْفِرِ اللهُ له، بل هو مُوجِبٌ لسَخَطِ اللهِ ومَقْتِه والخُلودِ في نارِ جَهنَّم، والعياذُ باللهِ.

والقِسْمُ الآخَرُ: الشِّرْكُ الأَصْغَرُ، وهو ما كانَ وَسِيلةً للشِّرْكِ الأَكْبَرِ وسُمِّيَ في النُّصوصِ شِرْكًا من غيرِ أن يَتَضَمَّنَ صَرْفًا للعِبَادَةِ لغَيْرِ اللهِ عز وجل.
ويَكُونُ بالقَلْبِ والقَوْلِ والعَمَلِ:

فمِثالُ الشِّرْكِ الأَصْغَرِ القَلْبِيِّ: اعتقادُ السَّبَبِيَّةِ فيما لم يَجْعَلْهُ اللهُ سَبَبًا شَرْعًا ولا قَدَرًا، كاعتقادِ نَفْعِ التمائمِ المُعَلَّقَةِ في دَفْعِ البلاءِ، والطِّيَرةِ.

ومثالُ الشِّرْكِ الأصغرِ العَمَلِيِّ: الرِّياءُ بتَحْسِينِ أداءِ الصلاةِ لطَلَبِ مَدْحِ الناسِ وإعجابِهم على عِبادتِه للهِ جل وعلا.
فهو صلى للهِ، لكنه أرادَ أن يَمْدَحَهُ الناسُ على حُسْنِ صلاتِه، وربما زَادَ في تحسينِها ليَزْدَادَ الناسُ في مَدْحِه.
وهو شِرْكٌ أصْغَرُ؛ لأنه لم يُخْلِصِ القَصْدَ للهِ جل وعلا، وليسَ بشِرْكٍ أكْبَرَ؛ لأنه لم يَعْبُدْ غَيْرَ اللهِ.
ومثالُ الشِّرْكِ الأَصْغَرِ القَوْلِيِّ: قولُ ما شاءَ اللهُ وشِئْتَ، والحَلِفُ بغَيرِ اللهِ، وقولُ: (مُطِرْنَا بنَوْءِ كذا وكذا).
والشِّرْكُ الأَصْغَرُ لا يُخْرِجُ من المِلَّةِ ولا يُوجِبُ الخُلودَ في النارِ، ولكنَّه ذَنْبٌ عظيمٌ يَجِبُ على مَن وَقَعَ فيه أن يَتُوبَ منه، فإنْ لم يَتُبْ فقد عَرَّض نَفْسَه لسَخَطِ اللهِ وأليمِ عِقابِه.

فصل: والشِّرْكُ منه جَلِيٌّ وخَفِيٌّ
فالشِّرْكُ الجَلِيُّ هو الشركُ البيِّنُ الظاهِرُ كدُعاءِ غَيْرِ اللهِ تعالى، والذَّبح للأوثانِ، وسَائِرِ أفعالِ الشِّرْكِ وأقوالِه الظَّاهرةِ.
والشِّرْكُ الخَفِيُّ منه أكبر وأصغر ؛ فالشرك الخفي الأكبر هو أعمال الشرك الأكبر الخفية ؛ كتعلق القلب بغير الله تعلقاً أكبر، منه ما يكونُ بتَقْديمِ طَاعةِ غيرِ اللهِ على طاعةِ اللهِ من غيرِ قَصْدِ عِبادةِ غيرِ اللهِ أو تَعَلُّقِ القَلْبِ بغَيْرِه.
وعن مَعْقِلِ بن يَسَارٍ رضِي الله عنه قال: انْطَلَقْتُ مع أبي بكرٍ الصِّدِّيقِ رضِي الله عنه إلى النبيِّ صلى الله عليه وسلم فقال: ((يا أبا بكرٍ، لَلشِّرْكُ فيكم أخْفَى من دَبِيبِ النَّمْلِ)).
فقال أبو بَكْرٍ: وهل الشِّركُ إلا مَن جعَلَ معَ اللهِ إلهًا آخَرَ؟
قال النبيُّ صلى الله عليه وسلم: ((والذي نفسي بيدِه، للشِّرْكُ أخْفَى من دَبيبِ النَّمْلِ، ألا أَدُلُّكَ على شيءٍ إذا قُلْتَه ذهَبَ عنكَ قَلِيلُه وكَثِيرُه))
قال: ((قُلِ اللهُمَّ إني أَعوذُ بكَ أن أُشْرِكَ بكَ وأنا أعْلَمُ، وأسْتَغْفِرُكَ لِمَا لا أعْلَمُ)). رواه البخاريُّ في الأدبِ المُفْرَدِ.

فالشِّرْكُ الخَفِيُّ لا يكادُ يَسْلَمُ منه أحَدٌ إلا مَن عَصَمَهُ اللهُ؛ لأن منه تَقْدِيمَ هَوَى النفسِ على طاعةِ اللهِ، وطاعة بَعْضِ المَخْلوقينَ في مَعْصِيَةِ الخَالِقِ، ويكونُ ذلك في الكبائرِ والصغائرِ.
وهذا الدعاءُ النَّبويُّ سَبَبٌ عظيمٌ في البراءةِ منه، وذَهَابِ أثرِه، ومَغْفِرَةِ اللهِ لصاحبِه.

وتحقيقُ التوحيدِ يكونُ بإسلامِ القلبِ والوَجْهِ للهِ تعالى فتكونُ طاعتُه للهِ، ومَحبَّتُه للهِ، وبُغْضُه للهِ، وعَطاؤُه للهِ، ومَنْعُه للهِ، وبذلك يكونُ المَرْءُ مُؤمِنًا مُسْتكمِلَ الإيمانِ، نسألُ اللهَ من فضلِه.

طاهر جبريل دكو
_4 _April _2013هـ الموافق 4-04-2013م, 12:21 AM
Darasi na takwas: Gargadi gameda shirka da bayanin naw'ukanta.
Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَاعْبُدُوا اللَّهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا﴾ [النساء: ٣٦].
Ma'ana:" Kuma ku bawtawa Allah kada kuyi maSa tarayya da komai" Q4ayata36.
Kuma Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿إِنَّ الشِّرْكَ لَظُلْمٌ عَظِيمٌ﴾ [لقمان: ١٣].
Ma'ana:"Lallai shirka zaluncine mai girma" Q31ayata13.
Kuma Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿إِنَّهُ مَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ حَرَّمَ اللَّهُ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ وَمَأْوَاهُ النَّارُ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنْصَارٍ﴾ [المائدة: ٧٢].
Ma'ana:"Lallai yadda al'amarin yake shine, duk wanda ya sanya wa Allah abokoin tarayya, to Allah Ya haramta masa Aljanna kuma makomarsa itace Wuta, kuma babu wani mataimaki ga azzalumai" Q5ayata72.
Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿إِنَّ اللَّهَ لَا يَغْفِرُ أَنْ يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَلِكَ لِمَنْ يَشَاءُ وَمَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا بَعِيدًا﴾ [النساء: ١١٦].
Ma'ana:"Lallai Allah baYa gafarta ayi maSa shirka, kuma Yana gafarta abinda bai kai hakaba ga wanda Yaso. Kuma duk wanda yayi shirka ga Allah, to hakika ya bata bata mai nisa" Q4ayata116.
Daga abdullahi dan Mas'udu (Allah Ya kara masa yarda) yacea: na tambayi Manzon Allah (S.A.W) wane zunubine mafi girma? Sai yace:
((أنْ تَجْعَلَ للهِ نِدًّا وهو خَلَقَكَ)). متفق عليه.
Ma'ana:" Ka sanyawa Allah kishiya alhali Shi Ya halicceka" Bukhari da Muslim.
Daga Jabir dan Abdullahi (Allah Ya kara masa yarda) yace: Manzon Allah (S.A.W) yace:
((مَن لَقِيَ اللهَ لا يُشْرِكُ به شَيْئًا دخَلَ الجَنَّةَ، ومَن لَقِيَهُ يُشْرِكُ به دخَلَ النَّارَ)). رواه مسلمٌ.
Ma'ana:"Duk wanda ya sadu da Allah alhali baya masa tarayya da komai zaishiga Aljanna. Wanda kuwa ya sadu da Allah alhali yana masa tarayya to zai shiga Wuta" Imamu Muslim ne ya ruwaitoshi.
Kuma shirka itace bawtan wanin Allah (Madawkakin Sarki). Saboda haka duk wanda ya kirayi wani tareda Allah –addu'ar bukata ko addu'ar ibada- to shi mushirikine kafiri ya sanyawa Allah abokin tarayya kuma kishiya acikin bawtarSa. Kuma Allah (Madawkakin Sarki) baYa yarda ayi masa tarayya da wani koda Annabine kuma Manzo ko kuma Mala'ika makusanci ga Allah ko waninsu. Saboda haka bawata hakkin Allahne Shi kadai. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:"
﴿إِنِ الْحُكْمُ إِلَّا لِلَّهِ أَمَرَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ﴾ [يوسف: ٤٠].
Ma'ana:"Babu hukunci face na Allah, Yayi umurni kada a bawtawa kowa face Shi" Q12ayata40. Kuma (Allah Madawkakin Sarki) Yace:
﴿قُلْ أَرَأَيْتُمْ شُرَكَاءَكُمُ الَّذِينَ تَدْعُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ أَرُونِي مَاذَا خَلَقُوا مِنَ الْأَرْضِ﴾ [فاطر: ٤٠].
Ma'ana:"Kace, kunga abubuwan shirkanku wadanda kuke kira koma bayan Allah, kununa mini menene suka halitta daga cikin kasa…" Q35ayata40. Kuma Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَمَنْ يَدْعُ مَعَ اللَّهِ إِلَهًا آَخَرَ لَا بُرْهَانَ لَهُ بِهِ فَإِنَّمَا حِسَابُهُ عِنْدَ رَبِّهِ إِنَّهُ لَا يُفْلِحُ الْكَافِرُونَ﴾ [المؤمنون: ١١٧].
Ma'ana:"Kuma duk wanda ya kirayi wani abin bawta na dabam tareda Allah, bashida wata hujja gamedashi. Kuma kawai hisabinsa naga Ubangijinsane. Yadda al'amarin yake shine, kafirai bazasu rabwtaba." Q21ayata117.
Saboda haka duk wanda yakirayi abin bawta koma bayan Allah, to shi mushirikine.
Kuma shirka itace mafi girman zunubbin da aka sabi Allah dashi, kuma itace mafi girman abinda Allah Yahana, kuma itace mafi girman zunubbai baki daya, kuma mafi girman dukkan zalunci, kuma warwarewane game da alkawarin Allah, kuma ha'incine gameda mafi girma cikin amanoni kuma mafi girma cikin hakkoki wanda shine hakkin Allah (Mai girma da dawkaka) cikin abinda Ya halicci halittu dominsa, shine bawtanSa Shi kadai batareda abokin tarayyaba.
Ba abanzaba, shiyasa ukubarta (wato shirka) ta kasance mafi girman ukubobi dukka a duniya da lahira.
Amma (ukubar) aduniya: (itace) kiyayyar Allah (Mai girma da dawkaka) da fushinSa, kamar yadda Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا يُنَادَوْنَ لَمَقْتُ اللَّهِ أَكْبَرُ مِنْ مَقْتِكُمْ أَنْفُسَكُمْ إِذْ تُدْعَوْنَ إِلَى الْإِيمَانِ فَتَكْفُرُونَ﴾[غافر: ١٠].
Ma'ana:"Lallai wadanda suka kafirta ana kiransu,(ana cewa dasu) hakika kiyayyar Allah (agareku) tafi girma bisaga kiyayyarku ga kawu kanku yayinda ake kiranku zuwaga imani amma kuna kafircewa" Q40ayata10.
Tareda abinda zai samesu aduniya na ukubobin da hannayensu suka jawo musu kamar bata da tabewa da tsoro da bakinciki da rudani da shakku da rikicewar al'amura da kuntatacciyar rayuwa asakamakon kawarda kai da sukayi daga shiriyar Allah, koda kuwa anjiyar dasu wata yar dadi anan duniya zuwa wani dan lokaci, to (wannan) azabace kawai agaresu da nawyi. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿لَا يَغُرَّنَّكَ تَقَلُّبُ الَّذِينَ كَفَرُوا فِي الْبِلَادِ (196) مَتَاعٌ قَلِيلٌ ثُمَّ مَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ وَبِئْسَ الْمِهَادُ﴾ [آل عمران: ١٩٦–١٩٧].
Ma'ana:"Kada jujjuyawar wadanda suka kafirta acikin garuruwa ya rudeka (196) Jin dadine kadan, sannan makomarsu itce Jahannama, tir da ita amatsayin shinfida (197). Q3ayata196 da 197. (Allah Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَمَنْ كَفَرَ فَلَا يَحْزُنْكَ كُفْرُهُ إِلَيْنَا مَرْجِعُهُمْ فَنُنَبِّئُهُمْ بِمَا عَمِلُوا إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ (23) نُمَتِّعُهُمْ قَلِيلًا ثُمَّ نَضْطَرُّهُمْ إِلَى عَذَابٍ غَلِيظٍ﴾ [لقمان: ٢٣–٢٤].
Ma'ana:" Kuma duka wanda ya kafirta kada kafircinsa ya bakanta maka rai. gareMu makomarsu take, saboda haka zaMu basu labari gameda abinda suka aikata. Lallai Allah Masanine gameda abinda ke cikin zukata (23) Muna jayaddasu dadi kadan, sannan Mu tilastasu ga shiga wata azaba kakkawra (24).
Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَمَنْ كَفَرَ فَأُمَتِّعُهُ قَلِيلًا ثُمَّ أَضْطَرُّهُ إِلَى عَذَابِ النَّارِ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ (126)﴾ [البقرة: ١٢٦].
Ma'ana:" Kuma wanda ya kafirta sai Injiyar dashi dadi kadan sannan in tilastashi ga shiga azabar Wuta. Kuma tir da (Wuta ta zama) makoma" Q2ayata126.
Amma alahira, lallai su tun daga sa'ilinda aka dawki rayukansu, suna cikin azaba mai tsanani wacce ke bibiyan juna sakamakon tsinuwar Allah akansu, saboda za'a fincike rayukansu fincika mai tsanani ana azabtar dasu da ita. Kuma za'a azabtar dasu da firgicinnan mafi girma da tashin hankali na azaban farko (afilin hisabi). (kuma za'a azabtar dasu) da ganin Mala'kun azaba, kuma za'a azabtar dasu acikin kaburburansu azaba mai tsanani, kuma za'a azabtar dasu a yayin da za'a tashesu (daga kabari) da tashin hankalin da ke filin kiyama, kuma za'a azabtar dasu da doguwar tsayuwa da kusantowar Rana garesu a yinin da gwargwadosa misalin shekaru dubu hamsinne, kuma za'a azabtar dasu a filin kiyama sannan akarshe makomarsu ta kasance zuwa Wutar Jahannama suna masu dawwama acikinta har abada, baza'a rangwanta musuba daga azabarta kuma su ba wadanda za'a fitar bane daga cikinta.
Kuma Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا وَمَاتُوا وَهُمْ كُفَّارٌ أُولَئِكَ عَلَيْهِمْ لَعْنَةُ اللَّهِ وَالْمَلَائِكَةِ وَالنَّاسِ أَجْمَعِينَ (161) خَالِدِينَ فِيهَا لَا يُخَفَّفُ عَنْهُمُ الْعَذَابُ وَلَا هُمْ يُنْظَرُونَ (162)﴾ [البقرة: ١٦١–١٦٢].
Ma'ana:"Lallai wadanda suka kafirta kuma suka mutu alhali suna kafirai, wadannan tsinuwar Allah tabbata akansu da ta Mala'iku da ta Mutane baki daya (161) Suna masu dawwama acikinta, baza'a sassawta musu azababa kuma baza'a sawrara musu ba (162) Q2ayata 161 da 162.
Kuma Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَالَّذِينَ كَفَرُوا لَهُمْ نَارُ جَهَنَّمَ لَا يُقْضَى عَلَيْهِمْ فَيَمُوتُوا وَلَا يُخَفَّفُ عَنْهُمْ مِنْ عَذَابِهَا كَذَلِكَ نَجْزِي كُلَّ كَفُورٍ (36) وَهُمْ يَصْطَرِخُونَ فِيهَا رَبَّنَا أَخْرِجْنَا نَعْمَلْ صَالِحًا غَيْرَ الَّذِي كُنَّا نَعْمَلُ أَوَلَمْ نُعَمِّرْكُمْ مَا يَتَذَكَّرُ فِيهِ مَنْ تَذَكَّرَ وَجَاءَكُمُ النَّذِيرُ فَذُوقُوا فَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ نَصِيرٍ (37)﴾ [فاطر: ٣٦–٣٧].
Ma'ana:"Kuma wadanda suka kafirta sunada Wutar Jahannama, baza'ayi hukunci akansu ba ballantana su mutu, kuma ba'a sawkaka musu daga azabarta. Kamar hakane Muke sakantawa kowane maiyawan kafirci (36) Kuma su, suna hargowar neman agaji acikinta. (suna cewa) "Ya Ubangijinmu kafitar damu, zamu aikata aiki sabanin wanda muka kasance muna aikatawa. Ashe, baMu rayar daku ba gwargwadon da mai tunani zaiyi tunani acikinsa kuma mai gargadi yazo muku? Saboda haka ku dandani (azaba) babu wani mataimaki ga azzalumi (37) Q35ayata36 da37.
Kuma Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿إِنَّ اللَّهَ لَعَنَ الْكَافِرِينَ وَأَعَدَّ لَهُمْ سَعِيرًا (64) خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا لَا يَجِدُونَ وَلِيًّا وَلَا نَصِيرًا (65) يَوْمَ تُقَلَّبُ وُجُوهُهُمْ فِي النَّارِ يَقُولُونَ يَا لَيْتَنَا أَطَعْنَا اللَّهَ وَأَطَعْنَا الرَّسُولَا (66) وَقَالُوا رَبَّنَا إِنَّا أَطَعْنَا سَادَتَنَا وَكُبَرَاءَنَا فَأَضَلُّونَا السَّبِيلَا (67) رَبَّنَا آَتِهِمْ ضِعْفَيْنِ مِنَ الْعَذَابِ وَالْعَنْهُمْ لَعْنًا كَبِيرًا (68)﴾ [الأحزاب: ٦٤–٦٨].
Ma'ana:"Lallai Allah Ya tsine wa kafirai kuma Ya tanadar musu da Wuta (64) suna masu dawwama acikinta har abada, basu samun wani majibinci ko mataimaki (65) A ranar da ake juya fusakunsu acikin Wuta suna cewa "Ya kaiconmu, inama da munyi da'a ga Allah kuma munyi da'a ga Manzon (Allah) (66) Kuma sukace "Lallai mu munyi da'a ga shuwagabanninmu da manyanmu sai suka fatar damu daga tafarki (67) Ya Ubangijimmu Ka basu ninki biyu na azaba kuma ka la'ancesu la'ana maigirma (68). Q33ayata64-68.
Kuma daga cikin abinda ke nuni zuwaga girman hadarin shirka da wajibcin kiyayewa daga fadawa cikinta shine kasancewar duk wanda yayi shirka ga Allah bayan ya kasance Musulmi to aikinsa ya rushe kuma ya kasance cikin kafirai masu hasara, tamkar bai taba aikata komaiba, saboda Allah baYa karban wani aiki daga Mushriki. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الْآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ﴾ [آل عمران: ٨٥].
Ma'ana:"Kuma wanda ya nemi wanin Musulunci ya zama addini agareshi, to ba za'a karba daga gareshiba, kuma shi alahira yana cikin masu hasara Q3ayata85.
Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَلَقَدْ أُوحِيَ إِلَيْكَ وَإِلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكَ لَئِنْ أَشْرَكْتَ لَيَحْبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ الْخَاسِرِينَ (65) بَلِ اللَّهَ فَاعْبُدْ وَكُنْ مِنَ الشَّاكِرِينَ (66)﴾ [الزمر: ٦٥–٦٦].
Ma'ana:"Kuma hakika anyi wahayi zuwa gareka kuma izuwa ga wadanda suka gabaceka cewa lallai idan kayi shirka tabbas aikinka zai rushe kuma a lahira zaka zamo cikin masu hasara (65). A'a Allah zaka bawtawa kuma kazamo cikin masu godiya (66) Q39ayata65 da66.
Kuma Allah Ya fadi bayan Ya ambaci Annabwa acikin suratul An'ami kuma Ya yabesu:
﴿وَمِنْ آَبَائِهِمْ وَذُرِّيَّاتِهِمْ وَإِخْوَانِهِمْ وَاجْتَبَيْنَاهُمْ وَهَدَيْنَاهُمْ إِلَى صِرَاطٍ مُسْتَقِيمٍ (87) ذَلِكَ هُدَى اللَّهِ يَهْدِي بِهِ مَنْ يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ وَلَوْ أَشْرَكُوا لَحَبِطَ عَنْهُمْ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ (88)﴾ [الأنعام: ٨٧–٨٨].
Ma'ana:"Kuma daga cikin iyayensu da zurriyyarsu da yan'uwansu, kuma Muka zabesu kuma Muka shiryar dasu zuwa tafarki madaidaici (87) Wannan shiriyar Allah ce yana shiryar da wanda Yaso da ita, kuma da sunyi shirka tabbas da ayyukanda suka kasance sunayi ya rushe (88) Q6ayata87 da 88.
Annabawama tareda kyan halinsu da matsayinsu da kusancinsu ga Allah (Madawkakin Sarki) da irin son da Allah Yake musu mai girma, amma (yace) bazai gafarta musu shirka da Allah (Mai girma da dawkaka)ba da ace tafaru dasu. Hakika mun rigaya mun san cewa lallai Allah Yakaresu daga (awkawa cikin) shirka, sabo da haka, wadanda ba Annabawaba su sukafi cancantan wannan hukuncin. Kuma hakika Allah Ya bar mana wannan maganar ana karantata garemu domin muyi nazari kuma muyi la'akari da ita kuma mufahimci girman laifi na shirka.
Shirka ta kasu kashi biyu:
Daya daga cikinsu: itace babbar shirka, kuma tana kasancewa acikin Rububiyya da Uluhiyya.
Babbar shirka acikin Rububiyya itace: kudurce cewa Allah (Madawkakin Sarki) Yana da wani abokin tarayya acikin ayyukansa, kamar yin halitta, da azurtawa, da mallaka dajujjuya al'amura.
Amma babbar shirka acikin Uluhiyya itace, kiran wanin Allah (Madawkakin Sarki) (addu'a) ta bukata ko (addu'a) ta ibada
Kuma babbar shirka takan kasance da zuciya, da Magana da ayyuka.
Misali gameda babbar shirka ta zuci: Kudurce cewa gumaka suna da ikon gudanarwa cikin halittu, kuma cewa suna sanin ilimin gaibu, kuma suna iya amfanarwa ko cutarwa. Hakananma son gumaka da dogaro garesu, da neman taimakonsu, duk wadannan suna cikin ayyukan bawta (na) zuciya wadanda baya halatta ayisu ga wanin Allah (Mai girma da dawkaka) to duk wanda ya sarrafa su ga wanin Allah (Madwkakin Sarki) to shi mushirikine kafiri.
Misalin shirka ta Magana: kiran gumaka koma bayan Allah, da maganganu na kafirci wadanda akwai girmama gumaka da yabonsu aciki, da kirkiren karya ga Allah.
Misalin shirka a cikin ayyukan gabbai: yin yanka domin wanin Allah, dayin bakance dominsa (wanin Allah), dayin sujjada dominsa.
Ita babbar shirka tana fitarwa daga addinin Musulunci, kuma duk wanda ya mutu bai tuba daga aikatata ba, to Allah bazai gafarta masaba, a'a ita dai tana wajabta fushin Allah da kiyayyarSa da kuma dawwama acikin Wutar Jahannama. Allah Ya tsare mu.
Daya kashin (na shirka) shine: Karamar shirka, wannar itace duk abinda ke zama tsani zuwaga babbar shirka, kuma an ambaceta ne acikin nassoshi da sunan shirka tareda cewa bata kunshi yin bawta ga wanin Allah (Mai girma da dawkaka)ba.
Kuma (itama) takan kasance ta (hanyar kudurin) zuciya da (ta hanyar) magana da aiki;
Misalin karamar shirka ta zuciya: Kudurce kasancewar wani abu sababi alhali Allah bai sanyashi sababiba bias (dalili na) shari'a ko kaddara, kudurce cewa layu da ake ratayawa domin tunkude bala'i da camfi suna amfanarwa.

Misalin karamar shirka acikin aiki: Shine riya, ta hanyar kyawtata aikin salla don neman yabo daga Mutane da burgesu game da bawtarsa ga Allah (Mai girma da dawkaka).
Shidai yayi sallane ga Allah, amma kuma yana nufin Mutane su yabeshi akan kyan sallarsa, wata kila ma ya kara kyawtatata domin Mutane su kara yabonsa.
Wannar ta zama karamar shirkace saboda bai tsarkake nufinsa ga Allah (Mai girma da dawkaka) ba acikinta.
Misalin karamar shirka ta Magana: Fadin (mutum) "in Allah Yaso kuma in kaima kaso, da rantsuwa da wanin Allah, da cewa "anyi mana ruwan sama domin (tawraruwa) kaza da kaza".
Ita karamar shirka bata fitarwa daga cikin Addini, kuma bata wajabta dawwama acikin Wuta. Saidai zunubine mai girma wanda ya wajaba ga wanda ya fada cikin aikatashi ya tuba daga aikatashi. Idan bai tubaba kuwa, to hakika ya bijirar da kansa ga fushin Allah da radadin ukubarSa.
Fasali:Daga cikin shirka akwai na fili akwai na boye.
Ita shirka ta fili itace bayyananniya kamar kiran wanin Allah (Madawkakin Sarki), da yin yanka ga gumaka, da dai sawran ayyukan shirka da maganganuta na zahiri.
Kuma ita boyayyar shirka cikinta akwai babbar shirka kuma akwai karama. Babbar shirka boyayya itace: dukkanin ayyukan shirka babba wadanda ke boye, kamar ta’allakar zuciya ga wanin Allah ta’allakawa mai girma, daga cikinsa akwai wanda ke kasancewa ta (hanyar) gabatarda biyayyar wanin Allah akan biyayya ga Allah, ba tareda nufin bawatar wanin Allah ba ko allaka zuciya gareShi.
Daga Ma'akilu dan Yasar (Allah Ya kara masa yarda) yace: na tafi tareda Abubakar Assidik (Allah Ya kara masa yarda) zuwa wurin Annabi (S.A.W) sai yace:
((يا أبا بكرٍ، لَلشِّرْكُ فيكم أخْفَى من دَبِيبِ النَّمْلِ)).
Ma'ana:"Ya kai Abubakar, lallai shirka acikinku tafi buya samada takun tururuwa"
Sai Abubakar yace; Ashe shirka ba itace kawai (aikin) wanda ya sanya wani abin bawta koma bayan Allahba? Sai Annabi (S.A.W) yace:
((والذي نفسي بيدِه، للشِّرْكُ أخْفَى من دَبيبِ النَّمْلِ، ألا أَدُلُّكَ على شيءٍ إذا قُلْتَه ذهَبَ عنكَ قَلِيلُه وكَثِيرُه))
Ma'ana:" Na rantse da wanda raina ke hannunSa, wallahi shirka tafi buya samada takun tururuwa. Shin bana shiyardakai zuwaga wani abuba, wanda inka fadeshi karamarta (wato shirka) da babbarta zasu tafi daga gareka? Sai yace:
((قُلِ اللهُمَّ إني أَعوذُ بكَ أن أُشْرِكَ بكَ وأنا أعْلَمُ، وأسْتَغْفِرُكَ لِمَا لا أعْلَمُ)). رواه البخاريُّ في الأدبِ المُفْرَدِ.
Ma'ana:"Kace:"Ya Allah lallai ni ina neman tsarinKa daga yi maKa shirka alhali ina sane, kuma ina neman gafararka gameda wacce (nayi) ba tareda saniba. Imamul Bukahrine ya ruwaitoshi cikin Adabul mufrad.
Saboda haka ita shirka boyayya kusan babu mai kubuta daga gareta sai dai wanda Allah Ya kare, domin daga cikinta akwai gabatarda son zuciya akan yiwa Allah da'a, da kuma yin da'a ga wasu ababen halitta cikin sabawa mahalicci. Kuma wannan yakan kasance cikin manyan zunubbai ko kanana.
Wannan addu'ar ta Annabta babbar sababice ta kubuta daga gareta (wato shika) da kuma gushewar tasirinta, da gafarar Allah ga ma'abucinta.
Kuma hakikance tawhidi yana kasancewane ta hanyar sallama zuciya da fiska ga Allah (Madawkakin Sarki), saboda haka sai biyayyarsa (wato bawa) ta kasance ga Allah, soyayyarsa don Allah, bayarwansa don Allah, hanawarsa don Allah.
Da wannanne mutum ke samun kammaluwar imani. Muna rokon Allah falalarSa.