تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس الرابع: بيانُ فَضْلِ التَّوحيدِ


عبد الله الداخل
_21 _March _2013هـ الموافق 21-03-2013م, 11:16 PM
الدرس الرابع: بيانُ فَضْلِ التَّوحيدِ


التوحيدُ هو: إخلاصُ الدينِ للَّهِ جل وعلا، وهو شَرطٌ لدخولِ العبدِ في الإسلامِ.
وهو معنَى شَهادةِ أن لا إلهَ إلا اللهُ، ومَن لم يُوحِّدِ اللهَ فليسَ بمُسلمٍ، وإن ادَّعَى الإسلامَ ونطَقَ بشَهادةِ التَّوْحيدِ بلِسانِه؛ فلا تَصِحُّ الشَّهادةُ منه حتى يَعْمَلَ بمُوجَبِها، وذلك بأن يُخْلِصَ الدِّينَ للهِ عز وجل، ويَجْتَنِبَ عبادةَ ما يُعْبَدُ من دونِ اللهِ، ويَتَبَرَّأَ من الشِّركِ وأهلِه.
قال اللهُ تعالى: ﴿لَا إِكْرَاهَ فِي الدِّينِ قَدْ تَبَيَّنَ الرُّشْدُ مِنَ الْغَيِّ فَمَنْ يَكْفُرْ بِالطَّاغُوتِ وَيُؤْمِنْ بِاللَّهِ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْوَةِ الْوُثْقَى لَا انْفِصَامَ لَهَا وَاللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ﴾ [البقرة: 256].
وقال تعالى: ﴿وَالَّذِينَ اجْتَنَبُوا الطَّاغُوتَ أَنْ يَعْبُدُوهَا وَأَنَابُوا إِلَى اللَّهِ لَهُمُ الْبُشْرَى فَبَشِّرْ عِبَادِ﴾ [الزمر: 17].
وقال تعالى: ﴿وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَسُولًا أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوتَ﴾ [النحل: 36].
1: فأعظمُ فضائلِ التوحيدِ أنه أصلُ دينِ الإسلامِ، فلا يَصِحُّ دُخولُ العبدِ في الإسلامِ إلا بالتوحيدِ.
وثوابُ المُوحِّدِ أعظمُ الثوابِ: وهو رِضْوانُ اللهِ عز وجل، والنَّجاةُ من النارِ، ودخولُ الجَنَّةِ، ورُؤيةُ اللهِ تبارك وتعالى.
عن مُعاذِ بن جَبَلٍ رضِي الله عنه أن رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قال: ((ما مِنْ أَحَدٍ يَشْهَدُ أَنْ لا إِلهَ إِلا اللهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ صِدْقًا مِنْ قَلْبِهِ إِلاَّ حَرَّمَهُ اللهُ عَلى النَّارِ)). رواه البخاري.
وعن عُبادةَ بن الصامتِ رضِي الله عنه، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم: ((مَنْ شَهِدَ أن لا إلهَ إلا اللهُ وَحْدَهُ لا شَرِيكَ لَهُ، وَأنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ ورَسُولُهُ، وَأنَّ عِيسى عَبْدُ اللهِ وَرَسُولُهُ وَكَلِمَتُهُ ألْقَاهَا إِلَى مَرْيَمَ ورُوحٌ مِنْهُ، وَأنَّ الجَنَّةَ حَقٌّ، وَالنارَ حَقٌّ، أدْخَلَهُ الله الجَنَّةَ عَلَى مَا كَانَ مِنَ العَمَلِ)) متفق عليه.
فالمؤمنُ المُوحِّد قد وَعَده اللهُ بدُخولِ الجنَّةِ، وإنِ ارتكَبَ من المعاصي ما ارتكَبَ، فإنه قد يَغْفِرُ اللهُ له ذنوبَه ويَعْفو عنه، وقد يُعذِّبُه على ما فعَلَ من المعاصي في الدنيا أو في قَبْره أو في عَرَصات يومِ القيامةِ أو في النارِ ثم يكونُ مآلُه إلى الجنةِ بإذن الله تعالى.
وأما المشركُ فإنَّ عُقوبتَه أعظمُ العقوباتِ: وهي غَضَبُ اللهِ عز وجل ومَقْتُه والخُلودُ الأبَدِيُّ في نارِ جَهنَّم، والحِرْمانُ من دُخولِ الجنَّةِ، والحِرْمانُ من رؤيةِ اللهِ عز وجل.
قال اللهُ تعالى: ﴿إِنَّهُ مَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ حَرَّمَ اللَّهُ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ وَمَأْوَاهُ النَّارُ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنْصَارٍ﴾ [المائدة: 72].
وقال: ﴿كَلَّا إِنَّهُمْ عَنْ رَبِّهِمْ يَوْمَئِذٍ لَمَحْجُوبُونَ * ثُمَّ إِنَّهُمْ لَصَالُو الْجَحِيمِ﴾ [المطففين: 15–16].
واللهُ تعالى لا يَغْفِرُ الشِّرْكَ، ولا يَعْفُو عن المشركين، بل أَوْجَب عليهم العَذَابَ الأليمَ المُقِيم إذا ماتوا على الشِّرْكِ ولم يتوبوا منه، كما قال اللهُ تعالى: ﴿إِنَّ اللَّهَ لَا يَغْفِرُ أَنْ يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَلِكَ لِمَنْ يَشَاءُ وَمَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا بَعِيدًا﴾ [النساء: 116]
وعن عبدِ اللهِ بنِ مَسعودٍ رضِي الله عنه قال: ( قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((مَن مات وهو يَدْعو من دونِ الله نِدًّا دخَلَ النارَ)) وقلت أنا: مَن مات وهو لا يَدْعو للهِ نِدًّا دخَلَ الجَنَّةَ ). رواه البخاري.
والشِّرْكُ معناه أن تَعْبُدَ معَ اللهِ أحَدًا غيرَه؛ فتَجْعَلَه شَرِيكًا للهِ في العبادةِ، ومَن أَشْرَكَ مع اللهِ أحَدًا حَبِطَ عَمَلُه وكان من الخاسرين، قال اللهُ تعالى: ﴿وَلَقَدْ أُوحِيَ إِلَيْكَ وَإِلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكَ لَئِنْ أَشْرَكْتَ لَيَحْبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ الْخَاسِرِينَ * بَلِ اللَّهَ فَاعْبُدْ وَكُنْ مِنَ الشَّاكِرِينَ﴾ [الزمر: 65– 66].
فمِن أعظمِ فضائلِ التوحيدِ: النجاةُ من العقابِ الذي أعَدَّه اللهُ للمشركين.

2: ومن فَضائلِ التوحيدِ: أنه شَرْطٌ لقَبولِ الأعمالِ، فكلُّ أعمالِ المشرك غَيْرُ مَقْبولةٍ، وكلُّ دِينٍ غيرِ دينِ الإسلامِ غيرُ مَقْبولٍ، قال اللهُ تعالى: ﴿وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ﴾ [آل عمران: 85].
وقال: ﴿وَلَوْ أَشْرَكُوا لَحَبِطَ عَنْهُمْ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ﴾ [الأنعام: 88].
وقال في الكُفَّار: ﴿وَقَدِمْنَا إِلَى مَا عَمِلُوا مِنْ عَمَلٍ فَجَعَلْنَاهُ هَبَاءً مَنْثُورًا﴾ [الفرقان: 23].
فعَمَلُ المُشرِكِ حابِطٌ مردودٌ غيرُ مَقْبولٍ؛ لأن اللهَ تعالى لا يَقْبَلُ من مُشركٍ عَمَلاً.
وعَمَلُ المُؤْمِنِ المُوَحِّد مَقْبولٌ وإن كانَ قليلاً، بل يُضاعِفُه اللهُ له أضعافًا كثيرةً.

3: ومِن فَضائلِ التوحيدِ ما يَجِدُه المُؤْمِنُ المُوحِّدُ من سَكينةِ النفسِ وطُمَأنينةِ القلب، ذلك أنَّ المُوحِّد يَدْعو ربًّا واحدًا سميعًا بصيرًا عليمًا قديرًا رَءُوفًا رَحِيمًا، بيدِه المُلْك كلُّه، وبيدِه النَّفعُ والضُّرُّ، لا إلهَ إلا هو، فيَعْبُدُه ويَتَوَكَّلُ عليه، ويَرْجُو رحمتَه ويَخْشَى عَذَابَه، ويَتَّبِعُ رِضْوانَه ويَتقَلَّبُ في فَضْلِه ورحمتِه، فهو مُطْمَئِنُّ القَلْبِ بذِكْرِ اللهِ، غَنِيٌّ باللهِ، عزيزٌ باللهِ، مُتوكِّلٌ على اللهِ، لا يَخافُ ولا يَحْزَنُ، ولا يَضِلُّ ولا يَشْقَى.
وأما المُشْرِكُ فيَدْعُو من دونِ اللهِ ما لا يَضُرُّه ولا يَنْفَعُه، حائرٌ قلبُه بين أربابِه الذين يَدْعُوهم من دونِ اللهِ، وهم عن دُعائِه غَافِلُونَ.
قال الله تعالى: ﴿أَأَرْبَابٌ مُتَفَرِّقُونَ خَيْرٌ أَمِ اللَّهُ الْوَاحِدُ الْقَهَّارُ﴾ [يوسف: 39].
وقال تعالى: ﴿ضَرَبَ اللَّهُ مَثَلًا رَجُلًا فِيهِ شُرَكَاءُ مُتَشَاكِسُونَ وَرَجُلًا سَلَمًا لِرَجُلٍ هَلْ يَسْتَوِيَانِ مَثَلًا الْحَمْدُ لِلَّهِ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ﴾ [الزمر: 29].
وقال تعالى: ﴿وَمَنْ أَضَلُّ مِمَّنْ يَدْعُو مِنْ دُونِ اللَّهِ مَنْ لَا يَسْتَجِيبُ لَهُ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ وَهُمْ عَنْ دُعَائِهِمْ غَافِلُونَ * وَإِذَا حُشِرَ النَّاسُ كَانُوا لَهُمْ أَعْدَاءً وَكَانُوا بِعِبَادَتِهِمْ كَافِرِينَ﴾ [الأحقاف: 5–6].
وقال الله تعالى: ﴿الَّذِينَ آمَنُوا وَلَمْ يَلْبِسُوا إِيمَانَهُمْ بِظُلْمٍ أُولَئِكَ لَهُمُ الْأَمْنُ وَهُمْ مُهْتَدُونَ﴾ [الأنعام: 82].
وفسَّرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم الظُّلْمَ في هذه الآيةِ بالشِّرْكِ، واستَدَلَّ بقولِه تعالى: ﴿إِنَّ الشِّرْكَ لَظُلْمٌ عَظِيمٌ﴾ [لقمان: 13].

4: ومِن فَضائلِ التوحيدِ أنه السَّبَبُ الأعظمُ لمَحَبَّةِ اللهِ عز وجل للعَبْدِ، وما يَتْبَعُها من بركاتٍ كثيرةٍ منها: مَغْفرةُ الذنوبِ، وتَفْريجُ الكُروبِ، ومُضاعفةُ الحسناتِ، ورِفْعةُ الدَّرجاتِ، والحِفْظُ من الشُّرورِ والآفاتِ، ورَدُّ كَيْدِ الأعداءِ، وزَوالُ الهُمومِ والغُمومِ، وحُصولُ النِّعَمِ والبركاتِ، واندفاعُ النِّقَمِ والعُقوباتِ، والتَّحَرُّرُ من رِقِّ النفسِ والشَّيْطانِ والعُبوديَّةِ للخَلْقِ، وذَوْقُ حلاوةِ الإيمان ولَذَّةِ الإخلاصِ، والشوقُ إلى لقاءِ اللهِ، والخروجُ من الظلماتِ إلى النورِ، فيَخْرُجُ من ظُلْمةِ الشِّرْكِ إلى نُورِ التوحيدِ، ومن ذُلِّ المعصيةِ إلى عِزَّةِ الطاعةِ، ومن ظُلْمةِ الجهل إلى نُورِ العلمِ، ومن حَيْرةِ الشكِّ إلى بَرْدِ اليقينِ، ومن سُبُلِ الضلالةِ إلى صِراطِ اللهِ المستقيمِ.

فصل: والمسلمون يتفاضلون في تحقيقِ التوحيدِ تفاضُلاً كبيرًا، وكلما كان العبدُ أعظمَ إخلاصًا للَّهِ جل وعلا كان نَصِيبُه من فضائلِ التوحيدِ أعظمَ، فيَزْدَادُ نصيبُه من رِضْوانِ اللهِ عز وجل وولايتِه وفضلِه ورحمتِه وبركاتِه وثوابِه العظيمِ في الدنيا والآخرةِ.
وعلى قَدْرِ إخلاصِه يكونُ تَخَلُّصُه من تَسَلُّطِ الشيطانِ وإيذائِه؛ كما قال اللهُ تعالى في بيانِ قَسَمِ الشيطان أن يُغْوِيَ بني آدمَ: ﴿قَالَ رَبِّ بِمَا أَغْوَيْتَنِي لَأُزَيِّنَنَّ لَهُمْ فِي الْأَرْضِ وَلَأُغْوِيَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ (39) إِلَّا عِبَادَكَ مِنْهُمُ الْمُخْلَصِينَ (40) قَالَ هَذَا صِرَاطٌ عَلَيَّ مُسْتَقِيمٌ (41) إِنَّ عِبَادِي لَيْسَ لَكَ عَلَيْهِمْ سُلْطَانٌ إِلَّا مَنِ اتَّبَعَكَ مِنَ الْغَاوِينَ (42)﴾ [الحجر: 39–42].
وقال تعالى: ﴿فَإِذَا قَرَأْتَ الْقُرْآَنَ فَاسْتَعِذْ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ (98) إِنَّهُ لَيْسَ لَهُ سُلْطَانٌ عَلَى الَّذِينَ آَمَنُوا وَعَلَى رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ (99) إِنَّمَا سُلْطَانُهُ عَلَى الَّذِينَ يَتَوَلَّوْنَهُ وَالَّذِينَ هُمْ بِهِ مُشْرِكُونَ (100)﴾ [النحل: 98–100].

ومَن بلَغَ درجةَ الإحسانِ في التوحيدِ فخلَّصَه من شوائبِ الشركِ الأكبرِ والأصغرِ وعَبَدَ اللهَ كأنه يَرَاه، دخَلَ الجنةَ بغيرِ حِسابٍ ولا عذابٍ، ونالَ الدرجاتِ العُلَى من الجنَّةِ، نسألُ اللهَ من فَضْلِه.

طاهر جبريل دكو
_31 _March _2013هـ الموافق 31-03-2013م, 05:27 PM
Darasi na hudu: Bayni gameda falalan tawhidi.
Tawhidi shine tsarkake addini ga Allah (mai girma da dawkaka) kuma [shi tawhidi] sharadine [wanda sai ansameshi] kafin bawa ya shiga Musulunci.
Kuma shine ma'anan Shahadatu alla'ilaha-illallahu [wato shaidawa babu abin bawtawa da gaskiya sai Allah, duk wanda bai kadaita Allah ba to shi ba musulmi bane, koda kuwa yana da'awar Musulunci kuma ya furta Kalmar shahada da harshensa, to wannan shahadar bazata inganta daga gareshiba har sai ya aikata abinda take wajabtawa, wnnan ko [zai farune] idan ya tsarkake addini ga Allah (mai girma da dawkaka) ya kuma nisanci bawtan ababen da ake bawtawa koma bayan Allah, ya kuma barranta daga shirka da ma'abuta shirka. Allah (madawkaki) Yace:
﴿لَا إِكْرَاهَ فِي الدِّينِ قَدْ تَبَيَّنَ الرُّشْدُ مِنَ الْغَيِّ فَمَنْ يَكْفُرْ بِالطَّاغُوتِ وَيُؤْمِنْ بِاللَّهِ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْوَةِ الْوُثْقَى لَا انْفِصَامَ لَهَا وَاللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ﴾ [البقرة: ٢٥٦].
Ma'ana:"Babu tilastawa a cikin addini, hakika shiriya ta bayyana daga bata, saboda haka wanda ya kafirta da dagutu[ababen bawta na karya] kuma yayi imani da Allah, to hakika yayi riko da igiya amintacciya babu yankewa agareta. Kuma Allah Mai jine, Masani. Q2ayata256.
Kuma (madawkakin sarki) Yace:
﴿وَالَّذِينَ اجْتَنَبُوا الطَّاغُوتَ أَنْ يَعْبُدُوهَا وَأَنَابُوا إِلَى اللَّهِ لَهُمُ الْبُشْرَى فَبَشِّرْ عِبَادِ﴾ [الزمر: ١٧].
Ma'ana:"Kuma wadanda suka nisanci shaidanu ga bawta musu, kuma suka maida al'amari ga Allah, sunada bushara. To kabada bushara ga bayiNa. Q39ayata17.
Kuma (madawkakin sarki) Yace:
وقال تعالى: ﴿وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَسُولًا أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوتَ﴾ [النحل: ٣٦].
Ma'ana:"Kuma hakika Mun aika da Manzo cikin kowace al'umma(yana cewa) kubawtawa Allah, kuma ku ninanci dagutu (ababen bawta koma bayan Allah). Q16ayata36.
1: فأعظمُ فضائلِ التوحيدِ أنه أصلُ دينِ الإسلامِ، فلا يَصِحُّ دُخولُ العبدِ في الإسلامِ إلا بالتوحيدِ.
Saboda haka mafi girma daga falalolin tawhidi, shine kasancewansa tushe ga addinin Musulunci, don haka musuluncin bawa baya tabbata har sai yayi tawhidi (wato kadaita Allah).
وثوابُ المُوحِّدِ أعظمُ الثوابِ: وهو رِضْوانُ اللهِ عز وجل، والنَّجاةُ من النارِ، ودخولُ الجَنَّةِ، ورُؤيةُ اللهِ تبارك وتعالى.
Kuma ladan tawhidi shine lada mafi girma, wanda shine yardan Allah (mai girma da dawkaka), da kuma kubuta daga (azabar) wuta, da kuma shiga aljanna, da ganin Allah (mai yawan albarkatu da dawkaka). Daga mu'azu dan Jabal (Allah Ya kara masa yarda) (yace) lallai Annabi (S.A.W) yace:
((ما مِنْ أَحَدٍ يَشْهَدُ أَنْ لا إِلهَ إِلا اللهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ صِدْقًا مِنْ قَلْبِهِ إِلاَّ حَرَّمَهُ اللهُ عَلى النَّارِ)). رواه البخاري.
Ma'ana:"Ba wanda zai shaida cewa babu abin bawtawa da gaskiya sai Allah, kuma lallai Muhammadu Manzon Allah ne (alhali yana) maiyin gaskiya cikin zuciyarsa [gameda abinda ya furta] face Allah Ya haramt shi ga wuta. Bukharine ya ruwaitoshi.
Daga Ubadah dan Samit (Allah Ya kara masa yarda), yace: Manzon Allah (S.A.W) yace:
((مَنْ شَهِدَ أن لا إلهَ إلا اللهُ وَحْدَهُ لا شَرِيكَ لَهُ، وَأنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ ورَسُولُهُ، وَأنَّ عِيسى عَبْدُ اللهِ وَرَسُولُهُ وَكَلِمَتُهُ ألْقَاهَا إِلَى مَرْيَمَ ورُوحٌ مِنْهُ، وَأنَّ الجَنَّةَ حَقٌّ، وَالنارَ حَقٌّ، أدْخَلَهُ الله الجَنَّةَ عَلَى مَا كَانَ مِنَ العَمَلِ)) متفق عليه.
Ma'ana:" Duk wanda ya shaida cewa babu abin bawtawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake baShida abokin tarayya, kuma lallai Muhammadu bawanSane kuma ManzonSane, kuma lallai Isa bawan Allahne kuma ManzonSne, kuma Kalmar Allah ce ya jefata zuwaga Maryam kuma shi[Annabi Isa] ruhine daga Allah, kuma lallai aljanna gaskiyace kuma wutama lallai gaskiyace, to Allah zai shigar dashi Aljannah bisaga abinda ya kasance akai na aiki. Bukhari da Muslin.
Saboda haka shi mumini wanda yake mai kadaita Allah hakika Allah Yayi masa alkawarin shiga Aljanna, koda kuwa ya aikata abinda ya aikata na sabon Allah, domin Allah na iya gafarta masa zunubbabansa Ya kuma yi masa afuwa, Yana kuma iya yi masa azaba akan ayyukan sabonda yayi, [tun] anan Duniya,ko a cikin kabarinsa, ko a fililn tashin kiyama, ko a cikin wuta, sannan sai makomarsa ta kasance aljanna da izinin Allah madawkaki.
Amma mushriki kuwa, shikam ukubarsa tace mafi girman ukubobi (baki daya) wacce itace fushin Allah (mai girma da dawkaka), da kiyayyarSa, da dawwama na har abada acikin wutan Jahannama, da haramcin shiga Aljanna, da haramcin ganin Allah (mai girma da dawkaka).
(Allah) Madawkakin sarki Yace:
﴿إِنَّهُ مَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ حَرَّمَ اللَّهُ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ وَمَأْوَاهُ النَّارُ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنْصَارٍ﴾ [المائدة: ٧٢].
Ma'ana:"Lallaine wanda yayi shirka ga Allah, hakika Allah Ya haramta Aljanna a gareshi, kuma makomassa itace Wuta, kuma (hakika) babu wani mataimaki ga azzalumai. Q5ayata72.
Kuma Yace:
﴿كَلَّا إِنَّهُمْ عَنْ رَبِّهِمْ يَوْمَئِذٍ لَمَحْجُوبُونَ * ثُمَّ إِنَّهُمْ لَصَالُو الْجَحِيمِ﴾ [المطففين: ١٥–١٦].
Ma'ana:"Hakika a wannan yinin su (kafurai) abin shamakancewane daga Ubangijinsu. Sannan kuma lallaine su masu shiga Wutar Jahima ne. Q83ayata15 da 16.
واللهُ تعالى لا يَغْفِرُ الشِّرْكَ، ولا يَعْفُو عن المشركين، بل أَوْجَب عليهم العَذَابَ الأليمَ المُقِيم إذا ماتوا على الشِّرْكِ ولم يتوبوا منه، كما قال اللهُ تعالى:
Shi Allah (madawkaki) baYa gafartawa gameda shirka, kuma baYa yin afuwa ga mushirikai, saidaima Ya wajabta azaba mai radadi dawwamamme akansu idan suka mutu akan shirka basu tubaba kamar yadda Allah (madawkaki) Yace:
﴿إِنَّ اللَّهَ لَا يَغْفِرُ أَنْ يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَلِكَ لِمَنْ يَشَاءُ وَمَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا بَعِيدًا﴾ [النساء: ١١٦]
Ma'ana:"Lallaine Allah baya gafarta ayi miSa shirka da wani, kuma Yana gafarta abinda bai kai shirka ba, ga wanda Yaso, kuma wanda yayi shirka ga Allah hakika ya bace bata mai nisa. Q4ayata116.
Daga Abdullahi dan Mas'udu (Allah Ya kara masa yarda) yace: Manzon Allah (S.A.W) yace:
((مَن مات وهو يَدْعو من دونِ الله نِدًّا دخَلَ النارَ)) وقلت أنا: مَن مات وهو لا يَدْعو للهِ نِدًّا دخَلَ الجَنَّةَ ). رواه البخاري.
Ma'ana:"Duk wanda ya muta alhali yana kiran wani [abin bawta a matsayin] kishiya ga Allah, zai shiga wuta. Nikuma (wato Abdullahi dan Mas'udu) nace: Duk wanda ya mutu alhali baya kiran wani (abin bawta a matsayin kishiya) ga Allah, zai shiga Aljanna. Bukhari ne ya ruwaitoshi.
Kuma ita shirka ma'anarta shine, kabawtawa wani tareda Allah koma bayanSa, wato ka sanyashi abokin tarayya ga Allah acikin bawta, to duk wanda ya bawtawa wani tareda Allah, hakika ayyukansa sun rushe kuma ya kasance daga cikin masu asara. Allah (madawkaki) Yace:
﴿وَلَقَدْ أُوحِيَ إِلَيْكَ وَإِلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكَ لَئِنْ أَشْرَكْتَ لَيَحْبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ الْخَاسِرِينَ * بَلِ اللَّهَ فَاعْبُدْ وَكُنْ مِنَ الشَّاكِرِينَ﴾ [الزمر: ٦٥– ٦٦].
Ma'ana:" Kuma lallai hakika anyi wahayi zuwa gareka da kuma zuwaga wadanda ke gabaninka. [cewa] lallai idan kayi shirka, hakika aikin ka zai baci, kuma lallai zaka kasance daga masu asara. A'aha! Allah kadai zaka bawtawa, kuma ka kasance daga cikin masu godiya. Q39ayata65 da66.
Saboda haka yana daga mafi girman falala na tawhidi;
1- kubuta daga ukuban da Allah Ya tanadar domin mushirikai.
2-Kuma yana daga cikin falalan tawhidi, kasancewassa sharadin karban ayyuka, saboda haka duk ayyukan musshiriki ba karbabbu bane, kuma dukkanin addinin daba Musulunci ba ba karbabbe bane, Allah (madawkaki) Yace:
﴿وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ﴾ [آل عمران: ٨٥].
Ma'ana:" Kuma duk wanda ya nemi wanin Musulunci ya zama addini (a gareshi) to baza'a karba daga gareshi ba. Q3ayata85. Kuma Yace:
﴿وَلَوْ أَشْرَكُوا لَحَبِطَ عَنْهُمْ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ﴾ [الأنعام: ٨٨].
Ma'ana:" Kuma da sunyi shirka, hakika da abinda suka kasance suna aikatawa ya rushe. Q6ayata88.
Kuma Yace gameda kafurai:
﴿وَقَدِمْنَا إِلَى مَا عَمِلُوا مِنْ عَمَلٍ فَجَعَلْنَاهُ هَبَاءً مَنْثُورًا﴾ [الفرقان: ٢٣].
Ma'ana:" Kuma Muka gabata zuwa ga abinda suka aikata na aiki, sai Muka sanyashi kura watsattsiya. Q25ayata23.
Saboda haka aikin mushiriki bataccene maidajje kuma ba karbabbe bane, domin Allah baYa karban wani aiki daga mushiriki.
Shi kuma Mumini mai kadaita Allah, ayyukansa karbabbune koda sun kasance kadan, ba haka kawai bama, Allah zai ninninka masa shi ninkin ba ninkin.

3- Kuma yana daga cikin falalar tawhidi, abinda mumini mai kadaita Allah yakeji a ransa na nutsuwa da kwanciyar hankali, dalili kuwa shine, saboda shi mai kadaita Allah yana bawtan Allah dayane mai ji mai gani masani mai iko mai jin kai mai tawsayi, wanda a hannunSa dukkanin mulki yake, kuma mallakar amfani da cuta duk naSane, babu abin bawtawa da gaskiya saiShi, saboda haka[mumini] yake bawta maSa kuma yake dogaro daShi kuma yake fatan samun RahamarSa kuma yana tsoron azabarSa kuma yake bin yardanSa kuma yake jujjuyawa acikin falalarSa da RahamarSa, saboda haka shi yana cikin nutsuwar zuciya saboda ambaton Allah, ya wadata da Allah, ya dawkaka da Allah, ya dogara ga Allah, bazai ji tsoroba bazai yi bakin ciki ba bazai bataba kuma bazai tabeba.
Amma shiko mushiriki, yana bawtan wanin Allah abinda bazai iya cutar dashi ko amfanar dashi ba, zuciyarsa na cikin rudani gameda ababen da yake bawtawa koma bayan Allah, alhali kuwa su [ababen da yake bawtawa] gameda kiran da yakeyi musu gafalallune.
Allah (madawkakin Sarki) Yace:
﴿أَأَرْبَابٌ مُتَفَرِّقُونَ خَيْرٌ أَمِ اللَّهُ الْوَاحِدُ الْقَهَّارُ﴾ [يوسف: ٣٩].
Ma'ana:"Shin ababen bawta mabambanta sune sukafi alheri kokuwa makadaici mai tankwasawa. Q12ayata39.
Kuma Allah (madawkakin Sarki) Yace:
﴿ضَرَبَ اللَّهُ مَثَلًا رَجُلًا فِيهِ شُرَكَاءُ مُتَشَاكِسُونَ وَرَجُلًا سَلَمًا لِرَجُلٍ هَلْ يَسْتَوِيَانِ مَثَلًا الْحَمْدُ لِلَّهِ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ﴾ [الزمر: ٢٩].
Ma'ana:"Allah Ya buga misali; wani mutum a ckinsa akwi masu tarayya masu matsnancin jayayya, da wani mutum [bawa] dukkansa mallakar wani mutum. Shin zasu daidaita ga misali? Godiya ta tabbata ga Allah. A'a mafi yawansu [mutane] basu sani ba. Q39ayata29.
Kuma Allah (madawkaki) Yace:
وقال تعالى: ﴿وَمَنْ أَضَلُّ مِمَّنْ يَدْعُو مِنْ دُونِ اللَّهِ مَنْ لَا يَسْتَجِيبُ لَهُ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ وَهُمْ عَنْ دُعَائِهِمْ غَافِلُونَ * وَإِذَا حُشِرَ النَّاسُ كَانُوا لَهُمْ أَعْدَاءً وَكَانُوا بِعِبَادَتِهِمْ كَافِرِينَ﴾ [الأحقاف: ٥–٦].
Ma'ana:"Kuma wanene mafi bata daga wanda ke kiran wanin Allah wanda bazai amsa masa ba, har ranar Kiyama, alhali [wadanda ake kiran] shagaltattune daga kiransu.
Kuma idan aka tara mutane, saisu zama makiya agaresu, alhali sun kasance masu ki ga ibadarsu. Q46ayata5 da 6.
Kuma (madawkaki) Yace:
[B] ﴿الَّذِينَ آمَنُوا وَلَمْ يَلْبِسُوا إِيمَانَهُمْ بِظُلْمٍ أُولَئِكَ لَهُمُ الْأَمْنُ وَهُمْ مُهْتَدُونَ﴾ [الأنعام: ٨٢].
Ma'ana:" Wadanda sukayi imani kuma basu cudanya imaninsu da zalunci ba, wadannan suna da aminci kuma sune shiryayyu. Q6ayata82.
Annabi (S.A.W) ya fassara "zalunci" acikin wannan ayar da [cewa shine] shirka, kuma ya kafa hujja da fadin Allah (madawkaki):
﴿إِنَّ الشِّرْكَ لَظُلْمٌ عَظِيمٌ﴾ [لقمان: ١٣].
Ma'ana:"Lallai shirka zalunci ne mai girma".
4- Kuma yana daga cikin falalolin tawhidi kasancewarsa shine mafi girman sabubba na soyayyan Allah (madawkaki) ga bawa, da abinda ke biye da ita na albarkoki masu yawa, daga ciki akwai: Gafarar zunubbai, yaye bakin ciki, ninninka kyawawan ayyuka, dawkakan darajoji, kariya daga sharrurruka da annoba, da maida kaidin abokan gaba, da yayewar kuncin zuciya da [gushewar] matsanancin bakin ciki, da samun ni'ima da albarkoki da tunkudar matsanancin azaba da ukubobi, da yantuwa daga bawtar son zuciya da shedan, da bawta ga halittu, da dandana dadin imani da gardinsa, da tsrkin niyya, da kwadaituwa zuwaga saduwa da Allah, da ficewa daga duffai zuwa haske, wato ya fita daga duhun shirka zuwa hasken tawhidi, daga kaskancin sabon [Allah] zuwa dawkakan biyayya [gaAllah], daga duhun jahilci zuwa hasken ilimi, daga dimuwar shakku zuwa ga nutsuwa ta yakini, kuma daga tafarkin bata zuwa tafarkin Allah madaidaici.
Fasali: Kuma Musulmai suna da fifiko a tsakaninsu gameda hakikance tawhidi fifiko mai girma, duk sa'adda ikhlasin bwawa ga Allah [wato tsarkin niyyarsa cikin bawtar Allah] ya kasance mafi yawa, to kasonsa acikin falalolin tawhidima yakan fi girma, saboda haka sai ya samu kaso mai yawa acikin yardan Allah (mai girma da dawkaka) da jibintan al'amarinSa da falalarSa da rahamarSa da albarkokinSa da sakamakonSa mai girma a Duniya da Lahira.
Kuma kubutar shi daga rinjayi da cutarwan Shedan ya ta'allakane da gwargwado na tsarkin niyyarsa cikin bawta ga Allah, kamar yadda Allah (madawkaki) Ya fadi cikin bayani game da rantsuwr da Shedan yayi cewa sai ya batar da yayan Adamu:
: ﴿قَالَ رَبِّ بِمَا أَغْوَيْتَنِي لَأُزَيِّنَنَّ لَهُمْ فِي الْأَرْضِ وَلَأُغْوِيَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ (39) إِلَّا عِبَادَكَ مِنْهُمُ الْمُخْلَصِينَ (40) قَالَ هَذَا صِرَاطٌ عَلَيَّ مُسْتَقِيمٌ (41) إِنَّ عِبَادِي لَيْسَ لَكَ عَلَيْهِمْ سُلْطَانٌ إِلَّا مَنِ اتَّبَعَكَ مِنَ الْغَاوِينَ (42)﴾ [الحجر: ٣٩–٤٢].
Ma'ana:"Yace, "Ya ubangijina! Ina rantsuwa da batarwan da kayi mini, lallai tabbas sai na kawata musu (barna) a bayan kasa, kuma lallai tabbas sai na batar dasu baki daya(39) Sai dai bayinka tsarkakakku (wato wadanda ka tsarkake daga shirka da riya) (40)
Sai (Allah)Yace:" Wannan (wato ikhlasi) shine tafarki zuwa gareni madaidaici (41)
Lallai bayiNa bakada iko akansu, saidai wanda ya bika daga cikin batattu (42). Qayata39 zuwa ta 42.
Kuma (madawkaki) Yace:
﴿فَإِذَا قَرَأْتَ الْقُرْآَنَ فَاسْتَعِذْ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ (98) إِنَّهُ لَيْسَ لَهُ سُلْطَانٌ عَلَى الَّذِينَ آَمَنُوا وَعَلَى رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ (99) إِنَّمَا سُلْطَانُهُ عَلَى الَّذِينَ يَتَوَلَّوْنَهُ وَالَّذِينَ هُمْ بِهِ مُشْرِكُونَ (100)﴾ [النحل: ٩٨–١٠٠].
Ma'ana:"Sa'annan idan (za) ka karanta Alkur'ani, ka nemi tsarin Allah daga Shedan jefaffe (98).
Lallaine shi bashida tasiri akan wadanda sukayi imani kuma (wadanda) ga Uban gijnsu suke dogaro (99).
Abin sani kawai, karfinsa yana (tasirine kawai) akan wadanda suke jibintarsa, kuma wadanda suke su gameda shi masu shirkane (100). Q16 ayata98zuwa ta100.
Wanda ya kai martabar ihisani acikin tawhidi, ya tsarkake shi [tawhidin] daga gawraye na babban shirka da karaminsa, kuma ya bawtawa Allah tamkar yana ganinSa, to zai shiga Aljanna ba tareda hisabiba kuma batareda azababa, kuma zai samu wata daraja madawkakiya a cikin Aljanna, muna rokon Allah falalarsa.