تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس الثاني: بيانُ معنَى شهادةِ أن مُحمَّدًا رسولُ اللهِ (صلى الله عليه وسلم)


عبد الله الداخل
_21 _March _2013هـ الموافق 21-03-2013م, 03:56 PM
الدرس الثاني: بيانُ معنَى شهادةِ أن مُحمَّدًا رسولُ اللهِ (صلى الله عليه وسلم)

شهادةُ أن مُحمَّدًا رسولُ اللهِ تَقْتَضِي الإيمانَ بأنَّ اللهَ تعالى أرسَلَ نَبِيَّه مُحمَّد بنَ عبدِ اللهِ بنِ عبدِ المُطَّلِبِ رسولاً إلى الجِنِّ والإنسِ جَمِيعًا يَأْمُرُهم بعبادةِ اللهِ وحدَه، واجتنابِ ما يُعبَدُ من دونِ اللهِ عز وجل، ويُبَيِّنُ لهم شَرائِعَ الدِّينِ.
وتَقْتَضِي الإيمانَ بأنه عبدُ اللهِ ورسولُه، ليسَ له حقٌّ في العبادةِ، ولا يَجوزُ أن نَغْلُوَ في مَدْحِه؛ فنَصِفَه بصفاتٍ هي من خَصائصِ اللهِ جل وعلا.
فعن عبدِ اللهِ بنِ عبَّاسٍ رضِي الله عنهما أنه سَمِعَ عُمَر بنَ الخَطَّابِ رضِي اللهُ عنه يقولُ وهو على المِنْبرِ: سمعتُ النبيَّ صلى الله عليه وسلم يقولُ: ((لا تُطْرُوني كما أَطْرَتِ النَّصارَى ابْنَ مَرْيَمَ، فإنَّما أنا عَبْدُه؛ فقولوا: عبدُ اللهِ ورسولُه)). رواه البخاري.

وشهادةُ أن مُحمَّدًا رسولُ اللهِ تستلزمُ ثلاثةَ أمورٍ عظيمةٍ هي:
1: مَحَبَّتُه صلى الله عليه وسلم، بل يَجِبُ علينا أن نُقدِّمَ مَحَبَّتَه صلى الله عليه وسلم على مَحَبَّةِ النفسِ والأهلِ والوَلَدِ.
فعن أنسِ بنِ مالكٍ رضِي الله عنه عن النبيِّ صلى الله عليه وسلم أنه قال: ((لا يُؤْمِنُ أحَدُكم حتى أكونَ أحَبَّ إليه من وَلَدِه ووَالِدِه والناسِ أجْمَعينَ)). متفق عليه.
2: تصديقُ ما أخْبَرَ به من أُمورِ الغيبِ وغيرِه، فكلُّ ما صَحَّ عن النبيِّ صلى الله عليه وسلم فهو حَقٌّ وصِدْقٌ.
3: طاعتُه صلى الله عليه وسلم، وذلك بامتثالِ أوامرِه، واجتنابِ نواهيه.
وشهادةُ أن مُحمَّدًا رسولُ الله صلى الله عليه وسلم أصلٌ عظيمٌ من أصولِ الدينِ، بل لا يَدْخُل العبدُ في الإسلامِ حتى يَشْهَدَ أن مُحمَّدًا رسولُ اللهِ، وإذا ارتكَبَ العبدُ ما يَنْقُضُ هذه الشهادةَ فليسَ بمُسلمٍ، بل هو كَافِرٌ مُرتَدٌّ عن دينِ الإسلامِ.

ومِمَّا يَنْقُضُ هذه الشهادةَ:
1: بُغْضُ النبيِّ صلى الله عليه وسلم، وسبُّه والاستهزاءُ به وبما جاء به من شرائعِ الدين، فمَن فعَلَ ذلك فهو كافرٌ بالرسولِ صلى الله عليه وسلم، قال اللهُ تعالى: ﴿فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤْمِنُونَ حَتَّى يُحَكِّمُوكَ فِيمَا شَجَرَ بَيْنَهُمْ ثُمَّ لَا يَجِدُوا فِي أَنْفُسِهِمْ حَرَجًا مِمَّا قَضَيْتَ وَيُسَلِّمُوا تَسْلِيمًا﴾ [النساء: 65].
2: تكذيبُ النبيِّ صلى الله عليه وسلم، والشَّكُّ في صِدْقِه؛ لأن كلاًّ من المُكذِّبِ والشَّاكِّ غيرُ مُصَدِّق، ومن لم يُصَدِّق الرسولَ صلى الله عليه وسلم فهو غيرُ مُؤمِنٍ به.
3: الإعراضُ عن طاعةِ الرسولِ؛ فيَرَى أنها لا تَلْزَمُه، أو يُعْرِضُ عنها إعراضًا مُطْلقًا؛ فلا يُبالِي بأوامرِ الرسولِ صلى الله عليه وسلم ونواهيه.
أما مَن كان يُؤمِن باللهِ ورسولِه، ويَفْعَلُ بعضَ المعاصي من غيرِ نَواقِضِ الإسلامِ؛ فهذا من عُصاةِ المسلمين، ولا نُكفِّرُه بسَبَبِ مَعْصِيَتِه، بل نرجو له من اللهِ العَفْوَ والمَغْفِرَةَ، ونَخْشَى عليه العذابَ الأليمَ بسَبَبِ عِصْيانِه.
وكلُّ مَن ارتكَبَ شيئًا من هذه النواقضِ التي تَنْقُضُ شهادةَ أن مُحَمَّدًا رسولُ اللهِ فهو غيرُ مُؤمِنٍ بالرسولِ صلى الله عليه وسلم، وإنْ نَطَقَ بالشَّهادةِ بلسانِه؛ فحالُه كحالِ المنافقين الذين قال اللهُ فيهم: ﴿إِذَا جَاءَكَ الْمُنَافِقُونَ قَالُوا نَشْهَدُ إِنَّكَ لَرَسُولُ اللَّهِ وَاللَّهُ يَعْلَمُ إِنَّكَ لَرَسُولُهُ وَاللَّهُ يَشْهَدُ إِنَّ الْمُنَافِقِينَ لَكَاذِبُونَ﴾ [المنافقون: 1].
فلا تَصِحُّ هذه الشَّهادةُ مِن عبدٍ حتى يَقومَ بمُقْتضاها من المَحبَّةِ والتصديقِ والطاعةِ.
وهذه الشَّهادةُ ليستْ كَلِمةً تُقالُ فحَسْبُ؛ بل هي مِنْهاجُ حَياةِ المسلمِ، وعليها مَدارُ عَمَلِه، وبتحقيقِها تَتحَقَّقُ نجاتُه وسعادتُه.
واللهُ تعالى لا يَقْبَلُ من عبدٍ عَمَلاً حتى يكونَ خَالِصًا له جل وعلا، وصوابًا على سُنَّة رسولِه صلى الله عليه وسلم.
فالإخلاصُ هو مُقْتضَى شَهادةِ أن لا إلهَ إلا اللهُ.
والمُتابَعَةُ هي مُقْتَضَى شَهادةِ أن مُحمَّدًا رسولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم.
والعبدُ لا يَكونُ مُتَّبِعًا للهُدَى حتى يكون مخلصاً لله متبعاً سُنَّةَ رسول اللهِ صلى الله عليه وسلم.
وكلُّ عَمَلٍ ليس على سُنَّةِ النبيِّ صلى اللهُ عليه وسلم فهو بَاطِلٌ مَرْدودٌ؛ لقولِ النبيِّ صلى الله عليه وسلم: (( مَن عَمِلَ عَمَلاً ليسَ عليه أَمْرُنا فهو رَدٌّ )) رواه مُسْلمٌ من حديثِ عائشةَ رضِي الله عنها.
وفي صحيحِ مُسلمٍ أيضًا من حديثِ جابرِ بنِ عبدِ اللهِ رضِي الله عنهما أن النبيَّ صلى الله عليه وسلم كان يقولُ في خُطْبتِه: (( أما بعدُ، فإنَّ خيرَ الحديثِ كتابُ اللهِ، وخيرَ الهَدْيِ هَدْيُ مُحمَّدٍ، وشرَّ الأمورِ مُحْدثاتُها، وكلَّ بدعةٍ ضَلالةٌ )).

والمُبتدِعُ عاصٍ للرسولِ صلى الله عليه وسلم غيرُ مُتَّبِعٍ للهُدَى، وهو ضالٌّ ببِدْعتِه، والبِدَعُ على قِسْمين:
ــ بِدَعٌ مُكفِّرةٌ
ــ وبِدَعٌ مُفسِّقَةٌ
فالبدعُ المُكفِّرةُ هي التي تَتضمَّنُ ارتكابَ ناقضٍ من نواقضِ الإسلامِ؛ إما بصَرْفِ عبادةٍ لغيرِ اللهِ عز وجل، أو تكذيبِ اللهِ ورسولِه، أو غير ذلك من النواقض، وصاحبُها كافرٌ مرتدٌّ عن دينِ الإسلامِ، ومثالُها: دَعْوَى بعضِ الفِرَقِ أن القرآنَ ناقصٌ أومُحرَّفٌ، ودَعْوَى بعضِ الفِرَقِ أن بعضَ مُعَظَّميهم يعلمون الغَيْبَ.
والبدعُ المُفسِّقةُ هي التي لا تَتضمَّنُ ارتكابَ ناقضٍ من نواقضِ الإسلامِ، ومثالُها: تَخْصيصُ بعضِ الأمكنةِ والأزمنةِ بعباداتٍ لم يَرِدْ تَخْصيصُها بها كالموالدِ النَّبويَّةِ.

· وهَدْيُ النبيِّ صلى الله عليه وسلم هو أحسنُ الهَدْي؛ وكمالُ العبدِ وفلاحُه إنما هو على قَدْر اتباعِه للهَدْي النبويّ؛ فكلما كان العبدُ أحسنَ اتباعًا كان أعظم ثواباً وأكرم حالاً ومآلاً ، وأقربَ إلى السلامةِ من الشُّرورِ والآثامِ وعُقوباتِ الذنوبِ المُترتِّبةِ على مخالفةِ هديه صلى الله عليه وسلم.
فإنَّ النبيَّ صلى الله عليه وسلم لم يَأْمُر إلا بما هو خيرٌ للعبدِ في دينِه ودنياه، ولم يَنْهَ إلا عما فيه مَفْسَدةٌ ومَضَرَّةٌ؛ وقد حُفَّت الجنَّةُ بالمَكارِهِ، وحُفَّت النار بالشهواتِ، فمَن كان ذا يَقينٍ بصِدْق الرسولِ صلى الله عليه وسلم اتبعَ هديَه واجتنَبَ الشهواتِ المُحرَّمَةَ وإن كانت تَهْواهَا نفسُه، وصَبَر على المَكَارِه المُحْتَملةِ لمعرفتِه بأحوالِ العواقبِ؛ فَسَلِمَ من العذابِ الأليم، وفاز بالثوابِ العظيمِ.

· وأما من خالَفَ هَدْي النبي صلى الله عليه وسلم فارتكب ما تهواه نفسُه من المُحرَّمات فإنَّه لا يأمَنُ أن يُعاقَبَ على ذنبِه بعقوباتٍ في دينِه أو دنياه.
وقد قال اللهُ تعالى: ﴿فَلْيَحْذَرِ الَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنْ أَمْرِهِ أَنْ تُصِيبَهُمْ فِتْنَةٌ أَوْ يُصِيبَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ﴾ [النور: 63].
فَفِعْلُ المعصية قد يَجُرُّ إلى فتنةٍ في الدين لا يَثْبُتُ فيها العبدُ فيَضِلُّ ويَهْلِكُ، وقد يُصيبُه على ذنبِه عذابٌ أليمٌ في الدنيا أو في قَبْرِه أو يوم القيامةِ.
· وأما المُتَّبِع لهَدْي النبي صلى الله عليه وسلم فهو في أمانٍ وسَكينةٍ وطُمَأنينةٍ، لا يَخافُ ولا يَحْزَنُ، ولا يَضِلُّ ولا يَشْقَى؛ لأنه قد سَلَك سُبَلَ السلامةِ من المخاوف والأحزان والضلال والشقاء في الدنيا والآخرةِ، قال اللهُ تعالى: ﴿يَا أَهْلَ الْكِتَابِ قَدْ جَاءَكُمْ رَسُولُنَا يُبَيِّنُ لَكُمْ كَثِيرًا مِمَّا كُنْتُمْ تُخْفُونَ مِنَ الْكِتَابِ وَيَعْفُو عَنْ كَثِيرٍ قَدْ جَاءَكُمْ مِنَ اللَّهِ نُورٌ وَكِتَابٌ مُبِينٌ (15) يَهْدِي بِهِ اللَّهُ مَنِ اتَّبَعَ رِضْوَانَهُ سُبُلَ السَّلَامِ وَيُخْرِجُهُمْ مِنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ بِإِذْنِهِ وَيَهْدِيهِمْ إِلَى صِرَاطٍ مُسْتَقِيمٍ (16)﴾ [المائدة: 15–16].
وقد فرَضَ اللهُ على رسولِه تبليغَ الرسالةِ، فبلَّغَها كما أُمِر، قال اللهُ تعالى:﴿يَا أَيُّهَا الرَّسُولُ بَلِّغْ مَا أُنْزِلَ إِلَيْكَ مِنْ رَبِّكَ﴾ [المائدة: 67].
وأوجَبَ اللهُ تعالى علينا طاعتَه فقال: ﴿قُلْ أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ فَإِنْ تَوَلَّوْا فَإِنَّمَا عَلَيْهِ مَا حُمِّلَ وَعَلَيْكُمْ مَا حُمِّلْتُمْ وَإِنْ تُطِيعُوهُ تَهْتَدُوا وَمَا عَلَى الرَّسُولِ إِلَّا الْبَلَاغُ الْمُبِينُ﴾ [النور: 54].
والرسولُ قد حُمِّلَ أمانةَ تبليغِ الرسالةِ، فأدَّاها كما أرادَ اللهُ، وقد سأل الناسَ في الجَمْع العظيمِ في حَجَّة الوداعِ: ((ألا هل بَلَّغْتُ؟))؛ فقالوا: نعم.
فقال: ((اللهم اشْهَدْ)).
ونحن نَشْهَدُ أنه قد بلَّغ الرسالةَ، وأدَّى الأمانةَ، ونصَحَ الأُمَّةَ، وجاهَدَ في اللهِ حقَّ جِهادِه حتى أتاه اليقينُ.
ونحن حُمِّلنا أمانةَ اتباعِ الرسولِ ظاهرًا وباطنًا؛ فمَن وَفَّى بهذه الأمانةِ أفْلَحَ ونَجَا، وفازَ بالثوابِ العظيمِ، ومَن خانَ هذه الأمانةَ خَسِر خُسرانًا عظيمًا، وقد قال اللهُ تعالى: ﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَخُونُوا اللَّهَ وَالرَّسُولَ وَتَخُونُوا أَمَانَاتِكُمْ وَأَنْتُمْ تَعْلَمُونَ﴾ [الأنفال: 27].

طاهر جبريل دكو
_27 _March _2013هـ الموافق 27-03-2013م, 07:30 PM
Darasi nabiyu: bayani gameda ma'anar Shahadatu anna Muhammadar Rasulu-llahi (S.A.W)



Shaidawa (Annabi) Muhammadu (S.A.W) Manzon Allahne yana hukunta yin imani cewa Allah (Madawkakin Sarki) Ya aiko Annabinsa Muhammadu dan Abdullahi dan Abdul muddalib a matsayin Manzo zuwaga Aljannu da Mutane baki daya, yana umurtansu da bawtan Allah Shi kadai da kuma nisantan abubuwanda ake bawta koma bayan Allah (Mai girma da dawkaka) kuma ya bayyana musu shari'o'in addini.



Kuma (Shaidawa –Annabi - Muhammadu Manzon Allahne) yana hukunta yin imani cewa lallai shi Bawan Allahne kuma Manzon Allah, bashida wani hakkina (cancantan) bawta, kuma bai halatta mu wuce gona da iri cikin yabonsaba ballantana mu sifantashi da sifofi dasuka kebanta ga Allah (Mai girma da dawkaka).



Daga Abdullahi dan Abbas (Allah Ya kara musu yarda) (yana cewa): lallai yaji Umar dan Khaddabi (Allah Ya kara masa yarda) akan minbari yana cewa: Naji Annabi (S.A.W) yana cewa:



((لا تُطْرُوني كما أَطْرَتِ النَّصارَى ابْنَ مَرْيَمَ، فإنَّما أنا عَبْدُه؛ فقولوا: عبدُ اللهِ ورسولُه)). رواه البخاري.

Ma'ana:" Kada kuwuce iyaka cikin yabona kamar yadda Nasara suka wuce iyaka gameda Isa dan Maryam, ni bakomai bane face bawa, saboda haka kuce bawan Allah kuma ManzonSa" Bukharine ya ruwaitoshi.



Kuma Shaidawa (Annabi) Muhammadu Manzon Allahne yana lazimta abubuwa guda uku muhimmai, sune:



1- sonsa (S.A.W) kai (bama haka kawiba), yawajaba akanmu mugabatadda sonsa (S.A.W) bisaga son kawukanmu da iyalanmu da yayanmu.



daga Anas dan Malik (Allah Ya kara masa yarda) daga Annabi (S.A.W) lallai yace:



((لا يُؤْمِنُ أحَدُكم حتى أكونَ أحَبَّ إليه من وَلَدِه ووَالِدِه والناسِ أجْمَعينَ)). متفق عليه.

Ma'ana:" Dayanku bazaiyi imani ba har sai naïf soyuwa agareshi bisaga dansa da mahaifinsa dama mutane baki daya". Bukhari da Muslim.



2 - Gaskata shi cikin abinda yabayar na labaru akan al'amuran gaibu da waninsa, saboda haka duk abinda ya inganta daga Annabi (S.A.W) hakikane kuma gaskiyane.



3 - Yi masa da'a ta hanyar aikata abubuwanda yayi umurni dasu da nisantan abubuwanda yayi hani



Kuma shaidawa Annabi (S.A.W) Manzon Allahne tushene maigirma daga cikin tussah na Addinin (Musulunci), kai bawa bai zama Musulmi bama har sai yashaida cewa lallai Annabi Muhammadu Manzon Allahne, kuma idan ya aikata wani abu dayake warware wannan shahadar to(daganan) shi ba Musulmi bane, kai, shi kafirinema wanda yayi ridda yabar Addinin Musulunci.



Daga ckin abubuwanda ke warware wannan shahadar:



1- Kin Annabi (S.A.W), da zaginsa da yin isgilanci gareshi ko ga abinda yazo dashi na hukunce hukuncen Addini, duk wanda ya aikata wannan ya kafircewa Manzon Allah (S.A.W). Allah (Madawkakin Sarki) Yace:



﴿فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤْمِنُونَ حَتَّى يُحَكِّمُوكَ فِيمَا شَجَرَ بَيْنَهُمْ ثُمَّ لَا يَجِدُوا فِي أَنْفُسِهِمْ حَرَجًا مِمَّا قَضَيْتَ وَيُسَلِّمُوا تَسْلِيمًا﴾ [النساء: ٦٥].

Ma'ana: " Ina rantsuwa da Ubangijinka bazasuyi imaniba har sai sun sanyaka mahukunci gameda abubuwanda ke faruwa atsakaninsu sannan kada suji wani kunci azukatansu gameda hukuncin da kayi, kuma su sallama sallamawa. Q4: V65.



2- Karyata Annabi (SAW) da yin shakka gameda gaskiyarsa. Saboda kowane daya tsakanin wanda ya karyata (shi) da wanda yayi shakka (game da gaskiyarsa) bai (cikin) masu gaskatawa, duk wanda ko bai gaskata manzon (Allah S.A.W) ba, to (lallai) baiyi imani dashiba.



3- Juya baya daga barin yiwa Manzon Allah biyayya, kamar yaga cewa lallai (yiwa manzon Allah biyayya) ba wajibi bane akansa ko kuma yakawar dakai daga (yin biyayyan) baki daya, bai damuwa da umurni ko hanin Manzon Allah (S.A.W).



Amma shi wanda ya kasance yana imani da Allah da Manzonsa amma yana aikata wani sashi na ayyukan sabon (Allah), aikinda bai cikin abubuwanda ke warware Musulunci, to wannan yana cikin Musulmai masu sabo, bazamu kafirtashiba asakamakon wannan sabon nasa, saidai muna masa fatan afuwr Allah da gafarasSa, kuma muna jiye masa tsoron azabar Allah mai radadi asakamakon fushinSa.



Kuma duk wanda ya aikata wani abu daga cikin wadannan abubuwanda ke warware Shahadatu anna Muhammadar Rasulu-llahi (S.A.W) to (lallai) baiyi imani da Manzon Allah (S.A.W) ba, koda kuwa ya furta shahadar da harshensa. Halinsa zai zama tamkar halin Munafukanda Allah Yace gamedasu:



﴿إِذَا جَاءَكَ الْمُنَافِقُونَ قَالُوا نَشْهَدُ إِنَّكَ لَرَسُولُ اللَّهِ وَاللَّهُ يَعْلَمُ إِنَّكَ لَرَسُولُهُ وَاللَّهُ يَشْهَدُ إِنَّ الْمُنَافِقِينَ لَكَاذِبُونَ﴾ [المنافقون: ١].

Ma'ana:" Idan Munafukai sukazo gareka sai su dawra cewa; mun shaida cewa kai Manzon Allahne. (lallai) Allah Yasan (cewa) kai ManzonSane, kuma Allah Ya shaida cewa lallai munafukai makaryatane. Q63: V1.



Saboda haka wannan shahadar bata inganta daga bawa har sai ya aikata abubuwanda take hukuntawa na soyayya da gaskatawa da biyayya.



Kuma ita wannan shahadar ba wai zancen da za'a furta da baka bane kawai tawadatar, a'a ita dai (wannan shahadar) itace tsarin rayuwar Musulmi (baki dayansa) kuma akanta ayyukansa ke kaikomo, kuma da tabbatadda itane tsirarsa da rabawtansa ke tabbata.



Allah baYa karban wani aiki daga bawa har sai (aikin) ya kasance tsarkakakke ga Allah (Mai girma da dawkaka) kuma ya zama daidai bisa sunnar Manzon Allah (S.A.W).



Saboda haka shi ikhlasi shine (yake kunshe da) ma'anar Shahadatu- allaa'ilaaha'illa-llahu (wato shaidawa babu abin bawtawa dagaskiya sai Allah).



Koyi da Manzon Allah (S.A.W) kuma shike kunshe da ma'anar Shahadatu anna Muhammadar-Rasulu- llahi (S.A.W). (wato shaidawa lallai Annabi Muhammadu Manzon Allah ne)



Kuma bawa bazai kasance mai bin tafarki (madaidaiciba) har saiya kasance mai ikhlasi ga Allah (wato mai tsarkake ibada ga Allah) kuma mai koyi da sunnar Manzon Allah (SAW).



Dukkanin aikin da bai kasance bisa sunnar Annabi (S.A.W) ba, to lalataccene abin maidawa, saboda fadin Annabi (SAW):



(( مَن عَمِلَ عَمَلاً ليسَ عليه أَمْرُنا فهو رَدٌّ )) رواه مُسْلمٌ من حديثِ عائشةَ رضِي الله عنها.

Ma'ana: "Duk wanda ya aikata wani aiki (wato na ibada) wanda babu umurninmu acikinsa to an mayar masa". Muslim ne ya ruwaitoshi daga hadisin A'isha(Allah ya kara mata yarda).



Kuma yazo cikin sahihu Muslim -harwayau- daga hadisin Jabir dan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda) cewa Annabi (S.A.W) ya kasance yana fada ahudubansa (yana cewa):



(( أما بعدُ، فإنَّ خيرَ الحديثِ كتابُ اللهِ، وخيرَ الهَدْيِ هَدْيُ مُحمَّدٍ، وشرَّ الأمورِ مُحْدثاتُها، وكلَّ بدعةٍ ضَلالةٌ )).

Ma'ana:"Bayan haka, lallai mafi alherin zance shine zancen Allah, kuma mafi alherin shiriya itace shiriyar Muhammad, kuma mafi sharrin al'amura sune kirkirarrunsu kuma dukkanin bidi'a batace".



Shi dan bidi'a mai sabawa Manzon Allahne (S.A.W) ba mabiyin shiriya bane, kuma shi bataccene sakamakon bidi'arnan tasa.



Kuma ita bidi'a iri biyuce, bidi'ar dake kafirtarwa, da bidi'ar dake fasikantarwa.



Bidi'ar da take kafirtarwa itace wacce take kunsheda aikata wani abu daga abubuwa masu warware Musulunci; kodai aikata wata ibada ga wanin Allah (mai girma da dawkaka) ko kuma karyata ManzonSa ko kuma wanin haka daga cikin abubuwanda ke warware musulunci. Ma'abucin (irin wannan bidi'ar kuwa) kafirine wanda yayi ridda ya bar addinin Musulunci.



Misalinta (shine) da'awarda wasu daga cikin bangarori (masu amsa sunan musulunci) keyi nacewa wai Alqur'ani yanada tawaya ko kuma jirkitaccene, da kuma irin da'awarda wasu bangarori keyi na cewa wai wasu daga cikin (shehunnan su) wadanda suke girmamawa sunada ilimin gaibu.



Itako bidi'a mai fasikantarwa itce wacce take batakunshi wani aiki dake warware Musulunciba, misalinta (shine); kebance wasu wurare da wasu lokuta ga wasu ibadu wanda dalili baizo akan kebancesu dashi ba kamar (bikin) mawlidin Annabi (SAW).



Shiriyar Manzon Allah (S.A.W) itace mafi kyawun shiriya, kuma kamalar bawa da rabawtansa kadai ya dangantane da gwargwadon biyayyarsa ga shiriyar Mazon Allah (S.A.W), saboda haka duk sa'adda biyayyar mutum ta kasance mafi yawa to sakamakonsa ma yakan figirma kuma yakasance mafi dawkaka (a cikin yanayinsa) anan (duniya) harma da makoma, kuma yafi kusanci zuwga kubuta daga sharrurruka da laifuffuka da ukubobi da zunubbai wanda ke faruwa asakamakon sabawa shiriyar Manzon Allah (SAW).



Don haka, (mu sani cewa) shi Annabi (S.A.W) baiyi umurniba face da abinda ke zama alheri ga bawa acikin addininsa da duniyarsa. Kuma baiyi hani ba face gameda abubuwanda ke bannatarwa da cutarwa, lallai an gewaye Aljanna da abubuwanda (rai) bayaso an kuma gewaye Wuta da abubuwana shi'awa. Saboda haka duk wanda keda yakini gameda gaskiyar Annabi (S.A.W) zaibi shiriyarsa kuma zai nisanci abubuwan shi'awa haramtattu koda kuwa (ransa ta riyamasa) son (wadannan abubuwan ), sai ya doge akan abubuwannan da rai ke hakuri dasu masu wahala saboda saninsa gameda (sakamako) a karshen al'amari; sakamakon haka, saiya kubuta daga azaba mai radadi ya rabawta da lada mai girma.



Amma shiko wanda ya sabawa shiriyar Manzon Allah (S.A.W), kuma ya aikata abinda ransa keso daga haramtattun abubuwa, to lallai shi (mai irin wannan sifar) bashida (tabbacin) amintuwa daga ukuba acikin addininsa ko aduniyarsa asakamakon zunubbansa. Allah (Madawkakin sarki) Yana cewa:



﴿فَلْيَحْذَرِ الَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنْ أَمْرِهِ أَنْ تُصِيبَهُمْ فِتْنَةٌ أَوْ يُصِيبَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ﴾ [النور: ٦٣].

Ma'ana:"Masu sabawa umurninsa (wato Manzon Allah (S.A.W)) su hanu (daga saba masa) saboda kada wata fitina tashafesu ko kuma wata azaba mai radadi. Q24: ayata63.



Saboda haka, aikata sabon (Allah) yana iya kaiwa zuwaga fitinuwa acikin addini, sai bawa ya gagara samun sabati acikinsa, sakamakon haka sai ya bata (daga tafarki) kuma yahalaka, kuma azaba mairadadi na iya shafansa anan duniya ko acikin kabarinsa ko kuma ranar tashin alkiyama.



Amma shiko wanda yabi shiriyar Manzon Allah (S.A.W), to yana cikin aminci da nutsuwa da kwanciyar hankali, bazai ji tsoroba kuma bazaiyi bakin cikiba, bazai baceba kuma bazai tabeba, saboda ya riga ya shiga tafarkin amintuwa daga ababen tsoro da ababen bakin ciki da bata da tabewa anan duniya da ranan karshe. Allah (Madawkakin sarki) Yace:



﴿يَا أَهْلَ الْكِتَابِ قَدْ جَاءَكُمْ رَسُولُنَا يُبَيِّنُ لَكُمْ كَثِيرًا مِمَّا كُنْتُمْ تُخْفُونَ مِنَ الْكِتَابِ وَيَعْفُو عَنْ كَثِيرٍ قَدْ جَاءَكُمْ مِنَ اللَّهِ نُورٌ وَكِتَابٌ مُبِينٌ (15) يَهْدِي بِهِ اللَّهُ مَنِ اتَّبَعَ رِضْوَانَهُ سُبُلَ السَّلَامِ وَيُخْرِجُهُمْ مِنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ بِإِذْنِهِ وَيَهْدِيهِمْ إِلَى صِرَاطٍ مُسْتَقِيمٍ (16)﴾ [المائدة: ١٥–١٦].

Ma'ana:" Yaku ma'abuta littafi (wato Yahudu da Nasara) hakika ManzonMu yazo muku yana mai bayyana muku abubuwa masu yawa daga cikin abubuwanda kuka kasance kuna boyewa daga cikin Littafi(Attawra da Injila) yana kuma afuwa gameda abubuwa masu yawa, hakika wani haske da Littafi bayyananne (mai bayani) yazo muku daga Allah (15) Dashine Allah Yake shiryar da wadanda sukabi yardansa (zuwaga) tafarkin aminci kuma Ya fitar dasu daga duffai zuwaga haske da izininSa kuma Ya shiryar dasu zuwaga hanya madaidaiciya. Q5: ayata15 da 16.



Kuma hakika Allah Ya farlantawa Annabi (S.A.W) isarda manzanci kuma hakika (Annabi (S.A.W)) ya isar da shi kamar yadda aka umurceshi. Allah (Madawkakin sarki) Yace:



﴿يَا أَيُّهَا الرَّسُولُ بَلِّغْ مَا أُنْزِلَ إِلَيْكَ مِنْ رَبِّكَ﴾ [المائدة: ٦٧].

Ma'ana:"Ya kai wannan Manzon, ka isar da abinda aka sawkar maka daga ubangijinka…" Q5: ayata64..



Mu kuma Allah Ya wajabta mana yi masa biyayya sai Yace:



﴿قُلْ أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ فَإِنْ تَوَلَّوْا فَإِنَّمَا عَلَيْهِ مَا حُمِّلَ وَعَلَيْكُمْ مَا حُمِّلْتُمْ وَإِنْ تُطِيعُوهُ تَهْتَدُوا وَمَا عَلَى الرَّسُولِ إِلَّا الْبَلَاغُ الْمُبِينُ﴾ [النور: ٥٤].

Ma'ana:" Kace (musu ya Muhammadu) ku yiwa Allah biyayya kuma kuyiwa Manzon (Allah) biyayya, to idan suka juya baya (suka ki yin biyayyan, su sani cewa); abinda aka wajabta masa kawai shine akansa, haka kuma abinda aka wajabta muku shine akanku. Kuma indan kukayi masa biyayya (zakusamu) shiriya, kuma babu wani abu akan Manzon (Allah) face isarwa bayyananne. Q24: ayata54.



Shidai Manzo (wato Annabi Muhammadu (S.A.W)) an dawra masa amanar isarda sakon Manzancine, kuma ya isar da shi kamar yadda Allah Ya so, hakika (Annabi Muhammadu (S.A.W)) ya tambayi mutane acikin gagarumin taro a (shekaran) hajjijn bankwana (yace musu):



"shin na isar ( wato da manzanci)?"sai suka amsa da cewa ; na'am ka isar. Sai Annabi (S.A.W) yace: "Ya Allah Ka shaida".

Kuma muma muna shaidawa cewa lallai ya isar da sakon (Allah) ya kuma sawke amanan ( da Allah ya dawra masa) ya kuma yi nasiha ga al'umma ya kuma yi jihadi saboda Allah hakikanin jihadinsa har saida yakini (wato mutuwa) tazo masa.



Mu kuma an dawra mana amanar bin Manzon Allah afili da boye, saboda haka duk wanda ya cika wannan amanar, to ya rabawta kuma ya tsira kuma ya samu rabo mai girma, shiko wanda ya ha'inci wannan amanar, yayi asara asara mai girma. Allah (Madawkakin Sarki) Yace:



﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَخُونُوا اللَّهَ وَالرَّسُولَ وَتَخُونُوا أَمَانَاتِكُمْ وَأَنْتُمْ تَعْلَمُونَ﴾ [الأنفال: ٢٧].

Ma'ana:" Yaku wadanda suka yi imani, kada kuha'inci Allah da Manzon (Sa) kuma kuha'inci amanoninku alhali kuna sani. Q8 ayata28.