المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : الدرسُ الخامسُ: بيانُ معنَى دينِ الإسلامِ


عبد الله الداخل
_21 _March _2013هـ الموافق 21-03-2013م, 11:19 PM
الدرسُ الخامسُ: بيانُ معنَى دينِ الإسلامِ


قال اللهُ تعالى: ﴿إِنَّ الدِّينَ عِنْدَ اللَّهِ الْإِسْلَامُ﴾ [آل عمران: 19].
وقال تعالى:﴿وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الْآَخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ (85)﴾ [آل عمران: 85].
وقال تعالى: ﴿فَإِلَهُكُمْ إِلَهٌ وَاحِدٌ فَلَهُ أَسْلِمُوا وَبَشِّرِ الْمُخْبِتِينَ﴾ [الحج: 34].
وقال تعالى: ﴿وَقُلْ لِلَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ وَالْأُمِّيِّينَ أَأَسْلَمْتُمْ فَإِنْ أَسْلَمُوا فَقَدِ اهْتَدَوْا وَإِنْ تَوَلَّوْا فَإِنَّمَا عَلَيْكَ الْبَلَاغُ وَاللَّهُ بَصِيرٌ بِالْعِبَادِ﴾ [آل عمران: 20].
وقال تعالى: ﴿وَمَنْ أَحْسَنُ دِينًا مِمَّنْ أَسْلَمَ وَجْهَهُ لِلَّهِ وَهُوَ مُحْسِنٌ﴾ [النساء: 125].

والإسلامُ معناه: إخلاصُ الدينِ للهِ عز وجل والانقيادُ لأوامرِه وأحكامِه.
وهو عقيدةٌ وشَريعةٌ؛ فالعقيدةُ مَبْناها على العلمِ الصحيحِ، والشريعةُ أحكامٌ يَجِبُ على العبدِ امتثالُها.
قال اللهُ تعالى: ﴿وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ وَذَلِكَ دِينُ الْقَيِّمَةِ﴾ [البينة: 5].
فلا يكونُ العبدُ مُسلمًا حتى يَجْمَعَ أمرين:
الأمر الأول: إخلاص الدينِ للهِ عز وجل؛ فيُوَحِّدُ اللهَ ويَجْتَنِبُ الشِّركَ.
الأمر الثاني: الانقياد للهِ تعالى، بامتثالِ أوامرِه واجتنابِ نَواهيهِ.
فمَن وحَّد اللهَ وانقادَ لأوامرِه فهو مُسْلِمٌ.
وبهذا تَعْرِفُ أن المُشْرِكَ غيرُ مسلمٍ؛ لأنه لم يُخْلِصِ الدينَ للهِ عز وجل.
والمُسْتكبِرُ عن عبادةِ اللهِ غيرُ مُسلمٍ؛ لأنه مُمْتنِعٌ غيرُ مُنقادٍ لأوامرِ اللهِ جل وعلا.
قال اللهُ تعالى: ﴿لَنْ يَسْتَنْكِفَ الْمَسِيحُ أَنْ يَكُونَ عَبْدًا لِلَّهِ وَلَا الْمَلَائِكَةُ الْمُقَرَّبُونَ وَمَنْ يَسْتَنْكِفْ عَنْ عِبَادَتِهِ وَيَسْتَكْبِرْ فَسَيَحْشُرُهُمْ إِلَيْهِ جَمِيعًا (172) فَأَمَّا الَّذِينَ آَمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَيُوَفِّيهِمْ أُجُورَهُمْ وَيَزِيدُهُمْ مِنْ فَضْلِهِ وَأَمَّا الَّذِينَ اسْتَنْكَفُوا وَاسْتَكْبَرُوا فَيُعَذِّبُهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا وَلَا يَجِدُونَ لَهُمْ مِنْ دُونِ اللَّهِ وَلِيًّا وَلَا نَصِيرًا (173)﴾[النساء: 172–173].
فصل: والمسلمون يتفاضلون في حسن إسلامِهم بتفاضُلِهم في الإخلاصِ، وحُسنِ الانقيادِ، فهُم على مراتبِ الدين الثلاثةِ التي بَيَّنَها النبيُّ صلَّى الله عَليهِ وَسلَّم كَمَا فِي حديثِ جبريلَ الطويلِ، وهي:
1: مَرْتبةُ الإسلامِ.
2: مَرْتبةُ الإيمانِ.
3: مَرْتبةُ الإحسانِ.
وأفضلُ هذه المَراتبِ مَرْتبةُ الإحسانِ، ثم مَرْتبةُ الإيمانِ، ثم مَرْتبةُ الإسلامِ.
فكلُّ مُؤمِنٍ مُسلمٌ، وليسَ كلُّ مسلمٍ مُؤمِنًا.
وأركانُ الإسلامِ خمسةٌ كما في الصحيحين من حديثِ عبدِ اللهِ بنِ عُمَر رضِي الله عنهما عن النبيِّ صلى الله عليه وسلم أنه قال: ((بُنِي الإسلامُ على خَمْسٍ: شهادةِ أن لا إلهَ إلا اللهُ وأن مُحمَّدًا رسولُ اللهِ، وإقامِ الصلاةِ، وإيتاءِ الزكاةِ، وحَجِّ البيتِ، وصَوْمِ رَمَضانَ)).
وقال النبيُّ صلى الله عليه وسلم: ((رأسُ الأمرِ الإسلامُ، وعَمُودُهُ الصلاةُ، وذِرْوةُ سَنامِه الجِهادُ في سبيلِ اللهِ)) رواه أحمد من حديث مُعاذِ بن جَبَلٍ رضِي الله عنه.

فصل: والمؤمنون يَتفاضلون في إيمانِهم فبعضُهم أكثرُ إيمانًا من بَعْضٍ؛ لأنَّ الإيمانَ تصديقٌ بالقَلْبِ، وقولٌ باللسانِ، وعَمَلٌ بالجوارحِ، يَزِيدُ ويَنْقُصُ.
وكلما كانَ العبدُ أعْظَمَ تصديقًا وأحْسَنَ قَوْلاً وعَمَلاً كان إيمانُه أعظمَ.
وإذا فَعَل العبدُ المَعْصيةَ نقَصَ من إيمانِه؛ فإذا تابَ وأصْلَحَ تابَ اللهُ عليه.
واستكمالُ الإيمانِ وَصَفَه النبيُّ صلى الله عليه وسلم بقولِه: ((مَن أحَبَّ للهِ، وأبْغَضَ للهِ، وأعْطَى للهِ، ومَنَعَ للهِ، فقَدِ اسْتَكْمَلَ الإيمانَ)). رواه أبو دَاوُدَ وغيرُه من حديثِ أبي أُمامة البَاهِلِيِّ رضِي الله عنه.
والحُبُّ للهِ أعمُّ من الحُبِّ في اللهِ، فهو يَشْمَلُ مَحَبَّةَ كلِّ ما يُحَبُّ لله جل وعلا من الأشخاصِ والأعمالِ والأقوالِ والأحوالِ والمقاصدِ والأخلاقِ والأَمْكِنَةِ والأزمنةِ وغيرِها.
وكذلك العطاءُ للهِ أعمُّ من أن يكونَ المرادُ به عطاءَ المالِ، بل هو شامِلٌ لكلِّ ما يُعْطَى من مالٍ وَجَاهٍ وعِلْمٍ وجُهْدٍ ووَقْتٍ، وكذلك المَنْعُ.
فمَن كان حُبُّه للهِ، وبُغْضُه للهِ، وعطاؤُه للهِ، ومَنْعُه للهِ، فهو مُؤْمِنٌ مُستكمِلُ الإيمانِ؛ نسألُ اللهَ تعالى من فِضْلِه.

فصل: وأُصولُ الإيمانِ سِتَّةٌ، بَيَّنَها النبيُّ صلى الله عليه وسلم بقولِه: ((الإيمانُ أن تُؤْمِنَ باللهِ وملائكتِه وكُتُبِه ورُسلِه واليَوْمِ الآخِرِ وتُؤْمِنَ بالقَدَرِ خَيْرِه وشَرِّهِ)).
وهذه الأصولُ يَجِبُ على كلِّ مسلمٍ الإيمانُ بها، ومَن كَفَر بأصْلٍ منها فهو كافرٌ غيرُ مُسلمٍ.
والإيمانُ له شُعَبٌ تَتَفَرَّعُ عن هذه الأصولِ كما تَتَفَرَّعُ الأغصانُ من الشَّجَرة، وكلما كانَ العَبْدُ أكثرَ أخْذًا بخِصالِ الإيمانِ وأعمالِه كانَ أكثرَ إيمانًا؛ فعن أبي هُريرةَ رضِي الله عنه أن النبيَّ صلى الله عليه وسلم قال: ((الإيمانُ بِضْعٌ وَسَبْعُونَ أَوْ بِضْعٌ وَسِتُّونَ شُعْبَةً، فَأَفْضَلُهَا قَوْلُ لا إِلَهَ إِلا اللهُ، وَأَدْنَاهَا إِمَاطَةُ الأَذَى عَن الطَّرِيقِ، وَالْحَيَاءُ شُعْبَةٌ مِن الإِيمَانِ)) رواه مسلم.
فشُعَبُ الإيمانِ هي خِصالُه وأجزاؤُه، ومنها قلبيٌّ وقوليٌّ وعمليٌّ، وقد مثَّل النبيُّ صلى الله عليه وسلم لكلِّ نوعٍ بمثالٍ: فقولُ (لا إلهَ إلا اللهُ) قولٌ باللسانِ، وإماطةُ الأذى عَمَلٌ، والحياءُ عَمَلٌ قَلْبِيٌّ.
وقد يَجْمَعُ العَبْدُ شُعَبًا من الإيمانِ وشُعَبًا من النِّفاقِ فيَكونُ فيه بَعْضُ خِصالِ النِّفاقِ حتى يَدَعَها، كما قال النبيُّ صلى الله عليه وسلم: ((أرْبَعٌ مَن كُنَّ فيه كانَ مُنافِقًا خَالِصًا، ومَن كانتْ فيه خَصْلَةٌ منهنَّ كانت فيه خَصْلَةٌ من النِّفاقِ حتى يَدَعَها؛ إذا اؤتُمِنَ خانَ، وإذا حدَّث كَذَب، وإذا عاهَدَ غَدَر، وإذا خاصَمَ فَجَرَ)). متفق عليه.

فصل: والإحسانُ بيَّنه النبيُّ صلى الله عليه وسلم بقولِه: ((الإحسانُ أن تَعْبُدَ اللهَ كأنَّكَ تَرَاهُ، فإنْ لم تَكُنْ تَرَاهُ فإنَّه يَرَاكَ)).
وقد خَلَقَنَا اللهُ تعالى ليَبْلُوَنا أيُّنَا أحْسَنُ عَمَلاً؛ وقد أخبرنا الله تعالى أن من مقاصد خلقه إيانا أن يبلونا أينا أحسن عملا كما قال تعالى: ﴿وَهُوَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ وَكَانَ عَرْشُهُ عَلَى الْمَاءِ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلاً﴾ [هود: 7].
وقال تعالى:﴿الَّذِي خَلَقَ الْمَوْتَ وَالْحَيَاةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلاً وَهُوَ الْعَزِيزُ الْغَفُورُ﴾ [الملك: 2]، قال فُضَيْلُ بنُ عِيَاضٍ: (﴿أَحْسَنُ عَمَلاً﴾ أي أخلصه وأصوبه).
فالعَمَلُ لا يَكونُ حَسَنًا حتى يَكُونَ خَالِصًا للهِ تعالى، وصَوَابًا على سُنَّةِ رسولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم.
واتِّباعُ هَدْيِ النبيِّ صلى الله عليه وسلم يَعْصِمُ العَبْدَ من الغُلُوِّ والتفريطِ.
وبهذا تَعْلَمُ أنَّ من نواقضِ الإحسانِ: الشِّرْكَ والبِدْعَةَ والغُلُوَّ والتفريطَ.
فالمُشْرِكُ مُسِيءٌ غَيْرُ مُحْسِنٍ، وكذلك المُبْتَدِعُ والغَالي والمُفَرِّطُ.

والإحسانُ على دَرَجتينِ:
الإحسانُ الوَاجِبُ: وهو أداءُ العِباداتِ الوَاجِبَةِ بإخلاصٍ ومتابعةٍ بلا غُلُوٍّ ولا تَفْريطٍ.
والإحسانُ المُسْتَحَبُّ: وهو التَّقَرُّبُ إلى اللهِ تعالى بالنَّوافِلِ، وتَكْمِيلُ مستحَبَّاتِ العباداتِ وآدابِها، والتَّوَرُّعُ عن المُشْتَبِهاتِ والمَكْرُوهاتِ؛ فيَعْبُدُ اللهَ كأنه يَرَاهُ؛ فيَجْتَهِدُ في أداءِ العباداتِ على أحسنِ وُجوهِها بما يَتَيَسَّرُ له؛ فلا يُكَلِّفُ نفسَه ما لا يُطِيقُ، ولا يُفَرِّطُ بتَرْكِ ما يَتَيَسَّرُ له من العباداتِ التي تُقَرِّبُه إلى اللهِ تعالى.
والإحسانُ يَكونُ في كلِّ عِبادةٍ بحَسَبِها، ويَجْمَعُ ذلك: قُوَّةُ الإخلاصِ وَحُسْنُ اتِّباعِ هَدْيِ النبيِّ صلَّى الله عَليهِ وَسَلَّمَ فِي تلكَ العِبَادةِ:
● فإِحسانُ الوُضوءِ يَكونُ بإِسباغِه وتكميلِ فروضِه وآدابِه وعدمِ مُجاوَزَةِ الحَدِّ المَشْروعِ من الغَسَلاتِ.
● وإحسانُ الصلاةِ يكونُ بإقامتِها وأدائِها في أوَّلِ وَقْتِها بخُشوعٍ وطُمأنينةٍ وحُضورِ قَلْبٍ، ويُصَلِّيها صَلاةَ مُوَدِّعٍ، فيُكَمِّلُ فُروضَها وسُنَنَها كأنه يَرَى اللهَ عز وجل.
● وإحسانُ الزَّكَاةِ والصَّدقةِ أنْ يُؤدِّيَ ما يَتصدَّقُ به مُتقرِّبًا إلى اللهِ عز وجل يرجو رَحْمتَه ويَخْشَى عذابَه، لا يُريدُ مِمَّن أحْسَنَ إليه جَزاءً ولا شُكورًا، ولا يُتْبِعُ نفقتَه مَنًّا ولا أَذًى، ويَتحرَّى إخراجَ الطَّيِّبِ من المالِ، فلا يُخرِجُ رديئَهُ وما تَعافُه النَّفْسُ، ولا يَمْطُلُ بصدقتِه ولا يُعَسِّرُ على المُحتاجِ في أَخْذِها، ولا يَتعالَى عليه، ولا يُسَمِّعُ بنَفَقتِه ولا يُرائِي بها.
وهكذا في سائرِ العباداتِ والمُعاملاتِ؛ يَنْبغِي للعبدِ أن يَتحرَّى الإحسانَ فيها ما استطاعَ ويَتَّبِعَ هَدْيَ النبيِّ صلى الله عليه وسلم في ذلك.
ومَن تَحرَّى الإحسانَ وحَرَصَ عليه وسَأَلَ اللهَ تعالى الإعانةَ عليه رُجِيَ له أن يُوَفَّقَ للإحسانِ، قال أبو الدَّرْداءِ رضِي اللهُ عنه: (إِنَّمَا العِلْمُ بالتَّعلُّمِ والحِلْمُ بالتَّحلُّمِ، ومَن يَتَحَرَّ الخيرَ يُعْطَه، ومَن يَتَوقَّ الشَّرَّ يُوقَه).
وأبوابُ الإحسانِ كثيرةٌ، ففي صَحيحِ مُسلمٍ من حديثِ شَدَّادِ بنِ أَوْسِ بنِ ثابتٍ رضِي الله عنهما عن النبيِّ صلى الله عليه وسلم قال: ((إنَّ اللهَ كتَبَ الإحسانَ على كلِّ شيءٍ؛ فإذا قَتَلْتُم فأحسِنوا القِتْلةَ، وإذا ذَبَحْتُم فأَحْسِنوا الذِّبْحةَ، وَلْيُحِدَّ أحدُكُم شَفْرَتَهُ وَلْيُرِحْ ذَبيحَتَهُ)).
فالإحسانُ مكتوبٌ على كلِّ شيءٍ، وإحسانُ كلِّ شيءٍ بحَسَبِه، وقد بَيَّن النبيُّ صلى اللهُ عليه وسلم هنا الإحسانَ في الذَّبْحِ، فمَن خالَفَ هَدْيَه فلم يُحِدَّ السِّكِّينَ ولم يُرِحْ ذَبِيحَتَهُ فليسَ بمُحْسِنٍ في ذَبْحِه.
وهذا مِمَّا يُبيِّنُ أهَمِّيَّةَ الفِقْهِ في الدينِ، فبه يَعْرِفُ طالبُ الإحسانِ هَدْيَ النبيِّ صلى الله عليه وسلم في العِباداتِ والمُعاملاتِ؛ فيَعْرِفُ هَدْيَهُ في الوُضوءِ والصَّلاةِ والصدقةِ والصيامِ والحجِّ والجهادِ والبُيوعِ والطَّعامِ والشَّرابِ والنَّوْمِ والنِّكَاحِ والمُعاشَرَةِ والبِرِّ والصِّلَةِ ومُعاملةِ الناسِ على اختلافِ أصنافِهم، وهكذا في سائرِ الأمورِ.
ولا يُدرِكُ العبدُ مَرْتبةَ الإحسانِ إلا بإعانةِ اللهِ وتَوْفيقِه، ولذلك شُرِعَ للعبدِ أن يَدْعُوَ دُبُرَ كلِّ صَلاةٍ: ((اللهمَّ أعنِّي على ذِكْرِكَ وشُكرِكَ وحُسنِ عِبادتِكَ)).
فحاجةُ العبدِ إلى إعانةِ اللهِ تعالى له على الإحسانِ دائمةٌ مُتكرِّرةٌ.

طاهر جبريل دكو
_12 _April _2013هـ الموافق 12-04-2013م, 05:18 PM
Darasina biyar: Bayani gameda ma’anar Addinin musulunci.
Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿إِنَّ الدِّينَ عِنْدَ اللَّهِ الْإِسْلَامُ﴾ [آل عمران: ١٩].
Ma’ana:”Laallaa’i addini a wurin Allah shine Musulunci. Q3ayata19.
Kuma Madawkakin Sarki Yace:
﴿وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الْآَخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ (85)﴾ [آل عمران: ٨٥].
Ma’ana:”Duk wanda ya nemi wanin (Addinin) Musulunci ya zamo masa addini, to baza’a taba karba daga gareshiba, kuma shi a ranar karshe yana cikin masu hasara. Q3ayata85.
Kuma madawkakin Sarki Yace:
﴿فَإِلَهُكُمْ إِلَهٌ وَاحِدٌ فَلَهُ أَسْلِمُوا وَبَشِّرِ الْمُخْبِتِينَ﴾ [الحج: ٣٤].
Ma’ana:”Kuma Abin bawtanku abin bawtane guda daya, saboda haka gareShi zaku mika wuya, kuma kayi bushara ga masu Kankan da kai. Q22ayata34.
Kuma Madawkakin Sarki Yace:
﴿وَقُلْ لِلَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ وَالْأُمِّيِّينَ أَأَسْلَمْتُمْ فَإِنْ أَسْلَمُوا فَقَدِ اهْتَدَوْا وَإِنْ تَوَلَّوْا فَإِنَّمَا عَلَيْكَ الْبَلَاغُ وَاللَّهُ بَصِيرٌ بِالْعِبَادِ﴾ [آل عمران: ٢٠].
Ma’ana:” Kuma kace wa wadanda aka baiwa littafi da Ummiyai (wadanda basu iya karatu da rubutu ba) “shin kun sallama? To idan sun sallama hakika sun shiriya, kuma idan sun juya baya, to, kawai abinda ke kanka shine isarwa. Kuma Allah Mai ganine ga bayinSa. Q3ayata20.
Kuma Madawkakin Sarki Yace:
﴿وَمَنْ أَحْسَنُ دِينًا مِمَّنْ أَسْلَمَ وَجْهَهُ لِلَّهِ وَهُوَ مُحْسِنٌ﴾ [النساء: ١٢٥].
Ma’ana:”Kuma wanene yafi kyaw ga addini samada wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhali kuwa yana mai kyawtatawa. Q4ayata125.
Kuma shi musulunci ma’anarsa shine, tasrkake addini ga Allah (Mai girma da dawkaka) da kuma da’a ga Allah cikin abubuwanda Yayi umurni dasu da hukunce hukuncenSa.
Kuma shi (Musulunci) akidane kuma shari’ace wanda ya ginu akan ingantaccen ilimi. Shari’a kuwa hukunce hukuncene wanda ya wajaba ga bawa ya aiwatar dasu.
Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ وَذَلِكَ دِينُ الْقَيِّمَةِ﴾ [البينة: ٥].
Ma’ana:”Kuma ba’a umurcesuba face su tsarkake addini ga Allah suna masu karkata zuwa ga gaskiya kuma su tsaida salla kuma su bada zakka. Wannan shine addinin wadanda suke kan hanyar kwarai. Q98ayata5.
Saboda haka bawa bazai zama musulmi ba har sai ya tara al’amura biyu:
Al’amarina farko: Tsarkake addini ga Allah (Mai girma da dawkaka) wato ya kadaita Allah kuma ya nisanci shirka.
Al’amarina biyu: Shine sallamawa ga Allah (Madawkakin Sarki) ta hanyar aiwatar da abubuwanda Yayi umurni dasu da nisantan abubuwanda Yayi hani.
Saboda haka duk wanda ya kadaita Allah kuma ya sakankance gareShi ya bi umurninSa, to shi Musulmine.
Kuma da wannan ne zaka fahimci cewa lallai mushiriki ba musulmi bane, saboda bai tsarkake addini ga Allah (Mai girma da dawkakaba)
Kuma mai girman kai ga barin bawtan Allah shima ba Musulmi bane, saboda shi kangararrene ba mai sallamawaba ga abubuwanda Allah (Mai girma da dawkaka) Yayi umurni dasu.
Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿لَنْ يَسْتَنْكِفَ الْمَسِيحُ أَنْ يَكُونَ عَبْدًا لِلَّهِ وَلَا الْمَلَائِكَةُ الْمُقَرَّبُونَ وَمَنْ يَسْتَنْكِفْ عَنْ عِبَادَتِهِ وَيَسْتَكْبِرْ فَسَيَحْشُرُهُمْ إِلَيْهِ جَمِيعًا (172) فَأَمَّا الَّذِينَ آَمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَيُوَفِّيهِمْ أُجُورَهُمْ وَيَزِيدُهُمْ مِنْ فَضْلِهِ وَأَمَّا الَّذِينَ اسْتَنْكَفُوا وَاسْتَكْبَرُوا فَيُعَذِّبُهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا وَلَا يَجِدُونَ لَهُمْ مِنْ دُونِ اللَّهِ وَلِيًّا وَلَا نَصِيرًا (173)﴾[النساء: ١٧٢–١٧٣].
Ma’ana:”Almasihu baya (taba) kyaman yazamo bawa ga Allah, kuma haka Mala’ikun nan makusanta. Kuma wanda yayi kyamar bawtarSa kuma yayi girman kai, to da sannu (Allah)zai tarasu gareShi baki daya (172) To, wadanda sukayi imani kuma suka yi ayyukan kwarai, to (Allah) zai cika musu ladaddakinsu kuma Ya kara musu daga falalarSa. Amma wadanda sukayi kyama kuma sukayi girman kai, to zai musu azaba mai radadi, kuma basu samun wani masoyi garesu ko mataimaki koma bayan Allah(173) Q4ayata172-173.
Fasali:Kuma musulmai suna da fifiko a tsakaninsu gameda kyawtatuwan musuluncinsu gwargwadon fifikon da ke tsakaninsu acikin sakankancewa da biyayya (ga Allah) saboda haka suna martabobine guda uku na addini wadanda Annabi (S.A.W) yayi bayaninsu kamar yadda yazo a cikin hadisin Jibril mai tsayinnan, sune:
Martaba ta farko: Muaulunci.
Martaba ta biyu: Imani.
Martaba ta uku: Ihisani.
Kuma mafi falala cikin wadannan martabobin (shine) Ihisani, sannan Imani, sannan Musulunci.
Saboda haka dukkan mumini musulmine amma ba dukkan musulmine muminiba.
Kuma rukunnan musulunci biyarne kamar yadda yazo acikin Bukhari da Muslim daga hadisin Abdullahi dan Umar (Allah Ya kara musu yarda) daga Annabi (S.A.W) cewa lallai yace:
((بُنِي الإسلامُ على خَمْسٍ: شهادةِ أن لا إلهَ إلا اللهُ وأن مُحمَّدًا رسولُ اللهِ، وإقامِ الصلاةِ، وإيتاءِ الزكاةِ، وحَجِّ البيتِ، وصَوْمِ رَمَضانَ)).
Ma’ana:” An gina Musulunci akan abubuwa biyarne, shaidawa babu abin bawtawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammadu Manzon Allahne, da tsaida salla da bada zakka da ziyartan dakin (Ka’aba) da azumtan watan ramadana”
Kuma Annabi (S.A.W) yace:
((رأسُ الأمرِ الإسلامُ، وعَمُودُهُ الصلاةُ، وذِرْوةُ سَنامِه الجِهادُ في سبيلِ اللهِ)) رواه أحمد من حديث مُعاذِ بن جَبَلٍ رضِي الله عنه.
Ma’ana:” Kan al’amarin shine Musulunci, gimshikinsa kuwa shine salla, tsololuwar tozonsa kuma shine yin jihadi don dawkaka Kalmar Allah” Imamu Ahmad ne ya ruwaitoshi daga hadisin Mu’azu dan Jabal (AllahYa kara masa yarda)
Fasali: Kuma muminai suna da fifiko a tsakaninsu game da imaninsu, domin wasunsu sunfi wasu yawan imani. Saboda shi imani gaskatawane da zuciya, da Magana da harce da aiki da gabbai, yana karuwa kuma yana raguwa.
Duk sa’adda bawa ya kasance mai yawan gaskatawa, mafi kyawun Magana, da aiki, imaninsa zai kasance mafi girma.
Idan bawa ya aikata wani aikin sabo sai wani (sashi na) imaninsa ya ragu. Amma idan ya tuba ya gyara sai Allah Ya karbi tubansa. Kuma Annabi (S.A.W)ya sifanta kammaluwar imani da fadinsa:
((مَن أحَبَّ للهِ، وأبْغَضَ للهِ، وأعْطَى للهِ، ومَنَعَ للهِ، فقَدِ اسْتَكْمَلَ الإيمانَ)). رواه أبو دَاوُدَ وغيرُه من حديثِ أبي أُمامة البَاهِلِيِّ رضِي الله عنه.
Ma’ana:”Duk wanda yayi soyayya saboda Allah, kuma ya yi kiyayya saboda Allah kuma ya bayar saboda saboda Allah, ya hana saboda Allah, to hakika ya samu kamaluwar imani” Abu Dawuda da waninsane suka ruwaitoshi daga hadisin Abu Umama Albahili.
Kuma shi so don Allah ya fi fadi sama da so ckin son Allah. Saboda haka shi (so don Allah) ya kunshi kawnar duk abinda ake kawna saboda Allah (Mai girma da dawkaka) daga mutane da ayyuka da maganganu da halaye da manufofi dabi’u da wurare da lokuta da sawransu.
Kuma hakananma bayarwa saboda Allah ya wuce ace shine kawai kyawtar dukiya. A’a ya kunshi dukkanin abinda ake bayarwa na dukiya da martaba da ilimi da kokari da lokaci, to hakananma hanawa.
Saboda haka duk wanda kawnarsa ta kasance saboda Allah, kiyayyarsa saboda Allah, bayarwarsa saboda Allah, hanawarsa saboda Allah, to shi muminine mai cikakken imani, muna rokon Allah falalarSa.
Fasali: rukunnan imani guda shidane, Annabi (S.A.W)yayi bayanin su acikin fadinsa:
((الإيمانُ أن تُؤْمِنَ باللهِ وملائكتِه وكُتُبِه ورُسلِه واليَوْمِ الآخِرِ وتُؤْمِنَ بالقَدَرِ خَيْرِه وشَرِّهِ)).
Ma’ana:”Imani shine kayi imani da Allah, da Mala’ikunSa da LittattafanSa da ManzanninSa da ranar karshe, kuma kayi imani da kaddara ta alheri da ta sharri”
Kuma wadannan rukunnan ya wajaba ga kowani Musulmi yayi imani dasu, duk ko wanda ya kafirce da rukuni daya daga cikinsu, to shi kafirine ba musulmi ba.
Kuma shi imani yanada rassa da suke rarrabuwa daga wadannan rukunnan kamar yadda rassan (bishiya) ke rarrabuwa daga bishiyar. Saboda haka gwargwadon rikon bawa ga dabi’un imani da ayyukansa, gwargwadon yawan imaninsa.
Daga Abuhuraira (Allah Ya kara masa yarda) yace; lallai Annabi (S.A.W)yace:
((الإيمانُ بِضْعٌ وَسَبْعُونَ أَوْ بِضْعٌ وَسِتُّونَ شُعْبَةً، فَأَفْضَلُهَا قَوْلُ لا إِلَهَ إِلا اللهُ، وَأَدْنَاهَا إِمَاطَةُ الأَذَى عَن الطَّرِيقِ، وَالْحَيَاءُ شُعْبَةٌ مِن الإِيمَانِ)) رواه مسلم.
Ma’ana:”Imani (yanada) rassa saba’in da wani abu, mafi falala daga cikinsu, shine fadin Laa’ilaaha-illa-llahu, mafi kankantan cikinsu kuma shine kawarda abu mai cutarwa daga kan hanya, kunyama wani reshene daga (rassan) imani” Imamu Muslimne ya ruwaitoshi.
Saboda haka su rassan imani sune dabi’unsa da sassansa, kuma daga cikinsu akwai aikin zuciya, da furucin baka, da aikin gabbai. Hakika Annabi (S.A.W) ya buga misali daya ga kowane daga cikinsu. Fadin Laa’ilaaha-illa-llahu furcine na harce, kawar da abu mai cutarwa daga hanya aikine na gabbai, kunya kuwa aikine na zuciya.
Yana yiwuwa bawa ya hada rassa daga rassan imani da (wasu) rassa daga rassan munafurci, sai ya kasance akwai wasu dabi’u na munafurci a taredashi har sai ya rabudasu, kamar yadda Annabi (S.A.W)yace:
((أرْبَعٌ مَن كُنَّ فيه كانَ مُنافِقًا خَالِصًا، ومَن كانتْ فيه خَصْلَةٌ منهنَّ كانت فيه خَصْلَةٌ من النِّفاقِ حتى يَدَعَها؛ إذا اؤتُمِنَ خانَ، وإذا حدَّث كَذَب، وإذا عاهَدَ غَدَر، وإذا خاصَمَ فَجَرَ)). متفق عليه.
Ma’ana:”Dabi’u guda hudu duk wanda suka kasance taredashi, ya kasance cikakken munafuki. Duk wanda kuma yakeda wani sashi daga cikinsu, to yana da wata dabi’a ta munafurci ataredashi har sai ya barta. Idan aka amince dashi sai yayi ha’inci, idan yayi zance sai yayi karya, idan akayi yarjejeniya dashi sai yayi yawdara, idan kuma akayi husuma dashi sai yayi fajirci. Bukhari da Muslimne suka ruwaitoshi.
Fasali: Shi Ihisani Annabi (S.A.W) yayi bayaninsa da fadinsa:
((الإحسانُ أن تَعْبُدَ اللهَ كأنَّكَ تَرَاهُ، فإنْ لم تَكُنْ تَرَاهُ فإنَّه يَرَاكَ)).
Ma’ana:”Ihisani (wato kyawtatawa) shine; ka bawtawa Allah kamar kana ganinSa, duk da cewa kai baka ganinSa, to fa Shi Yana ganinka.
Hakika Allah (Madawkakin Sarki)Ya haliccemune domin Ya jarrabemu, wanene daga cikinmu zaifi kyawtata ayyuka? Kamar yadda Madawkakin Sarki Yace:
﴿وَهُوَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ وَكَانَ عَرْشُهُ عَلَى الْمَاءِ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلاً﴾ [هود: ٧].
Ma’ana:”Shine wanda ya halicci sammai da kasa cikin kwanaki shida alhali al’arshinSa ya kasance a kan ruwa domin Ya jarrabeku, wai shin wanene yafi kyawun aiki” Q11ayata7. Kuma madawkakin Sarki Yace:
:﴿الَّذِي خَلَقَ الْمَوْتَ وَالْحَيَاةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلاً وَهُوَ الْعَزِيزُ الْغَفُورُ﴾ [الملك: ٢]،
Ma’ana:”Shine wanda Ya halicci mutuwa da rayuwa domin Ya jarrabeku wanene daga cikinku zaifi kyawtatawa cikin aiki?” Q67ayata2.
Fudailu bin Iyad yace: (abin nufi da) kyakkyawan aiki shine wanda ikhilasi yafi yawa acikinsa kuma wanda yafi zama daidai, shi aiki baya zama mai kyaw har sai anyishi saboda Allah (Madawkakin Sarki) kuma daidai bisa sunnar Manzon Allah (S.A.W).
Kuma bin tafarkin Annabi (S.A.W) yana kubutarda bawa daga wuce iyaka da sakaci.
Da wannanne zaka san cewa, daga cikin abubuwa masu warware ihisani, akwai, shirka, bidi’a,wuce gonada iri da sakaci
Saboda haka shi mushiriki mai munanawane ba mai kyawtatawaba, hakananma dan bidi’a da mai wuce iyaka da mai sakaci.
Kuma ihisani darajojine guda biyu:
Ihisani na wajibi, wanda shine, yin ayyukan bawta na wajibi bisa tsarkin niyya ga Allah kuma bisa karantarwan Annabi (S.A.W) ba tareda wuce iyakaba kuma ba tareda sakaciba.
Ihisanin mustahabbi kuwa shine; neman kusancin Allah ta hanyar aikata ayyukan nafilfilu da cikata ayyukan ibada mustahabbai da ladubbansu, da tsantseni daga abubuwa masu shubuha da makaruhai, wato (bawa) ya bawtawa Allah kamar yana ganinSa sai yayi kokari cikin aikata ayyukan ibada akan mafi kyawun tsarinta gwargwadon iyawarsa. Kada ya dorawa kansa abinda bazai iyaba, kuma kada yayi sakaci ya bar abinda yake iyawa na ibadar da zata kusantardashi ga Allah (Madawkakin Sarki)
Kuma ihisani yakan kasance acikin kowace ibada ne bisa gwargwado yanayinta, karfin ikhlasi da kyakkyawan koyi da shiriyar Annabi (S.A.W) acikin wannan ibadar shine mai gamewa ga (tabbatar da hakan).
Saboda haka ihisani acikin alwala yana kasancewane ta hanyar kyawtata alwalar da kamala farillaita da ladubbanta da rashin wuce iyakan da aka shar’anta wankewa.
Ihisani acikin salla kuma yana kasancewane ta hanyar tsaida ita a farkon lokacinta tareda khushu’i da nutsuwa da halartowar zuciya, kuma ya sallaceta irin sallar mai bankwana (da duniya) wato saiya cikata farillanta da sunnoninta tamkar yana ganin Allah (Madawkakin Sarki).
Ihisani acikin zakka da sadaka kuma shine ya bayarda abinda zaiyi sadakan dashi alhali yana mai neman kusancin Allah (Madawkakin Sarki) kuma yana mai tsammain rahamarSa yana mai tsoron azabarSa, baya nufin samun wani sakamako ko godiya daga wanda ya bawa sadakan, kuma baya biyarda gori ko cutarwa bayan sadakarsa, kuma yana iya kokarisa na ganin cewa ya fitarda abu mai kyaw daga dukiyarsa, saboda haka baya fitarwa daga mummunanta wanda rai yake kyama kuma baya jinkirin fitarda zakkarsa kuma baya tsanantawa ga mabukaci awurin karban zakkar, kuma baya masa dagawa kuma baya yayata sadakarsa kuma baya yin sadaka don agani ayaba.
To hakanan sawran ayyukan ibada da mu’amala, (suma) ya kamata ga bawa yayi kokarin kyawtatawa acikinsu gwargwadon iyawarsa kuma ya bi shiriyar Annabi(S.A.W) acikin su.
Duk wanda yayi kokarin yaga ya kyawtata kuma yayi kwadayin hakan ya kuma roki taimakon Allah (Madawkakin Sarki) akai, to ana masa fatan samun dacewa da yin ihisani. Abu-Ddarda’i (Allah Ya kara masa yarda) yace: shi ilimi ana samunsane kawai ta hanyar neman sani, hakuri ma ana samunsane ta hanyar kokari da danne zuciya, kuma duk wanda ya kokarta wurin neman alkhairi, za’a bashi, wanda kuma yayi kokarin kiyaye sharri, za’a kareshi daga gareshi.
Kuma kofofin ihisani suna da yawa, yazo acikin sahihu Muslim daga hadisin Shaddad dan Awsu dan Thabit (Allah Ya kara musu yarda) daga Annabi (S.A.W) yace:
((إنَّ اللهَ كتَبَ الإحسانَ على كلِّ شيءٍ؛ فإذا قَتَلْتُم فأحسِنوا القِتْلةَ، وإذا ذَبَحْتُم فأَحْسِنوا الذِّبْحةَ، وَلْيُحِدَّ أحدُكُم شَفْرَتَهُ وَلْيُرِحْ ذَبيحَتَهُ)).
Ma’ana:”Lallai Allah Ya rubuta ihisani akan komai, saboda haka idan zaku yi kisa sai ku kyawtata kisan, kuma idan zaku yi yanka ku kyawtata yankan, dayanku ya wasa wukarsa kuma ya hutarda abin yankarsa”
Kenan ihisani an rubutashi akan komai da komai. Kuma kyawtatawa cikin komai ya danganceshi. Hakika Annabi (S.A.W) anan yayi bayanin kyawtatawa acikin yanka. Saboda haka duk wanda ya sabawa shiriyarsa bai wasa wukarsaba kuma bai hutarda abin yankarsaba toshi baiyi ihisaniba acikin yankansa.
Wannan yana bayyana muhimmancin (karatu) fahimtar addini, domin dashine mai neman kyawtatawa zai san shiriyar Annabi (S.A.W) acikin ayyukan ibada da mu’amaloli, saiya san shiriyarsa acikin alwala da salla da zakka da azumi da hajji da jihadi da kasuwanci da abinci da abinsha da bacci da awre da zamantakewa da nagartattun ayyuka da sada zumunci zamantakewa da mutane mabambanta. To hakananma sawran al’amura.
Kuma bawa bazai kaiga martaban ihisaniba face da taimakon Allah da datarwanSa, shiyasa aka shar’antawa bawa ya rika rokon Allah a bayan kowace salla da (wannan addu’ar):
((اللهمَّ أعنِّي على ذِكْرِكَ وشُكرِكَ وحُسنِ عِبادتِكَ)).
Ma’ana:”Ya Allah, Ka taimakeni akan ambatonKa dag ode maKa da kyawtata ibadarKa”.