تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : الدرس الاول بيان معنى شهادة ان لا اله الا الله


عبد الله الداخل
_21 _March _2013هـ الموافق 21-03-2013م, 03:49 PM
معْنَى الشهادتين

الشهادتان هما: شهادةُ أن لا إلهَ إلا اللهُ، وشهادةُ أن مُحمَّدًا رسولُ اللهِ.
وهما أصلُ دينِ الإسلامِ ورُكْنُه الأولُ الذي به يَدْخُلُ العبدُ في دينِ الإسلامِ، فمَن لم يَشْهدِ الشهادتين فليسَ بمُسْلمٍ.
عن عبدِ اللهِ بنِ عُمرَ رضِي اللهُ عنهما عن النبيِّ صلى اللهُ عليه وسلَّم أنه قال: ((بُنِي الإسلامُ على خَمْسٍ: شهادةِ أن لا إله إلا اللهُ وأن مُحمَّدًا رسولُ اللهِ، وإقامِ الصلاةِ، وإيتاءِ الزكاةِ، وحَجِّ البيتِ، وصومِ رمضانَ)). متفق عليه.
فكان أوَّلُ ما يَجِبُ على العبدِ تعلُّمُه من دينِ الإسلامِ هو أصلَه الأَوَّلَ، فيَعْرِفُ معنى الشهادتين وأحكامَهما.
ولما بَعَثَ النبيُّ صلَّى الله عليه وسلم معاذَ بنَ جَبَلٍ إلى اليمنِ داعياً ومعلِّماً قال له: ((إنَّك تأتي قوماً من أهلِ الكتابِ فَادْعُهم إلى شهادةِ أنْ لا إلهَ إِلا الله وَأني رسولُ اللهِ؛ فإِنْ هُمْ أطاعوا لِذلكَ فأَعْلِمْهم أنَّ اللهَ افْتَرضَ عليهم خمسَ صَلَوَاتٍ في كلِّ يومٍ وَليلةٍ)) .. الحديث، رواه مسلم من حديث ابن عباس.
ورواه البخاري أيضاً ولفظه: ((فليكن أوَّلَ ما تدْعوهم إلى أن يوحِّدوا اللهَ))
وبيان ذلك أيضاً في حديثِ جِبْريلَ الطويلِ الذي سأل فيه النبيَّ صلى الله عليه وسلم عن مَرَاتِبِ الدِّينِ: الإسلامِ والإيمانِ والإحسانِ، ثم قال النبيُّ صلى الله عليه وسلم لأصحابه كما في آخِرِ الحديثِ: (( هذا جِبْريلُ أتاكم يُعلِّمُكم دِينَكُم )).
فأوَّلُ ما يَجِبُ تَعلُّمُه من أُمورِ الدينِ ما تَضَمَّنَه حديثُ جبريلَ، وأوَّلُ مرتبة من مراتب الدين مرتبة الإسلام، وأول ركن من أركان الإسلام: الشهادتانِ.



الدرس الأوَّل: بيانُ معنَى شهادةِ أن لا إلهَ إلا اللهُ

(لا إلهَ إلا اللهُ) أي لا مَعْبودَ بحقٍّ إلا اللهُ.
والإلهُ: هو المألوهُ، أي المَعْبودُ.
فكلُّ ما يُعْبَدُ من دونِ اللهِ فعبادتُه باطلةٌ، وَمَن عبدَ غيرَ اللهِ فهو مُشرِكٌ كافِرٌ، كما قال اللهُ تعالى:﴿وَمَنْ يَدْعُ مَعَ اللَّهِ إِلَهًا آخَرَ لَا بُرْهَانَ لَهُ بِهِ فَإِنَّمَا حِسَابُهُ عِنْدَ رَبِّهِ إِنَّهُ لَا يُفْلِحُ الْكَافِرُونَ﴾ [المؤمنون: 117].
فلا يَجوزُ أن يُعبَدَ مع اللهِ أحَدٌ، لا نَبِيٌّ مُرسَلٌ، ولا مَلَكٌ مُقرَّبٌ، ولا وَلِيٌّ من الأولياءِ الصالحين، ولا شَجَرٌ ولا حَجَرٌ، ولا غيرُ ذلك؛ لأن العبادةَ حقٌّ للهِ وحدَه، خَلَقَنا لأجلِها كما قال تعالى: ﴿وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ (56)﴾ [الذاريات: 56].
وقال تعالى: ﴿قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ﴾ [الإخلاص: 1].
وقال: ﴿وَإِلَهُكُمْ إِلَهٌ وَاحِدٌ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ الرَّحْمَنُ الرَّحِيم (163)﴾ [البقرة: 163].
وقال: ﴿هُوَ الْحَيُّ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ فَادْعُوهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ﴾ [غافر: 65].
وهذا هو معنَى التَّوْحيدِ، وهو إفرادُ اللهِ بالعبادةِ، فلا نَعْبُدُ إلا اللهَ وحدَه لا شريكَ له.
وبهذا التوحيدِ الذي هو معنَى (لا إلهَ إلا اللهُ) بَعَثَ اللهُ الرُّسلَ كلَّهم؛ قال اللهُ تعالى: ﴿وَمَا أَرْسَلْنَا مِنْ قَبْلِكَ مِنْ رَسُولٍ إِلَّا نُوحِي إِلَيْهِ أَنَّهُ لَا إِلهَ إِلَّا أَنَا فَاعْبُدُونِ (25)﴾ [الأنبياء: 25].
وقال: ﴿وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَسُولًا أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوتَ﴾ [النحل: 36].
وقد قَصَّ اللهُ علينا في كتابِه الكريمِ أنباءَ الرُّسلِ معَ أقوامِهم ، وبَيَّن لنا أنَّ أوَّلَ دعوةَ الرُّسُلِ كانت إلى توحيدِ اللهِ عزَّ وجلَّ، وبَيَّن لَنا عُقبَى المؤمنين الذين استجابوا لدعوةِ المُرْسَلين؛ وعاقبةَ الذين كَذَّبوا الرُّسلَ وأشركوا باللهِ ما لم يُنزِّلْ به سُلطانًا.
ــ قال اللهُ تعالى: ﴿لَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَى قَوْمِهِ فَقَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ مَا لَكُمْ مِنْ إِلَهٍ غَيْرُهُ إِنِّي أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ (59)﴾ [الأعراف: 59].
ــ وقال: ﴿وَإِلَى عَادٍ أَخَاهُمْ هُودًا قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ مَا لَكُمْ مِنْ إِلَهٍ غَيْرُهُ أَفَلَا تَتَّقُونَ(65)﴾ [الأعراف: 65].
ــ وقال: ﴿وَإِلَى ثَمُودَ أَخَاهُمْ صَالِحًا قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ مَا لَكُمْ مِنْ إِلَهٍ غَيْرُهُ﴾ [الأعراف: 73].
ــ وقال: ﴿وَإِلَى مَدْيَنَ أَخَاهُمْ شُعَيْبًا قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ مَا لَكُمْ مِنْ إِلَهٍ غَيْرُهُ﴾ [الأعراف: 85].
ــ وقال: ﴿وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ إِنَّنِي بَرَاءٌ مِمَّا تَعْبُدُونَ (26) إِلَّا الَّذِي فَطَرَنِي فَإِنَّهُ سَيَهْدِينِ (27)﴾ [الزخرف: 26-27].
ــ وقال: ﴿أَمْ كُنْتُمْ شُهَدَاءَ إِذْ حَضَرَ يَعْقُوبَ الْمَوْتُ إِذْ قَالَ لِبَنِيهِ مَا تَعْبُدُونَ مِنْ بَعْدِي قَالُوا نَعْبُدُ إِلَهَكَ وَإِلَهَ آبَائِكَ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَاعِيلَ وَإِسْحَاقَ إِلَهًا وَاحِدًا وَنَحْنُ لَهُ مُسْلِمُونَ﴾ [البقرة: 133].
ــ وقال يوسف عليه السلام: ﴿أَأَرْبَابٌ مُتَفَرِّقُونَ خَيْرٌ أَمِ اللَّهُ الْوَاحِدُ الْقَهَّارُ (39)﴾ [يوسف: 39].
وكذلك كانت دعوةُ النبيِّ صلى الله عليه وسلم إلى العالمين، كما قال الله تعالى: ﴿وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِلْعَالَمِينَ (107) قُلْ إِنَّمَا يُوحَى إِلَيَّ أَنَّمَا إِلَهُكُمْ إِلَهٌ وَاحِدٌ فَهَلْ أَنْتُمْ مُسْلِمُونَ (108)﴾ [الأنبياء: 107-108].
وقد بدأ النبيُّ صلى الله عليه وسلم دعوةَ قومِه بمَكَّةَ إلى التوحيدِ، فدعاهم إلى أن يقولوا: (لا إلهَ إلا اللهُ) ويَجْتنبُوا عِبادةَ الأصنامِ، فاستكبَرَ أكثرُهم وأَبَوْا أن يُجِيبوه إلى كلمةِ التوحيدِ؛ فكانوا كما قال اللهُ تعالى: ﴿إِنَّهُمْ كَانُوا إِذَا قِيلَ لَهُمْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ يَسْتَكْبِرُونَ (35) وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُو آلِهَتِنَا لِشَاعِرٍ مَجْنُونٍ (36)﴾ [الصافات: 35–36]. فردَّ اللهُ عليهم بقولِه: ﴿بَلْ جَاءَ بِالْحَقِّ وَصَدَّقَ الْمُرْسَلِينَ (37)﴾ [الصافات: 37].
فكلمةُ التوحيدِ هي كلمةُ الحقِّ التي دعا إليها المرسلون قبلَ النبيِّ صلى الله عليه وسلم، وهي دَعوةُ رسولنِا صلى الله عليه وسلم.
وقد فَهِم كُفَّارُ قُرَيشٍ أن الدعوةَ إلى التوحيدِ تَعْنِي تَرْكَ عبادةِ ما يَعْبُدون من دونِ اللهِ تعالى؛ فلا يَتَحَقَّقُ التوحيدُ إلا باجتنابِ الشِّركِ، وهذا هو معنَى (لا إلهَ إلا اللهُ).
وعن عُمَر بنِ الخَطَّاب رضِي الله عنه أن الرسولَ صلى الله عليه وسلم قال: ((أُمِرْتُ أن أُقاتِلَ الناسَ حتى يقولوا: (لا إلهَ إلا اللهُ) فمَن قال: (لا إلهَ إلا اللهُ) عَصَم مِنِّي مالَه ونَفْسَه إلا بحَقِّه، وحسابُه على اللهِ))متفق عليه.
ولمَّا بَعَثَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم برسائلِه إلى المُلوكِ دَعَاهم إلى توحيدِ اللهِ عز وجل؛ فعن ابنِ عَبَّاسٍ رضِي الله عنهما أن النبيَّ صلى الله عليه وسلم أرسَلَ إلى هِرَقْلَ مَلِكِ الرُّومِ: ((بسم الله الرحمن الرحيم، من مُحمَّدٍ رسولِ اللهِ إلى هِرَقْلَ عَظيمِ الرُّومِ، سَلامٌ على مَن اتَّبَعَ الهُدَى أمَّا بعدُ:
فإنِّي أدعوكَ بدِعايةِ الإسلامِ، أَسْلِمْ تَسْلَمْ، وأَسْلِمْ يُؤْتِكَ اللهُ أجْرَك مَرَّتين، فإن تَوَلَّيْتَ فإنَّ عليكَ إِثْمَ الأَرِيسِيِّينَ، و﴿يَا أَهْلَ الْكِتَابِ تَعَالَوْا إِلَى كَلِمَةٍ سَوَاءٍ بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ أَلَّا نَعْبُدَ إِلَّا اللَّهَ وَلَا نُشْرِكَ بِهِ شَيْئًا وَلَا يَتَّخِذَ بَعْضُنَا بَعْضًا أَرْبَابًا مِنْ دُونِ اللَّهِ فَإِنْ تَوَلَّوْا فَقُولُوا اشْهَدُوا بِأَنَّا مُسْلِمُونَ﴾ [آل عمران: 64])). متفق عليه.
وبَعَثَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم بنحوِ هذه الرسالةِ إلى كِسْرَى مَلِك الفُرْسِ، وإلى المُقَوْقِسَ مَلِك القِبْط، وإلى مَلِكِ الحَبَشَة، وإلى جَيْفَرٍ وعِيَاذٍ ابنَي الجُلَنْدَى بعُمَان، وإلى هَوْذَةَ بن علي باليَمامة، وإلى المُنْذِر بن سَاوَى بهَجَر، وإلى ابنِ أبي شَمِر الغَسَّاني، وهؤلاء هم المُلوكُ في زمانِه صلى الله عليه وسلم.
وفي صحيحِ مُسلمٍ من حديثِ أنسِ بن مالِكٍ رضِي الله عنه أن النبيَّ صلى الله عليه وسلم كتَبَ إلى كلِّ جَبَّار (أي مَلِكٍ) يَدْعُوهم إلى اللهِ تعالى.
وعن ابن عبَّاسٍ رضِي الله عنهما أن النبيَّ صلى الله عليه وسلم لَمَّا بعَثَ مُعاذًا إلى اليَمَن قال له: ((إنَّك تَقْدَمُ على قَوْمٍ من أهلِ الكتابِ، فَلْيَكُنْ أَوَّلَ ما تدعوهم إلى أن يُوحِّدوا اللهَ)).
فتوحيدُ اللهِ تعالى هو مِفْتاحُ الدخولِ في الإسلامِ، وبدونِه لا يكون المَرْءُ مُسلمًا، وإذا ارْتَكَبَ العبدُ ما يَنْقُضُ هذا التوحيدَ فهو كافرٌ مشركٌ خارجٌ عن مِلَّةِ الإسلامِ.
وعن مُعاذِ بن جَبَل رضِي الله عنه أن النبيَّ صلى الله عليه وسلم قال له: ((يا مُعاذُ، أتدري ما حَقُّ اللهِ على العِبَادِ؟))
قال مُعاذٌ: اللهُ ورسولُه أعلمُ.
قال: ((حقُّ اللهِ على العبادِ أن يَعْبدوه ولا يُشرِكوا به شيئًا))
ثم قال له: ((يا مُعاذُ، أتدري ما حقُّ العبادِ على اللهِ إذا فعلوا ذلكَ؟))
قال معاذٌ: اللهُ ورسولُه أعلمُ.
قال: ((حقُّ العبادِ على اللهِ إذا فعلوا ذلك أن لا يُعَذِّبَهم)). متفق عليه.
فإذا شَهِدَ العبدُ أن لا إله إلا اللهُ؛ فقد شَهِدَ ببُطلانِ ما يُعْبَدُ من دونِ اللهِ عز وجل، وشَهِدَ على نفسِه أن لا يَعْبُدَ إلا اللهَ عز وجل مُخْلِصًا له الدينَ.
وهذا هو الإسلامُ الذي أمَرَ اللهُ به، قال اللهُ تعالى: ﴿قُلْ إِنِّي نُهِيتُ أَنْ أَعْبُدَ الَّذِينَ تَدْعُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ لَمَّا جَاءَنِيَ الْبَيِّنَاتُ مِنْ رَبِّي وَأُمِرْتُ أَنْ أُسْلِمَ لِرَبِّ الْعَالَمِينَ (66)﴾ [غافر: 66].
وقال اللهُ تعالى: ﴿وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ وَذَلِكَ دِينُ الْقَيِّمَةِ﴾ [البينة: 5].
وقال تعالى: ﴿فَادْعُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ﴾ [غافر: 14].
وقال تعالى: ﴿قُلْ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنْ كُنْتُمْ فِي شَكٍّ مِنْ دِينِي فَلَا أَعْبُدُ الَّذِينَ تَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ وَلَكِنْ أَعْبُدُ اللَّهَ الَّذِي يَتَوَفَّاكُمْ وَأُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ (104) وَأَنْ أَقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفًا وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ الْمُشْرِكِينَ (105) وَلَا تَدْعُ مِنْ دُونِ اللَّهِ مَا لَا يَنْفَعُكَ وَلَا يَضُرُّكَ فَإِنْ فَعَلْتَ فَإِنَّكَ إِذًا مِنَ الظَّالِمِينَ (106)﴾ [يونس: 104-106].

الخُلاصة:
• معنَى (لا إله إلا الله ) أي: لا مَعْبودَ بحقٍّ إلا اللهُ.
• لا يَتحقَّقُ التوحيدُ إلا باجتنابِ الشركِ.
• الغايةُ التي خُلِقنا من أجلِها: عبادةُ اللهِ وحدَه لا شريكَ له.
• مَن عَبَد غيرَ اللهِ فهو مُشرِكٌ كافرٌ.
• كلُّ رسولٍ دعا قومَه إلى التوحيدِ واجتنابِ الشِّرْكِ.
• أصْلُ دعوةِ النبيِّ صلى الله عليه وسلم إلى التوحيدِ، فبدأ بدَعْوةِ قومِه إلى التوحيدِ، وأرسَلَ إلى الملوكِ يَدْعُوهم إلى التوحيدِ، وأَمَر أصحابَه أن تكونَ أوَّلُ دعوتِهم إلى التوحيدِ.
• التوحيدُ هو حقُّ اللهِ على العِباد.
• مَن لم يُوحِّد اللهَ فليسَ بمسلمٍ، وإنْ زَعَم أنه مُسْلِمٌ.

طاهر جبريل دكو
_26 _March _2013هـ الموافق 26-03-2013م, 08:38 AM
Ma'anar Kalmar shahada.
Shahadu biyu sune: Shaidawa babu abin bawtawa da gaskiya sai Allah, da shaidawa lallai Annabi Muhammadu Manzon Allah ne.
Kuma sune tushen addinin Musulunci kuma gimshikinsa na farko, wanda dashine bawa ke shiga Addinin Musulunci, saboda haka, duk wanda bai shaida da wadannan shahadu biyuba, to shi ba Musulmi bane
Abdullahi dan Umar (Allah ya kara musu yarda) ya ruwaito daga Annabi (S.A.W) cewa yace:
((بُنِي الإسلامُ على خَمْسٍ: شهادةِ أن لا إله إلا اللهُ وأن مُحمَّدًا رسولُ اللهِ، وإقامِ الصلاةِ، وإيتاءِ الزكاةِ، وحَجِّ البيتِ، وصومِ رمضانَ)). متفق عليه.
Ma'ana: : " An gina musuluncine akan (gimshikai) biyar, shaidawa babu abin bawtawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da aikin hajji, da azumtan watan ramadana." Bukhari da Muslim ne suka ruwaitoshi
Saboda haka, abu nafarko daya wajaba ga bawa ya fara sani acikin addinin Musulunci shine, gimshikinsa na farko, wato ya san ma'anar Kalmar shahada da hukunce hukuncenta.
Kuma Yayinda Annabi (S.A.W) ya aika Mu'azu dan Jabal zuwa Yaman amatsyin mai kira (zuwa ga Allah) kuma malami yace masa:
((إنَّك تأتي قوماً من أهلِ الكتابِ فَادْعُهم إلى شهادةِ أنْ لا إلهَ إِلا الله وَأني رسولُ اللهِ؛ فإِنْ هُمْ أطاعوا لِذلكَ فأَعْلِمْهم أنَّ اللهَ افْتَرضَ عليهم خمسَ صَلَوَاتٍ في كلِّ يومٍ وَليلةٍ)) .. الحديث، رواه مسلم من حديث ابن عباس.
Ma'ana: "Lallai zaka tafine zuwaga wasu jama'a daga ma'abuta littafi, saboda haka kafarada kiransu zuwaga shaidawa babu abin bawtawa da gaskiya sai Allah, kuma lallai ni (Muhammadu) manzon Allah ne, idan sukayi biyayya akan haka, sai ka sanardasu cewa Allah ya farlanta salloli biyar akansu cikin kowane yini da dare…" zuwa karshen hadisin. Imamu Muslimne ya ruwaitoshi daga hadisin Abdullahi dan Abbas
Hakananma Imamul Bukhari ya ruwaito shi da lafazin;
((فليكن أوَّلَ ما تدْعوهم إلى أن يوحِّدوا اللهَ))
Ma'ana:" Abu na farko da zaka kirasu zuwa gareshi ya kasance shine su kadaita Allah (wato, tawhidi)
Kuma bayanin wannan ya zo acikin hadisin (da akafi sani da hadisin) Jibril mai tsayinnan wanda (Jibrilu) ya tambayi Annabi (S.A.W) gameda martabobin addinin Musulunci, Imani, Musulunci da Ihisani, sannan sai Annabi (S.A.W) yace wa sahabbansa- kamar yadda yazo akarshen hadisin:
(( هذا جِبْريلُ أتاكم يُعلِّمُكم دِينَكُم )).
Ma'ana: "Wannan Jibirilune ya taho gareku don ya karantar daku addininku".
Saboda haka, abubuwa nafarko dasuka wajaba asani cikin al'amuran addini, suine abubuwanda hadisin Jibrilu yake kunshe dasu, kuma martaba tafarko daga martabobin addini, itace martabar Musulunci, a musulunci kuwa rukuni na farko daga cikin rukunnansa shine shaidawa babu abin bawtawa da gaskiya sai Allah kuma lallai Annabi Muhammadu manzon Allahne.

Darasi nadaya: Ma'anar Shahaadatu allaa'ilaaha- illa-llaahu.
Laa'ilaaha- illa-llahu tana nufin, babu abin bawtawa dagaskiya sai Allah.
Kuma (Kalmar) Al'ilaahu, wacce take daidai da Alma'aluhu ma'anarta shine; abin bawta.
Saboda haka duk abinda ake bawtawa koma bayan Allah, to wannan bawta batacciyace, duk kuma wanda yabawtawa wanin Allah to ya zama mushiriki kuma kafiri. Kamr yadda Allah (madawkakin sarki) Yace:
﴿وَمَنْ يَدْعُ مَعَ اللَّهِ إِلَهًا آخَرَ لَا بُرْهَانَ لَهُ بِهِ فَإِنَّمَا حِسَابُهُ عِنْدَ رَبِّهِ إِنَّهُ لَا يُفْلِحُ الْكَافِرُونَ﴾ [المؤمنون: ١١٧].
Ma'ana: "Kuma duk wanda ya kirayi wani abin bawta nadaban tareda Allah, to bashida wata hujja game da shi (wannan shirkan)
kuma hisabinsa kawai yanaga Allahne, lallai (yadda al'amarin yake shine); kafirai basa rabawta". Q23: ayata 117.
Saboda haka, baya halatta a hada Allah da wani acikin bawta, koda kuwa (wanda za'a bawtawa) Annbineshi kuma manzo, ko kuma Mala'ikine makusanci (ga Allah), ko kuma wani daga cikin waliyyai salihai, ko wata bishiya, ko wani dutse da makamantan haka, domin bawta hakkin Allahne Shi kadai, kuma dominta Ya haliccemu kamar yadda Ya fadi (Madawkakin sarki):
﴿وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ (56)﴾ [الذاريات: ٥٦].
Ma'ana: "Kuma ban halicci Aljannu da Mutaneba saidon su bawtamini". Q51: ayata56.
:Kuma Allah (Madawkakin sarki) Yace
﴿قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ﴾ [الإخلاص: ١].
Ma'ana: "Kace (Ya Muhammadu) Shine Allah Shikadai". Q112:ayata1.
: Kuma Yace
﴿وَإِلَهُكُمْ إِلَهٌ وَاحِدٌ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ الرَّحْمَنُ الرَّحِيم (163)﴾ [البقرة: ١٦٣].
Ma'ana: "Kuma abin bawtanku, abin bawtane guda daya, babu wani abin bawtawa dagaskiya sai Shi, Shine mai Rahama mai Jinkai". Q2: ayata163.
: Kuma Yace
﴿هُوَ الْحَيُّ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ فَادْعُوهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ﴾ [غافر: ٦٥].
Ma'ana: "Shine (Allah) Rayayye, babu abin bawta da gaskiya sai Shi, ku kirayeShi alhali kuna masu tsarkake addini gareShi". Q40: ayata65.
Kuma wannan shine ma'anan tawhidi, wato kadaita Allah da bawta, saboda haka, kada muyi bawta saiga Allah Shi kadai babu abokin tarayya gareShi. Kuma dawannan tawhidin wanada shine ma'anan Laa'ilaaha- illa-llaahu Allah ya aiko dukkanin Manzanni. Allah (madaukakin sarki) Yace:
﴿وَمَا أَرْسَلْنَا مِنْ قَبْلِكَ مِنْ رَسُولٍ إِلَّا نُوحِي إِلَيْهِ أَنَّهُ لَا إِلهَ إِلَّا أَنَا فَاعْبُدُونِ (25)﴾ [الأنبياء: ٢٥].
Ma'ana: "Kuma baMu aiko wani Manzoba gabaninka face Munyi wahayi zuwa gareshi (cewa) lallai (yadda al'amarin yake shine), babu wani abin bawtawa da gaskiya sai Ni (Allah), saboda haka ku bawtamiNi". Q21: ayata25.
: Kuma Yace
﴿وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَسُولًا أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوتَ﴾ [النحل: ٣٦].
Ma'ana: "Kuma hakika Mun aika manzo cikin kowace al'umma (yana cewa); ku bawtawa Allah (Shi kadai) kuma ku nisanci dagutu (wato duk ababen bawta na karya)". Q16ayata 36.
Kuma hakika Allah Ya kissanta mana –acikin littafinSa mai karimci- labarum manzanni tareda jama'unsu, kuma Ya bayyana mana cewa lallai farkon da'awar manzanni ta kasancene zuwaga kadaita Allah (mai girma da dawkaka), kuma ya bayyana mana (kaykkyawar) karshe na Muminai da suk amsa kiran Manzanni, da kuma (mummunan) karshe na wadanda suka karyata manzanni kuma suka sanyawa Allah abokin tarayya (wato sukayi shirka) abinda Bai sawkarda wani dalili ba game dashi. Allah (madawkakin sarki) Yace:
﴿لَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَى قَوْمِهِ فَقَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ مَا لَكُمْ مِنْ إِلَهٍ غَيْرُهُ إِنِّي أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ (59)﴾ [الأعراف: ٥٩].
Ma'ana: "Kuma hakika Mun aika Nuhu zuwaga jama'arsa, sai yace: Yaku jama'ata, ku bawtawa Allah (Shi kadai) bakuda wani abin bawta koma bayanSa. Lallaine ni ina jiye muku tsoron azabar wani yini mai girma". Q7: ayata59. Kuma Yace:
﴿وَإِلَى عَادٍ أَخَاهُمْ هُودًا قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ مَا لَكُمْ مِنْ إِلَهٍ غَيْرُهُ أَفَلَا تَتَّقُونَ(65)﴾ [الأعراف: ٦٥].
Ma'ana: "Kuma zuwaga Adawa (Mun aika musu) dan'uwansu Hudu, sai yace: Yaku jama'ata, ku bawtawa Allah (shi kadai) bakuda wani abin bawta koma bayanSa. Shin bazaku yi takawaba? (wato jin tsoron Allah ta hanyan kiyaye dokokinSa) ". Q7: ayata65. Kuma Yace:
﴿وَإِلَى ثَمُودَ أَخَاهُمْ صَالِحًا قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ مَا لَكُمْ مِنْ إِلَهٍ غَيْرُهُ﴾ [الأعراف: ٧٣].
Ma'ana: "Kuma zuwaga Samudawa (Mun aika musu) dan'uwansu Salihu, sai yace: Yaku jama'ata, ku bawtawa Allah (shi kadai) bakuda wani abin bawta koma bayanSa" Q7ayata73. Kuma Yace:
﴿وَإِلَى مَدْيَنَ أَخَاهُمْ شُعَيْبًا قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ مَا لَكُمْ مِنْ إِلَهٍ غَيْرُهُ﴾ [الأعراف: ٨٥].
Ma'ana: "Kuma zuwaga mutanen Madayana (Mun aika musu) dan'uwansu Shu'aibu, sai yace: Yaku jama'ata, ku bawtawa Allah (shi kadai) bakuda wani abin bawta koma bayanSa ". Q7: ayata85. Kuma Yace:
﴿وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ إِنَّنِي بَرَاءٌ مِمَّا تَعْبُدُونَ (26) إِلَّا الَّذِي فَطَرَنِي فَإِنَّهُ سَيَهْدِينِ (27)﴾ [الزخرف: ٢٦-٢٧].
Ma'ana: "Kuma ambata (musu ya Muhammad) yayinda Ibrahim yacewa mahaifinsa da jama'arsa; lallai ni mai barrantane daga abinda kuke bawtawa. Saidai wannan daYa kirkiri halittata, tofa Shine dasannu zai shiryar dani". Q43: ayata26 data27. Kuma Yace:
﴿أَمْ كُنْتُمْ شُهَدَاءَ إِذْ حَضَرَ يَعْقُوبَ الْمَوْتُ إِذْ قَالَ لِبَنِيهِ مَا تَعْبُدُونَ مِنْ بَعْدِي قَالُوا نَعْبُدُ إِلَهَكَ وَإِلَهَ آبَائِكَ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَاعِيلَ وَإِسْحَاقَ إِلَهًا وَاحِدًا وَنَحْنُ لَهُ مُسْلِمُونَ﴾ [البقرة: ١٣٣].
Ma'ana: "Shin! Ko kun kasance halartattune ayayinda mutuwa za halarto ga Yakuba? yayinda yacewa yayansa; me zaku bawtawa abayana? Sai sukace; zamu bawtawa Abin bawtawanka Kuma bin bawtawan iyayenka Ibrahima da Isma'ila da Is'haka abin bawtawa guda daya, kuma mu agareShi muke mika wuya". Q2: ayata133. Kuma (Annabi) Yusufu (amincin Allah ya tabbata agaresh), Yace: (wato ga abokan zamansa acikin kurkuku)
﴿أَأَرْبَابٌ مُتَفَرِّقُونَ خَيْرٌ أَمِ اللَّهُ الْوَاحِدُ الْقَهَّارُ (39)﴾ [يوسف: 39].
Ma'ana: "Shin! Ababen bawta mabanbanta sune sukafi alkhairi koko Allah daya Mai tankwasawa?"
Kuma hakannan da'awar Annabi tsira da amincin Allah sun tabbata agareshi- zuwaga dukkan Talikai- takasance, (wato zuwaga tawhidi) kamar yadda Allah madawkakin sarki) Yace:)
﴿وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِلْعَالَمِينَ (107) قُلْ إِنَّمَا يُوحَى إِلَيَّ أَنَّمَا إِلَهُكُمْ إِلَهٌ وَاحِدٌ فَهَلْ أَنْتُمْ مُسْلِمُونَ (108)﴾ [الأنبياء: ١٠٧-١٠٨].
Ma'ana: "Kuma baMu aikokaba face (don kazama) Rahama ga (dukkan) Talikai (107). Kace musu; kawai wahayi akeyimini cewa lallai abin bawtanku, abin bawtane guda daya, shin ku masu mika wuyane? (108)" Q23: ayata 107 data108.
Kuma hakika Annabi (S.A.W) ya farada kiran mutanensa a Makka zuwaga tawhidi (kadaita Allah) sai ya kirasu zuwaga furta (Laa'ilaaha-illa-llahu) da nisantan bawtan gumaka, amma sai mafi yawansu sukayi girman kai sukaki su amsa kiran (Annabi (SAW)) zuwaga kalmar tawhidi, saboda haka sai suka kasance kamar yadda Allah madawkakin sarki ya fadi:
﴿إِنَّهُمْ كَانُوا إِذَا قِيلَ لَهُمْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ يَسْتَكْبِرُونَ (35) وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُو آلِهَتِنَا لِشَاعِرٍ مَجْنُونٍ (36)﴾ [الصافات: ٣٥–٣6].
Ma'ana: "Lallaine, su sun kasance idan akace musu babu abin bawtawa da gaskiya sai Allah, sai su dawra girman kai (35) Kuma surika cewa; yanzu mu masu barin ababen bawtanmune saboda wani mawaki mahawkaci? (36)" Q37:ayata 35data36.
Sai Allah ya mayar musu da martini da fadinsa.
﴿بَلْ جَاءَ بِالْحَقِّ وَصَدَّقَ الْمُرْسَلِينَ (37)﴾ [الصافات: ٣7].
Ma'na: "A'a, yazo musune da gaskiya, kuma ya gaskata Manzanni. Q37: ayata37.
Saboda haka Kalmar tawhidi itce kalma ta gaskiya wacce dukkanin Manzanni sukayi kira zuwa gareta gabanin zuwan Annabi (S.A.W), kuma itace da'awar Annabi (SAW)
Hakika kafiran kuraishawa sun fahimci cewa lallai kira zuwaga tawhidi yana nufin barin bawtawa dukkanin ababen bawta koma bayan Allah madawkakin sarki, don haka (sunsan cewa) tawhidi baya tabbata face tareda nisantan shirka, wannan kuwa shine ma'anan (Laa'ilaaha-illa-llahu).
An ruwaito daga Umar dan khaddabi (Allah ya kara masa yarda) yana cewa; lallai ma'aikin Allah (S.A.W) yace:
((أُمِرْتُ أن أُقاتِلَ الناسَ حتى يقولوا: (لا إلهَ إلا اللهُ) فمَن قال: (لا إلهَ إلا اللهُ) عَصَم مِنِّي مالَه ونَفْسَه إلا بحَقِّه، وحسابُه على اللهِ))متفق عليه.
Ma'ana:" An umarceni da inyaki mutane harsai sun furta (Kalmar) Laa'ilaaha-illa-llahu, duk wanda ya furta Laa'ilaaha-illa-llahu, yakare dukiyarsa da rayuwarsa daga gareni saidai da hakkin Musulunci hisabinsa kuwa yanaga Allah." Bukhari da Muslim.
Kuma yayin da Annabi (S.A.W) ya aikada wasiku zuwaga sarakuna (yana kiransu zuwaga Allah) ya farane da kiransu zuwaga tawhidi (kadaita Allah) mai girma da dawkaka.
Daga Abdullahi dan Abbas ( Allah ya kara musu yarda) yace:"Lallai Annabi (S.A.W) Ya aika zuwaga Hirakla sarkin Rum (yana cewa):
((بسم الله الرحمن الرحيم، من مُحمَّدٍ رسولِ اللهِ إلى هِرَقْلَ عَظيمِ الرُّومِ، سَلامٌ على مَن اتَّبَعَ الهُدَى أمَّا بعدُ:
فإنِّي أدعوكَ بدِعايةِ الإسلامِ، أَسْلِمْ تَسْلَمْ، وأَسْلِمْ يُؤْتِكَ اللهُ أجْرَك مَرَّتين، فإن تَوَلَّيْتَ فإنَّ عليكَ إِثْمَ الأَرِيسِيِّينَ، و﴿يَا أَهْلَ الْكِتَابِ تَعَالَوْا إِلَى كَلِمَةٍ سَوَاءٍ بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ أَلَّا نَعْبُدَ إِلَّا اللَّهَ وَلَا نُشْرِكَ بِهِ شَيْئًا وَلَا يَتَّخِذَ بَعْضُنَا بَعْضًا أَرْبَابًا مِنْ دُونِ اللَّهِ فَإِنْ تَوَلَّوْا فَقُولُوا اشْهَدُوا بِأَنَّا مُسْلِمُونَ﴾ [آل عمران: ٦٤])). متفق عليه.
Ma'ana: "Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai. Daga Muhammadu Manzon Allah, zuwaga Hirakla maigirma (cikin) Rumawa, aminci ya tabbata ga wanda yabi shiriya, bayan haka, lallai ni ina kiranka da kira ta Musulunci, ka mika wuya (ka karbi musulunci)
saika aminta, kuma kamika wuya sai Allah Ya baka ladnka ninki biyu, inkuma ka juya baya (kaki ka mika wuya) to (kasani cewa) zunubban Arisiyyawa na kanka. " Yaku ma'abuta littafi, ku taho zuwaga (wata) kalma da take daidai atsakaninmu, cewa kada mu bawtawa kowa sai Allah, kuma kada mu hadashi dawni abokin tarayya, kuma kada sashinmu suriki sashi ababen bawta koma bayan Allah. Idan suka juya baya (sukaki imani), to ku (Musulmai) kuce; kushaida cewa mudai mun mika wuya. Q3 ayata64". Bukhari da Mualim.
Kuma Annabi (S.A.W) ya aika da kwatankwacin wannan wasikar zuwaga Kisra sarkin Farisa da Mukawkis sarkin Kibdawa, da sarkin Habasha, da Jaifar da iyadh yayan Juladay a(kasar) Umman, da Hudhata dan Aliyu a(kasar) Yamama, da Mundhir dan Saway a(garin) Hajar da Ibnu Abi Shamir mutumin Ghassana, wadannan sune sarakuna a zamanin Annabi (S.A.W).
Kuma yazo a cikin sahihu Muslim daga hadisin Anas dan Malik (Allah Ya kara masa yarda) (yana cewa) lallai Annabi (S.A.W) ya rubuta (wasika) zuwaga dukkan Jabbari (wato mai mulki) yana kiransa zuwaga Allah madawkakin sarki.
Daga Abdullahi dan Abbas (Allah Ya kara musu yarda) (yana cewa) lallai Annabi (S.A.W) yayinda ya aika Mu'adhu dan Jabal zuwa Yaman yace masa:
((إنَّك تَقْدَمُ على قَوْمٍ من أهلِ الكتابِ، فَلْيَكُنْ أَوَّلَ ما تدعوهم إلى أن يُوحِّدوا اللهَ)).
Ma'ana:" Lallai kai zaka tafine zuwaga wasu mutane daga ma'abuta littafi, abuna farko da zaka kirasu zuwa gareshi ya kasance (zuwaga) su kadaita Allah".
Saboda haka kadaita Allah madwkakin sarki (wato tawhidi), shine mabudin shiga Musulunci, idan babushi mutum bazai zama Musulmiba, kuma idan bawa ya aikata wani abu dake warware wannan tawhidin, to ya zama kafiri mushriki, fitacce daga addinin Musulunci.
Daga Mu'azu dan Jabal (Allah Ya kara masa yarda) (yace) lallai Annabi (S.A.W) yace dashi:
((يا مُعاذُ، أتدري ما حَقُّ اللهِ على العِبَادِ؟))
Ma'ana: "Ya kai Mu'azu, kasan menene hakkin Allah akan bayi? Sai Mu'azu yace:
اللهُ ورسولُه أعلمُ
"Allah da ma'ikinsa su sukafi sani.
Sai Annabi (S.A.W) yace:
((حقُّ اللهِ على العبادِ أن يَعْبدوه ولا يُشرِكوا به شيئًا))
"Hakkin Allah akan bayi shine su bawta maSa Shi kadai kada suyi maSa tarayya da komai (cikin bawta). Sannan sai (Annabi S.A.W) yace mishi:
((يا مُعاذُ، أتدري ما حقُّ العبادِ على اللهِ إذا فعلوا ذلكَ؟))
"Ya kai Mu'azu, kasan menene hakkin bayi akan Allah idan suka aikata haka (wato suka kadaitashi?)
Sai Mu'azu (Allah Ya kara masa yarda) yace:
: اللهُ ورسولُه أعلمُ.

"Allah da ma'ikinsa su sukafi sani. Sai (Annabi S.A.W yace):

((حقُّ العبادِ على اللهِ إذا فعلوا ذلك أن لا يُعَذِّبَهم)). متفق عليه.

"Hakkin bayi akan Allah idan suka aikata haka shine bazai azabtardasuba". Bukhari da Muslim ne suka ruwaitoshi.
Idan bawa ya shaida cewa babu abin bawtawa da gaskiya sai Allah, to hakika ya shaida (ne) da bacin dukkanin abubuwanda ake bawtawa koma bayan Allah (Madawkakin sarki) kuma ya shaidawa kansa cewa bazaiyi bawtaba face ga Allah (Madawkakin sarki) yana mai tsarkake addini gareshi.
Kuma wannan shine Musuluncinda Allah Ya yarda dashi. Allah (Madawkakin sarki) Yace:
﴿قُلْ إِنِّي نُهِيتُ أَنْ أَعْبُدَ الَّذِينَ تَدْعُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ لَمَّا جَاءَنِيَ الْبَيِّنَاتُ مِنْ رَبِّي وَأُمِرْتُ أَنْ أُسْلِمَ لِرَبِّ الْعَالَمِينَ (66)﴾ [غافر: ٦٦].
Ma'ana: "Kace (musu ya Muhammad) lallai Ni an hanani in bawtawa wadannan da kuke kira koma bayan Allah yayin da hujjoji suka zomin daga Ubangijina kuma an umarceni da (cewa) in mika wuya ga Ubangijin Talikai". Q40: ayata66. Kuma Allah (Madawkakin sarki) Yace:
﴿وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ وَذَلِكَ دِينُ الْقَيِّمَةِ﴾ [البينة: ٥].
Ma'ana:"Kuma ba'a umarcesuba (Ahalul kitabi) face su bawtawa Allah suna masu tsarkake Addini gareShi masu karkata daga karya zuwa gaskiya su kuma tsaida salla su bada zakka, kuma wannan shine Addinin wadanda suke kan hanyar kwarai". Q98: ayata5.
: Allah (Madawkakin sarki) Yace
﴿فَادْعُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ﴾ [غافر: ١٤].
Ma'ana: "Ku bawtawa Allah (alhali) kuna masu tarkake Addini gareShi ko da kafirai sunki". Q40: ayata14. Allah (Madawkakin sarki) Yace:
﴿قُلْ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنْ كُنْتُمْ فِي شَكٍّ مِنْ دِينِي فَلَا أَعْبُدُ الَّذِينَ تَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ وَلَكِنْ أَعْبُدُ اللَّهَ الَّذِي يَتَوَفَّاكُمْ وَأُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ (104) وَأَنْ أَقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفًا وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ الْمُشْرِكِينَ (105) وَلَا تَدْعُ مِنْ دُونِ اللَّهِ مَا لَا يَنْفَعُكَ وَلَا يَضُرُّكَ فَإِنْ فَعَلْتَ فَإِنَّكَ إِذًا مِنَ الظَّالِمِينَ (106)﴾ [يونس: ١٠٤-١٠٦].
Ma'ana: "Kace dasu (Ya Muhammad):"Yak u Mutane in har kun kasance cikin shakka gameda addinina, to (fa kusani cewa) ni bazan bawtawa wadanda kuke bawtawa koma bayan Allah ba, saidai (ni) zan bawtawa Allan da yake dawkan rayukanku, kuma ni an umurcenine da in kasance cikin Muminai (104) Kuma (an umurceni da cewa) ka tsaida fuskarka ga Addinin (Musulunci) kana mai karkata daga addinin karya zuwa addinin gaskiya, kuma kada kazama daga cikin masu yin shirka(105) Kuma kada ka kirayi (wani) koma bayan Allah abinda bazai (iya) amfanarkaba kuma bazai (iya) cutardakaiba. Inko ka aikata haka, to lallai da ka kasance daga cikin azzalumai (106). Q10: ayata14-16.

Khulasa:
Ma'anar (Laa'ilaaha –illa- llahu) wato babu abin bawtawa da gaskiya sai Allah.
Tawhidi baya tabbata tawhidi (na gaskiya) har saida nisantan shirka.
Manufar halittarmu itace bawtar Allah shi kadai batareda (sanya mishi) abokin tarayyaba.
Duk wanda ya bawtawa wani koma bayan Allah to shi mushrikine (kuma) kafirine.
Kowane Annabi (daga Annabawan Allah) ya kirayi jama'rsa zuwaga tawhidi da nisantan shirka.
Tushen da'war Annabi (S.A.W) shine tawhidi, ya fara kiran mutanensane zuwaga tawhidi kuma ya aika zuwaga sarakuna yana kiransu zuwaga tawhidi hakanan ya umarci sahabbansa da cewa abu na farko a da'awarsu ya kasance tawhidi.
Tawhidi shine hakkin Allah akan bayi.
Wanda duk bai kadaita Allah ba, to ba Musulmi bane koda kuwa yana riya cewa shi Musulmine.

عبد الله الداخل
_14 _August _2013هـ الموافق 14-08-2013م, 11:03 PM
http://www.youtube.com/watch?v=GEd9b51vSgk