المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس الثالث: بيانُ وُجوبِ طاعةِ اللهِ ورسولِه


عبد الله الداخل
_21 _March _2013هـ الموافق 21-03-2013م, 04:40 PM
الدرس الثالث: بيانُ وُجوبِ طاعةِ اللهِ ورسولِه

طاعةُ اللهِ ورسولِه أصلٌ من أصولِ الدينِ، ولا يكونُ العبدُ مسلمًا حتى ينقادَ لأوامرِ اللهِ ورسولِه، ويعتقدَ وجوبَ طاعةِ اللهِ ورسولِه، وأنَّ مَن أطاعَ اللهَ ورسولَه فاز برِضْوان اللهِ ورحمتِه وفضلِه العظيمِ، ونَجَا من العذابِ الأليمِ، ومَن عَصَى وتولَّى خَسِر الخُسْرانَ المُبين، وعرَّض نفسَه لسَخَطِ اللهِ وعقابِه.
ومن زَعَم أنه يَسَعُه الخروجُ عن طاعةِ اللهِ ورسولِه فهو غيرُ مُسلمٍ.
وقد قال اللهُ تعالى: ﴿وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلَا مُؤْمِنَةٍ إِذَا قَضَى اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَمْرًا أَنْ يَكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ وَمَنْ يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا مُبِينًا﴾ [الأحزاب: 36].
وقال تعالى: ﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَلَا تُبْطِلُوا أَعْمَالَكُمْ﴾ [محمد: 33].
وقال تعالى: ﴿وَأَطِيعُوا اللَّهَ وَالرَّسُولَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ﴾ [آل عمران: 132].
وقال تعالى: ﴿وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ يُدْخِلْهُ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا وَذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ (13) وَمَنْ يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَيَتَعَدَّ حُدُودَهُ يُدْخِلْهُ نَارًا خَالِدًا فِيهَا وَلَهُ عَذَابٌ مُهِينٌ﴾ [النساء: 13–14].
وقال تعالى: ﴿وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَالرَّسُولَ فَأُولَئِكَ مَعَ الَّذِينَ أَنْعَمَ اللَّهُ عَلَيْهِمْ مِنَ النَّبِيِّينَ وَالصِّدِّيقِينَ وَالشُّهَدَاءِ وَالصَّالِحِينَ وَحَسُنَ أُولَئِكَ رَفِيقًا (69) ذَلِكَ الْفَضْلُ مِنَ اللَّهِ وَكَفَى بِاللَّهِ عَلِيمًا﴾ [النساء: 69–70].
وقال تعالى: ﴿وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ فَازَ فَوْزًا عَظِيمًا﴾ [الأحزاب: 71].
وقال تعالى: ﴿وَمَنْ يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَإِنَّ لَهُ نَارَ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا﴾ [الجن: 23].
وقال: ﴿مَنْ يُطِعِ الرَّسُولَ فَقَدْ أَطَاعَ اللَّهَ﴾ [النساء: 80].
وقال: ﴿وَمَا آتَاكُمُ الرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَمَا نَهَاكُمْ عَنْهُ فَانْتَهُوا﴾ [الحشر: 7].
فدلَّت هذه الآياتُ على أن طاعةَ اللهِ ورسولِه واجبةٌ، وأن اللهَ تعالى قد وعَدَ من أطاعَه ورسولَه الفضلَ العظيمَ في الدنيا والآخِرة، وتوعَّد مَن عَصَاه ورسولَه بالعذابِ الأليم.
والطاعةُ تكون بامتثالِ الأمرِ واجتنابِ النَّهْيِ، وهذه هي حَقِيقةُ الدينِ: التَّعبدُ للَّهِ تعالى بفعلِ أوامرِه واجتنابِ نواهيهِ.
وقد يسَّرَ اللهُ لنا الدينَ، ولم يُكلِّفْنا إلا ما نستطيعُ، قال تعالى: ﴿فَاتَّقُوا اللَّهَ مَا اسْتَطَعْتُمْ﴾ [التغابن: 16].
وقال تعالى: ﴿لَا يُكَلِّفُ اللَّهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا﴾ [البقرة: 286]، وقال تعالى: ﴿وَمَا جَعَلَ عَلَيْكُمْ فِي الدِّينِ مِنْ حَرَجٍ﴾ [الحج: 78]، وعن أبي هُريرةَ رضِي الله عنه أن النبيَّ صلى الله عليه وسلم قال: ((إنَّ هذا الدينَ يُسْرٌ، ولن يُشادَّ الدينَ أحدٌ إلا غَلَبَهُ)). رواه البخاري
وعن أبي هُريرةَ رضِي الله عنه قال: قال رسولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم: ((ما نَهَيتُكم عنه فاجْتَنِبُوه، وما أَمَرْتُكم به فَأْتُوا منه ما اسْتَطَعْتُم)) متفق عليه.
والأوامرُ التي أمَرَ اللهُ بها وأمَرَ بها رسولُه على ثلاثِ درجاتٍ:
الدَّرَجةُ الأولى: ما يَلْزَمُ منه البقاءُ على دينِ الإسلامِ، وذلك بطاعتِه في توحيدِ اللهِ جل وعلا، والكُفْر بالطاغوتِ، واجتنابِ نواقضِ الإسلامِ.
ومَن خالَفَ في هذه الدرجة فأشرَكَ باللهِ عز وجل أو ارتكَبَ ناقضًا من نواقضِ الإسلامِ كتكذيبِ اللهِ ورسولِه أو الاستهزاءِ بشيءٍ من دينِ اللهِ عز وجل، ونحوِ ذلك من النواقضِ فهو كافرٌ خارجٌ عن ملَّةِ الإسلامِ.
الدَّرَجَةُ الثانيةُ: ما يَسْلَمُ به العبدُ من العذابِ، وهو أداءُ الواجباتِ، واجتنابُ المُحرَّماتِ، فمَن أدَّى هذه الدرجةَ فهو ناجٍ من العذابِ بإذن اللهِ، مَوعودٌ بالثوابِ العظيمِ على طاعتِه، وهذه درجةُ عبادِ اللهِ المُتَّقينَ.
الدَّرَجةُ الثالثةُ: أداءُ الواجباتِ والمُستحبَّاتِ، وتَرْكُ المُحرَّماتِ والمَكْروهاتِ، وهذه درجةُ الكمالِ للعبادِ، وأصحابُها من أهلِ الإحسانِ المَوْعودين بالدرجات العُلَى، نسألُ اللهَ من فَضْلِه.
واللهُ تعالى قد أكمَلَ لنا الدينَ وأتَمَّ علينا نِعْمةَ الإسلامِ، كما قال تعالى: ﴿الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا﴾ [المائدة: 3].
فدِينُ الإسلامِ كامِلٌ، وأحكامُ الشريعةِ شامِلةٌ لجميعِ شُئُونِنا، فلا نَقْصَ فيها، ولا اختلافَ، ولا تَناقُضَ، بل هي شَرِيعةٌ كاملةٌ سَمْحةٌ مُيَسَّرة صالحةٌ لكلِّ زمانٍ ومكانٍ، ومُهَيْمِنَةٌ على جميعِ أحوالِ العبادِ.
فالذي يُطيع اللهَ ورسولَه مُهتدٍ للتي هي أقْومُ في كل شأنٍ من شُئونِه؛ فإن اللهَ تعالى قال: ﴿إِنَّ هَذَا الْقُرْآنَ يَهْدِي لِلَّتِي هِيَ أَقْوَمُ﴾ [الإسراء: 9]، فلا يُمْكِنُ أن ينالَ العبدُ أمْرًا أفضلَ له بمعصيةِ الله عز وجل ومخالفةِ كتابِه.
وقال النبيُّ صلى الله عليه وسلم: ((وإنَّ أحْسَنَ الهَدْيِ هَدْيُ مُحمَّدٍ))
فلا هَدْيَ أحسنُ من هديِه، ولا يمكن أن يَنالَ العبدُ أمرًا أفضلَ له بمخالفةِ هَدْيِ النبيِّ صلى الله عليه وسلم، وإنما كمالُ العبدِ ونجاتُه وسعادتُه ومَبْلَغُ هدايتِه على قَدْرِ اتباعِه للنبيِّ صلى الله عليه وسلم.
قال اللهُ تعالى: ﴿قُلْ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنِّي رَسُولُ اللَّهِ إِلَيْكُمْ جَمِيعًا الَّذِي لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ فَآَمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ النَّبِيِّ الْأُمِّيِّ الَّذِي يُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَكَلِمَاتِهِ وَاتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ﴾ [الأعراف: 158].
فمَن اتَّبَعَ النبيَّ صلى الله عليه وسلم فهو مُهْتدٍ، ومَن عَصَاهُ فقد ضَلَّ.
وقد قال اللهُ تعالى: ﴿وَمَنْ يُشَاقِقِ الرَّسُولَ مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُ الْهُدَى وَيَتَّبِعْ غَيْرَ سَبِيلِ الْمُؤْمِنِينَ نُوَلِّهِ مَا تَوَلَّى وَنُصْلِهِ جَهَنَّمَ وَسَاءَتْ مَصِيرًا﴾ [النساء: 115].
فكلُّ مَن عصَى اللهَ ورسولَه في أيِّ أمرٍ من الأمورِ فهو فاسقٌ بمعصيتِه ضالٌّ في ذلك الأمرِ، وإن زَعَم أنه يُريدُ تَحْقِيقَ مصلحةٍ أو دَرْءَ مَفْسَدَةٍ؛ فإنَّ المصالحَ لا تَتحقَّقُ بمعصيةِ اللهِ، والمَفَاسِدَ لا تُدْرَأ بالتَّعرُّضِ لسَخَطِ اللهِ.
وكلُّ مَن أمَرَ بمعصيةِ اللهِ ورسولِه وزَيَّنَها للناسِ فهو شَيْطانٌ؛ سواءٌ في ذلك شياطينُ الإنسِ والجنِّ.
وعن عليِّ بنِ أبي طَالِبٍ رضِي الله عنه أن النبيَّ صلى الله عليه وسلم قال: ((لا طاعةَ لمَخْلوقٍ في مَعْصيةِ اللهِ)) رواه أحمدُ ومُسلمٌ.
وهذا يَشْمَلُ جميعَ مَن أمَرَ بمعصيةِ اللهِ في أمورِ العقيدةِ أو العبادات أو المُعاملات أو غيرِها من شُئونِ العبادِ.
وكلُّ مَن دَعَا إلى بِدْعَةٍ ومَنْهَجٍ غيرِ منهجِ النبيِّ صلى الله عليه وسلم فهو ضالٌّ مُضِلٌّ، وقد قال اللهُ تعالى: ﴿وَأَنَّ هَذَا صِرَاطِي مُسْتَقِيمًا فَاتَّبِعُوهُ وَلَا تَتَّبِعُوا السُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمْ عَنْ سَبِيلِهِ ذَلِكُمْ وَصَّاكُمْ بِهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ﴾ [الأنعام: 153].

طاهر جبريل دكو
_31 _March _2013هـ الموافق 31-03-2013م, 05:23 PM
Darasi nauku: Bayani gameda wajibcin yin da'a ga Allah da ManzonSa.
Yin da'a ga Allah da ManzonSa asaline daga cikin abubuwanda addini ya ginu akai, bawa bazai kasance muminiba har saiya sakankance ya mika wuya ga dokokin Allah da ManzonSa, kuma ya kudurce wajibcin yin da'a ga Allah da ManzonSa, kuma ya (kudurce) cewa lallaine wanda yayiwa Allah da ManzonSa biyayya zai rabawta da (samun) yardan Allah da rahamarSa da falalarSa mai girma, kuma zai tsira daga azaba mai radadi. Shiko wanda ya saba (wa Allah) ya juya baya, to yayi asara asara bayyananniya, kuma zai bijradda kansa zuwaga fushin Allah da ukubarSa.
Duk wanda ya riya cewa ya halatta gareshi ya yantu daga yiwa Allah da ManzonSa biyayya, to (wannan) ba Musulmi bane. Hakika Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
﴿وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلَا مُؤْمِنَةٍ إِذَا قَضَى اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَمْرًا أَنْ يَكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ وَمَنْ يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا مُبِينًا﴾ [الأحزاب: ٣٦].
Ma'ana:" Bai dacewa ga Mumini (na miji) hakama Mumina ( mace) ayayinda Allah da ManzonSa suka yanke hukunci gameda wani al'amari yazama sunada zabi acikin al'amarinsu. Kuma wanda ya sabawa Allah da ManzonSa hakika ya bace bata bayyananniya. Q33 ayata36.
Kuma (madawkakin sarki) Yace:
﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَلَا تُبْطِلُوا أَعْمَالَكُمْ﴾ [محمد: ٣٣].
Ma'ana:" Yaku wadanda sukayi imani, kuyiwa Allah da ManzonSa biyayya kadaku bata ayyukanku. Q47 ayata33.
Kuma (madawkakin sarki) Yace:
﴿وَأَطِيعُوا اللَّهَ وَالرَّسُولَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ﴾ [آل عمران: ١٣٢].
Ma'ana:"Kuma kuyiwa Allah da ManzonSa biyayya saboda ku samu rahama. Q3 ayata132.
Kuma (madawkakin sarki) Yace:
﴿وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ يُدْخِلْهُ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا وَذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ (13) وَمَنْ يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَيَتَعَدَّ حُدُودَهُ يُدْخِلْهُ نَارًا خَالِدًا فِيهَا وَلَهُ عَذَابٌ مُهِينٌ﴾ [النساء: ١٣–١٤].
Ma'ana:" Kuma (duk) wanda yayiwa Allah da ManzonSa biyayya (Allah) zai shigardashi gidajen Aljanna (wadanda) koramu ke gudana a karkashisu (yana mai) dawwama acikinsu. Wannan shine rabo mai girma. (13)Wandako ya sabawa Allah da ManzonSa kuma ya ketare iyaka cikin dokokin Allah, to (Allah) zai shigardashi cikin wuta yana mai dawwama acikinta, kuma yanada wata azaba ta walakanci. Q4 ayata13da14.
Kuma (madawkakin sarki) Yace:
﴿وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَالرَّسُولَ فَأُولَئِكَ مَعَ الَّذِينَ أَنْعَمَ اللَّهُ عَلَيْهِمْ مِنَ النَّبِيِّينَ وَالصِّدِّيقِينَ وَالشُّهَدَاءِ وَالصَّالِحِينَ وَحَسُنَ أُولَئِكَ رَفِيقًا (69) ذَلِكَ الْفَضْلُ مِنَ اللَّهِ وَكَفَى بِاللَّهِ عَلِيمًا﴾ [النساء: ٦٩–٧٠].
Ma'ana:" Wanda yayiwa Allah da ManzonSa biyayya, to wadannan suna tareda wadanda Allah ya ni'imta daga Annabawa da siddikai da shahidai da salihai, kuma wadannan sun kywtata suzama abokan zama (69) Wannan falalace daga Allah, kuma Allah ya isa zama masani (70). Q4ayata69 da70.
Kuma (madawkakin sarki) Yace:
﴿وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ فَازَ فَوْزًا عَظِيمًا﴾ [الأحزاب: ٧١].
Ma'ana:" Kuma wanda yayiwa Allah da ManzonSa biyayya to hakika ya rabawta rabo mai girma. Q33ayata71.
Kuma (madawkakin sarki) Yace:
﴿وَمَنْ يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَإِنَّ لَهُ نَارَ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا﴾ [الجن: ٢٣].
Ma'ana:"Kuma wanda ya sabawa Allah da ManzonSa, to lallai wutar jahannama ta tabbata agareshi(shi da ireirensa) suna masu dawwama acikinta har abada. Q72ayata23.
Kuma Yace:
﴿مَنْ يُطِعِ الرَّسُولَ فَقَدْ أَطَاعَ اللَّهَ﴾ [النساء: ٨٠].
Ma'ana:" Wanda yayiwa Manzon(Allah) da'a, to hakika yayiwa Allah da'a. Q4ayata80.
Kuma Yace:
﴿وَمَا آتَاكُمُ الرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَمَا نَهَاكُمْ عَنْهُ فَانْتَهُوا﴾ [الحشر: ٧].
Ma'ana:" Kuma (duk) abinda Mazon(Allah) ya kawo muku ku karba (haka) kuma (duk) abind ya haneku ku hanu. Q59ayata7.
Sai wadannan ayoyin duk sukayi nuni zuwaga wajibcin yiwa Allah da ManzonSa biyaya, kuma cewa Allah Yayi alkawarin falala mai girma a duniya da lahira ga wanda yayi maSa da'a da ManzonSa, kuma yayi alkawari na azaba mai radadi ga wanda ya saba maSa ya sabawa ManzonSa.
Ita biyayya tana kasancewane ta hanyar aikata umurni da nisantan hani, wannan ko shine hakikanin addini, (wato)bawtan Allah (Madawkaki) ta hanyan aikata abubuwanda Yayi umurni dasu da nisantan abubuwanda Ya hana.
Kuma hakika Allah Ya sawwake mana addini, bai dawra manaba face abinda muke iyawa. Allah (Madawkaki) Yace:
: ﴿فَاتَّقُوا اللَّهَ مَا اسْتَطَعْتُمْ﴾ [التغابن: ١٦].
Ma'ana:"Kuji tsoron Allah gwargwadon iyawarku. Q64ayata16. Kuma madawkaki Yace:
﴿لَا يُكَلِّفُ اللَّهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا﴾ [البقرة: ٢٨٦]،
Ma'ana:" Allah baYa dawrawa rai (wani aiki) face abinda take iyawa. Q2ayata286.
Kuma madawkaki Yace:
﴿وَمَا جَعَلَ عَلَيْكُمْ فِي الدِّينِ مِنْ حَرَجٍ﴾ [الحج: ٧٨]،
Ma'ana:" Kuma bai sanya muku wani kunciba acikin addini. Q22ayata78.
Daga Abu hurairata (Allah Ya kara masa yarda) (yace) lallai Annabi (S.A.W) yace:
((إنَّ هذا الدينَ يُسْرٌ، ولن يُشادَّ الدينَ أحدٌ إلا غَلَبَهُ)). رواه البخاري
Ma'ana:" Lallai wannan Addinin mai sawkine, babu wanda zai tsananta (a cikin) addini face yayi galaba akansa. Bukharine ya ruwaitoshi.
Daga Abu hurairata (Allah Ya kara masa yarda) yace: lallai Annabi (S.A.W) yace:
((ما نَهَيتُكم عنه فاجْتَنِبُوه، وما أَمَرْتُكم به فَأْتُوا منه ما اسْتَطَعْتُم)) متفق عليه.
Ma'ana:" Abinda na haneku gamedashi, to kunisanceshi, kuma abinda na umurceku da aikatashi, ku aikatshi gwargwadon iyawarku. Bukhari da Muslim.
Kuma abubuwanda Allah da ManzonSa sukayi umurni dasu, suna kan darajojine guda uku.
Daraja ta farko: Abubwanda tabbata acikin addinin Musulunci ke lazimta aikatasu, wanda shine yiwa Allah biyayya cikin tawhidi (wato kadaita Allah) (Mai girma da dawkaka), da kafircewa dagutu, da nisantan abubuwa masu warware Musulunci.
Duk wanda ya aikata sabanin wannan darajar, (wato) ya sanyawa Allah (Mai girma da dawkaka) abokin tarayya, ko kuma ya aikata wani abu daga cikin abubuwan dake warware musulunci kamar karyata Allah da ManzonSa ko kuma yin isgilanci ga wani abu daga addinin Allah (Mai girma da dawkaka) da makamantan haka cikin abubuwa masu warware musulunci, to shi kafirine wanda yayi ridda daga addinin Musulunci.
Daraja ta biyu: Abinda bawa ke kubuta daga azaba da aikatashi, wato aikata wajibai da nisantan haramtattun abubuwa. Duk wanda ya aikata wannan darajar, to shi kubutaccene daga azaba, da izinin Allah, (kuma) abin yiwa alkawari gameda lada mai girma saboda wannan biyayyar tasa, kuma wannan(darajar) itace darajar bayin Allah masu takawa.
Daraja ta uku: Aikata wajibai da mustahabbai, da barin haramtattu da makaruhai, wannan (darajar) itce daraja ta kamala ga bayi, kuma ma'abuta wannan darajar, suna cikin jama'ar Ihsani wadanda akayiwa alkawarin darajoji madawkaka. Muna rokon Allah Ya (azurtamu da) falalanSa.
Kuma Allah (madawkakin Sarki) Yariga Ya kammala mana addini kuma Ya cikata mana ni'imar Musulunci, kamar yadda Yace:
﴿الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا﴾ [المائدة: ٣].
Ma'ana:"Ayaw Nakammala muku addininku, kuma Na cika muku ni'imaTa, kuma Na yardammuku da Musulunci amatsayin addini. Q5ayata3.
Saboda haka shi addinin Musulunci kammalallene, kuma hukunce hukuncen shri'ar (Musulunci) gamammune ga dukkan al'amuranmu, babu tawaya acikinta, kuma babu sassabawa, kuma babu tufka da warwara. Ita shari'ar Musulunci kammalalliyace sawwakakkiya wacce take dacewa da kowane zamani da wuri, kuma wacce take galaba akn dukkan halayen bayi.
Saboda haka wanda keyiwa Allah da ManzonSa biyayya ya (samu) shiriya zuwaga abinda yake mafi zama daidai cikin kowane sha'ani daga sha'anoninsa, Lallai Allah (Madawkaki) Yace:
﴿إِنَّ هَذَا الْقُرْآنَ يَهْدِي لِلَّتِي هِيَ أَقْوَمُ﴾ [الإسراء: ٩]،
Ma'ana:" Lallai wannan Alkur'anin yana shiryarwa zuwaga abu mafi daidaito. Q17ayata9.
Don haka bai yiwuwa ga bawa ya kasance ya samu wani abu mafi alkhairi gareshi akan (hanyan) sabon Allah Mai girma da dawkaka da sabawa littafinSa, kuma Annabi (S.A.W) yace:
((وإنَّ أحْسَنَ الهَدْيِ هَدْيُ مُحمَّدٍ))
Ma'ana:" Kuma lallai mafi kyawun shiriya itace shiriyar (Annabi) Muhammadu.
Saboda haka babu wata shiriya da tafi tasa ( wato Manzon Allah (S.A.W)) kuma bazai yiwuba gabawaba ya dace da wani al'amari mafi falala agareshi ta hanyan sabawa shiriyar Annabi (S.A.W), shi dai bawa, kamalarsa da tsiransa da rabawtansa da kaiwa makura ackin shiriyarsa, ya ta'allakane da gwargwadon biyayyarsa ga shiriyar Annabi (S.A.W). Allah (Madawkaki) Yace:
﴿قُلْ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنِّي رَسُولُ اللَّهِ إِلَيْكُمْ جَمِيعًا الَّذِي لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ فَآَمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ النَّبِيِّ الْأُمِّيِّ الَّذِي يُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَكَلِمَاتِهِ وَاتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ﴾ [الأعراف: ١٥٨].
Ma'ana: " Kace (musu ya Muhammad) :"Yaku mutane, lallai ni Manzon Allahne zuwa gareku baki daya (Allah wanda) yake da mulkin sammai da kasa, babu abin bawtawa da gaskiya saiShi, yana rayarwa yana matarwa, saboda haka kuyi imani da Allah da ManzonSa, Annabinnan wanda yake Ummiyyi (wato bai san rubutu da karatuba) wanda yake yin imanida Allah da kalmominSa, kuma ku bishi domin kusamu shiriya.Q7ayata157.
Don haka duk wanda yabi Annabi (S.A.W) ya samu shiriya, duk wanda ya saba masa kuwa to babu shakka ya bata. Allah (Madawkaki) Yace:
﴿وَمَنْ يُشَاقِقِ الرَّسُولَ مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُ الْهُدَى وَيَتَّبِعْ غَيْرَ سَبِيلِ الْمُؤْمِنِينَ نُوَلِّهِ مَا تَوَلَّى وَنُصْلِهِ جَهَنَّمَ وَسَاءَتْ مَصِيرًا﴾ [النساء: ١١٥].
Ma'ana:"Duk wanda ya gefance daga Manzon Allah bayan shiriya ta bayyana gareshi kuma ya bi sabanin tafarkin muminai, to zaMu jibinta masa abinda ya jibinta kuma Mushigardashi Jahannama, kuma makoma ta munana idan ta kasance (Jahannama). Q4ayata115.
Kuma duk wanda ya sabawa Allah da ManzonSa cikin kowanne irin al'amari daga al'amura, to zai kasance fasiki da wannan sabon nasa, kuma batacce cikin wannan al'amarin, koda kuwa ya riya cewa yana nufin cimma wata maslahace ko kuma tunkude wata barna, domin lallai sabon Allah bai zama sanadin tabbatuwar maslaha, hakama barna, ba'a tunkudeta ta hanyar bijirar da kai fushin Allah.
Kuma duk wanda yayi umurni da sabon Allah da ManzonSa ya kuma kawatashi ga mutane, to shi shedanine, kuma shedanun mutane da na aljannu duk dayane acikin wannan. Daga Aliyu dan Abi Dalib (Allah ya kara masa yarda) yace: lallai Annabi (S.A.W) yace:
((لا طاعةَ لمَخْلوقٍ في مَعْصيةِ اللهِ)) رواه أحمدُ ومُسلمٌ.
Ma'ana:" Babu biyayya ga abin halitta cikin sabawa Mahalicci. Da Ahmad da Muslim ne suka ruwaitoshi.
Kuma wannan (hanin) zai kunshi dukkanin wanda yayi umurni da sabon Allah, cikin akida Da ibada da mu'amala da waninsu acikin sha'anin bayi.
Kuma duk wanda yayi kira zuwaga wata bidi'a da wani tsri sabanin tsarin Annabi (S.A.W), To shi bataccene mai batarwa, hakika Allah (Madawkakin Sarki) Yace:
: ﴿وَأَنَّ هَذَا صِرَاطِي مُسْتَقِيمًا فَاتَّبِعُوهُ وَلَا تَتَّبِعُوا السُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمْ عَنْ سَبِيلِهِ ذَلِكُمْ وَصَّاكُمْ بِهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ﴾ [الأنعام: ١٥٣].
Ma'ana:" Kuma wannan shine tafarkina madaidaici, saboda haka ku bishi, kada ku bi yan kananan hanyoyi saisu bashsheku daga tafarkinSa, wannan, dashi (Allah) Yayi muku wasiyya domin ku sami takawa. Q6ayata153.