تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس السابع: بيانُ معنَى الكُفْرِ بالطاغوتِ


طاهر جبريل دكو
_4 _April _2013هـ الموافق 4-04-2013م, 12:12 AM
الدرس السابع: بيانُ معنَى الكُفْرِ بالطاغوتِ

قال اللهُ تعالى: ﴿لَا إِكْرَاهَ فِي الدِّينِ قَدْ تَبَيَّنَ الرُّشْدُ مِنَ الْغَيِّ فَمَنْ يَكْفُرْ بِالطَّاغُوتِ وَيُؤْمِنْ بِاللَّهِ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْوَةِ الْوُثْقَى لَا انْفِصَامَ لَهَا وَاللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ﴾ [البقرة: ٢٥٦].
وقال تعالى: ﴿وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَسُولًا أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوتَ﴾ [النحل: ٣٦].
وقال تعالى: ﴿وَالَّذِينَ اجْتَنَبُوا الطَّاغُوتَ أَنْ يَعْبُدُوهَا وَأَنَابُوا إِلَى اللَّهِ لَهُمُ الْبُشْرَى﴾ [الزمر: ١٧].
فاجتنابُ عِبادةِ الطاغوتِ وإخلاصُ العبادةِ للهِ تعالى وَحْدَه لا شَرِيكَ له هو مَعْنَى التوحيدِ.
ولا يَكونُ المَرْءُ مُسلِمًا مُوَحِّدًا حتى يَكْفُرَ بالطَّاغُوتِ.
والطاغوتُ هو كلُّ ما يُعْبَدُ من دُونِ اللهِ تعالى، سَواءٌ أكانتْ عبادتُه بدعائهِ، والاستعانِة به، والتَّوكُّلِ عليه، والذَّبْحِ له، والنَّذْرِ له، أم باتِّباعِه في تحليلِ الحرامِ وتحريمِ الحلالِ، أم بالتَّحاكُمِ إليه والرِّضا بحُكْمِه.
قال ابنُ جَريرٍ رحِمه اللهُ: (والصَّوابُ من القولِ عندِي في "الطَّاغُوتَ" أنه كُلُّ ذِي طُغْيانٍ على اللهِ، فعُبِدَ من دونِه، إما بقَهْرٍ منه لمَن عَبَدَه، وإما بطَاعةٍ مِمَّن عبده له، وإنسانًا كان ذلك المَعْبودُ، أو شَيْطانًا، أو وَثَنًا، أو صَنَمًا، أو كائِنًا ما كانَ من شيءٍ).
فالطاغوتُ هو: الذي بَلَغ في الطُّغْيانِ مَبْلَغًا عظيمًا فصَدَّ عن سبيلِ اللهِ كثيرًا وأضَلَّ إضلالاً كبيرًا.

والطواغيتُ التي تُعْبَدُ من دُونِ اللهِ تعالى كثيرةٌ، وأشْهَرُ أصْنَافِ الطَّواغيتِ وأَكْثَرُها طُغْيانًا وصَدًّا عن سَبيلِ اللهِ ثلاثةٌ: الشيطانُ الرَّجيمُ، والأوثانُ التي تُعْبَدُ من دونِ اللهِ، ومَن يَحْكُمُ بغيرِ ما أنْزَلَ اللهُ.

الصِّنْفُ الأولُ: الشَّيْطانُ الرَّجيمُ
وهو أصْلُ كلِّ شِرْكٍ وطُغْيانٍ، بل كلُّ عِبادةٍ لغيرِ اللهِ تعالى فهي في حَقيقةِ الأمرِ عِبادةٌ للشَّيْطانِ؛ لأنه سَبَبُها والداعِي لها.
قال اللهُ تعالى: ﴿أَلَمْ أَعْهَدْ إِلَيْكُمْ يَا بَنِي آدَمَ أَنْ لَا تَعْبُدُوا الشَّيْطَانَ إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُبِينٌ * وَأَنِ اعْبُدُونِي هَذَا صِرَاطٌ مُسْتَقِيمٌ﴾ [يس: ٦٠–٦١].
وقال تعالى: ﴿إِنَّ اللَّهَ لَا يَغْفِرُ أَنْ يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَلِكَ لِمَنْ يَشَاءُ وَمَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا بَعِيدًا (116) إِنْ يَدْعُونَ مِنْ دُونِهِ إِلَّا إِنَاثًا وَإِنْ يَدْعُونَ إِلَّا شَيْطَانًا مَرِيدًا (117) لَعَنَهُ اللَّهُ وَقَالَ لَأَتَّخِذَنَّ مِنْ عِبَادِكَ نَصِيبًا مَفْرُوضًا (118) وَلَأُضِلَّنَّهُمْ وَلَأُمَنِّيَنَّهُمْ وَلَآَمُرَنَّهُمْ فَلَيُبَتِّكُنَّ آَذَانَ الْأَنْعَامِ وَلَآَمُرَنَّهُمْ فَلَيُغَيِّرُنَّ خَلْقَ اللَّهِ وَمَنْ يَتَّخِذِ الشَّيْطَانَ وَلِيًّا مِنْ دُونِ اللَّهِ فَقَدْ خَسِرَ خُسْرَانًا مُبِينًا (119) يَعِدُهُمْ وَيُمَنِّيهِمْ وَمَا يَعِدُهُمُ الشَّيْطَانُ إِلَّا غُرُورًا (120) أُولَئِكَ مَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ وَلَا يَجِدُونَ عَنْهَا مَحِيصًا (121)﴾ [النساء: ١١٦–١٢١]
وقد جعَلَ اللهُ تعالى من عُقوبةِ المُعْرِضينَ عن ذِكْرِه تَسْلِيطَ الشَّياطِينِ عليهم، قال اللهُ تعالى: ﴿وَمَنْ يَعْشُ عَنْ ذِكْرِ الرَّحْمَنِ نُقَيِّضْ لَهُ شَيْطَانًا فَهُوَ لَهُ قَرِينٌ (36) وَإِنَّهُمْ لَيَصُدُّونَهُمْ عَنِ السَّبِيلِ وَيَحْسَبُونَ أَنَّهُمْ مُهْتَدُونَ (37) حَتَّى إِذَا جَاءَنَا قَالَ يَا لَيْتَ بَيْنِي وَبَيْنَكَ بُعْدَ الْمَشْرِقَيْنِ فَبِئْسَ الْقَرِينُ (38) وَلَنْ يَنْفَعَكُمُ الْيَوْمَ إِذْ ظَلَمْتُمْ أَنَّكُمْ فِي الْعَذَابِ مُشْتَرِكُونَ﴾ [الزخرف: ٣٦–٣٩].
واجتنابُ هذا الطاغوتِ يَكونُ بالاستعاذةِ باللهِ منه، والحَذَرِ من كَيْدِه، وعَدَمِ اتباعِ خُطُواتِه، فهو عَدُوٌّ مُضِلٌّ مُبِينٌ ﴿كُتِبَ عَلَيْهِ أَنَّهُ مَنْ تَوَلَّاهُ فَأَنَّهُ يُضِلُّهُ وَيَهْدِيهِ إِلَى عَذَابِ السَّعِيرِ﴾ [الحج: ٤].
وتَوَلِّي الشَّيْطانِ يَكونُ باتِّباعِ خُطُواتِه وتَصْديقِ وُعُودِه واستشرافِ أَمَانِيِّه وفِعْلِ ما يُزَيِّنُه من المعاصي، والإعراضِ عن هُدَى اللهِ تعالى؛ فمَن فعَلَ ذلك فقد تَولَّى الشيطانَ.
والشيطانُ يَحْضُر ابنَ آدَمَ عندَ كلِّ شيءٍ من شأنِه، كما صَحَّ ذلك عن النبيِّ صلى الله عليه وسلم في صحيحِ مُسلمٍ وغيرِه من حديثِ جابرِ بنِ عبدِ اللهِ رضِي اللهُ عنهما.
وتَحقيقُ الاستعاذةِ من الشيطانِ يَكُونُ بصِدْقِ الالتجاءِ إلى اللهِ تعالى، واتِّباعِ هُدَى اللهِ العَاصِم من شَرِّ الشَّيْطانِ وشِرْكِه.
ومِمَّا هَدَانا اللهُ تعالى إليه ليَعْصِمَنا من شَرِّ الشَّيْطانِ: تَكْرَارُ الاستعاذةِ باللهِ تعالى منه، والإيمانُ باللهِ والتَّوكُّلُ عليه، والإخلاصُ، وكثرةُ ذِكْرِ اللهِ، والتَّعْويذات الشَّرعيَّة.
وحَذَّرَنا اللهُ من اتِّباعِ خُطُواتِ الشيطانِ، وفِعْلِ ما يَتسَلَّطُ به الشيطانُ من نَقِيضِ ما ذُكِرَ آنفًا؛ فضَعْفُ الإيمانِ وضَعْفُ التوكلِ والإخلاصِ، والغَفْلةُ عن ذِكْرِ اللهِ تعالى، والتَّفْرِيطُ في التعويذاتِ الشَّرْعِيَّةِ، كُلُّ ذلك من أسبابِ تَسَلُّطِ الشيطانِ على الإنسانِ.
وكذلك ما يَجِدُ به الشيطانُ على الإنسانِ مَدْخَلاً للتسلطِ عليه كالغَضَبِ الشديدِ، والفَرَحِ الشَّديدِ، والانْكِبابِ على الشَّهواتِ، والشُّذُوذِ عن الجماعةِ، والوَحْدةِ، ولا سِيَّما في السَّفَرِ، ونَقْلِ الحديثِ بينَ الناسِ، وخَلْوةِ الرجُلِ بالمرأةِ، والظنِّ السَّيِّئِ، وغِشْيانِ مَواضِعِ الرِّيَبِ.
وشُرِعت التسميةُ في كلِّ شأنٍ من شُئونِ الإنسانِ لحُصولِ البَرَكةِ والحِفْظِ من كيدِ الشيطانِ، فيُسَمِّي العبدُ إذا أكَلَ، وإذا شَرِبَ، وإذا دخَلَ المَنْزِلَ، وإذا خَرَجَ منه، وإذا أَصْبَحَ، وإذا أمْسَى، وإذا رَكِبَ، وإذا جَامَعَ، وإذا دخَلَ الخَلاءَ، وإذا أرادَ النَّوْمَ.
وفي صَحيحِ مُسلمٍ من حديثِ أبي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رضِي اللهُ عنه أن النبيَّ صلى اللهُ عليه وسلم قال: ((إذا تَثَاءَبَ أحَدُكُمْ فَلْيَكْظِمْ ما اسْتَطَاعَ؛ فإنَّ الشَّيْطانَ يَدْخُلُ في فِيهِ)).
وفي رِوَايةٍ لأحْمَدَ وعبدِ الرَّزَّاقِ: ((إذا تَثَاوَبَ أحَدُكم فَلْيَضَعْ يَدَهُ على فِيهِ؛ فإنَّ الشَّيْطَانَ يَدْخُلُ مع التَّثَاوُبِ)).
ومَن اتَّبَعَ ما أَرْشَدَ اللهُ إليه من الهُدَى كان في حِصْنٍ وأمانٍ من كَيْدِ الشيطانِ، ومَن قَصَّرَ وفَرَّط، لم يَأْمَن أن يَنْالَه شيءٌ من كيدِ الشيطانِ وإيذائِه وإغوائِه بسَبَبِ تَفْريطِه.

الصِّنْفُ الثاني: الأوثانُ التي تُعْبَدُ من دونِ اللهِ عز وجل
وهذه الطواغيتُ أنواعٌ:
فمن الأوثان: الأصنامُ والتماثيلُ التي تُنْحَتُ على شَكْلِ صُوَرٍ؛ إما صُوَرِ رِجَالٍ أو حَيواناتٍ أو غيرِ ذلك؛ فمِن المُشْركِينَ مَن يَزْعُم أنها تَنْفَعُ وتَضُرُّ، ومنهم مَن يَزْعُم أنها تَشْفَعُ لمَن يَدْعُوها ويَتَقرَّبُ إليها بالذَّبْحِ والنَّذْرِ وسؤالِ الحَاجاتِ.
قال اللهُ تعالى: ﴿أَتَعْبُدُونَ مَا تَنْحِتُونَ (95) وَاللَّهُ خَلَقَكُمْ وَمَا تَعْمَلُونَ﴾ [الصافات: ٩٥–٩٦].
وقال تعالى: ﴿وَاتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ إِبْرَاهِيمَ (69) إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ مَا تَعْبُدُونَ (70) قَالُوا نَعْبُدُ أَصْنَامًا فَنَظَلُّ لَهَا عَاكِفِينَ (71) قَالَ هَلْ يَسْمَعُونَكُمْ إِذْ تَدْعُونَ (72) أَوْ يَنْفَعُونَكُمْ أَوْ يَضُرُّونَ (73) قَالُوا بَلْ وَجَدْنَا آَبَاءَنَا كَذَلِكَ يَفْعَلُونَ (74) قَالَ أَفَرَأَيْتُمْ مَا كُنْتُمْ تَعْبُدُونَ (75) أَنْتُمْ وَآَبَاؤُكُمُ الْأَقْدَمُونَ (76) فَإِنَّهُمْ عَدُوٌّ لِي إِلَّا رَبَّ الْعَالَمِينَ (77) الَّذِي خَلَقَنِي فَهُوَ يَهْدِينِ (78) وَالَّذِي هُوَ يُطْعِمُنِي وَيَسْقِينِ (79) وَإِذَا مَرِضْتُ فَهُوَ يَشْفِينِ (80) وَالَّذِي يُمِيتُنِي ثُمَّ يُحْيِينِ (81) وَالَّذِي أَطْمَعُ أَنْ يَغْفِرَ لِي خَطِيئَتِي يَوْمَ الدِّينِ (82)﴾ [الشعراء: ٦٩–٨٢].
وقال تعالى: ﴿وَلَقَدْ آَتَيْنَا إِبْرَاهِيمَ رُشْدَهُ مِنْ قَبْلُ وَكُنَّا بِهِ عَالِمِينَ (51) إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ مَا هَذِهِ التَّمَاثِيلُ الَّتِي أَنْتُمْ لَهَا عَاكِفُونَ (52) قَالُوا وَجَدْنَا آَبَاءَنَا لَهَا عَابِدِينَ (53) قَالَ لَقَدْ كُنْتُمْ أَنْتُمْ وَآَبَاؤُكُمْ فِي ضَلَالٍ مُبِينٍ (54) قَالُوا أَجِئْتَنَا بِالْحَقِّ أَمْ أَنْتَ مِنَ اللَّاعِبِينَ (55) قَالَ بَلْ رَبُّكُمْ رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ الَّذِي فَطَرَهُنَّ وَأَنَا عَلَى ذَلِكُمْ مِنَ الشَّاهِدِينَ (56) وَتَاللَّهِ لَأَكِيدَنَّ أَصْنَامَكُمْ بَعْدَ أَنْ تُوَلُّوا مُدْبِرِينَ (57)﴾ [الأنبياء: ٥١–٥٧].
ومن الأوثانِ: بعضُ الأشجارِ والأحجارِ المُعظَّمة التي يَعْتَقِدُ فيها بعضُ المُشْركينَ اعتقاداتٍ كُفْريَّةً، فيَعْتَقِدُونَ فيها النَّفْعَ والضُّرَّ وأنَّها تَشْفَعُ عندَ اللهِ عز وجل لمَن يَدْعُوها ويَتقَرَّبُ إليها.
وقد كانتِ الأصنامُ والأشجارُ والأحجارُ التي تُعْبَدُ في الجاهليَّةِ كثيرةً جِدًّا، حتى كانَ حَوْلَ الكعبةِ وَحْدَها ثلاثُمائةٍ وسِتُّونَ صَنَمًا، وقد حَطَّمَها النبيُّ صلى اللهُ عليه وسلم لمَّا فَتَحَ مَكَّةَ.
وكانَ في بعضِ أحياءِ العَرَبِ أشجارٌ وأحجارٌ كثيرةٌ تُعَظَّم وتُعْبَدُ من دونِ اللهِ عز وجل.
ومن الأوثانِ: القُبورُ والمَشاهِدُ والأَضْرِحَةُ والمَقاماتُ التي تُعْبَدُ من دونِ اللهِ عز وجل، فيُطافُ حولَها تقرُّبًا لها، ويُذْبَحُ لها، وتُقَدَّمُ لها النُّذورُ والأموالُ، ويكونُ لبعضِها سَدَنَةٌ وخُدَّامٌ يأكلون أموالَ الناسِ بالباطلِ، ويَصُدُّونَ عن سبيلِ اللهِ، ويُزَيِّنُونَ لهم الشِّرْكَ باللهِ عزَّ وجلَّ، وسُؤالَ المَوْتَى، وقَضَاءَ الحاجاتِ ودَفْعَ البَلاءِ.

وقد قال النبيُّ صلى اللهُ عليه وسلم: ((اللهُمَّ لا تَجْعَلْ قَبْرِي وَثَنًا يُعْبَدُ)) رواه مَالِكٌ.
بل نَهَى النبيُّ صلى الله عليه وسلم عن اتِّخاذِ القبورِ مَساجِدَ لئلا تَجُرَّ إلى عبادةِ المَقْبورينَ فيها، فعن جُنْدَبِ بنِ عبدِ اللهِ رضِي الله عنه أن النبيَّ صلى الله عليه وسلم قال: ((إنَّ مَنْ كان قبلَكم كانوا يَتَّخِذُونَ قُبورَ أنبيائِهم وصَالحِيهم مَساجِدَ، ألا فلا تَتَّخِذوا القُبورَ مَسَاجِدَ، فإنِّي أنْهَاكُم عن ذلكَ)). رواه مُسلمٌ.
وقال أبو عُبَيدةَ عامِرُ بنُ الجَرَّاحِ رضِي اللهُ عنه: (كَانَ آخِرَ ما تَكَلَّم به نبيُّ اللهِ صلى الله عليه وسلم أنْ أخْرِجُوا يَهُودَ الحِجَازِ من جَزِيرةِ العَرَبِ، واعْلَمُوا أنَّ شِرارَ الناسِ الذين يَتَّخذونَ القُبورَ مَساجِدَ). رواه الإمامُ أحمدُ.

واتخاذ القبور مساجد هو أنْ يُصَلَّى عَليها، أَو يُصَلَّى إِلَيهَا، أو يُبْنَى عَليهَا مَسجداً ؛ فَمَن فَعَل واحدةً من هذِهِ الثَّلاثِ فقد وَقَع في المحذورِ.

ومن الأوثان: ما يَرْمُزُ للشركِ وعبادةِ غَيْرِ اللهِ عز وجل من الشِّعَاراتِ والتعاليقِ، ففي سُننِ التِّرْمذيِّ أن النبيَّ صلى اللهُ عليه وسلم رَأَى في عُنقِ عَدِيِّ بنِ حَاتِمٍ صَلِيبًا من ذَهَبٍ فقال له: ((يا عَدِيُّ، اطْرَحْ عنكَ هذا الوَثَنَ)).
والمَقْصودُ أنَّ كلَّ ما يُعْبدُ من دونِ اللهِ عز وجل فهو طاغوتٌ، سواءٌ كان صَنَمًا أو شَجَرًا أو حَجَرًا أو قَبْرًا أو غَيْرَهُ.
وعن أبي هُرَيرةَ رضِي اللهُ عنه أن النبيَّ صلى اللهُ عليه وسلم قال: ((يَجمعُ اللهُ الناسَ يومَ القيامةِ، فيقولُ: مَن كانَ يَعْبُدُ شيئًا فلْيَتبعه؛ فيَتبعُ مَن كانَ يَعبدُ الشَّمسَ الشَّمسَ، ويَتبعُ مَن كان يَعْبُدُ القَمَرَ القَمَرَ، ويَتبعُ مَن كانَ يَعْبُدُ الطَّواغِيتَ الطَّوَاغيتَ)). مُتَّفق عليه.
وهذا الاتباعُ يَكونُ إلى نارِ جَهَنَّم والعياذُ باللهِ، كما قال اللهُ تعالى: ﴿إِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ حَصَبُ جَهَنَّمَ أَنْتُمْ لَهَا وَارِدُونَ (98) لَوْ كَانَ هَؤُلَاءِ آلِهَةً مَا وَرَدُوهَا وَكُلٌّ فِيهَا خَالِدُونَ (99) لَهُمْ فِيهَا زَفِيرٌ وَهُمْ فِيهَا لَا يَسْمَعُونَ﴾ [الأنبياء: ٩٨–١٠٠].
الحَصَبُ هو ما يُحْصَب به، أي يُحْذَفُ به.
وهذه الآياتُ تَدُلُّ على أن هذه الأوثانَ لا تَنْفَعُ عَابِدِيها، بل تُقْذَفُ في النارِ يَوْمَ القِيامةِ هي وَمَن عبَدَها من دونِ اللهِ عز وجل قَذْفًا شديدًا.
وأمَّا مَن عُبِد من دونِ اللهِ وهو لا يَرْضَى بذلك، فليسَ بطاغوتٍ، وإنما اتَّخَذَه المشركون إلهًا وربًّا وطاغوتًا يَطْغُونَ بسَبَبِ اعتقادِهم فيه، وهو بَرِيءٌ من شِرْكِهم وطُغْيانِهم، قال اللهُ تعالى: ﴿اتَّخَذُوا أَحْبَارَهُمْ وَرُهْبَانَهُمْ أَرْبَابًا مِنْ دُونِ اللَّهِ وَالْمَسِيحَ ابْنَ مَرْيَمَ وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا إِلَهًا وَاحِدًا لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ سُبْحَانَهُ عَمَّا يُشْرِكُونَ﴾ [التوبة: ٣١].
وقال تعالى: ﴿إِنَّ الَّذِينَ سَبَقَتْ لَهُمْ مِنَّا الْحُسْنَى أُولَئِكَ عَنْهَا مُبْعَدُونَ (101) لَا يَسْمَعُونَ حَسِيسَهَا وَهُمْ فِي مَا اشْتَهَتْ أَنْفُسُهُمْ خَالِدُونَ (102) لَا يَحْزُنُهُمُ الْفَزَعُ الْأَكْبَرُ وَتَتَلَقَّاهُمُ الْمَلَائِكَةُ هَذَا يَوْمُكُمُ الَّذِي كُنْتُمْ تُوعَدُونَ (103)﴾ [الأنبياء: ١٠١– ١٠٣].
وكذلك الأولياءُ الصالحونَ الذين عَبَدَهم بعضُ المُشْركينَ ظُلْمًا وزُورًا بَرِيئونَ من هذا الشِّرْكِ.
وأما مَن رضِي أن يُعْبَدَ من دونِ اللهِ تعالى أو دَعَا إلى عبادةِ نَفْسِه، فلا شَكَّ أنه من الطواغيتِ، كما قال فِرْعونُ لقومِه: ﴿مَا عَلِمْتُ لَكُمْ مِنْ إِلَهٍ غَيْرِي﴾ [القصص: ٣٨].

الصِّنْفُ الثَّالِثُ: مَن يَحْكُمُ بغَيْرِ ما أنْزَلَ اللهُ
كلُّ مَن كانَ له سُلْطانٌ على الناسِ في بَلَدٍ من البُلْدانِ فأعْرَضَ عن تَحْكيمِ شَرْعِ اللهِ عزَّ وجلَّ فيهم، ووضَعَ لهم أحْكامًا يَحْكُم بها عليهم من تلقاءِ نفسِه؛ فيُحِلُّ لهم ما حَرَّم اللهُ، ويُحَرِّمُ عليهم ما أحلَّ اللهُ؛ فهو طاغوتٌ يُرِيدُ أن يُعْبَدَ من دونِ اللهِ عز وجل، وعبادتُه طاعتُه في تحليلِ الحرامِ وتحريمِ الحلالِ.
ودليلُ ذلك ما صَحَّ عن عَدِيِّ بن حاتمٍ الطائِيِّ رضِي الله عنه أنه سَمِعَ النبيَّ صلى الله عليه وسلم يَقْرَأُ قولَ اللهِ تعالى: ﴿اتَّخَذُوا أَحْبَارَهُمْ وَرُهْبَانَهُمْ أَرْبَابًا مِنْ دُونِ اللَّهِ﴾ [التوبة: ٣١].
قال: فقلتُ: إنَّا لَسْنَا نَعْبُدُهم.
قال: ((أليسَ يُحَرِّمونَ ما أحَلَّ اللهُ فتُحَرِّمُونَه، ويُحِلُّونَ ما حَرَّمَ اللهُ فتَسْتَحِلُّونَه ؟))
قلتُ: بَلَى
قال: ((فتلكَ عِبادتُهم)). رواه البخاريُّ في التاريخِ الكبيرِ، والتِّرمذِيُّ والطَّبَرانِيُّ، واللفْظُ له.
وقال حذيفةُ بنُ اليَمَانِ: (أمَا إنَّهم لم يُصَلُّوا لهم، ولكنَّهم كانوا ما أحلُّوا لهم من حَرامٍ اسْتحَلُّوه، وما حَرَّموا عليهم من الحَلالِ حَرَّموه؛ فتلك رُبوبيـَّتـُهم). رواه سعيدُ بنُ مَنصورٍ.
ومن الطواغيتِ: الكُهَّانُ والعَرَّافونُ والسَّحَرةُ الذين يَدَّعُون عِلْمَ الغَيْبِ ويَتحَاكَمُ إليهم الجَهَلةُ الضُّلالُ.
قال اللهُ تعالى: ﴿أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ يَزْعُمُونَ أَنَّهُمْ آمَنُوا بِمَا أُنْزِلَ إِلَيْكَ وَمَا أُنْزِلَ مِنْ قَبْلِكَ يُرِيدُونَ أَنْ يَتَحَاكَمُوا إِلَى الطَّاغُوتِ وَقَدْ أُمِرُوا أَنْ يَكْفُرُوا بِهِ وَيُرِيدُ الشَّيْطَانُ أَنْ يُضِلَّهُمْ ضَلَالًا بَعِيدًا﴾ [النساء: ٦٠].
ونهَى النبيُّ صلى الله عليه وسلم عن إتيانِ الكَهَنةِ والعَرَّافينَ والسَّحَرةِ، فعن أبي هُريرةَ رضِي الله عنه عن النبيِّ صلى الله عليه وسلم أنه قال: ((مَن أتَى كاهنًا أو عَرَّافًا فصَدَّقَهُ بما يقولُ، فقد كَفَرَ بما أُنْزِلَ على مُحمَّدٍ)). رواه الإمامُ أحمدُ من حديثِ أبي هُريرةَ رضِي الله عنه.
وقال ابنُ مسعودٍ رضِي الله عنه: ((مَن أتى كاهِنًا أو سَاحِرًا فصَدَّقه بما يقولُ فقد كَفَرَ بما أُنْزِلَ على مُحَمَّدٍ)). رواه البَزَّارُ.
والإِعْرَاضُ عن حُكْمِ اللهِ والتَّحَاكُمِ إلى شَرْعِه، وطَلَبُ حُكْمِ الطَّواغيتِ هو من أعمالِ المُنافقين الذين ذَمَّهم اللهُ في كتابِه الكريمِ؛ فقال تعالى: ﴿وَيَقُولُونَ آَمَنَّا بِاللَّهِ وَبِالرَّسُولِ وَأَطَعْنَا ثُمَّ يَتَوَلَّى فَرِيقٌ مِنْهُمْ مِنْ بَعْدِ ذَلِكَ وَمَا أُولَئِكَ بِالْمُؤْمِنِينَ (47) وَإِذَا دُعُوا إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ لِيَحْكُمَ بَيْنَهُمْ إِذَا فَرِيقٌ مِنْهُمْ مُعْرِضُونَ (48) وَإِنْ يَكُنْ لَهُمُ الْحَقُّ يَأْتُوا إِلَيْهِ مُذْعِنِينَ (49) أَفِي قُلُوبِهِمْ مَرَضٌ أَمِ ارْتَابُوا أَمْ يَخَافُونَ أَنْ يَحِيفَ اللَّهُ عَلَيْهِمْ وَرَسُولُهُ بَلْ أُولَئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ (50) إِنَّمَا كَانَ قَوْلَ الْمُؤْمِنِينَ إِذَا دُعُوا إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ لِيَحْكُمَ بَيْنَهُمْ أَنْ يَقُولُوا سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا وَأُولَئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ (51) وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَيَخْشَ اللَّهَ وَيَتَّقْهِ فَأُولَئِكَ هُمُ الْفَائِزُونَ (52)﴾ [النور: ٤٧–٥٢].

فصل: وكلُّ مَن اتَّبَعَ الطاغوتَ فإنما يَزِيدُه اتِّباعُه له ضَلالاً وخَسارًا وظُلْمةً، وأما مَن كَفَر بالطاغوتِ وآمَن باللهِ واتَّبَعَ هُداه فإنَّ اللهَ تعالى يُخرِجُه من الظُّلماتِ إلى النورِ، ويهديهِ سُبلَ السلامِ، ويُدْخِلُه في رحمتِه وفَضْلِه، قال الله تعالى: ﴿اللَّهُ وَلِيُّ الَّذِينَ آمَنُوا يُخْرِجُهُمْ مِنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ وَالَّذِينَ كَفَرُوا أَوْلِيَاؤُهُمُ الطَّاغُوتُ يُخْرِجُونَهُمْ مِنَ النُّورِ إِلَى الظُّلُمَاتِ أُولَئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ﴾ [البقرة: ٢٥٧].

فهؤلاء الطواغيتُ يُلْقونَ بأوليائِهم في ظُلماتِ الشِّرْكِ والجَهْلِ والضَّلالِ وحَيْرةِ الشَّكِّ، والعِيشةِ الضَّنْكِ، وسُوءِ الحالِ والمآلِ. نسألُ اللهَ السلامةَ والعافيةَ.

وأما المُؤمنونَ باللهِ فإنَّ اللهَ تعالى هو وَلِيُّهم الذي يُخرِجُهم مِنَ الظُّلُمَاتِ إلى النُّورِ فيخرجُهم من ظُلْمةِ الشِّركِ إلى نورِ التوحيدِ، ومن ذُلِّ المَعصيةِ إلى عِزَّةِ الطاعةِ، ومن ضَلالاتِ البِدَعِ إلى مِنْهاجِ السُّنةِ، ومن حَيْرةِ الشكِّ إلى بَرْدِ اليقينِ، ويُخْرِجُهم من الضِّيقِ والضَّنْكِ إلى السَّعَةِ والانْشِراحِ، ومن الهَمِّ والخَوْفِ والحَزَنِ إلى الطُّمأنينةِ والأمنِ والسكينةِ، ويَزِيدُ اللهُ الذين اهتْدَوْا هُدًى، فهم كلَّ يومٍ في ازديادٍ من الخيرِ والهُدَى، تَرْتَفِعُ بهم الدرجاتُ، وتَتَضاعَفُ لهم الحَسَناتُ، ﴿ذَلِكَ فَضْلُ اللَّهِ يُؤْتِيهِ مَنْ يَشَاءُ وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ﴾ [الجمعة: ٤]

طاهر جبريل دكو
_4 _April _2013هـ الموافق 4-04-2013م, 12:13 AM
Darasina bakwai: Ma'anar kafircewa dagutu.
Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿لَا إِكْرَاهَ فِي الدِّينِ قَدْ تَبَيَّنَ الرُّشْدُ مِنَ الْغَيِّ فَمَنْ يَكْفُرْ بِالطَّاغُوتِ وَيُؤْمِنْ بِاللَّهِ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْوَةِ الْوُثْقَى لَا انْفِصَامَ لَهَا وَاللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ﴾ [البقرة: ٢٥٦].
Ma'ana:"Babu tilastawa a cikin Addini. Hakika shiriya ta bayyana daga bata, saboda haka wanda ya kafircewa dagutu kuma yayi imani da Allah, to hakika yayi riko da igiya amintacciya wacce babu yankewa agareta. Kuma Allah Mai jine masani. Q2ayata256. Kuma Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَسُولًا أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوتَ﴾ [النحل: ٣٦].
Ma'ana:"Kuma lallaine hakika Mun aika Manzo cikin kowace al'umma (yana cewa) "ku bawtawa Allah kuma ku nisanci dagutu (wato ababen da ake bawtawa bisa karya). Q16ayata36. Kuma Allah(Madawkakin Sarki) Yace:

﴿وَالَّذِينَ اجْتَنَبُوا الطَّاغُوتَ أَنْ يَعْبُدُوهَا وَأَنَابُوا إِلَى اللَّهِ لَهُمُ الْبُشْرَى﴾ [الزمر: ١٧].
Ma'ana:" Kuma wadanda suka nisanci dagutu ga barin bawta musu kuma suka koma ga Allah suna da bushara, kuma kayi albishir ga bayiNa. Q39:ayata17.
Saboda haka nisantan bawtar dagutu da tsarkake bawta ga Allah(Madawkakin Sarki) Shi kadai babu abokin tarayya gareShi, shine ma'anan tawhidi.

Kuma mutum bazai kasance musulmi mai kadaita (Allah) ba har sai ya kafircewa dagutu.
Kuma shi dagutu, shine duk wani abu da ake bawtawa koma bayan Allah (Madawkakin Sarki), sawa'un an bawta masa ne ta hanyar rokonsa da neman taimakonsa da dogaro gareshi da yin yanka domin bawta gareshi da yin bakance dominsa, kokuwa (an bawta masane) ta hanyan biyayya agareshi cikin halatta haram da haramta halal ko kuma da dawkaka hukunci zuwa gareshi tareda yarda da hukuncinsa.

Ibnu Jarir (Allah Yayi masa Rahama) yace:" Ingantacciyar Magana gameda ma'anar dagutu agareni itace; cewa shi dagutu shine duk wani ma'abucin dagawa ga Allah, sai aka bawta masa koma bayanSa kodai bisa tilastawa daga gareshi ga wanda ya bawta masa hakanan wannan abin bawtan ya kasance mutum ne ko kuma shedani ko wani abu ko gunki kai koma menene ya kasance.
Saboda haka dagutu sihne: abinda ya kai wata makura mai girma cikin dagawa sai ya yawaita kange (mutane) daga hanyar Allah kuma ya batar (dasu) batarwa mai girma.

Kuma dagutan da ake bawtawa koma bayan Allah (Madawkakin Sarki) suna da yawa, amma mafi shaharan dagutai wadanda sukafi yawan dagawa da kangiya daga tafarkin Allah guda uku ne: Shedan jefaffe, gumakan da ake bawtawa koma bayan Allah da wanada ke hukunci bada abinda Allah Ya sawkarba.


Sinfi na farko, shedan jefaffe; shine tushen duk wata shirka da dagawa, kai ba wannan kawai bama, duk bawta ga wanin Allah (Madawkakin Sarki) a hakikanin al'amari bawtan shedanne, saboda shine sababinsa kuma mai kira zuwa ga aikata shi. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿أَلَمْ أَعْهَدْ إِلَيْكُمْ يَا بَنِي آدَمَ أَنْ لَا تَعْبُدُوا الشَّيْطَانَ إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُبِينٌ * وَأَنِ اعْبُدُونِي هَذَا صِرَاطٌ مُسْتَقِيمٌ﴾ [يس: ٦٠–٦١].
Ma'ana:"Ashe ban dauki alkawari agarekuba ya ku yayan Adamu cewa kada ku bawtawa Shedan lallai shi agareku makiyine mabayyani(60) Kuma ku bawta mini. Wannar itace hanya madaidaiciya(61). Q36ayata60 da61. Kuma Allah(Madawkakin Sarki) Yace:
﴿إِنَّ اللَّهَ لَا يَغْفِرُ أَنْ يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَلِكَ لِمَنْ يَشَاءُ وَمَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا بَعِيدًا (116) إِنْ يَدْعُونَ مِنْ دُونِهِ إِلَّا إِنَاثًا وَإِنْ يَدْعُونَ إِلَّا شَيْطَانًا مَرِيدًا (117) لَعَنَهُ اللَّهُ وَقَالَ لَأَتَّخِذَنَّ مِنْ عِبَادِكَ نَصِيبًا مَفْرُوضًا (118) وَلَأُضِلَّنَّهُمْ وَلَأُمَنِّيَنَّهُمْ وَلَآَمُرَنَّهُمْ فَلَيُبَتِّكُنَّ آَذَانَ الْأَنْعَامِ وَلَآَمُرَنَّهُمْ فَلَيُغَيِّرُنَّ خَلْقَ اللَّهِ وَمَنْ يَتَّخِذِ الشَّيْطَانَ وَلِيًّا مِنْ دُونِ اللَّهِ فَقَدْ خَسِرَ خُسْرَانًا مُبِينًا (119) يَعِدُهُمْ وَيُمَنِّيهِمْ وَمَا يَعِدُهُمُ الشَّيْطَانُ إِلَّا غُرُورًا (120) أُولَئِكَ مَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ وَلَا يَجِدُونَ عَنْهَا مَحِيصًا (121)﴾ [النساء: ١١٦–١٢١]
Ma'ana:"Lallaine Allah baYa gafarta ayi shirka gareshi, amma Yana gafarta abinda baikai (matsayin) shirkaba ga wanda Yaso. Kuma wanda yayi shirka ga Allah to hakika ya bace bata mai nisa(116).
Basu kiran kowa baicinSa face mata kuma basu kiran kowa face Sshedani mai tsawrin kai (117) Allah Ya la'aneshi. Kuma (shedan) yace; saina riki rabo yankakke daga bayinKa(118) Kuma lallaine saina batar dasu kuma lallaine sai na sa musu buri kuma lallaine saina umurcesu kuma lallaine sai sun kakkatse kunnuwan dabbobi, kuma lallaine zan umurcesu saisun canza halittar Allah. Kuma wanda ya riki shedan majibinci koma bayan Allah, hakika yayi hasara hasara bayyananniya(119) Yana yi musu ahkawari kuma yana sa musu buri, kuma Shedan baya yimusu wa'adi da komai face rudi (120).Wadannan matattararsu itace Jahannama, kuma basu samun makarkata daga gareta (121). Q4ayaata116-121.
Kuma hakika Allah Ya sanya daga cikin ukubar wanda ya kawda kai daga ambaton Allah shine cin nasarar Shedan akansu. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَمَنْ يَعْشُ عَنْ ذِكْرِ الرَّحْمَنِ نُقَيِّضْ لَهُ شَيْطَانًا فَهُوَ لَهُ قَرِينٌ (36) وَإِنَّهُمْ لَيَصُدُّونَهُمْ عَنِ السَّبِيلِ وَيَحْسَبُونَ أَنَّهُمْ مُهْتَدُونَ (37) حَتَّى إِذَا جَاءَنَا قَالَ يَا لَيْتَ بَيْنِي وَبَيْنَكَ بُعْدَ الْمَشْرِقَيْنِ فَبِئْسَ الْقَرِينُ (38) وَلَنْ يَنْفَعَكُمُ الْيَوْمَ إِذْ ظَلَمْتُمْ أَنَّكُمْ فِي الْعَذَابِ مُشْتَرِكُونَ﴾ [الزخرف: ٣٦–٣٩].
Ma'ana: Kuma wanda ya rayu ga barin ambaton mai Rahama, zaMu sanya masa wani Shedani yakasance abokinsa na dindindin.(36) Kuma lallai su hakika suna kangesu daga tafarkin (Allah) alhali su suna zaton cewa suna kan shriya. (37) Har sai (wanda shedan ya zama abokinsa) ya zo maNa (wato ya mutu) sai yace; kaicona, inama atsakanina da kai akwai nisan dake tsakanin gabar da yamma, tir da kai a matsayin aboki. (38) Kuma (wannan maganar) bazata amfanekuba ayaw yayinda kuka kasance masu zaluntar (kansu) lallai ku masu tarewane acikin azaba (39) Q43ayata 36-39.

Kuma nisantan wannan dagutu zai kasancene ta hanyan neman tsarin Allah daga (saharrin dagutun) da kiyayewa gameda kaidinsa da barin bibiyan matakansa, domin shi makiyine mai batarwa mabayyani. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿كُتِبَ عَلَيْهِ أَنَّهُ مَنْ تَوَلَّاهُ فَأَنَّهُ يُضِلُّهُ وَيَهْدِيهِ إِلَى عَذَابِ السَّعِيرِ﴾ [الحج: ٤].
Ma'ana:" An wajabta masa cewa lallai wanda ya jibinceshi to lallaine zai batar dashi kuma ya shiryar dashi zuwaga azaba mai tsananin kuna. Q22ayata4.
Jibintan Shedan yakan kasancene da bibiyan hanyoyinsa da kuma gaskata alkawarinsa da sa tsammani cikin burace buracensa, da aikata abinda yake kawatawa na ayyukan sabo, da kawar da kai daga shiriyar Allah (Madawkakin Sarki). Saboda haka, duk wanda ya aikata wannan hakika ya jibinci Shedan.
Kuma Shedan yakan halartowa dan Adam acikin komai daga lamurransa. Kamar yadda ya inganta daga Annabi (S.A.W) a cikin sahihu Muslim daga hadisin Jabir dan Abdullahi Allah Ya kara musu yarda.
Kuma hakikance neman tsari daga sharrin Shedan yana kasancewane ta hanyar komaw ga Allah (Madawkakin Sarki) komawa ta gaskiya, da bin shiriyar Allah wanda ke bada kariya daga sharrin Shedan da shirkansa.
Kuma daga cikin abubuwanda Allah Ya shiryar da mu zuwa gareshi domin Ya bamu kariya daga sharrin Shedan shine yawan maimaita neman tsarin Allah (Madawkakin Sarki) daga (sharrin) sa, da imani da Allah da dogaro gareShi da tsarkake niyya da yawan ambaton Allah da addu'o'in neman tsari shar'antattu.
Kuma Allah Ya gargademu gameda bin hanyoyin Shedan da aikata abubuwanda Shedan ke samun galaba (akan mutane) dasu daga kishiyoyin abubuwanda aka ambata dazu. Saboda haka rawnin imani da rawnin tawakkali da ikhlasi, da gafala daga barin Ambaton Allah(Madawkakin Sarki) da sakaci gameda addu'oin neman tsari shar'antattu, duk wadannan sabubbane na galaban Shedan akan Mutum.
Hakanan abinda Shedan ke samun mashiga nayin galaba akan Mutum dasu, kamar; matsanancin fushi, matsanancin farin ciki, da tsunduma cikin abubuwan shi'awa, da fita daga cikin jama'an(Musulmi) da hadinkai musamman ma a halin tafiya, da yada zance a tsakanin Mutane, da kadaicin Mutum na miji da mace (wanda ba muharramintaba), da mummunan zato da shiga wurare masu shubuha.
Kuma an shr'anta yin bisimilla cikin kowane sha'ani daga sha'anonin Mutum domin samun albarka da kariya daga kaidin Shedan. Sai bawa yayi bisimilla idan zai ci abinci, idan zai sha abinsha, idan zai shiga masawki, idan zai fita daga gareshi, idan ya wayi gari, idan ya yammaita idan zai haw abin hawa, idan zaiyi jima'i, idan zai shiga bandaki da kuma idan yayi nufin bacci.
Kuma yazo acikin sahihu Muslim daga hadisin Abu Sa'idin Alkhudri (Allah Ya karamasa yarda) yace lallai Annabi (S.A.W) yace:
: ((إذا تَثَاءَبَ أحَدُكُمْ فَلْيَكْظِمْ ما اسْتَطَاعَ؛ فإنَّ الشَّيْطانَ يَدْخُلُ في فِيهِ)).
Ma'ana:"Idan dayanku zaiyi hamma, to ya kame gwar gwadon iyawarsa domin lallai Shedan yana shiga cikin bakinsa". A wata riwayar a wurin Ahamd da Abdurrazzak yace:
((إذا تَثَاوَبَ أحَدُكم فَلْيَضَعْ يَدَهُ على فِيهِ؛ فإنَّ الشَّيْطَانَ يَدْخُلُ مع التَّثَاوُبِ)).
Ma'ana:"Idan dayanku zaiyi hamma, to ya dora hannunsa akan bakinsa, domin lallai shedani yakan shiga".
Duk wanda ya bi abinda Allah Ya shiryar zuwa gareshi na shiriya, zai kasance acikin kariya da aminci, wanda kuma ya gajiya yayi sakaci, bazai aminta ba daga wani kaidi na Shedan ya sameshi da cutarwansa da halakarwansa sakamakon dabi'arsa ta ko oho.
Sinfi na biyu: Abubuwan da ake bawtawa koma bayan Allah (Mai girma da dawkaka)
Suma wadannan dagutan naw'ukane (mabambanta)
Daga cikin abubuwan da ake bawtawa koma bayan Allah akwai gumaka da mutum mutumi wanda ake sassakashi a shakalin surori, kodai surorin mazaje ko dabbobi ko wanin wannan. Daga cikin mushirikai akwai wanda yake riya cewa lallai tana iya amfanarwa kuma tana cutarwa, kumaa daga cikinsu akwai wanda ke riya cewa tana bada ceto ga wanda yake kiranta kuma yake neman kusanci gareta da yanka da bakance da neman biyan bukatu. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿أَتَعْبُدُونَ مَا تَنْحِتُونَ (95) وَاللَّهُ خَلَقَكُمْ وَمَا تَعْمَلُونَ﴾ [الصافات: ٩٥–٩٦].
Ma'ana:"Yace:" Kuna bawtawa abinda kuke sassakawa? (95) Alhali Allah ne Ya halicceku gami ga abinda kuke aikatawa (96).
Kuma Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
وقال تعالى: ﴿وَاتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ إِبْرَاهِيمَ (69) إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ مَا تَعْبُدُونَ (70) قَالُوا نَعْبُدُ أَصْنَامًا فَنَظَلُّ لَهَا عَاكِفِينَ (71) قَالَ هَلْ يَسْمَعُونَكُمْ إِذْ تَدْعُونَ (72) أَوْ يَنْفَعُونَكُمْ أَوْ يَضُرُّونَ (73) قَالُوا بَلْ وَجَدْنَا آَبَاءَنَا كَذَلِكَ يَفْعَلُونَ (74) قَالَ أَفَرَأَيْتُمْ مَا كُنْتُمْ تَعْبُدُونَ (75) أَنْتُمْ وَآَبَاؤُكُمُ الْأَقْدَمُونَ (76) فَإِنَّهُمْ عَدُوٌّ لِي إِلَّا رَبَّ الْعَالَمِينَ (77) الَّذِي خَلَقَنِي فَهُوَ يَهْدِينِ (78) وَالَّذِي هُوَ يُطْعِمُنِي وَيَسْقِينِ (79) وَإِذَا مَرِضْتُ فَهُوَ يَشْفِينِ (80) وَالَّذِي يُمِيتُنِي ثُمَّ يُحْيِينِ (81) وَالَّذِي أَطْمَعُ أَنْ يَغْفِرَ لِي خَطِيئَتِي يَوْمَ الدِّينِ (82)﴾ [الشعراء: ٦٩–٨٢].
Ma'ana:"Kuma ka karanta musu (ya Muhammad) labarin Ibrahim (69) Yayinda yacewa mahaifinsa da mutanensa:"me kuke bawta? (70) Sukace muna bawtan gumakane, saboda haka muna dogewa bias lazimtansu (71) Yace:"shin suna jinku a sa'ilinda kuke kiransu? (72) Ko kuwa suna amfananku ko cutar da ku? (73) A'a mudai mun tarar da iyayenmu ne bias aikata haka (74) Yace kunga abinda kuka kasance kuna bawta? (75) Daku da iyayenku mafiya dadewa? (76) To lallaine su makiyane agareni face Ubangijin talikai (77) Wanda Shine Ya halicceni saboda haka kuma sahine zai shiryar dani (78) Kuma Shine wanda Yake ciyar dani kuma Yake sahayar dani (79) Kuma idan nayi rashin lafiya Shine yake warkar dani (80) Kuma wanda Yake matar dani kuma Ya rayar dani (81) Kuma Shine wanda nake kwadayin Ya gafarta min zunubbaina a Ranar sakamako (82) Q26ayata69-82.
Kuma Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَلَقَدْ آَتَيْنَا إِبْرَاهِيمَ رُشْدَهُ مِنْ قَبْلُ وَكُنَّا بِهِ عَالِمِينَ (51) إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ مَا هَذِهِ التَّمَاثِيلُ الَّتِي أَنْتُمْ لَهَا عَاكِفُونَ (52) قَالُوا وَجَدْنَا آَبَاءَنَا لَهَا عَابِدِينَ (53) قَالَ لَقَدْ كُنْتُمْ أَنْتُمْ وَآَبَاؤُكُمْ فِي ضَلَالٍ مُبِينٍ (54) قَالُوا أَجِئْتَنَا بِالْحَقِّ أَمْ أَنْتَ مِنَ اللَّاعِبِينَ (55) قَالَ بَلْ رَبُّكُمْ رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ الَّذِي فَطَرَهُنَّ وَأَنَا عَلَى ذَلِكُمْ مِنَ الشَّاهِدِينَ (56) وَتَاللَّهِ لَأَكِيدَنَّ أَصْنَامَكُمْ بَعْدَ أَنْ تُوَلُّوا مُدْبِرِينَ (57)﴾ [الأنبياء: ٥١–٥٧].
Ma'ana:"Kuma lallai hakika Mun bawa Ibrahima shiriyarsa tun gabani, kuma Mun kasance masana gamedashi (51) Sa'ilinda yacewa mahaifinsa da mutanensa:"menene wadannan mutum mutumai da kuke masu lazimta agaresu? (52) Sukace: "mun samu iyayen mu ne suna masu bawta agwresu (53) Yace:" lallai ne kun kasance daku da iyayenku acikin bata bayyananniya (54) Sukace "shin kai kazoo mana da gaskiyace, ko dai kai kana cikin masu wasane? (55) Yace "A'a Ubangijin ku Shine Ubangijin sammai da kasa wanda Ya kagi halittarsu. Kuma ni akan haka ina daga cikin masu shaidawa (56) Kuma lallai ina rantsuwa da Allah sai na yiwa gumakanku kaidi bayan kun juya kun bada baya (57) Q21ayata51-57.
Kuma yana daga cikin abubuwanda ake bawtawa koma bayan Allah: Wasu bishiyoyi da duwatsu wadanda ake girmamawa wadanda mushirikai suke da wasu kudurce kudurce na kafirci agame dasu. Saboda haka suna kudurin cewa suna da ikon amfanarwa da cutarwa, da kuma cewa suna ceto a wurin Allah (Mai girma da dawkaka ) ga wanda yake kiransu kuma yake neman kusanci garesu.
Kuma hakika gumaka da bishiyoyi da duwatsun da ake bawtawa a jahiliyya suna da yawa kwarai da gaske. Har ya kasance a gefen Ka'aba kadai akwai gumaka guda dari uku da sittin, lallai Annabi (S.A.W) ya rurruguzasu a yayin daya ci garin Makka da yaki. Kuma akwai daga cikin wasu kabilun larabawa wasu bishiyoyi da duwatsu masu yawa da ake girmamawa kuma ake bawtawa koma bayan Allah (Mai girma da dawkaka).
Kuma yana daga cikin abubuwanda ake bawtawa koma bayan Allah: Kaburbura da wuraren bawtan shedanu da makabartu da bigirorin da ake bawtawa koma bayan Allah (Mai girma da dawkaka), ana yin dawafi agefen su da nufin neman kusanci zuwa garesu, ana yanka domin (bawta gare) su, kuma ana gabatar da bakance da dukiyoyi garesu, wasun ma akan samu masu kulawa dasu wadanda keyi musu hidima suna cin dukiyoyin Mutane bisa zalunci, kuma suna kangewa daga tafarkin Allah, kuma suna kawata musu shirka ga Allah (Mai girma da dawkaka) da rokon matattu da biyan bukata da tunkude bala'i.


Hakika Annabi (S.A.W) yace:
((اللهُمَّ لا تَجْعَلْ قَبْرِي وَثَنًا يُعْبَدُ)) رواه مَالِكٌ.
Ma'ana:"Ya Allah, kada Ka sanya kabarina yazama wani gunki abin bawta" Imamu Maliku ne ya ruwaitoshi.
Bama haka kawai ba, Annabi (S.A.W) yayi hani gameda rikon makabartu a matsayin masallatai, saboda kada wannan ya kaiga bawtan wadanda aka binne acikinsu. Daga Jundubu dan Abdullahi (Allah Ya kara masa yarda) yace lallai Annabi (S.A.W) yace:"
((إنَّ مَنْ كان قبلَكم كانوا يَتَّخِذُونَ قُبورَ أنبيائِهم وصَالحِيهم مَساجِدَ، ألا فلا تَتَّخِذوا القُبورَ مَسَاجِدَ، فإنِّي أنْهَاكُم عن ذلكَ)). رواه مُسلمٌ.
Ma;ana:" Lallai ne wadanad suka gabaceku sun kasance suna rikon kaburburan Annabawansu da salihan bayi a cikinsu a matsayin masallatai. Ku sawrara, kada ku riki kaburbura a matsayin masallatai" domin lallai ni ina haninku daga wannan" Imamu Muslim ne ya ruwaitosh.
Abu Ubaidah Amiru dan Jarrah (Allah Ya kara masa yarda) yace:"Ya kasance abu na karshe da Annabi (S.A.W) ya yifuruci dashi shine; a fitar da Yahudawan hijazi daga yankin larabawa, kuma ku sani cewa mafiya sharrin mutane sune wadanda ke rikon kaburbura a matsayin masallatai. Imamu Ahmad ne ya ruwaito shi.

Abin nufi da rikon makabarta a mastayin masallaci shine yin salla a kai ko fiskantanshi don yin salla ko gina masallaci akai. Duk wanda ya aikata daya daga cikin wadannan abubuwa ukun hakika ya fada cikin aikata abin ki.

Har wayaw yana daga cikin abubuwanda ake bawta koma bayan Allah: Abubuwanda ake sanyawa a matsayin alamu na shirka da bawtan wanin Allah (Mai girma da dawkaka) daga tambura da rataye rataye. Yazo acikin sunanu –ttirmidhy cewa Annabi (S.A.W) ya ga kuross (alamar gicciye) da akayi da zinari a wuyan Adiyu dan Hatim sai y ace masa:
((يا عَدِيُّ، اطْرَحْ عنكَ هذا الوَثَنَ)).
Ma'ana:"Ya kai Adiyu, ka yasar da wannan gunkin daga barin ka.
Abin nufi ananshine, lallai duk wani abu da ake bawtawa koma bayan Allah (Mai girma da dawkaka), to dagutu ne shi, sawa'un gunkineshi, ko kuma bishiyace ko kuma dutse ko kabari ko waninsu. Daga Abu Hurairata (Allah Ya kara masa yarda) yace lallai Annabi (S.A.W) yace:
((يَجمعُ اللهُ الناسَ يومَ القيامةِ، فيقولُ: مَن كانَ يَعْبُدُ شيئًا فلْيَتبعه؛ فيَتبعُ مَن كانَ يَعبدُ الشَّمسَ الشَّمسَ، ويَتبعُ مَن كان يَعْبُدُ القَمَرَ القَمَرَ، ويَتبعُ مَن كانَ يَعْبُدُ الطَّواغِيتَ الطَّوَاغيتَ)). مُتَّفق عليه.
Ma'ana:" Allah zai tara Mutane Ranar tashin Alkiyama, sannan sai Yace:" Wanda ya kasance yana bawtan wani abu to ya bishi, sai masu bawtan Rana subi Rana, masu bawtan Wata subi Wata, masu bawtan dagutai subi dagutai" Bukhari da Muslim na suka ruwaitoshi.
Kuma wannan bibiyan zai kasancene izuwa Wutar Jahannama Allah Yayi mana tsari. Kamar yadda Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿إِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ حَصَبُ جَهَنَّمَ أَنْتُمْ لَهَا وَارِدُونَ (98) لَوْ كَانَ هَؤُلَاءِ آلِهَةً مَا وَرَدُوهَا وَكُلٌّ فِيهَا خَالِدُونَ (99) لَهُمْ فِيهَا زَفِيرٌ وَهُمْ فِيهَا لَا يَسْمَعُونَ﴾ [الأنبياء: ٩٨–١٠٠].
Ma'ana:"Lallai ku da abubuwanda kuke bawtawa koma bayan Allah makamashine na Jahannama, ku masu shigantane (98) Da wadannan (abubuwan bawtan naku) sun kasance abubuwan bawtane nagaskiya, da basu shigetaba. Kuma dukkaninsu masu dawwamane acikinta (99) Suna da wata hargowa acikinta alhali kuwa su acikinta basu sawraren komai (100) Q21ayata98-100.
Kalmar hasabu (wacce tazo acikin ayar) tana nufin abinda ake jifa cikin wuta dashi.
Kuma wadannan ayoyin suna nunine izuwaga cewa wadannan gumakan bazasu amfani masu bawta musuba, a'a suma za'a jefasu cikin Wuta aranar tashin Alkiyama dasu da wadanda ke bawta musu koma bayan Allah (Mai girma da dawkaka) jefawa mai tsanani.
Amma wadanda aka bawtawa koma bayan Allah alhali basu yarda da wannan bwatar, to sukam ba dagutai bane. Kawai mushirikai ne suka rikeshi Allah abin bawta kuma dagutu suna wuce iyaka asakamakon kudurinsu agamedashi alhali shi yanamai barranta daga shirkansu da wuce iyakarsu. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿اتَّخَذُوا أَحْبَارَهُمْ وَرُهْبَانَهُمْ أَرْبَابًا مِنْ دُونِ اللَّهِ وَالْمَسِيحَ ابْنَ مَرْيَمَ وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا إِلَهًا وَاحِدًا لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ سُبْحَانَهُ عَمَّا يُشْرِكُونَ﴾ [التوبة: ٣١].
Ma'ana:" Sun riki malamansu (wato Yahudu) da masu yawan bawta daga cikinsu ababen bawta koma bayan Allah da Almasihu dan Maryam. Kuma ba'a musu umurniba face da su bawtawa Allah Shi kadai. Babu abin bawtawa da gaskiya sai Shi. Tsarki ya tabbata gareShi daga barin abinda suke yina shirka. Q9ayata31. Kuma Allah (Madawkakin Sarki) Yace:

﴿إِنَّ الَّذِينَ سَبَقَتْ لَهُمْ مِنَّا الْحُسْنَى أُولَئِكَ عَنْهَا مُبْعَدُونَ (101) لَا يَسْمَعُونَ حَسِيسَهَا وَهُمْ فِي مَا اشْتَهَتْ أَنْفُسُهُمْ خَالِدُونَ (102) لَا يَحْزُنُهُمُ الْفَزَعُ الْأَكْبَرُ وَتَتَلَقَّاهُمُ الْمَلَائِكَةُ هَذَا يَوْمُكُمُ الَّذِي كُنْتُمْ تُوعَدُونَ (103)﴾ [الأنبياء: ١٠١– ١٠٣].
Ma'ana:"Lallai wadanda Kalmar yabo ta gabata daga gareMu agamedasu wadannan duk wadanda ake nisantarwane daga barinta (wato Wuta) (101) Bazasuji sawtin motsintba. Alhali kuwa su masu dawwamane acikin abinda rayukansu ke shi'awa (102) Firgicinnan mai girma bazata bakanta musu raiba, kuma Mala'iku na saduwa dasu (suna musu marhaban suna cewa) wannan shine yininku wanda aka kasance ana muku alkawarinsa (103) Q21ayata101-103.
Hakananma waliyyai salihai wadanda wasu mushirikai suka bawta musu bias zalunci da karya, (suma) zasu barranta daga wannan shirkar. Amma wanda ya yarda da cewa abawtamasa koma bayan Allah (Madawkakin Sarki) ko kuma ya kirayi mutane zuwaga su bawta masa, to babu shakka cewa lallai shi yana daga cikin dagutai. Kamar yadda Fir'awna ya fadi ga mutanesa (Allah Madawkakin Sarki) Ya bamu labari:


﴿مَا عَلِمْتُ لَكُمْ مِنْ إِلَهٍ غَيْرِي﴾ [القصص: ٣٨].
Ma'ana:"Bansan wani abin bawta gareku ba face ni (inji Fir'awna). Q28ayata38.
Sinfi na uku: Wanda ke hukunci da sabanin abinda Allah Ya sawkar. Duk wanda ya kasance yana da wani matsayi na shugabanci akan mutane a wani gari daga cikin garuruwa, sannan ya kawar da kai daga barin yin hukunci da shari'ar Allah (Mai girma da dawkaka) acikinsu, kuma ya sanya musu wasu hukunce hukunce da yake gina hukunci akansu garesu daga abinda shi ya tsara wa kansa, saboda haka ya halatta musu abinda Allah Ya haramta kuma ya haramta musu abinda Allah Ya halatta, to shi dagutune yana son abawta masa koma bayan Allah (Mai girma da dawkaka) kuma bawtamasa shine yi masa biyayya cikin halatta haram da haramta halal.
Kuma dalili akan haka shine abinda ya inganta daga Adiyyu dan Hatim Adda'i (Allah Ya kara masa yarda) cewa ya ji Annabi (S.A.W) yana karanta fadin Allah (Madawkakin Sarki):
: ﴿اتَّخَذُوا أَحْبَارَهُمْ وَرُهْبَانَهُمْ أَرْبَابًا مِنْ دُونِ اللَّهِ﴾ [التوبة: ٣١].
Ma'ana:" Sun riki malamansu (wato Yahudu) da masu yawan bawta daga cikinsu ababen bawta koma bayan Allah" Q9ayata31.

(Adiyyu) yace lallai mu ba bawta musu mukeyiba. (Sai Annabi (S.A.W)) yace:
((أليسَ يُحَرِّمونَ ما أحَلَّ اللهُ فتُحَرِّمُونَه، ويُحِلُّونَ ما حَرَّمَ اللهُ فتَسْتَحِلُّونَه ؟))
Ma'ana:" Ashe basu kasance sukan halatta muku haram kuma ku dawkesh haramun ba? Kuma su haramta muku halal kuma ku dawkeshi haramun ba? (Adiyyu) yace: "nace ee (hakane).
(Sai Annabi (S.A.W)) yace:
((فتلكَ عِبادتُهم)). رواه البخاريُّ في التاريخِ الكبيرِ، والتِّرمذِيُّ والطَّبَرانِيُّ، واللفْظُ له.
Ma'ana:" To wannan shine bawta garesu" Imamul Bukharine ya ruwaitoshi acikin (littafinsa Attarikhul kabir) da Imamu-ttirmidhi da Imamu-ddabarani kuma wannan lafazin nasane.
Huzaifa dan Yaman yace:Ai lallai su bawai salla sukayi musu ba, sai dai sun kasance duk abinda suka halatta musu na haram saisu daukeshi halal, kuma duk abinda suka haramta musa daga halal saisu dawkeshi haram, to wannan shine dawkansu ubanningiji" Sa'idu binu Mansurne ya ruwaitoshi.
Yana daga cikin (misalan) dagutu bokaye da masu duba da masihirta, wadanda suke da'awar ilimin gaibu kuma jahilai batattu suke maida hukunci garesu. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:"
﴿أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ يَزْعُمُونَ أَنَّهُمْ آمَنُوا بِمَا أُنْزِلَ إِلَيْكَ وَمَا أُنْزِلَ مِنْ قَبْلِكَ يُرِيدُونَ أَنْ يَتَحَاكَمُوا إِلَى الطَّاغُوتِ وَقَدْ أُمِرُوا أَنْ يَكْفُرُوا بِهِ وَيُرِيدُ الشَّيْطَانُ أَنْ يُضِلَّهُمْ ضَلَالًا بَعِيدًا﴾ [النساء: ٦٠].
Ma'ana:"Shin (ya Muhammadu) baka yi dubi ba izuwa wadannan da suke riya cewa sunyi imani da abin da aka sawkar gareka da abinda aka sawkar gabaninka suna nufin su kai kara zuwaga dagutu, alhali an riga an umurcesu dasu kafirce musu, kuma Shedan yana nufin ya batar dasu batarwa mai nisa" Q4ayata60.
Kuma Annabi (S.A.W) yayi hani gameda zuwa wurin bokaye da masu duba da masihirta. Daga Abu Hurairata (Allah Ya kara masa yarda) daga Annabi (S.A.W) lallai yace:
((مَن أتَى كاهنًا أو عَرَّافًا فصَدَّقَهُ بما يقولُ، فقد كَفَرَ بما أُنْزِلَ على مُحمَّدٍ)). رواه الإمامُ أحمدُ من حديثِ أبي هُريرةَ رضِي الله عنه.
Ma'ana:"Duk wanda ya je wurin boka ko mai duba saiya gaskatashi gameda abinda yake fadi, to hakika ya kafirce da abinda aka sawkarwa Muhammadu" Imamu Ahmad ne ya ruwaitoshi daga hadisin Abu Huraira (Allah Ya kara masa yarda)
(Abdullahi) dan Mas'udu yace:" Duk wanda ya je wurin boka ko mai sihiri saiya gaskatashi gameda abinda yake fadi, to hakika ya kafirce da abinda aka sawkarwa Muhammadu" Imamul Bazzar ne ya ruwaitoshi.
Kuma kawda kai daga hukuncin Allah da (kin) maida hukunci zuwaga shri'arSa da neman hukuncin dagutai yana daga cikin ayyukan munafukai wadanda Allah Ya zargesu a cikin littafinSa mai girma. Allah (Madaukakin Sarki) Yace:
﴿وَيَقُولُونَ آَمَنَّا بِاللَّهِ وَبِالرَّسُولِ وَأَطَعْنَا ثُمَّ يَتَوَلَّى فَرِيقٌ مِنْهُمْ مِنْ بَعْدِ ذَلِكَ وَمَا أُولَئِكَ بِالْمُؤْمِنِينَ (47) وَإِذَا دُعُوا إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ لِيَحْكُمَ بَيْنَهُمْ إِذَا فَرِيقٌ مِنْهُمْ مُعْرِضُونَ (48) وَإِنْ يَكُنْ لَهُمُ الْحَقُّ يَأْتُوا إِلَيْهِ مُذْعِنِينَ (49) أَفِي قُلُوبِهِمْ مَرَضٌ أَمِ ارْتَابُوا أَمْ يَخَافُونَ أَنْ يَحِيفَ اللَّهُ عَلَيْهِمْ وَرَسُولُهُ بَلْ أُولَئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ (50) إِنَّمَا كَانَ قَوْلَ الْمُؤْمِنِينَ إِذَا دُعُوا إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ لِيَحْكُمَ بَيْنَهُمْ أَنْ يَقُولُوا سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا وَأُولَئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ (51) وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَيَخْشَ اللَّهَ وَيَتَّقْهِ فَأُولَئِكَ هُمُ الْفَائِزُونَ (52)﴾ [النور: ٤٧–٥٢].
Ma'ana:"Kuma suna cewa munyi imani da Allah kuma (munyi imani) da Manzon (Allah) kuma munyi biyayya sannan sai wata jama'a daga cikinsu ta juya baya abayan haka. Wadannan ba muminai bane (47) Kuma idan aka kirasu zuwaga Allah da manzonSa domin suyi hukunci a tsakaninsu, sai kaga wata jama'a daga cikinsu tana mai bijirewa (48) Kuma idan hakki ya kasance agaresune, zasuje masa suna masu mika wuya (49) Shin acikin zukatansu akwai cutace ko kuwa dai suna shakkane ko kuwa suna tsoron kada Allah Ya zaluncesune da Manzonsa? A'a wadancan sune azzalumai (50) Maganar muminai idan aka kirasu zuwaga Allah da ManzonSa domin suyi hukunci atsakaninsu, ta kasance kawai suce "munji kuma muyi biyayya. Kuma wadannan sune masu cin nasara(51) Kuma wanda yayi biyayya ga Allah da ManzonSa, kuma ya ji tsoron Allah, ya kuma ya biShi da takawa, to wadannan sune masu rabawta (52) Q24ayata 47-52.

فصل: وكلُّ مَن اتَّبَعَ الطاغوتَ فإنما يَزِيدُه اتِّباعُه له ضَلالاً وخَسارًا وظُلْمةً، وأما مَن كَفَر بالطاغوتِ وآمَن باللهِ واتَّبَعَ هُداه فإنَّ اللهَ تعالى يُخرِجُه من الظُّلماتِ إلى النورِ، ويهديهِ سُبلَ السلامِ، ويُدْخِلُه في رحمتِه وفَضْلِه، قال الله تعالى:
Fasali: Kuma duk wanda ya bi daguta, to biyayyarsa gareshi bazata kara masa komai ba face bata da hasara da duhu, amma (shiko) wanda ya kafirce wa dagutu kuma yayi imani da Allah ya kuma bi shiriyarSa, to lallai Allah (Madawkakin Sarki) zai fiddashi daga duffai zuwa ga haske, kuma Ya shiryar dashi izuwaga tafarkin aminci ya kuma shigar dashi cikin RahamarSa da FalalarSa. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿اللَّهُ وَلِيُّ الَّذِينَ آمَنُوا يُخْرِجُهُمْ مِنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ وَالَّذِينَ كَفَرُوا أَوْلِيَاؤُهُمُ الطَّاغُوتُ يُخْرِجُونَهُمْ مِنَ النُّورِ إِلَى الظُّلُمَاتِ أُولَئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ﴾ [البقرة: ٢٥٧].
Ma'ana:"Allah Shine majibincin wadanda sukayi imani, Yana fitar dasu daga duffai zuwa ga haske. Wadanda suka kafirta kuwa, masoyansu sune dagutu suna fiddasu daga haske zuwa duffai. Wadannan sune ma'abuta Wuta, su masu dawwamane acikinta" Q2ayata257.
Wadannan dagutan suna jefa masoyansu cikn duffan shirka da jahilci da bata da rudani da shakka da kuntatacciyar rayuwa da mummunan yanayi a cikin rayuwar (Duniya) da makoma. Muna rokon Allah aminci da afuwa.

Amma su masu imani da Allah, to Allah (Madawkakin Sarki) Shine majibincinsu wanda ke ciresu daga duffai zuwa haske, sai Ya fiddasu daga duhun shirka zuwa hasken tawhidi, daga kaskancin sabo zuwa izzar da'a, daga bacebacen bidi'o'i zuwa ta farkin sunna, daga rudanin shakka zuwa sanyi na yakini, ya fiddasu daga kunci da mawuyacin hali zuwa yalwa da walwala, daga bakin ciki da tsoro da tashin hankali zuwa nutsuwa da aminci da kwanciyar hankali. Kuma Allah Yana kara shiriya ga wadanda suka shiriya saboda haka su akullum suna cikin karuwane na alkhairi da shiriya, darajarsu tana kara dawkaka kuma ladaddakinsu na ninninkuwa.
﴿ذَلِكَ فَضْلُ اللَّهِ يُؤْتِيهِ مَنْ يَشَاءُ وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ﴾ [الجمعة: ٤].
Wannan falalar Allahce Yana bada ita ga wanda Yaso, Kuma Allah ma'abucin falalane maigirma. Q62ayata4.